Hariji Book 1Hausa Novels

Hariji Book 1 Page 17-18

Sponsored Links

Free page 17&18

*Alheri writers Asso.*

By…Oum Aphnan
Marubuciyar
*Bagidajiya*
_Laylerh_
*Jarababben Namiji*
Indo maqata
*Ramuwar gayya*
Qasaitattun mata
*Rayuwar Afredarh*
Namijin kishi
*Akan dadiro nah*
Jinin sarauta

Related Articles

And now

*°•°•° Hariji °•°•°•*

 

_Like father like Son_

Gama duk aikinda ummi takeyi, tayi. sannan tasa tsintsiya ta share gaba ďaya dandaɓaryan ƙasan gidan,wanda ya daɓe kamar sumunti,saboda tsabagen gyara da shara da yike samu a wajen ummi,duk ƙurar ya kwanta,ta gama sharesa…daganan janyo ruwa tayi a daga kwakwareren rijiyarsu,datake a bude kasa na zabtarewa yina komawa ciki,haka ta gama zuba ruwan a bokati ta saka a inda rana yike fitowa,da nufin yayi dumi taje tayi wanka dashi,itakuma kafin nan ta kewaya bayan gidan tana gyara wajen shukan ɗatan ta(shuwaka).

***
Wulƙawar ummi baya keda wuya ,hajara ta shigo gidan ,da sauri ,sauri ta fara jan ghana must go ɗinta na suturu tana fitar dasu ƙofar gida.
Ta janyo na ƙarshen ummi ta kewayo,anan sukayi kici6is
“Anty Hajjo,ina zuwa da kaya haka”
Ɗan sassauta muryarta tayi ,kamar mara gaskiya
“Shishhh ,ki magana a hankali tareda wani gaye nike a ƙofar gida ,da dalleliyar motarsa ,ya rakoni ne in kwashe kaya ,bayan naje gidan uncle ɗin GRA ba roƙeshi Arziƙi zan koma can da zama ,don gaskiya ina mugun kunyata ,idan samarina sukazo ,sukaga wai wannan buscuit house ɗin shine gidan mu,a take nike ganin alamun raini a ƙwarar idonsu,don haka in umma tazo kice mata na koma GRA zan ringa zuwa muna gaisawa,don yanzu haka ma nacema wannan gayen ne,nan gidan da nike kai wanki ne nazo in kwasa kayana..”

Tunda hajjo ta soma magana ,ummi tayi mata sakatata da baki ta kasa furta ko 1 kalma,itakuwa taja jakar kayanta tayi ficewarta

“Ohni oum kulthoom ,inaji da yayyu,In baka mutu ba zakaga abu ,Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu”

Daganan taje ta ɗauki ruwan wankanta ta wuce banɗaki abunta.

**
*4 Pm*
Sallama ummi taji daga ƙofar gida,itakuma a daidai tana ƙoƙorin saka safa zata wuce Islamiyya,ɗan ɗaga murya tayi kaɗan,tana amsa sallamar ,sannan tayi hanyar fita da sauri,gabanta na faɗi, ko da wanne yau a kazo ohoo?

Turus tayi ganin baba mai anguwa a bakin ƙofa.
“Sannu baba ,ina wuni”
“Lafiya lou,ummulkaltume ƴar Albarka anyi shirin islamiyyar?”
“Eh baba me unguwa,wani kake nema ne?”
“Eh to,da babanki naso gani,amma dai tunda na ganki zance ya ƙare,tunda dama mune almuhimmun kuma zancen ta kanmu ya biyo,watakon *ALƘALIN ALƘALAI NA ƘASA* Ne takanas ya taso don ku gana akan magana mai muhimmancin gaske ,dikda bai faɗa mana ba,to nasan yanzu mara zuciyar ubanki baza’a samesa a gidaba ,wataƙil yina bakin tasha ,to don haka na taso in shaida maki zuwansa ,wataƙila akan bai rasa nasaba da shari’arku .A don haka,yayi maki saura ki ɗauko tabarma ki shimfiɗa masa a soro ,ko kuma ki masa tujara irin na gantalallun ƴan uwanki,da suka saba,kedai kin fice masu zakka! Don haka Ki riƙe matsayinki Ato”

Tunda ya fara magana kanta ke sunkuye ranta na tururi,kowa ya tashi zagi! ,zagi dai akan iyayenta da danginta,basu tunanin duk lalacewarsu ina sonsu a hakan? .
Saida ya ƙare ɗiban Arziƙinsa ya wuce,itakuma kamar yanda ya bata umurni ta shiga gida ta ɗauko wata tsohuwar tabarma ta shimfuɗa masu a zaure,jimawa kaɗan sai gashi ya dawo bayansa ,wani ƙasurgumin Alhaji cikin wata ɗanyar shaddar gezna dark blue sai ƙamshi takeyi.
Can daga bakin ƙofar shiga gida ta zauna gamida rafka tagumi
A haka take gaishesu kanta a sunkuye,saida suka gaisa sannan baaba mai unguwa ya fita ,shikuma yayi gyaran murya.

“Malama Oummu” bata samu zarafin iya amsawa ba,sakamakon yanda muryarsa ya haifar mata da jin nauyinsa gamida ninkuwar kwarjininsa,don haka a nutse ta watsa lulun Eyes ɗinta a kansa a karon farko tun zuwansa.

“Kin ganeni?” da sauri ta girgiza masa kai “ban sanka ba yalla6ai”
Murmushi yayi irin tasu ta girma
“In tuna maki ko ni wanene?” Gyaɗa kai tayi shaye da mamakinsa

*…..3 years back*
Dambene ya kacame tsakanin Hajjo(Hajara keken maza ) da Uwale (Jamila) duk akan saurayin Jamila da yaga hajara yaci amanar uwale ya koma yina nemansu gabaɗaya,shine a ranar asirin su ya tonu ta kamasu a ɗakin saurayin tana kwance akan katifarsa da shi,itakuma tun a ɗakin bala’i ya ruguntsume shine har gida…Bala’i yayi bala’i har maƙota saida suka shigo sasanci,saidai ba ko kunya ana tambayarsu abunda ya faru sai tace wai daga ta ganni akan katifar saurayinta,to shiɗin aurenki xaiyi,ai gwara kowa ya yaga rabonsa…”
Itama umma ba kunya take bin bayan uwale,wai hahara ce ba gaskiya tinda ai ba saurayinta bane

Kuka sosai ummi takeyi a lokacin tana shekaranta na farko a makarantar midwifery ɗinta,kwata kwata shekaranta sha shida
Haƙurin duniya ta basu sunƙi haƙura saima duk suka juyo da akalar faɗar kanta

“To Algunguma,ina kika fito school,ina zaki makaranta,ai yanzu kema kika fara tasowa,duk muna kamar ki bamusan daɗin maxa ba ,amma a juri zuwa rafi,don indai ke jinin abbah da ummah ne to harijanci a jininmu yike,Alfarma ɗaya zakiyiwa kanki ki samu miji kiyi aure,saidai kuma kashh har yanzu ba mashinshini…”

“Ya isa uwale,kiyimun duk tujaranki ,allah na gani,kuma inshallah yau ɗinnan zan fita ,zanje duk namijin da na fara haɗuwa dashi,shi xan aura…wannan alƙawari na ɗaukarwa raina da ziciyata,don bazan ta6a yarda in lalaceba,koda kuwa kwartanci a jininmu yike…”

Tana kaiwa nan ta fice da sauri tana sharar ƙwalla

Titi ɗoɗar ta ɗauka ,tana faman waige² jiri na ɗibarta,har tahau babbar titin da zai kaika babbar titin gidan sarkin kano

Wata ƴar ƙumbular mota ne ta shararoo da gudu,saidai tundaga nesa ya fara jan ham,saboda yanda ya hangota tana shiga ma titin,hakan mai makon ya ankarar da ita saima kamar ya ƙara tsoratar da ita.,haka kuwa ta daɗa shigewa titin…ƙiiiiiiiiiii yaja burki ,tareda ɗan ƙurzan ta a hankali ta faɗi ƙasa rikica…aikuwa taba faɗi,ta miƙe da sauri ta tattare siket xata fyalla da gudu ,sosai ya kawo tanada psycho problem ,don haka cikin zafin nama ya damƙeta
Ya turata a motarsa ,ya kewayo zai tuƙa ta kallesa

“Alhaji”
“I haƙuri,yanzu zan kaiki asibiti daga nan”
“Alhaji zaka aureni?”
A mugun bazata kalmarta yazo masa
“Ke kinada lafiya kuwa?” kuka ta fashe masa dashi,tana bubbuga masa gaban mota ,wajen fitar sauti
“Ka saukeni ni lafiyata ƙalau ,damuwata mijin aure kuma kai nikeso,ni ka saukeni in baka yarda da tayina ba”
Ƙare mata kallon ƙurilla yayi,yarinya kyakyawa black beauty,hancinta ɗan gajere da ya dace da faffaɗar fuskarta mai ɗaukeda dimple a kowani ɓangare,idonta dara dara,masu haske kamar madara,wanda kuka da damuwa suka surkasa zuwa ja ja…Ɗan nazartan ta yayi,gadai ta yarinya dake kan ƙuruciyarta da bazata wuce sa’oinsu rufaidah ba(ɗiyarsa) ,wanda suke just in their midst ,a sweet sixteen ,to meye haka??

Tsaida tunaninsa yayi waje guda,yaja burki ya tsaya ,akan kwaltan gefensa ya dauke idonsa cikin rashin kula ,yace “Fita!”
A tsorace ta fara dambe da mirfin ƙofar saidai ta kasa buɗewa
Wani dabban tsawa ya buga mata
“I said out!”
Da sauri ta fita ,sannan ta ƙara da gudu har tana tuntu6e….

….Sunkuyar dakai ummi tayi ,saboda tunowa da abinda ya faru tsakaninsu ,sai yanxu ta ganesa,kunyane ya lulluɓeta
“Alhaji wautace da ƙuruciya kayi haƙuri bansan ko kai wanene ba”
Murmushi yayi irin tasu ta manya

“Nasan hakan,saidai yanxu na bibiyi tarikhin ki,kuma na gano abunda kikayi daidai ne,saidai bakiyi ta hanyar da ta dace ba,a lokacin ina saurine zanje wajen aminina sarkin garin nan,sai daga baya nadamar wulaƙancin da nayi maki ya kamani,saidai abun takaicin bansan inda zan ganki ba,sai sanadiyyar shari’arki da aka sanya a gidan talabijin NTA…A ƙarshe gani nazo a wannan karon badon amsa tayinki ba,A’ah saidai don na hango wasu charisma a tare dake oummu,kuma ni a shirye nike in aureki a duk ranar da kika shirya ,Ni namijine mijin mata uku,matana akwai bayarbiya,banufiya da inyamura,zaki yarda in cike ƙofa dake matsayinki na yarinya jinin Hausa /Fulani?…

***
*Hariji @#200Regular group @#400 vip group ta 7782217014 ,muhammed Hassana,fcmb ko mtn card ta 09065990265….ga masu son duk littafaina zasu sameshi akan kuɗi #1000 only a matsayin sauke farashi,amma banda na wannan littafin,don Allah in baki shiryaba karki biyoni*

Uwale daga gidansu gidan saurayinta da ya kirata a waya ta wuce wato maiwada,saida ta sauka akan mashin sannan ta daɗa kiransa a waya
“Gani a bakin kwanan gidan kazo ka sallami ɗan Acaɓan”
Minti kaɗan ya fito cikin shigar kamala,rigan yadi tazarce,inka gansa bazaka kawo mai fajirciba.
Makullin ɗakin matarsa ya bata,shiga gidan ki buɗe ɗakin ,gafaƙar an tafi yawon ta zubar,kinga muma sai mu murje gyaɗarmu son ranmu,tace kwana zatayi,iba fatan dai kin zo da shirinki,kinsan dai banda sauƙi
“Ai daɗinta nima kasan ba sauƙi garenba,nidai kamun ka shigo ka taho mun da abun motsa baki kurum”
“Angama ranki ya daɗe,uwale kenan *kankana gidan ruwa🍉* ai namiji yayi maki komai don juriyarki ga ruwa da an ta6aki kin hau tsiyaya kenan”
“To ai sai ka tona muna asiri ,adai kan hanya muke”
Sosa ƙeya yayi kamar me kunya
“Santin kine tawan”

_Kar ku damu daga gobe zamu fara abubuwa🙈,Sis akwai raraka da zungura ,daga gobe xa’a fara book ɗinnan ma zance,kuma inshaallah fejin gobe shine zai zana na ƙarshe,in baki biyaba ,maza ki biya kar ayi maki ta leƙo,ta koma😂09065990265_
_Typing ✍🏾_

 

*HARIJI*
(Original Romantic love story)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button