Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 23-24

Sponsored Links

*23-24*_

 

Juyawa yayi ya fice daga dakin yaja qofar ya rufe ta miqe ta bude labule tana kallonsa ya bude dayan bangaren ya shiga ya mayar ya rufe taja fasali tare da ajiyar zuciya ta koma ta bude ledar gasasshiyar hanta ce da taji kayan lambu sai qamshin takeyi dayar ledar kuma kaza ce itama ta hadu taja fasali ta zauna da farko kamar kartaci zuciyarta ta raya mata garama taci rabonta ne idan bataci bama ba gwaninta zatayi ba.
Sake budewa tayi ta dauki hantar takai bakinta saida taci iyakar cinta ta kora da lemon ta miqe ta cire mayafinta ta shiga bathroom ta bata lkc tana kallon bayin tana mamakin irin tsaruwarsa kafin ta dauki sabon brush ta bude ta matsi man goge haqori ta wanke ta cire kayanta ta fara kokawa da shower ta hada ruwa tayi wanka ta fito ta shafa mai ta bude wadroop din ta dauko doguwar rigar bacci tasa ta karkade gadon ta haye taja bargo tayi kwanciyarta.

 

Baccinta tayi cikin kwanciyar hankali saboda gajiyar biki bata farka ba sai safiya ta tashi tayi wanka tayi sallah tana saman sallaya taji an taba qofar ta juya ta kalli qofar jin shiru baa qara tabawa ba yasata tunanin babu kowa taxi gaba da lazuminta sake taba qofar ne yasata miqewa tana tambayar “waye” ba ayi mgn ba ta bude qofar taja da baya da sauri Aseem ne tsaye cikin shirinsa na tafiya aiki da tarkacen laptop da takardu a hannunsa.
Qasa tayi cikin ladabi tace “ina kwana” Idanunsa ya dauke daga kanta ya juya ya fara tafiya saida ya kusa step din benen sannan yace “Mimee tana jiranki kije ki hada mata break” wani abune ya caki zuciyarta tana kallonsa ya fice hawaye suka sulalo mata na baqin ciki wannan baqin qasqanci da mahaifinta ya siya mata Allah wadarai dashi, komawa tayi ciki ta dauki wayarta da keta ring ganin number ya mudam tasan Innah keson mgn da ita ta kara a kunnenta a sanyaye, yanayin yanda tayi sallama ya tabbatarwa Innah ba qalau ba taja ajiyar zuciya tace “ya akayine ma’uh na?” Cikin kuka ta durqushe a qasa ta kwashe duk abinda Aseem din ya fada mata ta sanar da Innah Sosai Innah ta girgiza dajin wannan qasqanci da rayuwar Asma’uh ta tsinci kai a ciki amma a fili sai tace “duk a cikin ibada ne kiyi hqr zakiga ribarsa a gaba don Allah badon niba ki mayar da komi ya zama ba komi ba koda anyi abinda ya kamata ki kalla ki kawar dakai wataran sai labari”

 

Cikin mutuwar jiki tace “yanzu Innah yimata zanyi?” Murmushi Innah tayi tace “qwarai kuwa yi zakiyi domin Allah ai lalura ta kori komai kema wataran zata taimakeki” haka inna ta rinqa tausar Asmah hardai ta hqr ta saki ranta ta miqe ta dauki hijjab dinta ta nufi part din Mimee ta qwanqwasa aka bata izinin shiga ta bude ta shiga cikin nutsuwarta me tsayawa a rai tayi sallama, a qasan maqoshi mimee ta amsa tanajin wani kishi na taso mata duk yanda su Saimah sukazo suke koda kyawun matar yayan nasu ganin idonta sai taga tafi haka duk da kasancewar ba fara bace amma a sahun kyawu dole ta karbi lambar yabo.
Rusunawa tayi tace “Ina kwana Aunty….” Numfashi Mimee ta sauke tace “normal ina fatan Honey ya zayyana miki aikinki a gdannan ko?” Jinjina kai tayi Mimee tayi murmushi tace “ok sai a tashi a fara ina buqatar kunun tsamiya ne da qosan bread” miqewa tayi ta fara neman kitchen din ta nuna mata tace “ai basai kin wahala ba da part dinki da wannan duk iri daya ne bambamcin kawai a matsayi yake ” duk da Asmah tasan mgn Mimee ta fada mata bata kula ba ta nufi kitchen din a hargitse yake gabadaya kayan sunyi qura ta jinjina kai ta lalubi tukunya ta dora ruwa ta rinqa bude kitchen cabinet din har allah yasa ta samu duk abinda take buqata ta hada ruwan kununta sannan ta debi surfaffen wake tasa masa ruwan zafi ya tashi ta hada tattasai da albasa da attaruhu da duk abinda tasan zata buqata ta wanke ta zuba a blander, a wannan lkcn ilimi ne kawai yake aiki bawai sani ba duk kayan aikin baqine a gurinta hakanan dai ta ganganda ta gama hada komai ta Jere a dinning din ta koma kitchen din ta fara gyaransa saida ta gyareshi tsaf ta wanke kayan da sukayi qura ta mayar dasu muhallinsu sannan ta fita parlor shima ta gyara tayi duk abinda ya dace sannan ta juya zata tafi taji Mimee dake zaune tana kallo tace “ki hau sama ki gyara masa dakinsa”

 

Tuni wani riqaqqen baqin ciki ya cika zuciyarta taji kamar tayi tafiyarta kalaman Innah ne kawai suka sata juyawa ta nufi saman ta bude dakin farko Allah kuwa ya taimaketa shi dinne ta shiga ta fara gyarawa saida ta gyareshi tsaf kayan da ya cire duk ta ninke tasa a kwandon zuba kayan wanki ta wanke bathroom ta fesa turare ta janyo ta fito ta rusuna gaban mimee tace “na gama” daganta kai kawai tayi ta juya tayi tafiyarta ta koma nata part din ta gyara ta nemawa kanta abinda zataci ta dawo ta zauna a parlor ta kunna kallo tana kallo tana karyawa bayan ta gama ta haura saman tayi wanka tayi kwanciyarta

 

Wayar tace ta dauki ruri ta daukota ta duba taja ajiyar zuciya Dijanta ce ta kara a kunnenta tayi sallama dijah ta amsa da sanyin murya tace “inanan inata tausayinki ance mazan da sukasan dadin mace sunfi rashin tausayi a daren farko Ma’uh nikam naci wuya ji nake kamar kar a qara” sarai ta gane inda ta dosa tayi dariya me qarfi tace “lallai inayi murna kice har Ali yaga Ali?” Ajiyar zuciya Dijah tayi tace “yanzu ke haka kuka kwana yana kallonki kina kallonsa duk irin maqudan kudadan daya kashe Allah bai fanshe ba?”

 

Numfashi taja tace “nifa banson gulmarki nan ina ruwanki tunda kedai anyi miki abinda kikeso” sanin hali yasa Dijah cewa “kekam kin fiya masifa daga na kiraki mu jajantawa juna zaki kama yimin fada to ai shikenan sai kiyita yi nidai nazama cikakkiyar mace yarinya ko iyanan alamu sun nuna nafiki” murmushi tayi tace “to meye na gorin abinnan da ba dambe ba kowacce mace ma tana zuwa gurin lkc dai igiya uku ke gareki nima itace dani saboda haka banga bambamcin ba”………
Kashe wayarta tayi ta gyara kwanciyarta tasha bacci sosai har wajen daya sannan ta tashi tayi sallah ta gyara gadonta ta nufi part din Mimee har yanzu tana kwance inda ta barta mamaki ya cika Asmah tayi mata sannu da gda ta dago ta kalleta saida gabanta ya fadi ganin irin kwalliyar da Asmah ta caba cikin wani tsadadden less dake cikin lefenta, sarai take kallon Asmah tun daga sama har qasa ta zubawa hips dinta ido tuni Asmah ta fahimci kallon qurillar da takeyi mata tayi qaramin murmushi a ranta tace “jira dai madam ba damuwata mijinki ba amma dole ne kisan nafi qarfin matsayin da kuka ajeni”
Dagowa tayi tace “me kike buqata?” Iska Mimee ta furzar ta qanqance ido tace “kewai bakisan matsayinki bane a gdannan? Waye ya baki damar kwalliya?” Dagowa tayi ta dubi mimee tace “wai dake naji sunanmu daya a duniya Matan Dr Aseem Shaheed shiyasa nabawa kaina yancin kwalliya a gdan mijina…..”

 

Wata muguwar tsawa mimee ta daka mata tace “Ubanwa yace miki matsayinmu daya dake yar matsiyata? Ke mece a mata da har zaki hada kanki dani??” Abinda Asmah takeso kenan ta juya cikin salonta na iskanci tana kada mata mazaunai tace “In kinga dama ma ki kirani da tafi haka nidai inajin kaina matsayin matar Mijinki bawai isar ki ce tasa na qudurta yi miki wannan aikin da kuka bani ba not sister tausayinki ne a matsayinki na patient kuma naji mijina yace cikine dake zaki haifa mana sanyin idaniya” tsayawa tayi ta juyo tace.
“Bari kiji wani abu ko Maryam naso ko bataso Asma’uh ta Aseem Shaheed ce zabinsa ce sannan inayi ne don farin cikinsa tabbas zanyi komai indai zaisa mijina abin alfaharina Happy domin nasan zamusha mango harda gwanda ke har water milon zan yanka nabashi a baki…..”
Dafe kuncinta tayi da sauri ta dago sukayi ido hudu da Aseem dake tsaye, ya hade rai sai huci yakeyi maimakon tayi qoqarin yin wani abu sai kawai ta shammaceshi ta fada jikinsa ta qanqameshi ta rushe da kuka, raunin Aseem kenan A duniya baya qaunar kuka a cikin kukanma ya rasa masifar da tasa indai Asmah zatayi kuka sai yafi dagansa hankali fiye da yanda kukan kowa yake dagansa.
Sake qanqameshi tayi tana tura masa nononta a qirjinsa tuni baisan sanda ya dagata ba cak ya nufi saman da ita Mimee na tsaye sake da baki tana kallon ikon Allah suna shiga ya ajiyeta saman resting chair ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa a ransa yanajin zafin kukan da ta zauna tanata rerawa har wani qara sauti takeyi, badan ya gaji da wankan ba ya dauro towel ya fito yace “oh gud ki daina wannan kukan haka na fada miki banso ko?” Ajiyar zuciya ta rinqa jerawa ya tsugunna gabanta ya kamo hannunta yace “ki daina yi mata rashin kunya duk abinda zakiyi ya tsaya iyakar ni dana daukoki” miqewa tayi zata fice ya fincikota da qarfi ya hadata da bango ta saki qarawa hawayenta qarfi tanajin sanda yasa hannu ya shafa shatin inda ya maretan yace “kinga gurin har ya tashi” tureshi tayi ya sake ruqota ya hadata da qirjinsa ya murdawa qofar key ya matseta sosai a sanyaye yace “me kika bawa Mimee taci da safe?….” Bai gama rufe bakinsa ba yaji an turo qofar an shigo, ya saketa d sauri Idanun mimee akansu wani murmushi Asmah tayi tace “Insha Allahu bazan qaraba kayi hqr kaji mijina” tana fadin haka ta juya ta fice tana yiwa Mimee Murmushin qeta, kitchen ta wucce zuciyarta tas ta fara hada abinda zata girka lkcn uku har da rabi tayi tuwon shinkafa ta dora ta rage gas din ta fice ta nufi part dinta tayi sallah da gayyah ta sake wanka ta canza kaya ta fito ta koma taci gaba da aikinta miyar zogale tayi musu ta sake yi musu jallop din taliya ta jere musu a dinning ta zuba a nata a collar ta bude qofar baya tayi ficewarta tanajinsu sunata bala’i itadai ko a jikinta an qudurta tayi ko zai rinqa zagin iyayenta bazata sake Mimee ta fahimta ba gara idan sun kebe sucinye iyayensu ma…..

 

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

 

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: https://chat.whatsapp.com/IJkh1cP8h62Avsz2Zrcr2x

 

_*Zarrah*_

 

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

 

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button