Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 34

Sponsored Links

Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank….. Kindly send your evidence via 08119237616 Book 1 and 2 1k.

Naso yin typing ɗin ya fi haka yau Sadakar Bakwan rasuwar da akai mini🙏🏿 Mu haɗu weekend a arewabooks.*_Huhuu! To bance komai ba, amma ya kuke yaƙin neman MIJIN MALAMA Don’t you know cewa na kuɗi ne? Mata masu fama da Jinkirin aure wannan littafin sadaukarwa ne a gareku🤓😥….. A daina shelar neman Mijin Malama tunda akwai Mazan da yawa Allah kaɗai yasan waye mijin Madam come and Subscribe before you read, meye wata ƴar 1k da zata muku wahala?…….. Chat me via WhatsApp 08119237616_*

Kasa bata amsa tayi saboda tashin hankali, ganin kowa ya yi shiru ya sa ta ce “Finally, ni ma na zama matar aure Allah na gode maka bisa wannan tarin Ni’imar da kayi mini, na ƙara yadda wani jinkirin alheri ni Anti, gashi yanzu Ubangiji ya bani nagartaccen miji” Majeederh ta yi murmushi tana goge hawayen farin ciki, duk wani zafi da ƙunci ya kau a ranta, tabon dake cinta a zuciya ya hanata sukuni gabaɗaya ta neme shi ta rasa. Aurenta da Yayanta Alpha ya zama abu na farko wanda ba zata taɓa iya mantawa fashi ba.
Anti ta juya ta kalli Aaliyyah da Sona ta ce “We need privacy, ku je waje yanzu zan fito” Aaliyyah ta yi waje, Sona ma ta bi bayanta. Anti ta kalli Majeederh tana murmushi wanda bai kai zuciya ba ta ce “To Amarya” Kunyar Anti ta kamata, ta ɗan yi ƙasa da kanta a hankali Anti kamar kazar da ƙwai ya fashewa ta ce “Ki je ki yi sallah, wanka,cin abinci we need to talk ok” Majeederh ta miƙe tsaye da sauri ta dafe gefen kanta “Sorry kan ne dai?” Anti ta tambaya tana riƙe kan nata, jijiyoyin kan duk sun fito sai har bawa suke idanunta jajir, ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali ta ce
“Abbu ma zai farin ciki ko Anti? Zai yi farin ciki yaga aurena, ni kuma zan aurar da Aaliyyerh” Gabaɗaya Anti tunanin dake sarrafa ƙwaƙwalwarta ne ya tsaya da aiki ta tsaya ta dinga kallon Majeederh da ƙyar ta iya cewa “Ki je ina jiranki Majeederh” Ta nufi bathroom da ƙyar ta yi wanka tare da sallolin dake kanta, Anti ta kawo mata wata atamfa Valisco milk da yafin blue a jiki, ɗinkin duguwar riga Ashap. Majeederh ta dinga kallon kayan domin bata saba saka irin su ba, tina cewa ko wacce amarya irin kayan da take sakawa kenan sai bata ce komai ba, ta shirya tsaf tayi wani irin masifaffen kyau, kamar irin Fulanin Usul ɗin nan ko na Daji ko kuma irin Half-caste ɗin nan jinsan larabawa da yankin Niger na Agadas ko Sudawa. Idanunta zuru-zuru tayi muguwar rama kamar kuɗin guzuri, fuskarta kamar tafin hannu. “Anti na kira number Yaya a kashe fa? Zan yi masa godiya da aurena da ya yi” Anti ta kasa bata amsa ta juya da sauri tare da ficewa daga bathroom ɗin ta nufi part ɗin Uncle Isma’il lokacin yana zaune saman kujera yana waya, tana zuwa ta rushewa Uncle Isma’il da kuka tsabar firgici ya saki wayar hannun sa tare da miƙewa jikinsa na rawa ya ce “Subuhanallah! Ƴar Aljanna ke dawa?” Anti ta dinga kuka jikinta har rawa yake kai kace Uncle Isma’il ne ya rasu, ko kuma an aiko mata da mutuwar mahaifinta daga Gombe.
Cikin kuka ta ce “Mun shiga Uku Yallaɓai, mun shiga uku Abban Jawaad” Uncle Isma’il ya ce “Ba mu shiga uku ba da izinin Allah, Ubangiji na tare damu” Ya saka hannu ya ɗagota yana riƙe fuskarta ya ce “Majeederh ko?” Ta kasa magana sai kuka Uncle Isma’il ya rasa yadda zai rarrashi matar tasa ya kamo ya rungume ya ce “Haba bansan fulani da raguwar zuciya ba, haba jinin Gwambawa haba ƴar Bafullatanar matata uwar ƴaƴana kukanki azaba ne a zuciyata” Ya yi murmushi cikin dauriya ya ce “Akanki bulala nawa na shanye? Gwambawa sun gana mini azaba a haka na shanye shaɗin na aureki, mene ya kawo haka? Kinga juriya ce da yadda da Allah da ƙarfin addu’a, ki zama jaruma kamar yadda na zama jarumi a soyayyarki ki yi haƙuri don Allah uwar Jawaad da Sona, garkuwar Du’a haba matar Isma’il amarya kuma uwar gida, idan baki jure ba ina zaki samu ƙarfin qiwwar rarrashin Majeederh” Ya goge hawayen da suke bin idanunta tana shassheƙa ta ce “Na rasa yadda zan yi babu kalaman ban haƙuri ga Majeederh, wannan yaron ya cucemu he disappointed us” Uncle Isma’il ya ce “Da wannan salon yaudarar taki da kika sace zuciyar Isma’ila da shi zaki rarrasheta, komai na rayuwa yin Allah ne ba namu ba, bama da ikon hana komai ko faruwar shi take heart please” Miƙewa tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta nufi part ɗin da Majeederh take ciki. A zaune ta sameta idanunta rufe ƙirjinta na ɗagawa kamar wacce asthma ɗin ta take shirin tashi, kafin ta ƙarasa ta nufi wajan freezer ruwa ta ɗauka mai sanyi ta tsiyaya a kofi ta ce “Drink”
“Azumi nake” Majeederh ta bata amsa, Anti ta ce “Ai kowa zaki karya azumin me?” Ta yi ƙasa da kai ta ce “Nuna godiya ga Ubangiji” cewarta.
Anti ta nemi waje ta zauna tana bin bedroom ɗin da kallo a hankali ta ce “Hawwa’u!”
“Na’am Anti” Ta amsa gabanta na faɗuwa haka kurum. Anti ta ce “Mece ƙaddara?” Da mamaki Majeederh ta kalli Anti sai kuma ta ce “Jarrabawa ce da Ubangiji yake jarabtar bawansa domin gwada imaninsa, shi ya sa aka ce yarda da ƙaddara shi ne cikin imanin ko wanne musulmi” Anti ta sauke ajjiyar zuciya ta ce
“Allahamdulillah” Wajan ya yi shiru can dai Anti ta ƙara kiran sunan Majeederh a wannan karam kasa amsawa tayi ta ce “Hawwa’u mace da ciki da ciki ta mutu, miji ya rasu ya bar matarsa da yaransa, uwa ta rasu tabar miji da yaranta, iyaye sun rasu sun bar yara, Gabaɗaya hakan tsarin waye? TSARIN ALLAH, Ubangiji ke da ikon ƙaddara kuma shi ne wanda masarrafar rayuwarmu ke hannunsa, ya haliccemu domin bauta masa dayin biyya da iyaye duk mutumin da ya cika haka bazai taɓa tuzarta ba, ƙaddara shuɗaɗɗiyya ce, ba za’a taɓa hana zuciya ƙuntata ba, domin baka da ikon yin haka amma akwai mataki na kare kai, Majeederh ki yarda Allah ke tsara duk abinda zai faru, Mu so wanda ya ke son mu shi ne soyayya, mu so Mutum ya so me shi ne dacewa a soyayya, mun so abu babu damuwa maybe abin ya dace aso shi saboda nagartar da yake da ita, rasa abinda zuciyar mu ke so, bashi yake nufin rasa rayuwarmu ba, watakila rabonmu na ta wani wajan yana jiranmu, idan soyayya na gudunm ƙauna ta har abada tana can wata duniya idanu rufe tana nemanmu, faɗuwa a soyayya nuni na cewa hakan ba alheri bane a ranmu, ba laifi bane don munyi kuka idan an yaudaremu, babbar asara ce ka komawa wanda ya guje ka ko ya yaudareka, hakan na alƙinta mana mun rasa wani abu a baya inma mu rayuwa inma mutum mu rayu da sanin Ubangiji ke zana komai cikin tsaftaccen allon lauhil mahfuz, yi kuka Majeederh akan farin ciki kada ki yi kuka akan baƙin ciki….” Anti ta yi shiru kana a hankali cikin rauni tausayi da fargaba ta ce “Ba a ɗaura aurenki da Alpha ba, domin ya gudu bisa ra’ayinsa na ƙin auren wanda Ubangiji ne kaɗai ya san dalili” Da wani irin Expression Majeederh take kallon Anti, kallon da sai da hantar cikinta ta motsa, gabanta ta faɗi domin bata taɓa ganin rikiɗewar idanu lokaci ɗaya irin na Majeederh ba, ƙarar tsayawar abu a wuyan Majeederh yasa Anti taɓata ta ce “Majeederh ki yi haƙuri ki yi haƙuri, ban san yaushe ne hakan ta faru ba, ban san mene ya sauyawa Alpha ra’ayi ba, amma nasan yana son ki ina ganin hakan acikin idanunsa, rabonki yana wani tsagin rabo mai girma rabon da zai bawa kowa mamaki,ki yi haƙuri da rayuwa Majeederh” Maimakon kuka sai taga Majeederh ta saki Murmushi, murmushi mai kyau wanda bata taɓa ganin irinsa a fuskarta ba, irin wanda dashi gwara kayi kuka irin sa yafi kuka ciwo a zuciya hakan na nufin Mutum yana cikin halin da kuka ya yi masa kaɗan. Ta miƙe tsaye ta ce “Zani gida”
“Majeederh are you okay?” Ta ce “In sha Allah” A hankali ta ce “Kiyi haƙuri ki miƙa lamuranki ga Ubangiji please” Ta ƙara yin murmushi ta ce “Ba komai, bani hijabi da liƙab ɗin Sona” Ba zata iya tsayar da ita ba, akan Idanunta ta saka hijabin da liƙab ɗin tare da amsar kuɗin napep wajan Anti ganin haka yasa Anti ƙwalawa Aaliyyah kira ta ce “Maza jeki ku tafi akwai matsala” Jefa ƙafafuwanta kawai take without knowing ina take takawa, da gudu kuma Aaliyyah ta cimmata ta tsare mai napep ta ce masa Lodge Road….. Misalin 8 na dare wani irin ciwon kai ya kama Majeederh har bata iya gani sosai ga jiri da ƙyar ta miƙe ta nufi part ɗin Abbu da yake kiranta tana zuwa ta zube a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta kasa cewa komai. Ya dubeta ya ce “Kin kyauta”
Da sauri ta kalle shi tana son tambayar mai tayi sai kuma tayi sbd nauyin da harshenta ya yi mata wanda ya tilasta mata kame bakin. Ya gyara zama da kyau ya ce “Kin tuzartani cikin dangi Majeederh,kin kunyatani kin cin mutuncin shekaruna, akan namiji? Yanzu me gari ya waya? Kin barwa kanki abin gori kin bar mini nima koma babu komai tarihi zai kafo akan Alpha ya gudu saboda baya ƙaunar aurenki” Ya girgiza kai ya ce “Majeederh kin yarda ni mahaifin ne?” Da sauri ta ce “Wallahi Abbu ban taɓa kokwanto hakan ba” Ya miƙe tsaye tare da ɗakko Alkur’ani mai girma daman yana da alwala ya ɗora hannunsa akan Alqur’ani izzu sittin ya ce “Wallahi wallahi Allah Majeederh ni ne ubanki mahaifinki, wanda jinina ke yawo a jijiyoyinki, na rantse da Allah ni ne mahaifinki ni Alhaji Abdul’aziz Khan” Ta dinga girgiza kai babu hawaye ko ɗaya a Idanunta ta ce “Don Allah Abbu ka bari” Ya kalleta ya ce “Amma ni ina tunanin kamar an sauya mini ɗiyata, kamar ke ɗin ba Majeederh ta bace”A rikice ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Ya Allah wallahi bana gane komai ko fahimta” Ya zauna ya ce “Kin kasa bani abinda nake so nake buri Majeederh, na rasa yadda zan yi dake kin kasa rufa mini asiri, Hawwa’u aure fa ba dole bane tunda zaki iya riƙe kanki, kuma ni na san jinkiri ne kawai kika mijinki nan zuwa ki taimaka mini, ni mahaifinki ne” Majeederh ta ce “Ka yafe mini, ba sake cewa ina son kowa ba shi na don Yayana ne ai kaga ma bai aurenin ba shikenan sai na fara neman aiki” Abbu ya saki kuka wiwi yana cewa “Faɗa kawai kike Majeederh ki je kawai nama haƙura kiyi aurenki kawai kuma na yafe” A rikice, rikicewar da ko sanda aka faɗa mata Alpha ya gudu ya fasa aurenta ba ta yi ba ta riƙe ƙafar Abbu ta ce
“Nayi asara Abbu, rayuwata ta halaka na shiga uku akaina kake zubar da hawaye mai yasa zaka ja mini azabar Ubangiji Abbu Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Abbu kuka kake a kaina??” Ganin yadda halinta ya tashi ƙarara yasa ya ƙara rushewa da kuka tashin hankali ya bayyana akan Majeederh amma ko ɗison hawaye babu a fuskarta zuciyarta ta ƙafe ta ce “Na tuba, wallahi na tuba gobe zan nemi aiki zan fara nayi maka al’ƙawarin wadataka da abinda kake so iya kacin iyawata, za ka yi alfahari dani Addu’arka da albarka ka nake nema kawai” Ya share waye ya ce “Da gaske zaki aikin?” Ta ce “Na yi alƙawari” Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ce “Kin cika ƴa, na gode ƙwarai Allah ya yi miki Albarka” Ta miƙe da ƙyar zata fita ya ce “Ga mata nan da yawa na garari duka babu aure, shi fa auren nan lokaci ne kiyi ta azumi” A wannan lokacin bata fahimtar komai, dishi dishi take gani ga jiri ga kuma haki da ƙyar ta lalubi hanya ta nufi part ɗin tana ta faɗi wanwarsa a tsakiyar ɗakin babu numfashi….. Bayan kwana bakwai da faruwar komai Latifa na driving fitowar su kenan daga B.u.k sun shiga duba wani ita da Majeederh, ganin ta ɗauke hanya ya sanya Majeederh ɗago kai a hankali tare da zubawa titin idanun sai dai bata ce komai ba, ta maida idanunta ta rufe mamakinta kuma bai shige ganin yadda Latifa take wani Mahaukacin driving ba. A hankali ta ce “Kee” Murmushi kawai Latifa ta yi cikin sauri ta ce “Ina da hankali ba kashe mu zan ba, nasan adadin giyar dana saka ban shige limit ba” Ta juya ta kalli Majeederh suka haɗa idanu ta ɗaga mata gira ta ce
“Afuwa Malamarmu zan shiga Tahir Quest Palace ne” A gajarce Majeederh ta ce “Hotel?” Latifa ta ce “Eh, Abu zan amsa ai” Majeederh ta yi shiru tana tunani me zai sanya ita kowa ta shiga hotel? Ai hakan babban zunubi ne, kayi ta ganin kartin maza ba zata iya wannan mummunan saɓon ba. Bata ce komai suna zuwa gate ɗin shiga Majeederh ta ce “Wait”
“Like how? Kamarya na tsaya?” Ta ya motsa fuska ta cikin liƙab ta ce “Amai nake ji” Jin hakan yasa Latifa tsayawa Majeederh ta fito da ƙafafuwanta daga cikin motar tana fitowa ta ce “Shiga,ki saman nan” Girgiza kai kawai Latifa ta yi taja motar a 150 ta shige cikin Hotel…. Tana tsaye bakin Hotel ɗin ta ji an ce “Malama Majeederh me kike a nan?” Da sauri ta ɗago kanta ganin ɗan unguwarsu yasa tayi saurin jan jikinta baya daidai nan mai napep ya tsaya ta shiga, saurayin ya dinga mamakin ganinta a bakin hotel. Har sama da awa guda Latifa bata fito ba, can sai ga motar ta ganin babu Majeederh ya sanya ta kirata a waya ta ce “Kina ina ne?” A taƙaice ta ce “Gida”
“Gida kuma? Au tafiya ki kai” Ta ce “Kamar uzurinki babba ne, ni kuma ina jina Uncomfortable a wajan” Kafin ta yi magana Majeederh ta kashe wayar. Lokacin da Latifa ta isa gida ta samu Aliyu tsaye a balcony sanye da wata farar singlet sai gajeren wando hannunsa riƙe da coke yana sha, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ƙarasa inda yake tana murmushi ta ce “Sweetheart harka dawo?” Bai ce komai ba. Ta saka hannu ta karɓe coke ɗin hannunsa tana sha ta ce “Am sorry”
“For…?” Aliyu ya tambaya yana zuba mata narkakkun idanunsa. A hankali ta ce “Da daɗewa, na raka Majeederh meeting ne a Tahir Quest Palace” Ya dinga kallonta sai kuma ya ce “Ohk” ta zauna a cinyarsa ta ce “Me kake yi kai ɗaya?” Ya haɗe fuska sosai ya ce “Ɗaga ni” Ta ɗaga shi ya dinga kallonta up to toe kana ya ce “Exlty, tun jiya kayan nan ke jinki kenan baki wanka ba?” Ta yi shiru ya miƙe tsaye tare bi ta gefenta ya shige ciki, yana zuwa ya haura sama not too long ya fito cikin tattausan voyel fari tas sumarsa kwance luf hannunsa zube cikin Aljihu ganinsa haka ta ce “Ina zaka?” Ya dinga kallon parlourn kamar na mahaukata sai warin yawu yake, Aliyu ya rasa me ma zai ce can ya ce “Ki tabbatar kin gyara gidan nan, Hajia na hanya” Yana faɗin hakan ya fice, ya ɗauki good 20 minutes kafin ya shigo yana fitowa daga mota ya nufi cikin gida, yadda yabar parlourn tun jiya haka yake ya ajiye takeaway ɗin hannunsa cikin ɓacin rai ya nufi bedroom ɗinta yana toshe hanci, ganinta ya yi durƙoshe jini na zuba ta ƙasanta a rikice ya nufeta yana faɗin “Wife lafiya badai cikin ne ya sake zubewa ba?” Cikin mawuyacin hali ta ce “Aliyu shikenan yanzu ma mun rasa shi, na rasa babyna Aliyu cikin ya zube” Gabaɗaya Aliyu ya rikice tashi ƙaddarar kenan ya ce “Taya kika san ya zube? Wife kada ki tarwatsa mini zuciya” Da ƙyar ta ce “Wallahi ya zube” Bai magana ba ya sunkuceta zuwa mota, suna zuwa likita ya tabbatar ya zube Aliyu har kuka ya yi domin wannan shi ne karo na uku…. Majeederh na zaune tana shigar da bayananta domin ta samu offer a B.u.k za tana koyarwa, da kuma gidan t.v akan yiwa mata wa’azi musamman da Ramadan ke gabatuwa. Mami ce ta fito fuskarta ɗauke da murmushi ta ce “Yawwa Majeederh shirya yanzu ki je gidan Amani ƴar wajan Hajiya Nusaiberh haihu tayi kuma babu wanda zai zauna mata” Majeederh ta kalli Mami ta ce “Mami kuma ni zan zauna mata? Ina cewa ko Aaliyyah ta girmi yarinuaty? Ina Hajja? Kakar Amani ɗin?” Mami ta ce “Hajja tana Gombe, yayyun Amani kuma duka aure ne da su Kinga ai ba a ce suzo ba suna gidan mazajen su, Su Raihana ma haka, za a Turo Hajja na ce kawai ta zauna ke kyaci tunda kina zaune gida ke ba aure ba, ki je kiyi mata arba’in ɗan wanki da abincinta dana mijinta” Majeederh ta kasa cewa komai ga biyya da take da ita bisa dole ta shirya ta nufi Badalawa…. Daddare Majeederh ta gama abinci tsaf tana zaune a parlour Amani ta ce “Allah sarki ashe Alpha guduwa ya yi wai za a ƙaƙaba masa ke kuma baya so? Haka Raihana ta ce mini, ni dai don Allah ba ruwanki da mijina daya dawo ki shige bedroom kawai haka kurum yadda mata suke kwantai ki aure mini miji na shiga uku” Majeederh dai ta yi shiru Amani ta ce “Kema dai ƙuruciya ke damunki ina ke ina Alpha? Yaran zamani kenan” Majeederh ta miƙe zuciyarta a ƙun ta ce wai ƙanwar ƙanwarta take faɗa mata haka? Maybe ƴar cikinta da auren wuri ta yi…..Majeederh ta fara koyarwa a B.u.k kuɗi take samu sosai ta zama feminist ɗin dole, a cikin shekarar Abbu ya je makka arziƙi ya ci uban nada, tsakanin Majeederh da kuɗi siyan suttura itama ba da yawa ba gudun kada Abbu ya ce ta kashe kuɗin….

After 3yrs*
Lokacin Majeederh nada shekaru 31 cif a duniya a lokacin ta ƙara cin ta ƙara cin gasar Alkur’ani ta duniya, Nigeria ta ƙara ɗaukan award, kuɗin data samu ba zai faɗo ba, wannan karan a Saudiyya akai murmushi kwance a fuskarta ta tarawa Abbu dukiya tana tsaye riƙe da Award idanunta ya sauka akan wani Matashin ko magidanci da yake ta kallonta Without blinking his eyes sai ta ji ta tsargu ta shafa fuskarta ta jita a rufe ta sauke numfashi, tana ƙoƙarin barin hall ɗin musabaƙar ta ji an ce “Tagawa lafiya Meke faruwa?” Ta sauri ta juya idanunta ya sauka akan kyakkyawar fuskarsa sai ya motsata yake kamar yaro ga wata ilhama dake kwance a kanta, ta ƙara ware idanu a ranta ta ce “Ƙhulud’s husband, Ajlaal?” Gabaɗaya fadawa suka rufe shi ruf ganin sai zufa ce ke yanko masa jikinsa na wani irin ɓari “Sannu Tagawa, Allah ya ƙarawa sarki lafiya” A ranta take Mamakin yaushe Ajlaal ya zama sarki? Kuma ta san sarkin Makka ai bai mutu ba, tana tsaye a wajan aka shigar dashi wata ƙaramar mota mai azabar kyau aka nufi Palace da shi. Ta ɗan taɓe baki ta nufi mota zuwa masauki domin a gobe zata koma ƙasarta Nigeria tabar Saudiyya ɗin, Majeederh ta zama kamar namiji sbd jajir cewa ƙoƙari da neman na kai, sai dai ba ruwanta da kowa magana sai ya zame dole ga bala’in ji da take a lokacin kuma gabaɗaya dangi kowa ya shiga yar bata da habaici babu aure sai gantali Anti ce kawai ke bata baki Uncle Isma’il ma ganin laifinta yake aka juya mata baya ko taro ta daina shiga……

Titin Government house cike yake da abun hawa an tara uban go-slow manyan mototci da ƙanana, masu napep da barura hankalin kowa a tashe yake sbd ranar data ƙwalle, an kuma rasa abinda ya haddasa go-slow ɗin… Abbu ya gyara zamansa a bayan mota yana jan tsaki ya ce “Nigeria ba zata sauya ba” Driver ya ce “Wallahi Alhaji kamar faɗa ake a tsakiyar titin ma” Abbu ya ƙara jan tsaki ya ce “Fita if there’s any way sai ka bi” Driver ya fita, cikin sauri yake kutsawa har ya ƙarasu tsakiyar titin. Wata baƙar mota ce lafiyayyiya daka gani ba a jima da siyanta ba, ita ta tare kan titin, sai wasu ƴan matasa wajan su goma tsaye a wajan sun saka wani a tsakiya wanda bakinsa ya fashe jini na zuba, sai a lokacin ya ƙara lura da sauran motocin da sukai blocked hanyar…. “Fouk You” Wani ya furta daga cikin samarin daga shi sai gajeren wando ko riga babu jikinsa kansa babu ko gashi sbd tabbatacce ne shi Ya nuna guy ɗin da suke doka ya ce “Kai dan ubanka sa’an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?” Taj ya saki dariya ya ce.
“You’re just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria, Legas ma babu wanda ya isa damu balle Kano”

“Exlty, We are Nigerians, we will decide, we will say whether it is heard or not, there is no one behind us….. Tell them” John Ya faɗa yana murza gun ɗin hannunsa. Taj ya ƙara sakin dariya ya ce ya ce “Speak louder John, ba wani shege” Joshua ya ce “Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa ƙafar daba da hannun hango a zubar titi” Driver ya zare idanu. A na kana wani police ya zo ya ce “who are you? Waye uban a garin nan? Dalla ku matsa akan titi…..,”
“What if we refuse?heeee?” Gabaɗaya Gang team ɗin suka juya idanunsa ya sauka akan shi, fitowarsa kenan daga cikin mota, Matashin saurayi mai ji da ƙuruciya. Police ɗin ya ce “I’ll report, za ku yi prison for life” Guy ɗin daya fito daga motar yana wata iriyar tafiya majestic har ya ƙarasa gaban police ɗin a taƙaice ya ce. “Ohhh” Ya faɗa yana hura masa yahaƙin Cigarettes… Police ransa ya ɓaci ya ɗaga hannu zai nuna shi da yatsa cikin zafin nama guy ɗin ya kama hannu tare da murɗewa nan take hannun ya kare…….Kuka Abbu yake wiwi hannunsa dafe da Alkur’ani ya ce “Wallahi wallahi Majeederh ni ne ubanki, mahaifinki ni na haifeka jinina ke yawo a jijiyoyin jikinki, Majeederh ina tunanin ke aka sauya mini kin tuzartani kin ɓata mini suna a dangin kina roƙan Soyayyar namiji? Ni na cancanci haka?” Majeederh ta ce “Ka yafe mini, zan yi aikin ba zan ƙara ba kuma ba ai bai aurenin ba he left me”…… Shekarunta 31 cif tun ranar ba wanda ya ƙara cewa yana sonta balle aure, a haka ta ƙara zama Gwarzuwar Alkur’ani wacce aka gabatar a Saudiyya…..

Sun cike titi babu wajan da mota zata shige, sun haddasa go-slow na ban mamaki wasu ne da basu da maraba da ƴan fashi wajan su goma a tsakiyar titin sun saka wani a tsakiya suna duka.

” Kai dan ubanka sa’an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?” ” Wanda suke doka ya ce “Me nayi muku?” Taj ya ce “You’re just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria Bama kano ba, Lagos ma babu wanda ya isa damu balle Kano”

Joshua ya ce “Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa ƙafar daba da hannun hango a zubar titi” Wani police ne ya ce “Ku titin iyayenke ne? Zaku jawa kanku dilla ko kwashe motocin ku, ku bawa jama’a waje.

Daga bayansa aka ce “What if we refuse?heeee?” Gabaɗaya Gang team suka kalli Bad boy wanda ya fito daga mota, police ɗin ya ɗaga hannu zai nuna Bad boy kafin ya yi pointing ɗinsa ya kama hannu tare da karya shi nan take….

https://arewabooks.com/chapter?id=64ac50ef324ef73a495e70b9″This is the first and last da za ki yi pointing nawa da finger, Dog!” Guy ɗin ya furta hakan a tsawa ce, mai da police ɗin ma ce ta hanyar faɗin “Za Ki yi” Saboda rashin cikakkiyar hausa maganar ta shi ma a gurɓace take. Sosai Police yake jin azaba nan take hannun ya kumbura zufa na yanko masa ya ce “This is not fair, su waye ku? You came and blocked the road and prevented the vehicles from entering”….“Your Father” Guy ɗin ya faɗa. Yana ware kuma dara-daren idanunsa akan Ɗan sandan, Kyakkyawan saurayi ne mai ƙarancin shekaru domin baifi 16yrs ba, kulawa da kwanciyar da jin daɗin rayuwa haɗi da samun duk wani abun da yake so ya sanya jikinsa wani irin mahaukacin buɗewa, domin gabaɗaya cikin Gang team ɗin yafi kowa girman jiki, tsayi da kauri jikinsa a murɗe yake ga wasu six-pack da suka bayyana musamman saman ƙirjinsa, baƙi ne shi sosai irin baƙin ƴan America ɗin kana ganinsa kaga Ba’amurke baƙar fatarshi mai kyau da sheƙi irin baƙin da yafi farar fata kyau da ɗan kan idanu. Gabaɗaya jikinsa zanen tattoo ne daga wuya har zuwa ƙirjinsa da hannaye ga wata ƙatuwar sarƙa mai tabon Cross a jiki. Sumar kansa a murmurɗe kamar indomie wacce ta ƙara fito da kayan fuskarsa da jajeyen laɓɓansa…. he is outstandingly handsome and robust, very masculine. Cikakken namiji mai iko da tsayawa akan ra’ayinsa. Police ɗin ya nuna kansa ya ce “Ni ka ke zagi?”
“An zage ka titin na ubanka ne?” Taj ya faɗa yana nufar kan Police ɗin ganin haka yasa ya yi saurin yin baya tare da barin wajan. Taj ya ja tsaki ya juya ya kalli Guy ɗin daya karyawa police ɗin Hannu ya ce
“Abraham let’s go” Da wani irin kallo wanda aka kira da Abraham ɗin yake bin Taj da shi cikin warning ya ce “Sai na ci Babarka, duk sanda ka sake ce mini Abraham” Ya faɗa cikin harshen turanci. Da sauri drivern Abbu ya juya zuwa wajan mota yana isa jiki na rawa ya ce “Yallaɓai wallahi ƴan fashi ne, mun shiga uku” Abbu ya ɗago kai ya dubi driver a hankali ya ce “No! Ba ƴan fashi ne, ƴan fashi da rana??” Driver ya ce “Kwarankwatsa su ne, hadda bindiga irin ta film na gani fa? Innalillahi mun shiga uku” Abbu ya ajjiye Jaridar hannunsa domin meeting ne da shi na gaggawa akan wata contract da zai yi signing akan papers ɗin. Ganin haka ya sa Driver buɗewa Abbu ƙofa ya fito yana tattare babbar riga cikin sauri kana ganinsa kaga manyan Alhazawan nan masu tashe da kuɗi, ya dinga ratsa mototci yana shigewa har ya isa tsakiyar Gang team ɗin. Abraham na tsaye hannunsa riƙe da Cigarette yana busawa tare fitar da yaƙinta zuwa sama. Taj ya ce
“Guy’s let’s go, go go” Abraham na ƙoƙarin shiga mota ya ji an damƙi wuyansa ta baya, abinda tunda uwarsa da haife shi ba a taɓa yi masa ba, kasa juyawa ya yi saboda tsananin mamaki kafin a ankare ya ji an fizgoshi tare da sauke masa wasu tagwayen maruka. Gabaɗaya Gang team ɗin, Taj, Joshua, John… Da sauran sukai kan Abbu kowa yana fito da bindiga Jikin Abraham har wani tsuma yake naman wajan na wata kakkarwa idanunsa sukai jajur Yatsun Abbu suka fito raɗau a saman kyakkyawar fatarsa. Da wata murya ya daka musu tsawa ya ce “Noo!!!!! Don’t shoot him” John ya ce “But why? Marinka ya yi, He slapped you, waye shi a Kano? Ubansa ma ubansa zamu ci dan kaza kazanshi” Abraham dai kallon Abbu yake without blinking his eyes. “Ni ne zan hukunta shi, Ba a taɓa mini haka ba in my whole life” Abraham ya basu amsa. Cikin sauri kuma ya ƙwaci bindiga a hannun Taj zai bugawa Abbu kan bindigar ya ji Abbu ya ce “Wato kune irin gagararrun da muke da su a kano ko? Haihuwar kan titi wanda baku san girma da darajar kowa ba? Shegu gayyar tsiya, gayyar na ayya” Cak Abraham ya tsayar da hannunsa dab da fuskar Abbu ya runtse rinannun idanunsa. Ganin ya tsaya Gang team ɗin suka haɗa baki wajan faɗin “Bad boy Shoot, Shoottt him” Ko motsawa bai yi ba balle ya yi ƙoƙarin harbin Abbu, murmushi Abbu ya yi ya ce “Idan kai ɗan halak ne harbeni, ɗan daba masu kwacan wayoyi sisi babu a aljihu maimakonsa ku nemi aikin yi kun bige da sata da bashi da makami, me ake da talauci shi yake saku irin wannan Allah wadaran naka ya lalace” Wani acikin jama’ar wajan ya ce “A’a Alhaji ɗa ai na kowa ne, ka yi musu fatan shirya idan da rabo watarana sai kaga sun zama wasu a Nigeria bana jihar nan ba” Abbu ya girgiza kai ya ce “Goodness! Ai basu da rabon shiriya irinsu da haihuwar su gwara ɓarin su, basu da wani muhimmaci talakawan banza, maybe na shan wiwi da sigari basu da shi” Yadda jikin Abraham ke ɓari kaɗai zai bawa mutum tabbacin maganganun sun shige su, duk da ba komai yake fahimta ba cikin yaren Hausar.
“Useless” Abbu ya ƙara furtawa yana tofar da yawu. Kafin su Taj su lura Abraham ya shigo dukan kansa da ƙasan bindigar nan nan da nan jini ya fara zubar masa. Ganin hakan ya sa John nufar Abbu Gadan-gadan zai harbe shi kafin ya ƙarasa Abraham ya cimmasa yana zuwa ya dunƙule ya naushi John a ciki yana huci kamar zaki ko kumurcin maciji cikin ƙara ji ya ce “I said no!”
“Bad boy akan wannan tsohon ka ke cutar da kan ka?” A fusace ya sake juyawa kan Taj ya ce “Abu ɗaya ka ƙara cewa zan kashe ka, I’ll kill you Taj” Yana faɗin haka ya ƙwaci key ɗin motar shi hannun Joshua motar da tafi ko wacce mugun kyau ya nufa yana zuwa ya buɗe tare da shiga ya jata da wani irin sauri kamar zai tashi sama haka yabar wajan, ganin irin gudun da yake saka Gang team ɗin suka shiga mota tare da marawa Bad boy baya, Abbu ya ja tsaki tare komawa a hankali masu tsaron kan hanyar suka dinga bawa mutane hannu suna shigewa “Ƴan iskan yara gantalallu” Abbu ya faɗa bayan driver ya shige da shi zuwa hanyar su da Murtala Muhd way…. Gudu kawai Abraham yake idanunsa yana zuwa kan corner da zai You-turn danja ta tsayar da shi, a hankali ya ɗora kansa akan string motar zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito sbd wani irin baƙin ciki da takaici da yake ji, This is the second time he finds himself in this situation, bai damu da jinin da yake zuba daga kansa ba burinsa kawai ya tuna inda ya taɓa jin muryar, tabbas ya san muryar Abbu but where? Ba a taɓa riƙe wuyan rigarsa ba balle wani ya yi attempting marinsa, bai kuma san dalilin daya sanya ya kasa yin komai akan Dattijon ba, da alama he’s special da wani da wallahi sai ya kuntile hannu idanunsa har wani ruwa ne ke kwanciya sbd tsabar zuciya da taurin rai…. Knocking Glasses ɗin motarshi ya ji ana yi a fusace ya ɗago zai zabga ashar idanunsa ya sauka akan wata yarinyar wacce take duƙun-duƙun ya ja siririn tsaki ganin yadda fuskar yarinyar take duk majina, idanunsa ya ɗauke tare da rufe shi yana jin komai ya duniyar ya fice masa a rai, ya yi dana sanin dawowa ƙasar bakiɗaya. Ci-gaba da knocking kawai tayi ya zuge Glasses ɗin zuwa ƙasa da sauri ta ce “Ka taimaka mini dana abinci saboda Allah Yallaɓai” Bai san meta ce ba, amma ya ji sunan Allah sarai sai ya ci gaba da kallonta, nan da nan zuciyar tausayin sa ta motsa musamman akan ɗiya mace yana da tausayin mata ƙwarai tashin hankalinsa yaga mace na kuka, ya ɗauke yana kwaso kuɗi ya watsa mata ta ƙofa da sauri kuma ya ja motar ya yi gaba… Tun daga ƙofar gate ɗin gidan yake danna horn kafin gatekeeper ya fito ya yi saurin fitowa kansa a ƙasa domin baya jira bai yarda kuma a jira shi ba, ya nufi ƙaramar ƙofar shiga tare barin motar a buɗe a waje, cikin sassarfa cike da kuzari duk da jiri na ɗaukarsa haka ya nufi cikin gidan ya tsaya a ƙofar farko yana danna password ƙofar ya buɗe, a Main parlour ya tsaya cikin zafin nama kamar Mahaukaci ya shiga ɗaukan duk abinda hannunsa ya je kai yana doka shi da ƙasa… Daga saman upstairs aka ce “Grandson!” Abraham bai tsaya daga abinda yake ba, ganin zai jiwa kansa ciwo ya sa David ya shiga sakkowa daga steps ɗin benen da sauri yana zuwa ya kama hannun Abraham ya ce “Waye? Kai da wa?” Yaƙi cewa komai sai huci da yake jikinsa na rawa David ya san Abraham ba zai taɓa magana ba, hakan yasa ya ja hannunsa zuwa saman kujera ya damƙa masa wani cup ya ce “Drink”
Bai tsaya tantance mene ba ya amsa tare da kafawa a baki ya shanye tas, David ya ƙara zuba masa wata ya shanye daga nan ya miƙe ya nufi wani part not too ya dawo hannunsa riƙe da first-aid box ya gyara masa wajan.

“Who is he?” David ya tambaya, cikin mayen daya fara ɗaukar shi ya ce “I don’t know, but i knw him na san muryar” David ya ce “Where?” Ya yi shiru… Ganin yana cikin maye kuma zai fi ɗaukar magana ya sa ya ce “Look Grandson, na ce ko da wasa bana son ganin jini a jikinka gwara ka fitarwa da wani jini da a fitar maka, ka ci mutuncin wanda ya ci naka, ka taka wanda ka ke so, kai ɗaya nake da shi a gefena You’re my grandson exit? Babanka yabarka, baka da Mother baka da kowa a duniya sai ni, ni ne Grandfather naka, idan kuɗi na maganin komai a duniya to duk irin bala’in daka ɗauko zan ji da shi, ni ne shugaban church ni ne Pasto bayan haka kafi kowa sanin matsayina a ƙasar nan bana country ba, ina da kuɗi mai kuɗi shi ke da magana, a top 5 na masu kuɗin Nigeria zan shiga ciki, Mahaifinka Daniel zai shiga…..,” “Stop calling his name, i hate him he’s not my father” Abraham ya faɗi hakan idanunsa na lumshewa ya shiga surutan maye yana faɗin
“She left me, Mamina Grandpa, Mamina Mamina” Sai kuma jikinsa ya shiga jijjiga. Grandpa ya yi shiru kafin ya ce “Mamin nan taka maybe she’s no more bata ra….,” Tasss! Ya ji saukar Glasses ya miƙe da sauri yana riƙe Abraham ya ce “Am so sorry Dear, Maminka na nan I’ll find out where she’s hiding to” Da ƙyar bacci ya ɗauke Abraham bakinsa ɗauke da sunan “Mamin, JEENA” Ganin ya yi bacci yasa Grandpa kiran Taj a waya ta prvt line nasa yana ɗagawa ya ce “What’s happened?” In brief Taj ya faɗa masa komai Ya ce “Ka nemi mai Zane ya yi drawing na mutumin ka kawo mini nan gida” Taj ya ce “Bad boy fa? Ai zai fi yin zanen yadda ake so” Grandpa ya ce “It’s secret”….
Saudiya. Majeederh na zaune saman kujera gabanta ɗauke da laptop tana duba abubuwan da zatai a B.u.k idan ta koma Nigeria, komai nata maturel ne nutsuwa ga wani irin jan aji da kamon kai bata sakewa kowa fuska, har office ya buɗe wanda za a dinga samunta kai tsaye a ranakun weekend, ba ruwanta da batun tama sakawa ranta ba zatai ba tunda babu wanda ya ƙara tunkararta tana jin surutai na yawo a unguwa harda Social media ba ga family taƙi yin aure sai yawo… Door bell ta ji ta yi ƙara a hankali ta ɗan zame hannunta daga keyboard ɗin laptop ɗin, tare da ɗan yi shiru tana tunanin who is there by this time? Bata da appointment da kowa amma waye kuma? A hankali ta miƙe tana saka sunglasses ɗin ta na medical kana ta ƙarasa jikin ƙofar ta ce “Who’s there?” Aka amsa da “Messenger” “Ok came in” Ta faɗa a gajarce, tana kowa tayi saurin saka hijabi da liƙab kana ta buɗe ƙofar, da mamaki ta dinga kallon mutumin ganin uniform ɗin masarauta a jikinsa da alamar Bafade ne shi yana ganinta ya zube a ƙasa yana kwarara mata gaisuwa, ita dai bata ce komai ba ya miƙe mata wata envelope ya ce “Saƙo ne daga Palace ranki ya daɗe Gwarzuwar Nigeria” Da hannu ta nuna masa ya ajjiye nan ƙasa ya ajjiye bayan ya tafi ta durƙosa ta ɗauka envelope ɗin tana komawa cikin bedroom ɗin, a hankali ta ware iya haɗuwa Envelope ta haɗu wani irin zaibar rubutu ne manne a jiki an rubuta.

_Your Highness Ajlaal Sultaan_
Invite
_Malama Majeederh Abdul’aziz Khan_

Ta duba date yau kenan sai kuma time 4 na yamma, ta dinga juya Envelope ɗin Ajlaal mijin Ƙhulud Arzaan kenan? za taga Ƙhulud farin ciki ya wanzu a zuciyarta duk da fargabar kiran ya ɗarso a zuciyarta…. 3:45 Daidai ta fito cikin wata Abaya dark blue tayi rolling kanta da vail sai liƙab da wani sirrin Glasses a Idanunta hannunta riƙe da hand bag da wayarta, tafiya take cikin tarin nutsuwarta kamala da sanin ya kamata, harta isa motar da ake jiranta tana zuwa driver ya buɗe zata shiga gaba ya ce “Ranki ya daɗe baya, ni driver ne” Ta ɗan girgiza masa kai kamar ba za tayi magana ba sai ta ce “Ina so gaban” Ta shiga ta zauna cikin sauri taja motar sai Palace…. Ƙhulud Arzaan na tsaye cikin shigar larabawa ga tsohon ciki a jikinta wanda shi ne karo na farko da zata haihu, fuskarta ɗauke da murmushi Majeederh na yin sallamawa Ƙhulud ta fasa ihu tare da nufar Majeederh, cak ta tsaya idanunta na gizo mata wani abu sai kuma ta nufeta suka rungume juna sosai sukai farin ciki bayan shekaru nawa sun sake haɗuwa, Ƙhulud ta ce “Ina mijinki fa?” Majeederh ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce “Ban yi aure ba” Cikin wasa Ƙhulud ta ce “Kina jiran haɗaɗɗan namiji ko?” Murmushi kawai ta yi sai kuma ta ce “Kamar labari littafi? Kawai Allah bai kawo ba” Ƙhulud ta ce “Ubangiji ya kawo na gaban kwatance amma na yi mamaki na ɗauka ma kin haihu wlh” Majeederh ta yi shiru Ƙhulud ta ce “Mu je wajan Granny Zaytoon” Suka miƙe wani plat suka nufa mai kyau da tsari. Zaytoon na zaune saman ladduma gabanta cike da kayan itatuwa ana mata firfita suna shiga Zaytoon ta sauke wani irin kyakkyawan murmushi tana tafa hannu ta ce “Lale lale da babbar Malama” Gabaɗaya Hadiman suka fita Majeederh ta zube gaban Granny tana gaisheta ta amsa da “Ma sha Allah, Allahamdulillah Sannu kin ji ina sake tayaki murna” Ita dai kanta a ƙasa, Granny ta dinga kallonta ko zata cire liƙab ɗin fuskarta amma taƙi itama kuma bata ce ta cire ba sbd she don’t want interfere a rayuwar Majeederh. Majeederh ta ɗago kai idanunta ya sauka akan wata matashiyar mata mai wani kyau kamar ba mutum ba, ta dinga kallon matar sai kuma ta ce “Ina yini?” Granny ta juya ta kalli matar da Majeederh ke gaisarwa wacce take zaune saman wheelchair Granny ta ce “Wai Gimbiya kike gaidawa? Allah sarki Hawwa’u ai bata da lafiya bata magana bata tafiya hannunta kawai ke motsawa” Cikin tausayawa Majeederh ta ce “Allah sarki, Allah ya bata lafiya” Granny ta ce “Ƙarasa wajanta mana, takwararki ce sunanta Hawwa’u yadda take kallon naki kamar ta sanki bayan ko Nigeria bata taɓa zuwa ba” Majeederh ta ƙarasa gaban matar ta durƙosa ta ce “Sannu Allah ya baki lafiya” Ga mamakinsu sai su kaga tayi murmushi harda hawaye ta riƙe hannun Majeederh ƙam! Sun jima kafin ta ce “Naga saƙon kira” Ƙhulud ta ce “Ohh Takawa ke kiranki” Gabanta ya faɗi ta ce “Mai martaba Sultaan?” Ƙhulud ta ce “Tsohon zance tuni muka ture shi mijina ke kan karaga ai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ke kiranki” Ta yi shiru bata ce komai ba Granny ta ce “Fulani rakata mana, yana part ɗinsa ai ya bar fada tuni sai miskilanci yake ji jiya da yau” Ƙhulud ta ce “A’a jinin sarauta ke yawo a jikinsa fa, ba wani miskilanci” Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye Majeederh ta miƙe ƙirjinta sai bugawa yake a haka suka ƙarasa wani irin ƙyakƙyawan plat mai ɗaukar kyau ga matso tsaran ƙofa nan birjik suna ganin Fulani suka zube Ƙhulud ta yi murmushi tare shigewa Majeederh ta bi bayanta, suna shiga Ƙhulud ta yi sallamawa yana zaune hakimce idanunsa rufe yana cikin wata Jallabiya mai kama da Alkyabba, ya ɗora hirami a saman kansa ga gefensa fuskarsa suma ta sakko kamar ka taɓa shi jini ya fito, bai amsa gaisuwar Ƙhulud ba, bai kuma buɗe idanunsa ba, Ƙhulud ta miƙe ta ce “Ina zuwa Majeederh” Majeederh kamar ta saka kuka ta cikin liƙab ɗin, amma ta kasa ko motsi. Wajan ya yi shiru ita ba tayi magana ba shi ma bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai ɗin, shafewar seconds kafin Majeederh ta ce “Barka da hutawa Takawa” muryarta na rawa domin ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba, tana jin kanta Uncomfortable a gabansa musamman da taga kamar bai taɓa sanin wani Abu Annuri ba a saman fuskarsa. Ta ɗauka bai ji ba ta ƙara maimaita gaisuwar nan ma shiru tana ɗago idanunta da niyyar ganin ko baya wajan cikin rashin sa a idanunsu ya sarke cikin na juna, Ajlaal Sultaan ya kafeta da narkakkun idanunsa can kuma ya taɓe baki kana ya janye idanunsa a hankali ta ce “Gani” Ya jima kafin ya ce “Ke wa?” Tama ɗauka ba zai magana ba sai ta ji ya ce hakan. “Ance kana kirana” Bai ce komai ba ganin tana ƙoƙarin wulaƙanta kanta gabansa duk da tarin nata kimar ya sa ta miƙe tare nufar hanyar fita, sai da ta je bakin ƙofa ta ji an ce “Wait” Bata ɗauka da ita yake ba duka jikinta rawa yake Allah ya gani bata taɓa ganin mutum nai haibar Ajlaal ba zata fita ta ji an ɗora hannu akan hannunta dake jikin Handle da sauri ta juya ta ganshi tsaye kamar ya haɗiyeta gabaɗaya ya yi mata rumfa da ƙaton jikinsa rawar jikinta ya tsananta haka ma bakinta ƙirjinta na ɗagawa tunda uwarta ta haifeta bata taɓa yin kusanci da namiji kamar yadda sukai da Ajlaal ba, hannunsa ya murza akan nata kana jata zuwa cikin bedroom ɗinsa ba parlour ba……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button