Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 40

Sponsored Links

Wani mugun kallo ya watsama Faridan batare daya damu da maganan mutanen wajen ba ya juya zai tafi, kafarshi Islam ta rike gam gam tareda daura fuskarta akan gwuiwar shi tafashe da mugun kuku harda shesheka tace “bakace kana sona ba, inhar kanasona son gaskiya, so sabida Allah to ka yarda ka auri Farida, dan girman Allah do it for me” fincike kafarshi yayi yakara juyawa zai tafi da sauri tabishi da gwuiwa ta kama kafarshi again gam sanan ta dago kai ta kallai suka hada ido, ahankali ta saki kafarshi tahada hannayenta tace “inhar kanasona da gaske, ka aure ta karta kashe kanta, yar uwata ce bazan taba yafema kaina ba idan wani abu yasa metaba, dan darajan Allah am begging you” yanda take kuka tana rokanshi yasa ya tsugunna ya dagota sama kallon cikin idonta yay yace “stop crying” ahankali ta tsayar da kukan tana kallon fuskarshi yace “abinda kikeso kenan na auri Farida?” Ya tambayeta “jama’a zataci shinkafar fa” da sauri Islam ta juya ganin Farida na kokarin kai shinkafar bakinta ta daga hannu tace “stop, stop Faree ya yarda, zai aureki” kallon ta Farida tayi sanan ta kalli Khaleel din tana goge hawaye, Islam ta kallai tace “please tell her ka yarda” yadade yana kallon fuskar Islam din kafin ahankali ya juyo ya kalli Faridan da kyar ya iya cewa “yea na yarda I will marry u” murmushi Islam tayi tana goge hawayen dataji ya zubo mata, Farida takara goge hawayen dasuka ki dena zuba tace “and kayarda dazaran na sakko zamuje gida direct ku fadama Abba kun yarda” yadade yana kallon fuskar ta sanan yace “yea, now come down” yasa hannu ya danne mata ladder, murmushi Farida tayi ta kabar da shinkafar rice din dake hanunnata tafara sakkowa saida ta sakko kasa ta fada jikinshi ta rungumeshi tana kuka sosai tace “I love you so much Mk, wlh Ina mugun sonka, Allah ya jarabceni da sonka, I love you my superman” ihu mutanen wajen sukeyi suna tafi da sauri Islam ta sanya hijabin ta tarufe fuskarta jin kuka yazo mata sosai, da sauri ta juya zatabar wajen karaf taji anrike hanunta hakan yasa ta dago da rinannun idanunta taga Khaleel ne wanda Farida ta shige jikinshi tana kuka yana kallon kwayar idonta, fizge hanunta tayi da gudu tabar wajen tai bakin titi Keke napep ta tare ta shiga ciki tacemai suje sosai take kuka mai Keke na tambayan ta lpy.

Cireta daga jikinshi yayi batare daya kalli fuskarta ba yace “mutafi” yana gaba tana biye dashi suka karasa har wajen motar ya shiga itama ta bude gaba ta shiga sai murmushi take tana kallon fuskarshi kaman yau tafara ganinshi, kunna motar yayi sukabar wajen, a kofar gida suka ganta zaune akan bencin mai gadi, parking yayi suka fito ta kalli Farida tace “dama kunake jira mutafi wurin Abban” da sauri ta bude gate ta shiga batare data kalleshi shiba Farida ta kallai tace “muje my superman” Atare suka shiga cikin gidan direct falon Abba sukayi suka shiga da sallama, yana zaune tareda Mum dake tayashi arranging some business papers. Daga Abba har Mum din binsu sukai da kallo ganin yanayin idanun yaran nasu.

Gaban Abba Islam taje ta tsugunna ahankali tace “Abba dan Allah kahada Farida da Khaleel aure bada niba please Abba, don’t ask me why amma dan Allah kahada su aure ni banaso” tunda take maganan Khaleel yay folding hanunshi akirji yana kallonta idanunshi sunyi jaa, with so much confusion Abba ya kalleta sanan ya kalli Farida da Khaleel dake tsaye sanan yadawo da kallonshi ga Islam yace “wai meke faruwa ne Ummi, wanan wace irin magana ne kikazomin dashi haka, meke faruwa?” gyara zama Mum tayi tace “Alaji zan fadama” dan shiru tayi tana kallon fuskar Islam sanan ta kalli Alhajin tace “ni dama ban fadamaka bane sabida banason kaga kaman na tsangwami Islam ne, ka tuna fadan da ita da Farida sukayi kwanakin baya, to ashewai Islam ce bayan Farida tagama bata labarin soyayyar ta da Khaleel shine Islam taje ta kwacema Farida dake son Khaleel sosai Khaleel” shiru Abba yayi yana nazarin maganar Mum sanan ya kalli Islam yace “haka abin yake Ummi?” ahankali ta gyada kai ganin yanda Abba ke kallonta yasa tace “am sorry Abba” batare daya kalleta ba yakira Farida, ahankali Farida tazo gabanshi ta tsugunna Abba yace “haka zancen yake?” gyada kai tayi sanan tace “Abba inason Khaleel sosai shine ta kwacemin shi” tafashe da kuka tareda daura kanta akan cinyar Abba, shiru Abba yayi sanan ya kalli Islam ahankali yace “kinason Khaleel ko baki sonshi, tell me the truth?” ahankali ta juya ta kalli Khaleel da ita yake kallo sanan ta kalli Mum data jeho mata wani uban hararan, kallon Abba tayi sanan ta girgiza kai tana kokarin hadiye kukan dake zuwan mata tace “a’a bana sonshi” da sauri Abba yace “dama kinyi hakane dan ki bakan tama yar uwarki rai ko?” da sauri ta girgiza kai, dago kai Abba yayi ya nunama Khaleel kujera, kasa zama yay akujeran ya zauna akasa, ahankali Abba yace “Wakake so cikin su wazaka aura? Banason tauyema kowa hakkin sa, yaran zamanin nan kuncika matsala wlh, ka fadamin gaskiya Khaleel wakake so acikin su wazaka aura?” kallon Islam yayi hadamai hannu tayi sanan ta girgixamai kai tana hawaye da sauri ya dauke kai, ya kalli Farida dake kallonshi kirjinta na bugawa idanunta sun cicciko da hawaye ahankali yace” “Farida” murmushi Abba yayi yace “shikenan Allah Sanya albarka, Allah muku albarka dukan ku saikaje ka sanar da iyayenka” Ahankali yatashi yafita daga dakin, sauka yayi yafita daga gidan ya shiga mota ya daki sit din motar yafi sau dari, wani bakin ciki mara misultuwa yaji yanaji da kyar ya iya tuka kanshi yakai gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button