Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 1

Sponsored Links

1…..

Mata ne makil a babban compound din gidan dayasha simenti duk sun sanya anko iri daya, yara da manya sai hayaniya ake anacin shinkafa, wasu nashan pate, wasu nacin tuwon shinkafa da miyan taushe, wasu nacin fried rice da zobo, daga gefe kuma wasu tsofaffi ne daketa rera waka suna buga kwarya, wasu mata na rawa ana shewa ana manna musu kudi, ana guda kana gani kasan gidan biki ne.

Babban gidane mai fadin gaske wanda saika wuce inda ake bikin sanan kabi wata kofa kaje dayar sasan dasuke kira da sasan kaka.
Kasancewar sasan kaka baida girma sosai babu mutane a tsakar gidan, saidai ko ina fess simentin kasa sai kyalli yake tsabagen neatness din wurin saikuma pampoo dayake diddiga da ruwa dil dil dil da alamu duk wanda yay amfani dashi na karshe bai rufe da kyauba, flat daya ne a sasan kaka dake dauke da wani babban fankacecen falo da akalla zai iya daukan mutane hamsin, falon na dauke da wasu irin hadaddun kujeru maroon color, sai ledan daki mai shegen kyau shima maroon, sai wayansu hadaddun kwaryaye da ake jera ajikin bangon dakin, kana ganin dakin kaga dakin tsohuwa. wani magidanci ne ke zaune yasha fararen shadda inda akamai malum malum sai wata tsohuwa wacce akalla zatakai 79 agefenshi taci atampa daketa gyalli kaman an shafa mai ajikinta, an mata rigan kayan buba da zanin data daura akan rigan, sai kafanta da gabaki dayanshi yasha jan lalli tai lallin da akafi sani da dungulmin tsohuwa, farace tsohuwar, gashin idanunta dana giranta sun koma fari sabida tsufa, sai hancinta daketa uban zufa, dudda tsufanta bai hana kamanninta da magidancin dake zaune kusa da ita bayyana ba alamun mahaifiyarshi ce, cikin muryanta na tsofaffi kuma cikeda masifa tace “Sama’ila, Sama’ila, Sama’ila kaga dai sau uku nakiraka ko, wlh to nagaji, kodai ka tsawatar wanan karan, kona tattara yinawa yinawa nabarma gidanka nakoma chan kauye abina, aikin banza kawai” yanda take masifan yasa mutumin data kira da sama’ila ya sassauta murya yace “kiyakuri Umma na” “bawani zancen na yakuri” ta mishi ihu akah tana nunashi da yatsa tace “iskanci Hamida yay yawa kuma uwarta ke daure mata gindi inba hakaba iskokai ne mutane datake jin tsoron taro iyye? Mayune jama’a? Cha nayi duk yan uwane da abokan arziki suka cika gidan, yau bikin yayarta, yayarta fa Sama’ila amma ace tun safe ba’aga yarinya ba tasaci hanya ta sabe tafice, yo kajimin yar bazan yarin…” shiru tayi sabida sallaman da akayi wata kyaykyawan mace mai jiki doguwa tasa hadadden paper lace doguwan riga pitch da akamai stone work, ta shigo dakin fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso ciki ta gaida tsohuwar. “sannu da hutawa Umma” hararanta tsohuwan tayi batare data amsaba hakan yasa matar ta dubi mutumin dake kallonta tace “gani Alhaji ka aiko akirani” cikin fushi yana girgiza kafa yace “ina Hamida?” shiru tadanyi tana kallonshi kafin ta sauke ajiyan zuciya cike da damuwa tace “Alhaji nima bansan inda take ba” “karya takeyi na rantse maka Sama’ila, matar nan makira ce, itake kara lalata Hamida, wlh, wlh Sama’ila kajini na rantse maka na sake rantsewa in bata nemo Hamida ba saina bar gidan nan nakoma kauye abina dama nafi samin kwanciyan hankali achan” takarashe maganan tana uban huci kaman tana filin yaki, kallonta mutumin yayi cike da takaici yace “haba Umma, to kibari nai magana mana, nace kiyakuri babu inda zaki, kiyakuri kinji” kwafa tayi tawani juya ido tana karkada kafa tace “nayi, yi maganan ka” kallon matar yayi datai shiru tana kallonsu, anatse yace “Halimatu ina Hamida taje?” ahankali tace “wlh Alhaji nima bansani ba, bansan inda tayiba, ina fama da jama’an biki ban masan bata gidan ba saida Ihsan tazo ta fadamin” cikin fushi da tsananin takaici yace “to kije koma ina take ki nemota kindaisan Umma tace da ita za’akai yayarta chan legas gidan mijinta ko, na fadamiki kinemota ta dawo gidan nan right away” dan ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi kafin ta girgiza kai kawai cike da takaici ta juya zata fita daga dakin saikuma ta juyo ta kalleshi da idanunta da sundan chanza kala tace “amma Alhaji kasan matsalan yarinyar nan batun yauba ko, batun yau mukasan matsalan Hamida na Agoraphobia ba, batasan mutane, tanada tsoron shiga taro, tun tana yarinya haka take, yanz…” cikin fushi ya katseta ta hanyar cewa “yanzu yarinya ce? Me amfanin ki amatsayinki na mahaifiyanta? Kinga kisan yanda zakiyi kinemo Hamida kindaiga ran Umma abace yake kina kara bata lokaci ne karfe biyar za’a zo daukan Habiba yanzu karfe uku harda kwata” juyawa tayi ahankali tafita daga dakin, da kyar ta iya saita fuskanta ta amsa gaisuwan da mutanen tsakar gida ke mata amatsayin ta na uwar amarya ta wuce ta shiga bangaren su inda falon ma ke cike da jama’a makil, corridor su tayi tabude wani daki ta shiga mace dayace a zaune a dakin tana hada kayan akwatin amarya data ciro kana ganin matar kaga kamaninta da matar data shigo, maida kofar tayi ta rufe ta shigo ta zauna kan gado dabas da sauri tasa hannu tana goge kwallan daya zubo mata, da sauri matar dake hada kaya a akwati ta saki kayan hanunta tazagayo tazo ta gabanta tace “menene kike kuka Maman Ayush?” share idanunta tayi tanadan nishi alamun kuka nacinta tace “Yaya narasa yanda zanyi da Hamida, kullum, kullum dakika sani saita jamin cin mutunci daga wurin Alhaji da Umma, laifinane Yaya? Nina hallice ta? Munanan dake ai inata trying number ta baya shiga, natura yan uwanta duksunje makota kiramin ita ba’a ganta ba, Yaya ya zanyi? Narasa yanda zanyi na chanza Hamida, narasa wace irin yarinya ce, imagine fa Yaya yau bikin yar uwarta ma ta gudu tabar gidan, ni yanzu a ina zan ganta, yaya zanyi da raina?” takarashe maganan cikin daga murya sosai hawaye na gangarowa daga idanunta, da sauri Yayar tata mai suna Yaya Lami wacce take her only sister a duniya ta rungumeta ta daura kanta acikinta tana shafa bayanta tace “ya isa, ya isa dena kukan, bari na gwada kiranta kozai shiga, is okay.”

_Kukkuruku old train station._

Babban train station ne that has been abandoned for years yanzu, ba’a amfani dashi sabida sabon da aka bude, wajen shiru babu mahaluki ko daya sai wani tsoho baba mai gadi dake kwance kan wata yar katifa yakafa babban radio dinshi a kunenshi yaja antenna waje yana sauraran labaran rana.

Zaune take akan dan danddamalin dake kusada railway, tana sanye da bakin hijabi har kasa daya rufe har takalmin kafanta, gefen fuskarta nake hangowa, farace sosai tana sanye da farin eye glasses, gashin idanunta bakin kirin dogaye, lips dinta kananu sunyi pink sosai sun bushe danko mai bata shafa akansu ba, gefenta wani karamin black and white jakane na MK sai wasu duwatsu yan kanana dake gefenta da akalla zasukai guda hamsin, ahankali ta zare hanun damanta dake cikin hanun hijabi data kankame ajikinta ta daura hanun akan duwatsu, farine hanunta sol da dogon yatsun ta sirara inda farcenta ke dauke da jan lalli, ahankali tai picking one stone tana kallon railway ta sauke ajiyan zuciya mai sauti cikin wata irin siriruwan murya nai bala’in dadi tace “Kakan mu!” jefa dutsen tayi akan railway tabi dutsen da kallo harya sauka akasa dutsen ya hargitsa duwatsan wajen ahankali tace “dutsen nan is just like Kakan mu, duk inda take saita hargitsa komi, Kakan mu! Kaman zakaran dawaki ce kukanta ba na alheri bane, Kaka! she’s the definition of Iska ba nauyi gare kiba sai kada itace” wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu ahankali tace “wanan ne Baba, duk inda Kakan mu take yana wurin, baya tsalleke abinda tace, in kana neman sa kanka a bala’i a wurin Abba ka batama Kaka rai, hausawa sunce, Allah ya sauwake wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa” wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu tace “Mama! Mamana! My everything” shiru, ahankali tace “Mama kaman rake take, tanada zaki amma batada tau…” shiru tayi sabida ringing din da wayarta yafara dake cikin jaka.
_🌹IN BANI🌹_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button