Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 5

Sponsored Links

*5…….*
Ta ko’ina suke jifa mata duwatsun jikin ƙaramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya ɗauki wani dutse tare da faɗin. “Fasiƙa, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ƴar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari” yana faɗin haka ya sakar mata dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah take kira da neman ɗaukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake fatan ɗaya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.
“To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ƙona mazinaciyya mai ci da musulunci, a kuma ƙone mugun iri!”
Wani wanda yake da ɗan hankali ya ce “Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita” cewarsa.
Saurayin ya ce “A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa yankata ya dace ayi”
Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da suke kan hanya.
Gabaɗaya suka kalla motar mai ƙirar Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving har ya ƙara su wajan, ta cikin motar yake ƙare mata kallo ganinta durƙoshe har yanzu ko motsi ba tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raɗaɗi yake ji sosai abinda yake ji tsayin shekaru ya ƙara yawa a ƙirjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya ɗan danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.
“Meet me at my house right now” Yana faɗa ya ɗauki face mars ya sanya tare da ɗaukan Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke ɗawainiyya da shi. Ya fito daga motar fuskarsa haɗe duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama nata a firgice ta ɗago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce
“Kuyi mini komai, ban taɓa jikina” “ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda najasa…,”
Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji marin shatin yatsun His Excellency ya fito raɗau a fuskar.
Ya ƙara kai hannu zai riƙe nata hannun domin taimaka mata tayi saurin ɗauke hannu kamar bai son magana murya can ƙasa ya ce “Please Hawwa’u, akwai jama’a”
Ta girgiza kai numfashinta na fita da ƙyar ya ƙara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya ya ce “Haba Jiddo” ganin da gaske take ya sanya ya tattara ƙarfinsa waje guda tare da sunkutar ta gabaɗaya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn tare da ɗaukarsa ya nufi ɓangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu ɗaya ya fara driving cikin sauri ɗaya hannun kuma ya rungume jaririn, keɓantaccen gidansa ya nufa da ita direct.
Wani tsohuwo ya ce
“To ba ga irinta ba, ɗaya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya ɗauketa, ai ni duk wani ɗan shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa”
Haka suka dinga surutu, suna faɗin duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.
Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a ɗinsa na tsaye yana jiran zuwansa, Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake ɗauke da jaririn yana zuwa ya miƙawa Hammad jaririn shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya ɗauki zafi sosai a ransa yake istigifari kafin ya tattara ya ɗauketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya shige ciki da jaririn wani ɓangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi data barci, ya yi mata dressing yana yi yana ɗauke kansa, raunin jikinta bai hana shi ganin asalin kyanta ba, asalin kyawun Fulanin Usul. Zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito ya razana da kyanta sosai shi ya sa ko Hammad bai bawa damar shigowa ba sai da ya gama komai ya sanya mata driving tana ta barcin wahala.
After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana zuwa ya faɗa saman kujera idanunsa rufe. “Amma yana da kyau ka huta Your Excellency” ya ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce
“P.a, kana tsaya iya aikin ka” “Am sorry sir, bayan p.a you’re my best friend hakƙina ne na faɗa gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hakƙin Majeederh tana bawan Allan nan kada ya kama mu yana da kyau a bata wasiƙar ta karanta” ɓacin rai wanda Hammad bai taɓa gani ba ya bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar murya ya ce
“Kasan me hakan ke nufi?” Ya shiga kaɗa ƙafa a duk sanda ransa ya ɓaci kafin can ya ce
“She never choice me, ba zata taɓa zaɓata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata gane shekarun da nayu ina jiranta ba” ya miƙe yana kai kawo
“Sunanta na sanya jinina, sunanta na sakawa ƴata Jiddo, ko sunan mahaifiyata ban sanya ba sai nata, shi kaɗai ya isa yasa ka gane, zan iya adalci a mulkina al’ummata, amma ba zan iya adalci akan soyayyar Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ba, duk hanyar da zan bi na raba ta da kowa zan yi”
Hammad zai magana Abu-turab ya daka masa tsawa ya ce
“Get out” dole ya fita amma shi a ransa ya san babban kuskure ne su riƙe wasiƙar nan.
“Ya Allah!” Abu-turab ya furta yana ɗaukan gorar ruwa mai sanyi, sai da ya shanye tas kafin ya yi cilli da Robber.
Babyn daman yana wajan wata maid yana ta barci ya ji ruwan zafi da kaya masu kyau ga madara da aka bashi sai numfashi yake saukewa.
Yadda Majeederh ta kwana kan gado haka ya kwana a parlour, lokaci zuwa lokaci yana zuwa a cikin daren sai da ya sanya mata drip uku kansa cewar ruwan na tafiya da sauri. Kiran sallar Subhi ya sa ya nufi bedroom ɗinsa farar singlet ɗin jikinsa ya cire ya sakarwa kansa shower ruwa na saukar masa, alwala ya yi ya shirya cikin ash ɗin jallabiya masallacin dake gefen gidansa ya shiga lokacin ana kuraye kirayen Assalatu….
Assalatun ya yi daidai da farkawar Bar Aliyu Sufyan Alhassan a gadon asibiti ya motsa a hankali yana dafe kansa dake masa ciwo kamar ya rabe gida biyu, dishi dishi ya fara gani kafin ganinsa ya daidaita idanunsa ya sauka akan Hajia ta ce “Zakina, sannu ka ji” ya yi ta kallonta kafin ya juya ya kalli Papa shi ma ya ce “Sannu Haydar, ya jikin?”
“Ba sauƙi Papa” Papa ya ce “Meke maka ciwo?”
Ya mutsa fuska ya yi yana rufe Idanu “Meke damunka? Almustapha kira Dr”
“Babu abinda zai iya”
Almustapha ya ja tsaki ya ce “To ai kun ji, shi fa sam baya tausyain kansa ina can gidana tare da matata ku kirani wai jikinsa ya tashi kamar shi kaɗai kuka haifa? Mene abin so a wajan wata Majeederh tsohuwar ko me?” Aliyu kamar zai kuka ya kalli Hajia ya ce
“Kin ganshi ko?” Hajiya ta ce “Ka fita idanuna Almustapha, kabar mini yaro ya ji da abinda ke damunsa” “I love her”
Cewar Aliyu. “Kayi haƙuri zaka sameta idan rabonka ce” Almustapha kamar ya shaƙe Aliyu haka yake ji ya ƙara yin tsaki ya ce
“Gashi nan an sallame ka daga court ɗin da ka ke aiki, sai ka zauna zaman kashe wando kana jiran wata” Zaki ya kwaɓe fuska ya ce “In sha Allah sai Allah ya ɗora maka son wacce bata son ka” Dariya sosai Almustapha ya yi kafin ya ce
“Ai matata ƴar Aljanna ce ta wada tani da komai na kwanciyar hankali to me zai sanya na fara tunanin yi mata kishiya?”
Sai a lokacin Papa ya shiga dramar ya ce
“Shi ma tashi matar ai ƴar Aljanna ce” “Barshi Papa idan ya cika ya zo ya dauki Latifa ya sata a wuta, matar taka duk raguwar mai”
Yana faɗin haka ya juya zuwa ga Hajiya tare da ɗora kansa a cinyarta ya ce “Hajia zuciyata babu daɗi ki taimaka mini” ta shiga lallashinsa ta ce “Yanzu yana da kyau ka shaidawa duniya baka da haɗi da ɗan gidan Majeederh, after that sai ka fara shirin nemanta ko?” Ya kalli mahaifiyar tasa sosai sai bai ce komai ba. Misalin 12 na rana lokacin an sallami Aliyu zuwa gida yana zaune ya faɗa sosai kamar wanda ya yi jinyar shekara kamar daga sama ta faɗo bai kalleta ba, ƙamshin turarenta kawai ya ji ya fahimta “Ya jikin?” A gajarce ya ce “lfy” ta zauna ta ce
“Amma ka fasa aurenta?” Ya dubeta ya ce “Ita wa?” Kai tsaye ta ce “Waccar Mazinaciyyar mana” ya yi murmushin kawai bai ce komai ba ta ce “Magana nake kayi shiru” ya juya gabaɗaya tare da saka hannu ya riƙe fuskarta ya ce “Kina son rabauta ko Wife? Me ya sa ki kewa mijinki haka?” Ta ce “Idan har zaka ƙara aure zaka iya ganin fiye da haka” ya sake ta yana kwanciya jikin kujera ya ce
“Sai dai idan bana raye, Latifa Omar ke baki tausayina ne? Sai fa Majeederh zata zo gidanki ki ke gyarawa, tsafta zero, kwalliyya zero, girki zero, mu’amalar aure zero, aikin ki kawai ki sani, yanzu mene ribarki don ki aibata mijinki? yaran da zaki haifa sune abin zai zamewa tabo not me or Majeederh” ta miƙe tsaye ta ce “Divorce me”
“Never, ki jira zama tare da sweetheart” baƙin ciki ya cika mata zuciya ya zari key car tabar gidan ya bita da kallo.
Tunda ta farka daga nauyayyen barcin ko tari ba tayi ba, tsoran ta buɗe idanu taga su waye akanta take, bata so ta samu ɗauki ba ta so ace mutuwa ce ta risketa.
Mama dake zaune ta zabga tagumi ta ce “Baiwar Allah kenan, Allah ya saka miki” ta goge hawayen Idanunta Hammad ya ce
“Kamar ta farka ai” Mama ta ce “Ato gwara ta tashi ai, ga ɗan yana ta kuka gwanin tausayi” a hankali ta buɗe Idanunta ba tare data kalli kowa ba sai gefe guda, yadda take ji zaka ɗauka kuka za tai ta rusawa amma idanunta a ƙafe komai na tunaninta ya sabunta hanyar da zata bi ta zama cikakkiyar karuwa kawai take nema.
“Sannu Malama, Sannu kin ji” sai a lokacin ta juya ta kalli Mama tana jinjina kai. Gently ta mayar da Idanunta ta rufe daidai shigowarsa yana gyara zama babbar rigar jikinsa, nutsuwa da haiba tattare da shi.
“Barka da zuwa Your Excellency” Abu-turab ya jinjina kai tare da neman kujera ya zauna idanunsa kwance a kanta,daga nan Mama miƙewa tayi. Jin shirun ya yi yawa yasa ta juya cikin sa a suka haɗa idanu tayi saurin ɗaukewa. A ransa ya ce “Ma sha Allah, Tubarkallah” a fili kuma ya furta “Jiddo ya jiki?”
Ta haɗe rai sosai “akwai ciwo?” Nan ma shiru tayi gani take yanzu kowa ya tsaneta. Sosai ya gane bata san waye a gabanta ba domin ƙwayar idanunsa kawai ta kalla. Yana ƙoƙarin magana ya ji ƙarar bindiga na tashi ta karaɗe gabaɗaya gidan, ya buɗe idanu da mamaki yasan akwai securities amma harbin na mene? Hammad ya fice da sauri tsoro ya kama Majeederh ta runtse Idanunta cikin rauni ta ce “Ni za a kashe”
“What? Kisa wake shirman haka” ya ajjiye babyn ta ɗauke ɗanta da sauri ta duba hijabin dake gefe wanda yake sabo ta ɗauka ta saka jikinta jiri na ɗaukarta ta rungume ɗanta tare da nufar wajan domin ta miƙa kanta gare su.
His Excellency Abu-turab Alƙasim ya fito yana kallon Hammadala dake ɓoyewa cikin nutsuwa ya shiga nufar wajan da harbin ke tashi Hammad ya ce “No Your Excellency, kada ka je wani Mahaukaci ne da bindiga yake harbi kawo yanzu ya harbi securities guda uku”
“In my house? Mahaukaci?” Hammad bakinsa na rawa ya ce “Yes Sir, kuma wallahi riƙaƙƙen Mahaukaci ne kayan jikinsa tamkar sun yi shekara ɗari a jikinsa, gabaɗaya jikinsa zane ne kamar na tattoo gashi baƙiƙƙirin…

Na’ima Sulaiman Sarauta
08119237616*🌈 MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta
*_Follow my account👇🏾_*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

Related Articles

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button