Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 37

Sponsored Links

*Lokaci da dama ina son yin magana amma bani da lokaci ko zarafin fidda abinda ke maƙale a zicciyana, sautari kuma ina ganin abinda zan faɗa ya sha bamban da zaton ku, lissafin ba zai zo nan ba, _ALLAH YANA GANI_ kuma shi ne shaida, ban yi haka da nufin ci zarafi wani ɗan-adam ba, domin ni ba macace mai damuwa da al’amuran mutane ba, balle na fahimci y rayuwarka take har na rubuta wani abu na yaɗawa jama’a, abinda baku sani ba ban taɓa sha’awar rubuta true life story ba, ina da labarai na gaske irin su *MUNAFIKIN MIJI* *labari ne da ko wacce ƴa mace zata so ji da sani, amma ban rubuta ba, sbd ban fiya son surutu ba, shi kuma baki tsatsa ne guba ne, dole ka ji tsoro a hakanma muna tare da falaƙi da nasi su ayatul kursi🤓. Ya zama last time da mace zata zo mini da maganar ina na santa na ɗauki labarin rayuwarta na rubuta, wlh da true life story zan rubuta zaku sha mamaki a nan media, bana cika baki bana cewa na iya ba zan taɓa cewa na iya ba, kafin kayi rubutu wasu sun yi, bayan kayi rubutu wasu sun yi, rayuwar ai kamar juyin waina a danta ne🤓 gobe kai ne jibi wani, to gaskiya kai na baya iya ɗaukan tension _ALLAH YANA GANI_ Ina masifar son mai suna da ƙaunar rubutuna, wala writer’s wala reader’s, kawai ka kame kanka yadda Allah ya yika shikenan, gaisuwa ta musamman ga NIMCY REAL FANS irin su Mom Sani paid🤣su Oum Safna da ake fama da laulayi su Balkisa mai awara, su Ruƙayya Sabo Gambo mai adawa da Khalil, Ummu imam kwaila🤔 Nazeefa sabo Nashe, Fareeda Abdullahi writer, Ummu Fatima writer, Mom muhseen writer, Amjat writer, Aishamadawaki, Hajja Ayusher, Hajja FATIMA, Hajja Fatima M Maddibo, Hamzzatumaimunat👐🏼👐🏼 huhuhu a bini bashi*

*Ga special people group hajiyoyi salamu alaykum🤣 ga Arewa readers irin su Zaleehat, Salmerh, Mr 🌹🌺su Maryam Abba zannah su Farida, Sophia sadeeq, Aisha Isma’il Dalhat, shertu sweet Bakery, Easha, Lubabatumuhammad, Rabi, Baby samdi… Sauran mu haɗu Monday…. Zaku samu MIJIN MALAM tun daga 89 zuwa 100 Arewabooks daga weekend zuwa Monday, love you🌹💋👐🏼*

Follow me on Facebook
@Na’ima Sulaiman Sarauta

John was looking at the doctor with excitement all over his face, yana jin wata nutsuwa na saukar masa jin bayan shuɗewar shekaru biyu da watanni yau Khalil ya farka daga halin jinyar daya samu kansa a ciki, John ya kalli Dr ɗin ya ce mata “Are you sure? Khalil has really recovered from his situation?” Ta jinjina kai ta ce “Yes, Sir” Ya shafa kai yana rufe idanunsa a hankali ya furta “Ma sha Allah, Alhamdulillah” Farar matashiyar wacce ita ta kasance Dr ta kalli John domin sam bai mata kama da Musulmi ba, wata line ta ɗan danna ta shiga magana da turanci akan ɓangaren da Khalil yake kana ta ambaci sunansa John, ta kalle shi ta ce “He felt so relieved, kana iya zuwa ka gansa” John jiki na rawa ya ce “Thank you Dr” Yana faɗin hakan ya juya zuwa direction ɗin ɓangaren Da Khalil yake na musamman. A hankali ya tura handle ɗin ƙofar tare da turawa ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, haɗaɗɗan bedroom ne wanda ya kasance a cikin hospital ɗin, ba zaka taɓa cewa ɗakin jinya bane, Idanun John ya sauka akan Khalil dake zaune a tsakiyar bed kamar wani sarki ya tankwashe ƙafafuwansa, hannayensa zube akan cinyoyinsa kansa a ƙasa idanunsa a lumshe, wata green ɗin riga ce a jikinsa kamar uniform, shi kansa John ɗin green ɗin riga aka bashi ya saka, wata hular leda itama green ga safar ƙafa data hannu, farin ciki kwance a fuskarsa ya ƙarasa sai kuma ya kalli Dr wanda ke ciki yana duba abubuwa ya ce “Dr how is he? Da matsala ko wani abu?”
“Not yet, but jikin ya yi sauƙi, daga yanzu zuwa ko yaushe zaku iya tafiya” Dr ya ɗan duba abu sai Kuma ya ce “Babu matsala dangane da zuciyarsa hatta wajan da wuƙar ta ɗan shafa a gefen zuciyar yanzu lafiya take, matsala ɗaya tasirin da poison ɗin tayi a jikinsa, zafin zuciyarsa will increase more than before, baya buƙatar reasons wajan yanke hukunci, zai dinga acting madly, rashin maganar shi zai ƙaru da zarar ka masa ihu aka, kansa zai fara juyawa daga nan zuciyar zata fara aikinta na zafi, sai abu ɗaya…” Dr ya ɗan yi shiru yana kallon Khalil wanda sarai yana jinsu kuma yana fahimta, kawai abubuwa ne sukai masa yawa a zuciya yana farkawa kuma da sunan “Jeena” Ya farka. John ya ce “Go on, Dr”
Dr ya sake kallon Khalil ganin yana ɗan hargitsa sumarsa ya sake wani masifaffan kyau ya sauya gabaɗaya, duk baƙin fatarsa sai da tayi haske tai wani chocolate saboda tsananin kulawar da ake basa, ba zaka ɗauka jinya yake ba, ya zama jibgege ya kuma buɗe sosai musamman daga ƙirjinsa, ga wata suma da saje data sake yawa a fuskar zuwa madaidaicin Geminal ya yi wani kyakkyawan yanayi na ɗaukan hankali, kai tsaye Dr zai iya fahimtar halin da Khalil ke ciki musamman da yaga yana lullumshe Idanu a hankali kuma yake cije lip’s ɗinsa sai hargitsa kai yakeyi. John ya taɓa Dr ya ce “Are you with me? Akwai damuwa ne bayan haka? Is there any problem? Badai matsala ya samu ba? Da tunaninsa ba kuma loosing memory ya yi ba?” Dr ya yi murmushi ya ce “Before that is he was married?” John ya kalli Khalil sosai sai kuma ya ce “Yes of course, yana da mata da ciki ma ya barta” Dr ya zare Idanu sai kuma ya ce “If I remember correctly, his wife has already given birth?” John ya jinjina kai ya ce “Sai dai basu san yana raye ba ai Dr” Da mamaki Dr ya kalli John da Khalil da yanzu ya ɗago idanunsa jin ance ba a san yana raye ba? Kamar kuma ji ya yi ance zuwa yanzu matarsa ta haihu? What’s going on?

“Tunanin waye wannan?” John ya ce “I have no choice, no option, no opportunity, bayan ɓoye Khalil, tun zuwan Khalil Pakistan muke ƙasar nida Joshua, muna bin duka wani motsin Khalil musamman da a kwana ki biyun baya mai da hankalinsa akan companies ɗinsa, lokacin da ake haska faɗan shi da Ddmaster Joshua na wajan jami’an, gurin wani abokinsa, a nan yake ganin komai immediately yazo wajena, banyi zaton wani abu zai faru har haka ba, na ɗauki mota sak irin wacce Joshua ya ɗauka, sai shi ya tsaya wani lungu ni kuma na nufi wajan Khalil, bayan an biyoni sai na shige lungun da Joshua yake saboda i was very afraid da yadda naga muggan makamai, Joshua didn’t stop to hear the explanation I was going to give him, He didn’t give me a chance to speak at all, sai ya ja motarshi ya fita mutanen suka bisa” John ya yi shiru yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa a hankali ya sauke numfashi ya ce. “As Khalil’s wife often says, everything that happens to a person is written as adestiny, No one can change his destiny, ajali ya ja Joshua zuwa Pakistan, He sacrificed his life to save Khalil’s, akan idanuna Joshua ya babbake, da shi da motar suka zama toka, mutane sun ɗauka ni da Khalil ne muka mutu tunda motar iri ɗaya ce ba wanda ya tsaya ya duba su waye a ciki, na ji tsoro, kuma tsoron Allah ya sake kamani ainun na ƙara yadda da imani babu abin kaɗaitawa sai shi, Annabi Muhammad S.A.W Manzon Allah ne” John ya sauke kansa ƙasa a hankali ya ce “Na ji a raina kamar mutanen Ddmaster bom za su bibiyi rayuwar Khalil, na yanke shawarar nesanta shi da ƙasar bakiɗaya domin ayi masa magani, babu abinda ke motsi a jikinsa haka muka taho U.s da visar mara lafiya urgently, nama yi zaton ya mutu Likitoci suka karɓe shi immediately, a haka muka dinga zama a U.s secretly har tsayin shekara biyu da wata shida”

Dr wanda yake da zurfin tunani sosai gashi so friendly, zuciyarsa mai kyau da tsafta duk da kasancewar shi Kirista, amma zaka ɗauka Muslimi ne a fuska saboda nutsuwa, ya sauke numfashi ya ce “To tabbas matarsa idan har tana raye yanzu ta haihu, babbar damuwar zata iya yin wani auren ma” Sai a lokacin suka ji saukar muryar Khalil a ɗan raunace irin ta zallar marasa lafiya da ƙyar ya buɗe baki yana dafe kansa ya ce “Tunda na kasance a raye, My wife most definitely be alive” Suka kalle shi lokaci ɗaya ba zaka ɗauka shi ya yi maganar ba, can ya ɗago kai idanunsa sun yi masifar jaa saboda halin da yake ciki a ɗan gaggauce ya ce “She will never marry, she made me a promise that she will never forget me, balle ta haɗa jiki da wani, idan na tabbatar wani ya aureta…” Ya cije bakinsa yana girgiza kai irin bai ma san me zai ba, domin ko bai cirewa mutum mazantakar shi ba, wallahi sai ya nakasa shi, har ƙasan zuciyarsa yake jin ba zata taɓa yarda da ya mutu ba, ko uban kowa zai yarda, ya samu labarin tayi auren “Uhm” Da mijin, da wanda ya haɗa auren, da waliyyan wallahi sun shiga uku. John ya ce “Dr kana magana ɗazu, me kake son cewa?” Dr ya ce “Poison d’in ta ƙarawa kuzarin shi lafiya, ta ƙara masa zafi, da hauhawar sha’awa ta neman iyali, maybe an yi hakan ne domin a sanya shi neman mata kamar hauka, domin at least zai iya neman mace sau uku a rana, ƙarfinsa ya ƙaru kamar zaki na gudu lokacin da yaga nama ne, ko yanzu abinda ke damunsa kenan, bai dai fahimta bane, so the choice is yours” Yana faɗin haka ya fita abinsa, John ya kalli Khalil yana riƙe dariyarsa a hankali ya ce “Kai ai gata poison ɗin nan tayi maka, yanzu ya? A kawo taimako ne ko zaka rakata haka?” Khalil did not look at John, and he did not speak, he was silent and acting like a king. Khalil ya kwanta tare da mirginawa ya yi rufda ciki yana lumshe gajiyayyun idanunsa, sai a lokacin komai ke dawowa kansa can ƙasa daga shi sai zuciyarsa ya ce “Ummie? Clara?” Wani irin so da ƙauna haɗi da kewar mahaifinsa ya wanzu a zuciyarsa.
Wajan 6 na yamma John ya sake dawowa ya samu Khalil ya yi wanka ya yi sallah, gefensa ga cup ɗauke da green tea a ciki, kamar yadda ya ganshi ɗazu yanzu ma haka yake, yana tsakiyar gado ya tankwashe ƙafafuwansa, ya ɗan zuba hannunsa a saman cinyoyinsa, John bashi da tabbacin Khalil ya amsa sallamar or not, domin kansa a ƙasa yake idanunsa a lumshe, a hankali yake sauke ajiyar zuciya yana danne lip ɗinsa na ƙasa wanda yayi jajur. John ya ce “Ranka ya daɗe” Khalil ya yi shiru John ya sake cewa “Jinin sarauta ya fara aikinsa kenan, have you eaten Ranka ya daɗe?” Khalil ya ɗago kansa yana zubawa John rinannun rikitattun idanunsa wanda sukai laushi da sanyi, yadda idanun Khalil sukai ya sanya John tuntsirewa da wata mahaukaciyar dariya yana durƙushewa ya ce “Goodness, kamar zaka ci babu? Have you eaten?” Khalil ya yi shiru sama da 40 seconds kafin John ya ji Khalil ya furta.
“Zani gida, i want to see my wife and child” John ya ce “Ka ganta? Ko ka yi having….” Wani hargitsatsen kallo na mutuwa da Khalil ya yi wa John ya tilasta masa yin shiru kafin ya ce “Tuba nake ranka ya daɗe, sai nan da kwana goma zamu koma” Khalil ya rausar da kansa gefe yana ɗan kwaɓe fuska “Have you eaten?” A fusace Khalil ya juya saboda ya fara jinsa sama sama ya kasa riƙe kansa da yanayin wani tsoko yake jin mararsa ke masa “Ka daure kaci ko fruits ne” A hankali a sanyaye cike da shagwaɓa ta ɗan fari data motsa masa yana kwaɓe fuska a taushashe ya furta “Ban jin daɗin komai, i want my Jee” John ya girgiza kai ya ce “Akwai matsala, naga wata baturiya nata zagawa ko a kirata?” Khalil ya ce “Ubanka zan mata?” John ya miƙawa Khalil visa ya ce “Congratulations, Our flight will leave for Nigeria at nine o’clock tonight” Khalil ya dinga kallon John so yake ya ce “Thank you” Amma ya kasa bakinsa ya masa nauyi sosai “I understood, ur Wlcm”

Majeederh na zaune a parlour kanta a ƙasa kullum hijab ne a jikinta kamar mai takaba, tun safe kuma ta gudu daga gidan Alpha dake kusa dana Uncle Bello, yanzu ma kamar wanda ake family meeting akanta, kowa faɗa yake mata da wa’azi akan tayi aure tayi accepting Alpha as her husband, wanda ya mutu baya taɓa dawowa har gaban abada, ita musulma ce ta yarda da Allah tayi imani da Manzon Allah, da Sahabban shi, ta yarda da Alk’ur’ani mai tsarki, ta yarda da tauhidi ya zama dole ta yarda Khalil ya mutu ba zai taɓa dawowa ba. A hankali ta furta “To” Yaya Bilkisu ta ce “A’a ba wani to, cewa zakiyi ba komai Allah ya yi ma tsohon mijinki rahama ya sada shi da Mala’ikun rahama, na amince da ɗan uwana kuma jinina matsayin mijina zan masa biyayya In sha Allah” Ta ɗaga jemammun idanunta da suke farare tas ta kalli Yaya Bilkisu, ba tare da tayi musu ba ta ce “In sha Allah” deep down na zuciyarta ta san Khalil yana raye ko baya raye ba zata taɓa cin amanar ruhin sa ba, har abada tana so da ƙaunar ruhinsa ya kwanta cikin salama ba tare da tunani ko zargin taci amanar so da ƙaunar da yake mata ba, balle yadda take jin zuciyarta ta san he’s still alive. Yaya Bilkisu ta ce “Allah ya yi miki Albarka, ya raya miki Alhassan da Al’hussain, daman ba ruwana da Alhassan Mai masifar zuciya, ɗazu fa tas ya fashewa Barrister Glass cup ɗinta saboda ba’a haɗa masa tea da wuri ba” Uncle Bello murmushi kawai yake, Innati ta fashe da kuka ta ce “Amma ba wasa wallahi ba a kyautawa kululu ba, daga mutuwar mijinta sai a laƙaba mata mutumin daya gudu ya barta? Daman ni fa ba wani sanin zuciyar sojan nan na yi ba, yarinyar kamar wacce ake farin ciki da mutuwar mijin nata?” Kuka sosai Innati keyi kamar ranta tana fyace majina da gefen zani ta ce “Ni dai Allah yana gani ba ruwana, kada ma ruhin mijinta ya ƙullacan balle ya dinga mini fatalwa, ina ake haka a cikin ƙabilar Hausawa? Mace sai tayi shekara goma cif tana takaba ba uhm ba uhm’uhm ruwa ma sai dole zata sha balle abinci, don Allah kiyi haƙuri ni dai ƙarfina suka fi amma a kaf duniya iya legas ne zasu iya aikin gaɓa gaɓan da su Isma’ila sukai” Tayi ƙasa da murya ta ce “Ai dake legas ba wasu cikakkun Hausawa bane a can, gawa ma ba a wani damu da ita ba, acan mukai ƙuruciya da Aminiyyata Naila babar Mai martaba Abduljabar, lokacin da ɗansa Zain ya mutu matarsa Haukacewa tayi fa? Ita Kululu a barta tayi kuka na cikakken shekara ɗaya ma ƙunci sai masifar aure shi ma Sojan dake tsohon maye ne bayan duk nasan me ya kewa?” Ba wanda ya kulata, Latifa Omar ta shigo duk ta jeme ta fita hayyacinta, Majeederh na ganinta ta miƙe tana ɗaukan Alhassan da baya taɓa yadda ya yi bacci idan ba a jikinta ba. “Don Allah don Annabi Majeederh ki tsaya ki saurare ni don Allah” Majeederh ta ce “Look Latifa ni abinda ya daman ya isheni, bana buƙatar jin hujja ko dalilin ki na abinda kikayi” Tana faɗin hakan tayi ciki, Baby Khalil daya girma ya yi wayo ya zubawa Latifa Omar idanu itama shi take kallo sai kawai ta miƙe ta fice ba wanda kuma ya kulata a cikin su.

Misalin 1:20 na dare Majeederh na bacci a bedroom ɗinta dake gidan Uncle Bello domin bata koma gidan Alpha ba, a hankali ta ji ƙamshin da har gaban abada ba zata manta da shi ba, ta kasa buɗe idanu saboda nauyin da sukayi mata, Sosai ƙamshin ke ratsa hancinta zuciyarta na mata sanyi nauyin da tayi mata yana raguwa, ajjiyar zuciya mai sanyi ta saki jin ana zagaye lip’s ɗinta da yatsa mai taushi, kuma an yi mata rumfa, gently kuma taji ana sauke siririn hannun rigarta zuwa ƙasa, cikin wani irin hargitsatsen yanayi jikinta na tashi yana zubewa, tana jin kamar she in dreaming ta ji an kifa kai tsakanin ƙirjinta hannunta ya sauka a lallausan sumar kansa cikin wata kalar raunatacciyar murya ta ce “Who…. who are you?” Daidai kunnenta ta ji an furta “Mu’azzam, ur husband” Ta ɗauka da gaske irin mafarkan da take da shi ne na kullum gasu tare sai bata damu ba, ko ta buɗe Idanu tasan ba zata ga komai ba sai darkness or shadow, yadda ake sauke numfashi a gaggauce a wuyanta da yadda ake bin ko’ina na jikinta da wani irin mahaukacin deep and hot irin italian kisses ɗin nan ya sanya ta buɗe baki da ƙyar za tayi magana ta ji saukar tattausan lip’s cikin bakinta a haukace….
[

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button