Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 74

Sponsored Links

Wuraren 8 suka tafi airport din bata wani dau kayaba banda hadadden lace din dake jikinta orange da black shikuma shadda ce ajikinshi fara gizna sai uban kamshi yake, karfe goma da arba’in jirginsu ya sauka a yola driver su daya kira yazo ya dauke su dayake Abba yafadi mai a general hospital suke nan direct yasa driver ya kaisu, parking yayi suka fiffito gabanta sai faduwa yake yanda taga ko kallonta bayayi wani super market ya shiga yayo sayayya dabatasan nameba sanan yadawo yana gaba tana biye dashi abaya har cikin asibitin cardio ward taga sun nufa daki na uku taga yay salama ya shiga tabi bayanshi, Mummy ce kadai adakin da Farida take kwance oxygen manne a hancin ta tana bacci, Mum tabisu da kallo Khaleel yace “ina kwana Mum yamai jiki” daidai nan Islam ta karaso gabanta ahankali tace “ina kwana Mummy yamai jiki” ko kallonta Mum batayi ba saima kallon Khaleel tayi tace “sannu da zuwa Muhammad, Alhamdulillah gatanan dai jiki da sauki” dudda abin ya daki ranshi yanda bata amsa gaisuwan Islam ba sai bai nuna komiba yawuce inda Farida take yaja kujera ya zauna a saitin fuskarta yana kallon fuskar ta tareda ijiye ledar hanunshi agefen ta yay shiru, kasa karasowa wurin gadon tayi sabida yanda Mum ke hararan ta, tashi Mum tayi ta kalli Khaleel tace “ina zuwa Khaleel zanje naduba ko testes dinta are ready nakaima likitan ta” ahankali yace “to mumy saikin dawo” fita daga dakin tayi tareda wanke Islam dawani irin mugun harara, daidai lokacin Farida tafara mutsu mutsu da ido zata tashi da kyar ta iya bude baki tace “Mk, Mummy ku kiramin Mk” kara jan kujeran yayi ya matso kusa da gadon sosai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar ta ahankali yace “Farida na” wani irin dukan zuciyar ta sunan yayi hakan yasa ta dago kai ta kalleshi da sauri, ta wutsiyar ido yake kallon fuskarta hakan yasa yasake cewa “Farida na bude idonki gani nan nazo” ganin tana kokarin bude ido yasa yajuyo fuskar nan kaman bai taba murmushi ba yace “dan bamu wuri” kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta juya tafita daga dakin, bude ido Farida tayi dasukai jajir, dishi dishi take gani amma bai hanata ganshi ba kokarin cire oxygen din take daga hancin ta yataya ta cire wa, ahankali tace “Kaine ko idonane kemin gizo” dan murmushi yayi dan ta mugun bashi tausayi yace “nine” wani irin fashewa tai da kuka tana tari da kyar ta iya cewa “kayafe min dan Allah kadaina fushi dani, nariga na hakura nabar ma Islam kai, banason na mutu kana fushi dani please” takarashe maganan tana tari, hanunshi yay folding a kirji tareda daure fuska yana kallonta yace “fine naji zan hakura zan yafe miki only idan kin yarda zaki warke, forget everything and move on, and I promise zan kula dake like a sister, deal?” gyada mai kai tayi da sauri tana murmushi tace “deal” dan murmushi yamata shima yace “gud” ta wutsiyar ido ya hango Islam na leko su ta window kaman wata munafuka dan kasa hakura tayi ga zuciyar ta sai wani iri take mata, dan murmushin gefen baki yayi ganin ta ya kalli Farida yace “zakici abinci?” da sauri ta gyada mai kai, tashi yayi ya koma ta bayan gado ya dago da gadon ta yanda kanta zaiyi sama kaman ta zauna sanan ya koma, ledan daya shigo dashi ya bude ya dauko pringles ya budemata ya mika mata ta karba ya dauko bottle water ya budemata shima ta karba tasha tanata kallonshi, ahankali ta tsulalle ta tsugunna wajen window tanajin wani irin kuka kuka, zafi zafi, fushi fushi, daci dacin dabatasan ko nameba taji tanaji, gawani irin abu daya tokare mata zuciya, kallon Farida yayi dakeci ahankali tanata kallonshi tana sauke ajiyar zuciya yace “bari naje gida zan dawo anjima” gyada mai kai tayi yafita daga dakin. Fitowan shi data gani yasa ta mike da sauri tabi bayanshi ko kallonta baiyi ba saida yakai wajen motar su sanan ya juyo ya kalleta, shi itama take kallo da idanunta dasuka dan chanza kala zatai magana ya tari numfashin ta yace “basai kinbani ba kiyi zaman ki agidan ku zan aiko miki da takardar ki sabida afara shirye shiryen aurena da Farida” yabude mota ya shiga batare daya jira mezatace ba suka bar hospital din, jingina tayi dawata motar dake wurin jin zata fadi kafin ta tsugunna tana wani irin numfarfashi kaman mai asma, wani irin kukane taji yazo mata wuya ba shiri tafara rera shi.
[7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button