Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 19

Sponsored Links

Paid book
MIJIN MALAMA
0811923761621
Sosai Majeederh ke kuka kamar ranta zai fita har da shassheƙa Mami dake tsaye ta riƙe haɓa ta dubi Majeederh ta ce “Yanzu ke kina Ina yaron ya zare sakata ya yi nasa waje” Ta kasa cewa komai sai kuka gabaɗaya hankalinta ya ta shi ta zama kamar ƙaramar yarinya. Mami ta ƙara tafa hannu ta ce “Yaro ne mai shegen karambanin tsiya, ko gidan uwar wa ya sani wanne hannu zai faɗa ohho, ga yadda ƴan mafiya da ƴan kidnaping su ka yi yawa a gari” Majeederh ta ƙara rushewa da kuka ta ce “Little ba zai taɓa buɗe ƙofa ya fita ba, ina yaga tsayin?” Aaliyyah ta ce
“Kuma ko ya iya buɗe Ƙofar ɗakin ki Anti Jeederh ai ba zai iya buɗe ƙofar waje ba” Abbu wanda ya fito da shirin fita Masallaci ya gyara muryar kowa ya shiga hankalinsa kamar sun ga mala’ika ya dube su ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce “Lafiya?” Ruma ce ta ce “Abbu wai Little ne ba a gani ba” Ya yi jim alamar tunani kana ya kalli Majeederh dake fuskarta ta yi jajur a cikin wutar lantarkin dake gidan. “Hawwa’u garin ya ya?” Jikinta na rawa ta ce “Abbu wallahi ban sani ba, tare muka kwanta sai da ya yi bacci na yi, yanzu na farka nayi raka’atul fjr na ga babu shi” Ta goge hawayen fuskarta wasu na sake zubuwa ta ce “Na rufe ƙofa, amma na ganta a buɗe” Ya dubeta sosai yana nufar waje ya ce “Allah ya bayyana shi, akwai ban mmki? Wani ya shigo? Wani ya buɗe masa ƙofar? Ko fita ya yi da kansa?” Ruma ta ɗaga kafaɗa tare da shigewa ɗakin da suke kwana su uku, ita, Raihana, Aaliyyah. “Abbu zan je duba shi?” Da sauri ya ce
“Ina?” Kanta a ƙasa tana shassheƙa ta ce “Waje, maybe yana waje ko police please Abbu”
“…. Bada yawona ba”
Cewar Abbu. Ta marairaice fuska ta ce “Ka tausaya mini, bashi da kowa” Cikin tsawa ya ce “Ki fita daga idanuna Hawwa’u, ke bakya tausayin kan ki sai yaron da baki san waye ba? Kin san wanne kallo ake miki a unguwa? Wasu tunaninsu ɗanki ne kawai kike ɓoyewa, to wahainiyarki ta kiyaye ramata, nan da waje kika fita dalilin neman yaron nan ban yafe ba, ina akan shi kika ƙi zuwa karɓo form wato kin girma kin manta wahalar dana sha akan ki, har ki ka yi growing zuwa yanzu? Idan kika je Misira yanzu kin san irin matsayin da zaki taka? Ni za Hawwa’u ni mahaifinki?” Ya ƙare maganar yana nuna kansa da yardarshi. Majeederh ta zube gaban Abbu akan gwiwoyinta hawayenta ya tsaya zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ta kasa tantance wanne kalar yanayi take ciki. Ta riƙe ƙafafuwan Abbu ta ce”Na tuba Abbu, na tuba na bi Allah na bika Mahaifina ka yafe mini zan zama yadda ka ke so, zan yi karatu zan je matakin da kake buƙata ka yafe mini Abbu don Allah?” Aaliyyah kukan tausayin yayarta Majeederh ya kamata ta durƙoshe a wajan tana kuka sosai. Abbu ya ɗan sassauta murya ya ce “Ki je anjima zan kira ki, amma ki cire maganar yaron nan a ranki” A karon farko a iyakacin rayuwarta da za ta yi wa Abbu magiya ta ce “Abbu please… Little.,”
“This is noises!”
“Ka yi haƙuri” Jikinta duk rawa yake kamar ba babbar ƴar daya haifa ba ta yi cikin ɗakinta. Sosai Raihana ta ji tausayin Anti Jeederh amma babu yadda ta iya, ta ja bakinta ta yi shiru. Mami ma ɗakinta ta yi tana ɗaukan hijabi domin daman da alwala a tare da ita. Aaliyah ta miƙe bayan ta ci kuka ta ƙoshi sosai ta nifi ɗakin Majeederh. A zaune ta sameta bakin gado ta sanya hannunta a tsakanin cinyoyinta tana kaɗawa a hankali kanta sunkuye. Jiki ba ƙwari cikin muryar kuka sosai Aaliyyah ta ce “Anti Jeederh mene haka? Me yake shirin faruwa? Me ya sa sai ke kawai?Anya Abbu shi ne Ubanmu? Wannan abun it’s too much, this is not fair zuciyata ta fara raya mini bashi ne Ubanmu ba ko Uncle…..,” Kau! Majeederh ta ɗauke Aaliyyah da wani kyakkyawan mari har sai da ta yi baya daga tsugunen take. Ta fashe da kuka sosai ta ce “Anti Jeederh ki dakeni son ranki, beat me amma ba zai iya sauya tunanin da zuciyata ta fara wanzar mini da shi ba, na buɗe idanu da soyayyar da kike mini Anti Jeederh, na fahimci kece madadin uwa a gareni ko da baki shaida mini Mami ba ita ta haifemu ba, Innati ta faɗa mini komai, amma kullum kina nuna mini hanzar tsira hanzar da zan kare kai na a matsayina na ɗiya mace, na tashi naga yadda Abbu ke son ki ya fifita ki da kowa, komai Hawwa’u musamman ɓangaren karatu, Anti Jeederh baki da lokacin kan ki kullum karatu kullum karatu, mene nufin Abbu? Imran ya zo neman aurenki ya ce ba aure zai miki yanzu ba, ya yi masa korar kare, yanzu kuma ya amshi kuɗin auren Ruma bayan kece babba kece ya kamata ki fara yin aure kafin ita…” Kuka ya ci ƙarfin Aaliyyah ta ce “Soyayyar kenan? Za a ci karatu ne? Idan bai barki kin yi aure ba yanzu sai yaushe, Anti Jeederh tun kina jss 3 na ji kina faɗawa Yaya Latifa aure kike so, idan ya tilasta miki yin karatu ya hanaki aure shin ya miki adalci? Mufa ƴa ƴa ajjiye ce, amana ce a wajan iyayenmu za a tambaye su yadda suka kula damu, Malaminmu ya faɗa mini duk ɗiya macen da ta ce ayi mata aure bata son karatu mafi alheri shi ne a aurar da ita, domin ita tasan me take ji,mene ya sanya ta ce tana son auren, idan ba a aurar da ita ba komai yana iya faruwa da ita kuma….” Majeederh ta yi saurin toshe bakin Aaliyyah tare da rungume yarinyar a jikinta ta ce “Enough, enough is a enough, ok”
Kukan zuci take wanda ya fi komai cin rai da sanya damuwa da ciwo a zuciya, bata son hawayenta ya zuba gudun ƙarawa Aaliyyah nata kukan da damuwa. Sun jima a haka tana jin Aaliyyah na kuka tana bubbuga bayanta a hankali har ta fara sauke ajjiyar zuciya kafin ta ɗagota tana riƙe fuskarta murmushin dole bayyane a fuskarta ta ce “Stop crying my dear, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, Abbu yana so na, soyayya ce ta sanya ya yi haka, kuma yana da iko kaina, yana ganin kuma karatu ya dace dani ba aure ba, shi ne mahaifinmu our own father, biological father ok ba a taɓa sauya tuwo suna, kuma idan na yi karatu zan samu aiki Abbu zai ji daɗi i most be proud, zai alfahari da ni, zan gyara mana gida, na siya masa mota, na kaisa Makka na buɗe masa wajan aiki ya fita daga halin talaucin da yake ciki” Da sauri Aaliyyah ta ce “Aure fa?”
“Zan yi, idan da rabo” Ganin zata sake magana Majeederh ta haɗe fuska sosai ta ce “Je sallah, kiyiwa Fulani addu’ar samun rahama a kabarinta, kiyiwa Abbu addu’a da su Ruma da Mami” Ta ce “Anti Jeederh ke ma zan miki addu’ar Allah ya kawo miki mijin aure ko gobe ne” Majeederh bata ce komai ba, a ranta tana jin cewa karatu zata aura shine zai zame mata miji da zuri’a. Bayan fitar Aaliyyah kuka taci ta ƙoshi son ranta, kukan ya dace da ita ƙilan hakan zai sanyaya mata zuciyarta daga yadda take ji, idan ta tuna babu Little bata san kuma inda zata same shi ba, bata san wanne hannu zai faɗa ba zai samu kula ko ba zai samu ba sai zuciyarta ta karaya damuwarta ta ƙaro fiye da ko yaushe. Ga Abbu ya yi mata katangar ƙarfe tsakaninta da nemo Little ɗinta. Tunaninta ya tsaya ta rasa me za ta yi, rashin Little tamkar rasa wani gefe ne na rayuwarta. Ganin lokaci na tafiya ya sa ta miƙe tare da shiga banɗaki yau ko wankan da take da asuba domin kiyaye jikinta daga mafarkan da take yi bata samu zarafin yi ba, ta ɗaura alwala tare da shimfiɗa ladduma ta yi sallah raka’a biyu. Ta jima tana addu’a akan Allah ya dawo mata da Little ɗinta abin sonta, abin wasanta, abin hirarta, me ɗauke mata kewa. Ta yi shiru na rashin abin yi har ƙarfe 7 tana zaune kanta ƙasa sai wajan 7:48 bacci ɓaraho ya ɗauketa.
Misalin 11 na safe Hajia dake zaune cikin haɗaɗɗen parlourn gidanta ta yi ado cikin atamfa mai kyau da ɗaukan Idanu (Valisco) fara ce kamar buzayen Niger. Ta dubi agogo dake parlourn ganin lokacin na tafiya ya sanya ta ɗauki wayarta tana ƙoƙarin kiran Aliyu taga Almustapha ya fito, ta ajjiye wayar idanunta akansa tare da duban bayansa har ya iso ya zauna dab da ita ya ce “Good mrng Hajia” Ta dube shi kafin ta ce “Mrng, Zaki fa?” Ya ɗaga kafaɗa ya ce “Tun sallar Subhi rabona da shi” Ta yi shiru “Bai fito bane?” Almustapha ya faɗa yana miƙewa, Hajia ta ce
“Jeka kawo mini Yarona”
“Ya zama dole ai” Tsakanin part ɗin Musty dana zaki ba nisa suna opposite da juna ko wanne ha haɗu kasancewar su masu rufin asiri sosai. Komai na part ɗin zaki light blue ne, looking so Masha Allah. Furniture’s ɗin ƴan Turkiyya sbd yadda suke ɗaukan Idanu. Ganin ƙofar shiga cikin bedroom ɗin a buɗe bayan ta parlournsa dake buɗe ya tura kai ciki, ƙamshin room air-freshener, a hankali Musty ya shiga hannunsa ɗaya yana gyara hular kansa yana faɗin “Autan Hajia bacci har yanzu? U have to wake up” Jin shiru ya sa Musty ƙarasawa har bakin bed ɗin da Zaki ke kwance ya lulluɓe jikinsa bakiɗaya idanunsa rufe numfashinsa na sauka a hankali. Da mamaki Musty ya ce “Zufa?”
Ya duba yaga A.cn ɗakin na working domin har yawa taso yi, ya ɗan bubbuga pillown da kansa yake kai. Slowly a hankali Aliyu-haydar ya shiga buɗe idanunsa wanda su ka yi masa nauyi, ganin sauyin idanun Zakin Hajia musamman da yake cikakken Baushi Nigerian, ya bawa Musty tsoro. Suka kalli juna ya ce “Lafiya kake?”
“In capital letters, FINE”
Aliyu-haydar ya faɗa yana janye jikinsa daga bed ɗin kansa ya yi masa nauyi sbd rashin bacci na kwana biyu, hakan ma jiya ta kasance masa sai daya dawo daga masallaci bacci ya ɗauke shi. Musty ya bisa da kallo musamman yadda yake tafiya kamar bai so sai kawai ya girgiza kansa ya shiga danna waya. Yana zaune har Aliyu ya fito ɗaure da towel cikin sauri ya shirya cikin wani carton ɗin Yadi mai kyau da taushi wando da half ɗin riga sai hannun rigar half dark blue ya haska farar fatarshi. Bai saka hula ba sai sunglasses daya saka ko gyara sumar shi bai ba. Ya nufi waje kai tsaye, Musty ya miƙe yana mita “Ji wulaƙanci na gama gadinka har ka shirya shi ne zaka fita?”
“Waya kake dannawa fa Yaya?” Suna fitowa a jere Hajia ta miƙe tsaye a daidai lokacin Papa ya fito cikin shirin fita office. Ya dubi samarin yaran nashi a tare suka ce
“Mrng Papa”
“Babana, Almustapha, kun makara yau” Almustapha ya ce “Yanzu zan fita” Papa ya juya ga Aliyu-haydar ya ce “Kai fa?” Ya ɓata fuska ya ce “Ina gida” Da mamaki Papa ya ce “Gida? Daga fara aikin?” Nan da nan Aliyu ya nuna Autansa a fili ya marairaice fuska tare da langwaɓewa, Papa murmushi kawai ya yi ya ce “Hajia bari na fita” Hajia ganin yadda idanun yaran nata ya sauka akanta suna jiran su ji me zata ce, ta girgiza ƙafa kawai ta ce “Allah ya tsare ya kiyaye” Papa ya yi jim kamar na jiran wani abu sai kuma ya ce “Amin” A tare suka fice shi da Almustapha kowa ya shiga mota, Almustapha na driving kansa, Papa kuma yana baya Busy reading news paper driver na jansa a haka suka fice. Hajia ta dubi Aliyu ta ce “Auta sai yanzu?” Ya rufe idanu ya ce “Just woke up Hajia”
“Ka yi breakfast?” Ya girgiza kai kawai tare da miƙewa tsaye ya ce “Ki mini addu’a zan fita yanzu zan dawo” Tana lura da yadda yake yawan lumshe idanunsa yana riƙe kai ta ce “Allah ya tsare” Hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗaya riƙe da key ya nufi harabar gidan, motarshi ya shiga yana yi mata key while yana kiran number Latifa Omar. Majeederh na zaune idanunta ya yi zururu sun faɗa fuskar nan jajur karan hancinta ya yi jaa sosai sbd damuwa. Da ƙyar ta cira kai ta kalli Latifa Omar ta ce “To ya zan yi? Mahaifina ne, na haƙura da Little” Latifa Omar ta ce “haka zaki zauna Takaicin Uba na cin zuciyar ki?” Kallon da Majeederh ta yiwa Latifa Omar ya sa ta fahimci bata ji daɗin maganar ba ta ce “Ki yi haƙuri, yanzu kina nufin bakya nan zan yi aure?” Kamar ba za ta yi magana ba ta ce “Aure zaki?” Latifa ta yi dry tana gyara zama ta ce “Aure zan yi In sha Allah, ina wannan wanda ya kaimu gidan Uncle Isma’il da Yaya Bilkisu? To shi ne ya ce yana so na, na ji tsoro ganin shi ne wani ne masu arziƙi kuma ni gani ƴar gidan Malam Shehu, amma ya ce babu komai iyayensa basu da matsala yana da kyawawan hali” Ba zata iya gane yanayin reaction na Majeederh ba kanta a ƙasa yake. “Majeederh kina ji na?” Ta ce “Allah ya sanya albarka” Kafin Latifa Omar ta yi magana wayarta ta fara ƙara ganin wanda yake kira yasa tafiya murmushi hannunta na rawa ta ɗauka ta ce “Hello”
“Is not allowing, Assalamu alaiki” Majeederh ta miƙe zuwa ɗakin Abbu cikin ƙaton hijabi har ƙasa kana kallonta kasan a hargitse take. Ta yi sallama yana zaune hannunsa riƙe da wani file na takardun Majeederh ya ce “Hawwa’u kin fito? Yanzu zan office ɗin zaki?” Ta ɗaga masa kai ya ce “To ya za ayi? Bani da kuɗin mota” A sanyaye ta ce “Ina da shi” Ya miƙa mata file ɗin yana murmushi na nuna jin daɗi ya ce “Allah ya yi miki Albarka, Kinga kina zuwa Misira Shekaru takwas kin gama karatunki, idan da hali kawai ki yi zamanki a can ki fara aiki ance albashinsu akwai auki sosai” Ba zata iya tantance halin da maganar Abbu ya sanya zuciyarta a yanzu ba, kuma ta yi alƙawarin ba zata sake masa ƙorafi ba. Ta miƙe taiwa masa sai ta dawo taiwa Mami ma, Aaliyyah da su Ruma na makaranta. A hankali ta nufi waje kanta a ƙasa ga yunwa domin kafin ta farka har an cinye abinci abincin safen, jiri na ɗaukarta a haka ta yi waje ganin mota a ƙofar gidansu ya sanya ta ɗaga kanta cikin rashin sa a Idanunta ya faɗa cikin nasa suka kafe juna da wani irin kallo….

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button