Mijin Malama Book 2 Page 14
Bakinta na rawa ta ce “Ni ce Abbu” Mamaki ya hana Abbu ƙara cewa komai yana jingine da jikin bango har lokacin idanunsa zube a kanta, kallonta kawai yake da tarin mamaki da al’ajabi haɗi da ta’ajjujjin abubuwa da dama a ran na shi, yaushe ta girma har haka? Yana ina? Yaushe ya samu wannan tafkeken gidan ya ja idanunsa ya lumshe kafin a nutse yana riƙe da kansa har lokacin ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin nata dake faman ƙamshin room air-freshener na strawberry mai kwantar da sanya nutsuwa a zuciyar mai shaƙar shi, ya nemi bakin bed ya zauna yana yin ƙasa da kansa can kuma ya ɗago ya ƙara zuba mata idanu a hankali ya ce
“Come here” Ya faɗa yana nuna mata kusa da shi Majeederh da yanayin mahaifin nata ya fara mata mamaki ta ƙarasa wajan shi bata zauna saman bed ɗin ba, ta nemi ƙasan carpet daidai ƙafafuwansa ta zube tana ƙoƙarin yin ƙasa da kanta taji ya ɗora nasa hannun a saman kanta yana shafawa ya yi shiru calmly muryarsa bata fita sosai ya ce “How are you Hawwa’u?” A hankali ta ce “Allhamd, ya jikin naka Abbu?” Ya yi shiru gabaɗaya jinsa yake kamar new Abdul’aziz ganin komai yake tamkar _Reflection_ “How old are you?” Ta ce “35yrs”
Ya zare idanu “To ina kikai girma haka?” Majeederh kamar za ta yi kuka ta ce “Abbu kana gidan nan” Ya riƙe kansa yana furta “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ya daɗe yana furtawa kafin ya ce “Kin yi aure ne?” Daman was the first question da yake son tambayarta ya kasa tun ɗazo ta jinjina kai cike da kunya ya ce “When?” A hankali ta ce “Not too long” Ya sauke numfashi a hankali yana riƙe yanayin daya riske shi a yanzu ɗin da kyau zuciyarsa na shanye mamakin da al’amarin rayuwa da juyawarta ke bashi ya ce “Kin haihu? Waye mijinki?” Ta ɗaga kai ta kalle shi kuma ta ce “Ina da yaro ya kusa 1yr na haife shi before I got married” Da wani irin sauri Abbu ya ture Majeederh ya miƙe tsaye jikinsa na rawa da ɓari da ƙarfi ya ce “What?” Daga bakin ƙofa aka ce “Exlty, wannan shi ne magana ta gaskiya, she’s right ta haihu kafin tayi aure tana da yaro Khalil” Cewar Uncle Isma’il ya kalli Aaliyyah ya ce “Bring the baby” Ta juya, Uncle ya ƙarasa shigowa haka Uncle Bello da Mami cikin wata kalar murya Abbu ya ce “And who is the father’s son? I’ll kill him I won’t forgive him” murmushi kawai Uncle Isma’il ya yi kafin ya ce “Shi ne mijin nata yanzu” Abbu ya ƙara cewa “Who is he” Ya ce “Mijin Malama, the president’s son” Idan kaga Abbu at this time sai ka tausaya masa zaka san cewa he’s totally confused baya ganewa baya fahimta ya ce “I need to see him right away, na ji hujjar shi na lallata mini rayuwar yarinya ya shiga sabgar daba na shi ba” Uncle Isma’il mai ƙarfin hali ya ƙara cewa “Gaskiya; you supposed to know that” Sai a lokacin Maman Alpha ta kalli Majeederh ta ce “Malama mene Genotype naki dana Khalil? Da blood group?” Kan Majeederh a ƙasa ta ce “O positive: 35% shi ne nasa, Genotype nasa AA ne, ni blood group nawa A positive: 30% G/AA” Maman Alpha ta ce “Na yi tunani daidai kenan, then muna buƙatar DNA test” Uncle Isma’il ya ce “DNA for?” Ta ce “Baby Khalil Genotype ɗinsa AS ne sikila but kariya” Ya ce “Kenan ina aka samu S ɗin?” Ta ce “That’s what i was thinking too….!” Abbu ya ce “Plx ku fahimtar dani what’s going on? What did i missed? Wlh ina jin kamar bani ne ba” A take Uncle Isma’il ya faɗawa Abbu all abubuwan daya aikata bai ɓoye masa komai ba, tun daga mutuwar Fulani Mahaifiyar su Majeederh zuwanta Misira, gasar da taci aure daya hanata batun Abraham da musuluntar shi har zuwan sarkin Makka His Highness Ajlaal Sultaan da auren Majeederh da Ibrahimul-khalil da abin da ya faru ɗazo everything ya faɗa abin da Allah bai bashi ikon faɗa ba shi kawai ya manta…. Abbu ya riƙe ƙirjinsa idanunsa na lumshewa ya ce “Ya isa, Ya isa enough please Yaya zuciyata zata buga” Ganin haka ya sa Uncle Isma’il idanunsa da suka fara sauyawa ya ce “Me kake son nuna mana ne Alhji Abdul’aziz? Kana son ka ce baka san komai ba? Har tsinewa Majeederh…,” Wani irin numfashi da Abbu ya ja da ƙarfi yana riƙe Uncle Isma’il da raguwar kuzarinsa cikin wani mawuyacin hali ya ce “Yaya karka ce ni na aikata haka wa Hawwa’u don girman Allah, karka furta hakan, wlh ban san komai ba Allah da Manzonsa su ne shaida, wanne irin uba ne ni Yaya? Shin da wanne Idanu zan kalli Fulani? Da wanne baki zan labarta mata na watsar da amanarta, meke damuna waye ni ina jin kamar bani ba i feel Uncomfortable, ina jin nauyi da kunyar Allah ba cancanci zama uba a gareta ba, ba cancanci riƙon…” Ya yi saurin yin shiru yana runtse idanunsa sbd wani dishi dishi da yake gani, Uncle Isma’il ya riƙe shi da kyau a jikinsa shi ma kukan yake ya ce “I don’t know what comes over you, ba kuma zan tuhumeka akan hakan ba Alhji Abdul’aziz ba zan hakan ba, ina me baka haƙuri dana zama silar wargatsa zumunci da kuma raba tsakanin uba da ƴar shi I’m very sorry for that, haƙuri ya yi kaɗan ya wanke dafin dake zuciyarka ka yi haƙuri ka yi haƙuri ka yi haƙuri” Cikin rashin fahimta ya ce “Haƙuri name? Bana buƙatar haƙuri a yanzu, tambayar da nake wanne hali nake ciki I don’t know until my daughter grows up, ta haihu ba aure, na yi forcing nata zuwa outside country Yaya? Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ba zan yafewa kai na ba, ina jin kamar yanzu Majeederh ta shigo gida daga islamiyya na mata karatu na kwantar da ita nima naje na kwanta shi ne ban farka ba sai yanzu, duk a cikin baccina na aikata wannan Yaya? Ina na samu arziƙi har haka?” Gabaɗaya Abbu ya rikice Uncle Isma’il kuka yake sosai Mami ma haka, daman Maman Alpha ta gama cin kukan nata tuni tishi kawai take… Uncle Bello ne ya kira Khalil wayar nata ringing tana gab da tsinkewa ya ɗaga Uncle Bello ya ce “Ibrahim kana ina?” Ya yi jim sai kuma ya ce “Is there any problem?” Ya ce “Come, immediately” Muryar shi dake a nutse ba hargowa ya ce “Mami lafiya take? Little Khalil?” Ya ce “Matarka da ɗan ka lafiya suke Ibrahim, surukinka ne ba lafiya kamar wanda ya zauce” Kashe kawai Khalil ya yi not too long ya shigo hannunsa riƙe da wata first acid-box lokacin kuma tuni Abbu ya samu bacci Khalil ya duba shi da kyau ya yi masa injection paracetamol dai drip daya saka masa Uncle Bello ya ce “Ya jikin na shi?” Khalil ya ce “Good, kasai tension ne da shock sukai masa yawa nutsuwa yake so”…. Majeederh na zaune ta ci kuka son ranta ta ƙoshi ta zubawa Baby Khalil idanu dake bacci tayaya wannan yaron za a ce yana da sikila? Wannan mugun ciwon yanzu ya zai iya ɗauka? Gangar jikinsa sam ba zata iya ɗaukan zafin ƙaddarar ciwon nan ba. Khalil ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo ya jima tsaye a kanta hannunsa zube cikin Aljihu kafin ya ƙarasa ya zauna gefenta yana leƙa fuskarta sai kuma ya ce “Take heart Mami” Ta ɓata fuska tayi kicin kicin da fuska ta ce “Ni ba sunana haka ba” Silently yana lumshe idanunsa ya ce “Ya sunan yake?” Ta ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan,or Hawwa’u ko Jiddatul-khairy” Ya tsoro mata narkakkun idanunsa sai kuma ya yi murmushi yana girgiza kansa daya saba idan ransa ya ɓaci ya ce “Goodness” Ta ce “Me?” Ya tsaya da girgiza kan da yake idanunsa tuni ya jaa sbd kishi ya ce “You want me to keep telling you the name your old boyfriends used to call you” Ya zuba mata idanu bata kalle shi ba ta ce “Jiddatul-khairy ko Hawwa’u? ba gwara su ba da wani Malumana kamar wata bargo” Shi dai Kallonta yake ta kuma san ba lallai ya yi magana ba can ta ji ya ce “Ai ban iya Hausa bane, i don’t know how to pronounce the name, kuma ke ai bargon lulluɓe jikin Ibrahimul-khalil ce” Ya ɓata fuska tare da langwaɓar da kansa gefe ya ce “Kamar bani da” Ya nuna ƙirjinsa alamar zuciya ya ce “Baki san waye mijinki, and don’t worry zan samu wani sunan” Tayi shiru ganin Baby Khalil na bacci yasa Khalil matsawa zai jawota jikinsa aka buɗe Ƙofar ɗakin Mami tayi tsaye tana kallonsa ta miƙawa Majeederh cup ta ce “Drink” Ta juya kan Khalil ɗin ta ce “Yau nan kwana kenan ko Ibrahim?” Ai kowa bai bata kunya ba wajan kwaɓe fuska ya ce “I’ll sleep here” Ta nuna masa bakin ƙofa ta ce “To ni na sallameka good night Ubangiji ya bamu alheri mara kunya kawai” Khalil ya miƙe har ya je bakin ƙofa ya dawo ta ce “Ya akai” calmly ya ce “Key” Ya durƙosa kamar zai ɗauki ya buɗe baki tare da manna mata kiss a wuya can ciki ya ce “Mine” Da sauri ya juya yana buɗe rigarsa baya son Mami taga yanayin nasa ta girma har haka, ta girgiza kai tare da ficewa itama… Misalin 2:37 na dare tana bacci tana ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious yana ratsa ko’ina na hancinta, a hankali a nutse sanyin shi mai daɗi ke kwantar da zuciyar mai shaƙa a bisa tilas ba tare daya shirya hakan ba, a hankali kuma ta ji ana mata tafiyar tsotsa a tafin ƙafarta ta matsar tana kwaɓe fuska irin bata so ɗin nan, ƙafar data ɗauke aka sake biyo wa da tafiyar tsotsa kafin kuma ta ji ana lasar wuyanta da sauri ta buɗe idanun da kyau ta juya taga Zizi dake bacci ya saka hannu ya ɗagota ya ce “I need you” Ta kama kunnensa ta ɗora bakinta ta ce “Why kai Stubborn ne?” Shi ma ya kama nata kunnen rabi magana rabi cizo ya ce “A haka kika raine ni” Ya kwaɓe fuska ya ce “Food first, than you than Barth” Tayi kamar bata ji ba, ya hau gadon tayi saurin sauka tana nuna masa Zizi ya ce “Eh tashinta zan naji uban daya shigo da ita, me ya sa bata bi iyayenta ba?” Majeederh ta kama hannunsa ta buɗe Ƙofar balcony dake bayan bedroom ɗinta ta saka key ta rufe ta ce “Naga sai rawan jiki take ka manta muna shirin rabuwa ko?” Ya yi kamar bai jita ba ya ga wata duguwar kujera ga hasken farin wata daya fara haskawa ya cire rigar shi ta sama ya kwanta saman kujerar idanunsa rufe kamar mai bacci zata juya ya saka hannu ya fizgota yana daga kwancen ta faɗo jikinsa ya matseta gam yana fidda wani irin numfashi yadda ƙirjinsa ke ɗagawa da ƙarfi zaka san maganar ya shige shi da kyau, sun jima a haka kafin yanayin nasa ya daidaita suna ta kwance a haka har yaji saukar numfashinta a ƙirjinsa ya zuba mata Idanu…. Washegari da safe Latifa na zaune a parlour Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya sakko daga upstairs ɗin shi daga shi sai singlet da three quarter ya nemi waje ya zauna yana danna waya a hankali yake waya da hajiyarsa cikin shagwaɓa ya ce “Plx hajiata i want surprise her, zan je airport na ɗakko ta idan jirgin nasu ya sauka ita da Anti Biba da Antin Turkey” Ya ɗan yi shiru can ya ce “I agree with you, Buhayyerh nada hankali sosai, don haka i like her i mean i love Hayyerh na shirya aurenta” Bai san mene ya faru ba sai ganin Latifa ya yi a kansa ta ce “Aure sai dai idan ana yi a lahira kayi, yadda tun farko baka auri Majeederh ba yanzu ba babu wacce ka isa ka aura” Ya dubeta yana girgiza kai sai kuma ya ce “Ko zan shekara ɗari a raye idan har Majeederh zata fito daga gidan mijinta to ni Aliyu Sufyan Alhassan na shirya aurenta ko yara talatin ta haife, idan kin so na gaskiya kuma domin Allah shi ne son da na kewa Majeederh, bana son kina sawa ina ɗaukan zunubi ina cewa ina son matar aure, kuma ke dai a yanzu bani da time ɗinki, ba zan taɓa sakin ki ba, aure kuma babu fashi Mrs zero zero empty head” Yana faɗin hakan ya nufi waje ya amshi order breakfast da ya yi a Gusto. Wayarta ce ta ringing ganin number babarta yasa ta ɗaga cikin sauri ta ce “I’ll come, gani nan” Cikin sauri ta shiga mota ta nufi Murtala Muhammad hospital, kai tsaye babban ɗaki ta nufa I.C.U ta samu wani a ƙofa wai shi Saifullahi ɗan guntu baƙi da shi but friendly to everyone ta ce “An dawo da Malam Umar nan?” Ya ce “Sure” Ta shiga Inna ta samu zaune ta ce “Wai jini za a saka masa fa” Latifa ta ce “To ai na ce a ɗauki nawa tun shekaranjiya an tabbatar ina da wadataccen jini kuma ba wata matsala har an ɗauka” Inna ta ce “Ana ɗaukan na mace daman?” Latifa Omar ta ce “Why not Inna? Kawai a nan arewa ake ganin kamar wani mugun abu” Dr ne ya ƙarasu hannunsa riƙe da files da wasu takardu ya ce “Wlcm Mrs, daman ina son magana dake” Ta ce “Kafin wannan me ya ba a saka masa jinin ba?” Dr ya ce “Akan jinin ne, jininki da nasa bai zo ɗaya ba, ina nufin ƙwayar haihuwar shi bai nuna ke ƴar shi bace, to tun a lokacin muka sakawa wani bawan Allah wanda komai naku ya zo ɗaya da shi” Latifa Omar ta ji maganar kamar saukar aradu, har yanzu gani take ƙarya ne Khalil ba ɗan shugaban ƙasa bane kawai plan ne domin ta saka ranta Majeederh ba zata taɓa finta da gidan miji ba ta ce “Sorry!” Ya ce “Ba san yadda zan miki bayani ba, amma idan kin iya biology fine idan kuma a’a ina nufin bincike ya nuna ke ba ƴar Malam Umaru ba ce, idan baki yarda ba ana iya yin DNA test” Latifa ta juya ta kalli Inna da sauri Inna ta sunkuyar da kanta ƙasa……
Mijin Malama isn’t free book, pay before you read zan tafi hutu idan har aka ci-gaba da fitar mini da book wlh 08119237616