Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 1

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©️®️Hafsat Rano

PAGE 1

Related Articles

***** Sau da dama, rayuwa na farawa ne cike da kalubale mabanbanta, kalubalen da ka iya sawa a banbance masu shi da marasa shi, kalubalen da ka iya zama nakasu a rayuwa har a rasa YANCIN da gatan da RAYUWAR take tafe dashi.
Kanta ta daga zuwa wani sashe na daga cikin dan madaidaicin dakin nata me dauke da dan karamin dressing mirror da medium size bed sai yar karamar wardrobe sai dan karamin toilet daga gefen wardrobe din,ajiyar zuciya ta sauke ta sake maida kallon ta zuwa babban textbook din da ke gabanta, tun da ta zauna kusan awa biyu take ta kokarin solving equation din amma ta kasa,shine last part din da ya rage mata gashi babu alamun zata iya gama shi a yanzu. Time ta duba a wall clock din dake saman gadon taga biyar har da yan mintuna. Mikewa tayi bayan ta rufe book din ta hau zare rigar jikinta, ta sauya ta da navy blue uniform din su ta kama gashin kanta da yake da matukar sulbi da tsayi ta tattare shi ta cusa shi cikin kan sannan ta saka hula ta rufe shi ruf. Hijab ta dauka madaidaici ta dora akan doguwar navy blue uniform din nata sannan ta karasa da rufe fuskarta da nikaf ta sanya wa kafarta black socks cikin mintunan da basu gaza biyar ba. Fitowa tayi bayan ta jawo kofar dakin ta rufe ta nufi main building din gidan ta baya, tana tafiya a nutse tana tunanin yadda RAYUWAR ta a yanzu take ciki da rashin yanci da walwala. Bata da zabin kanta sai abinda aka zaba mata, bata isa ta yanke wa RAYUWAR ta wani hukunci ba sai abinda aka yanke mata, duk da haka zata iya cewa yafi mata RAYUWAR ta, ta baya tunda a yanzu tana kan bigiren cikar burin ta, wanda ba dan su ba, da tuni bata san a yanzu tana wanne hali ba. Cikin wannan tunanin ta karasa kofar bayan da zata sadaka da tangameman kitchen din gidan me dauke da komai na kayan amfani kama daga electronic har zuwa foodstuffs babu abinda babu. A hankali ta tura kofar ta saka kanta ciki da tunanin babu kowa a ciki. Tsaye suke su biyu mace da namiji, namijin ya bawa kofar baya yana daga jikin cabinet din kitchen din, sai macen da ke fuskarta ta, tana kallon shi da alamun magana sukeyi. Chak ta tsaya da yinkurin karasowa ciki, ta rike kofar tana sauke kanta kasa da sauri.

“Get out!” Macen tace mata tana watsa mata harara. Da sauri ta saki kofar amma kafin ta kai ga fita ya dakatar da ita.

“Wait…”

Sai ya kalli macen da tayi saurin bata fuska

“Who’s she? Wacece ita?”

“Househelp.”

Ta fada kanta tsaye tana sake bata fuska. Waigawa yayi ya kalli inda take tsaye, cikin doguwar riga da nikaf, ya sauke kallon sa zuwa kafarta dake sanye da socks baka wanda duk bala’in ka, baka isa ka iya gano kammin ta ba, idonta ta dago daidai lokacin yana kallon ta, kyakkyawan eye ball dinta black sosai wanda yake kewaye da farin kal kal ya shigar masa ido, maganar da yayi niyar yi ce ta makale saboda wani irin fusgar sa da idanun nata sukayi, ganin haka yasa da sauri Anisa tace

“Ki fita ki dawo nan da 15min.”

Ta fada ganin yadda yake kallonta cikin son gano wani abu. Da saurin ta cikin jiran kiris ta saki kofar ta fice har da dan gudun ta. Kallon sa ya maida kam Anisan cikin neman karin bayani, amma kafin yayi magana tayi saurin cewa

“Rules din Mummy ne, not mine.”

“Clothes and everything?” Sai ta daga masa kai alamar eh tana sake bata fuska. Dan shiru yayi kaman me nazari, sai kuma ya dage kafadarsa alamun i don’t care yace

“Muje ciki mu karasa maganar.”

“Ok.” Tace ta dauki glass cup din da ta shigo dauka ta fita yabi bayan ta suna cigaba da maganar da suke tun farko.

Gefen wani dutse ta zauna daga dan kusa da kofar, kusan mintuna ashirin tana wajen a durkushe har magriba ta soma kawo jiki, sai ta mike a sanyaye ta karasa jikin window din kitchen din ta dan leka kadan, babu haske hakan ya tabbatar mata da basa kitchen din saboda wutar sensor ce idan da mutum a ciki take haske, idan babu sai ya dauke. Shiga tayi da dan saurin ta, ta nufi kofar da zata maida ka ainihin cikin gidan ta rufe ta, sannan ta dawo ciki ta zare Hijab da nikaf din ta ajiye a in da ta saba ajiye wa, sannan ta dauki apron wankakkiya ta daura ta a jikinta, ta shiga fiddo da abubuwan da zata bukata, ta riga ta san me zata dafa dan ta kusan hada komai dazu ta yanka na yankawa, hakan yasa ta yi saurin gamawa ta zuba su a manyan warmers din da aka tadanar bayan ta tabbatar da tsaftar su, ta jera komai akan iceland din sannan ta dauki Hijab da Nikaf din ta mayar ta danna bell din dake makale daga gefen kofar sannan ta zare lock din da tasa a kofar ta koma ta tsaya jikin Iceland din.
Turo kofar yayi ya shigo sanye da uniform din sa shima, ta dauko plate ta bude warmers zuba abincin a plate ta zuba komai sannan tayi Bismillah ta ci, yana tsaye yana kallonta har ta cinye wanda ta saka a bakin ta.

“You can go.”

Yace mata, sai ta dauki plate din ta juya ta fice, tana fita ya rufe kofar sannan ya dawo kitchen din ya tsaya.
A saman bedside drawer ta dora plate din sannan ta wuce toilet da dan saurin ta domin magriba ta fara nisa tana tsoron lokacin ta ya fita ba tare da ta yi ba, a gaggauce tayi alwala tazo tayi sallar sannan ta dauki abincin tace tana gama ci aka kira Isha, ta tashi tayi sannan ta zauna a saman abun sallar tana fadawa dogon tunani, tunanin irin rayuwar da ake yi a wannan gidan. A tunanin ta arziki shine yafi komai a rayuwar nan, sai dai a yanzu ta yarda da babu wani abu da yafi dadi sama da kwanciyar hankali, domin tarin arziki babu abinda yake tattare dashi sai wahala da tsoro. A irin tarin dukiyar da Allah ya bawa ahalin gidan nan, ta dauka zasuyi rayuwa ne me cike da yanci da jin dadi, sai gashi hatta abincin da zasu ci su rayu a tsoroce suke cin sa, bata fata ko burin irin wannan dukiyar wanda kowa yake burin ganin bayanka. Ta dan dau lokaci a haka kafin ta mike ta nannade abun sallar, ta ajiye sannan ta jawo littafin ta, ta cigaba da dubawa kafin lokacin da zata kwanta yayi, saboda tashin asuba.

***Jerin motoci ne guda hudu suke sharara gudu a kan titin FCT, tun daga airport road suke tafe a jere har suka haura Asokoro, yana kishingide a bayan Rolls-Royce Boat Tail, hankalin sa gaba daya na kan wayar sa yana duba wasu mails masu matukar muhimmanci.

“Sir mun shigo Asokoro.” Saddam yace yana dan waigowa bayan motar.

“Garki, alone.” Yace a hankali kasa kasa.

“Ok.”

Saddam yace ya dan taba Bluetooth din wayar sa yayi magana sannan ya katse. Juya motar driver yayi suka haura zuwa Garki din sauran motocin kuma suka wuce. Kashe wayar yayi ya daga kansa zuwa waje yana kallon titin da ke dan cike da motoci kasancewar yamma ce kowa yana kokarin tafiya gida. Hankalin sa na kan titin har suka karaso garki din, wanda daga nan zaka haura Garki village. Kamar irin wanchan lokacin yau ma tana rike da hannun namijin, sai dayan hannun ta dauke da littafi suna tafe suna hira cikin annashuwa da jin dadi, fuskarta fayau da wani irin amintaccen kyau me matukar sanyi da dadin kallo. Da kallo ya cigaba da binsu har suka tsallaka titin sannan suka shiga Garki Village din.

“Can I follow them Sir?” Saddam yace ganin zasu sake bace musu kamar wanchan ranar

“No, please. Bana son a samu matsala.”

“Ok sir.”

“Mu juya kawai.”

“Ok, turn.”

Juya motar driver yayi, suka sake komawa. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, ya shafi kwantacciyar sumar kansa yana jin kamar ya juya ya bi bayan su yaje ya same su yayi musu magana, sai dai yin hakan daidai yake da katsewar sanyayyan murmushin da yake hanga a saman fuskokin su, wanda baya taba musu fatan gushewar sa nan

Alarm din da ya saka ne ya tada shi, yayi salati yana tuna mafarkin da yayi, mafarkin da ya zamar masa tamkar ibadah, babu ranar da zata fito ta fadi be yi mafarkin ta ba, tun bayan ranar be sake ganin ta ba, duk kuwa da yaje wajen yafi a irga,amma be taba ganin ko da me kamar ta bace ba, haka ya hakura ya tattaro ya taho Scotland, gashi har an kwashe shekara biyu cif, be taba gajiya da tunanin ta ba.

“Ya Allah!” Ya furta a hankali sannan ya ja iska ya fesar yana jin kansa na dan sara masa. A hankali ya yaye duvet din da ya rufa dashi saboda sanyin da ake yi duk kuwa da room heater din dake dakin amma sai yake jin yau sanyin na musaman ne. Saukowa yayi ya wuce toilet ya hada ma kansa ruwa me zafi sosai yayi wanka sannan ya fito ya hau shiryawa a tsanake cikin matukar nutsuwa da kamewa. Tara da yan mintuna ya kammala shiryawa cikin sweatpant da hoodie ya zura castor slippers dinsa na company DKNY ya nufi living room dake ground floor. A shirye ya tarar da breakfast dinsa kamar kullum, ya zauna ya dan ci kadan yana jin cikin nasa a chushe ba dadi. Tashi yayi ya nufi wajen da brief case dinsa take ya dauko ta ya fiddo wasu papers ya ajiye akan reading table dinsa ya bude system dinsa da take a sleep ya shiga duba ayyukan da zasu gabatar a yau da karfe biyu na rana. Zai yi kokari ya tattara duk abinda zai yi cikin week din ya kammala dan ya kai matukar karshe a yadda ya dauki lokaci a kasar duk da course din gaba daya na one year ne sai gashi ana maganar kusan two years ya gama amma still ayyukan da suke gaban sa sun sha kansa har sun masa yawan da ya ajiye duk wasu damuwar sa a gefe ya rungumi ayyukan da gasken gaske. Dama shi sam bashi da wani YANCI na zartarwa rayuwar sa abinda yake so a aiwatar sai abinda AJI ya tsara masa.🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button