Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 6

Sponsored Links

YANCI DA RAYUWA

©️®️ Hafsat Rano

Page 6

Related Articles

***Part dinsu ya wuce direct babu kowa a gidan suna baya dan haka babu wanda yaga shigowar sa. Dakin sa bude yake a gyare tsaf ya ajiye backpack din sa a saman sofa ya kwanta rigingine duk gajiya na saukar masa.
Abubuwa biyu zuwa uku ne suke masa yawo akai tun sanda ya diro Nigeria abubuwan dake damu da nukurkusar zuciyar sa, akwai babban al’amarin da yake jiran sa tabbas ya sani a wannan dawowar da yayi sai dai bashi ne a gaban sa ba yanzu, duk da yana da matukar muhimmanci ya sakashi cikin jerin abinda ya kamata ya dame shi din amma dole zai bashi kafa yayi focusing gaba daya akan harkar business dinsa da na AJI sai kuma rayuwar sa da yake jin yana da bukatar yin wani abu na daban.
Kusan mintuna goma sha biyar ya dauka a kwance kafin ya mike ya shiga zare kayan jikinsa a hankali yana kallon babban frame din da ke dauke da family picture dinsu na yarinta a lokacin da be san komai ba sai rayuwa irin ta jin dadi da walwala.
Girgiza kai kawai yayi ya wuce toilet ya yi wanka sannan ya dauro alwala yazo ya zura sabuwar milk jallabiyar sa da ya siyo a saudiya ya bada bashin sallar da ake bin sa sannan ya dauki wayarsa ya kunna ta, ya lalubi number Saddam ya kirashi yace suzo su dauke shi ta gate din baya. Kusan mintuna goma suka karaso ya kirashi ya sanar dashi ya tashi ya dauki wayarsa guda daya sannan ya fito ya sake bin bayan. A daidai wajen da yaci karo da ita ya tsaya yana kallon wajen, babu abincin an share an gyara wajen, dakin da yaga ta shiga ya kalla mamakin sa na karuwa, tabbas tana da alaka da gidan sai dai ya lura akwai wani abu game da ita tun daga kan shigarta da yadda ta rude ta rikice akan kuskuren da ya faru, yasan yadda tsarin gidan nasu yake akan masu aiki da yadda mummy take bautar dasu sai dai be taba ganin irin haka ba. Wucewa yayi kawai zuwa gate din ya tarar da me gadin wajen a zaune ba kamar dazu da ya shigo ba duk da yaji motsin sa a kusa amma be ganshi ba.
Da sauri ya mike cikin matukar mamaki sai kuma ya russuna ya gaishe shi har kasa.

“Ina ka shiga dazu? Har na shigo baka gate din.”

Rudewa yayi cikin in-ina yace

“Bayi na zaga wallahi.”

“Ka kula sosai.” Yace yana wuce shi, da sauri ya bishi ya bude masa kofar maimakon ya fita sai ya tsaya ya juyo

“Wanchan building din, su waye a ciki?”

“Wanchan?” Ya nuna da hannun sa

“Eh.”

“Cook din bangaren Hajiya ce sir, yarinya ce karama me hankali.”

Ficewa yayi kawai be sake magana ba, ya samu Saddam a tsaye yana jiran fitowar sa, hannu ya mika masa alamun su gaisa amma sai ya ki karba ya duka ya gaishe shi ya amsa yana fadawa bayan motar, ganin haka yasa da sauri shima ya shiga gaba driver ya ja suka bar unguwar.
Sai da suka daidai ta a titin sannan Saddam ya juyo bayan yace

“Oga ya hanyar? An dawo lafiya?”

“Alhamdullillah, me yasa baku zo kunyi picking dina a airport ba?”

“Wallahi Sir Hajiya ce tace mu barshi zata tura daga nan, gashi wayar ka a kashe shiyasa ban ma sanar da kai ba, but muna unguwar sanda kuka iso ma dan naga shigar ka.”

“Ya ake ciki? Ina maganar mu ta kwana? Kasan na fada maka ba zan taba tambayar ka komai akai ba, nasan kayi abinda ya dace kuma nasan zan samu kyakkyawan labari.”

Sai da gaban Saddam ya fadi, duk da dama yasan za’a yi haka amma be tunanin a yau yau ba yana dawowa.

“Ina jinka, don’t tell me an samu matsala.”

“Wallahi sir, da farko komai yana tafiya daidai har school din da take zuwa da komai na sani, but daga baya sai komai ya lalace, Alhaji yasan duk zuwan da mukeyi yasa an kore su daga gidan sannan ya sa aka batawa mahaifin ta suna, sannan…”

“Ya Isa!!!!

Yace cikin karaji, hannun sa ya dunkule ya daki kujerar gaban motar, har sai yaushe zai kyale shi? Me yasa yake so ya kuntata ma rayuwar sa har haka. Dafe kansa yayi da hannu biyu zuciyar sa tamkar zata hudo kirjin sa ta fito saboda tsananin bacin rai, me yasa zai lalata musu rayuwa, akan me bayan shi duk abinda yake be taba tunkarar su ba, duk dan yana gujewa halin mahaifin nasa, yana masa matukar biyayyar da wani irin tsoro da gwarjini.

“Sorry sir.”

Saddam yace da sauri jin yadda ransa yayi matukar baci, abinda yake tsoro kenan, shiyasa ya kasa sanar masa duk da dama yace masa baya son sanin komai.

Wayar sa dake hannun Saddam din ce tayi kara, da sauri ya miko masa wayar ganin me kiran nasa,kin karba yayi ya maida idon sa ya kulle su ruf zuciyar sa na tafasa sosai.

“Sir Alhaji ne.”

“Pick it.” Yace still idanun nasa na rufe, hannu na rawa Saddam ya daga

“Kana ina?”

“Alhi barka da dare.”

“Ina Rafeeq din yake?”

“Baya kusa ne, zan fada m…”

Kit ya kashe wayar,ajiyar zuciya Saddam ya saki dan cike da tsoro ya daga wayar ba abun yace ba zai daga ba ya samu matsala gashi dagawar ma daidai take da sanadin aikin sa.

Yawo suke a titin su sauka wannan su hau wannan sai da yaji zuciyar sa ta sakko kadan sannan yace su kaishi Apo, suna zuwa ya sauka ko wayar sa be dauka ba sai Saddam din ne ya biyo shi da ita dan baya so ta zauna a hannun sa AJI ya sake kira yanzu ma dama tunda suka taho Asim da Aneesa suke kira be ce ya daga ba. A falo ya ajiye masa wayar ya jawo masa kofar ya fito yana sauke ajiyar zuciya.
A falon ya bar wayar ya wuce bedroom dinsa ya kwanta yana kashe hasken dakin ya zama dim dan baya bukatar hasken ko kadan ga wani irin ciwon kai da yake damun sa tun kwana biyu dama da suka wuce. Shi da kansa be san adadin dadewar da yayi a kwancen ba sai da ya soma dawowa daidai sannan ya mike ya fito living room din, ya wuce kitchen ya duba ko zai samu wani abun ya dan ci sai yaga ledoji masu tambarin Uber Eats. Aikin Saddam ne dan haka ya bude ya dauki abinda zai ci yayi microwaving ya dawo falon ya zauna sai a sannan ya dauki wayar sa ya tarar da missed calls masu tarin yawa. Kiran Asim ya fara bi yana zaune a hotel room dinsa ransa babu dadi da abinda Rafeeq din yayi wa mummy din, a kalla tunda har ta yi inviting mutane be kamata ace yaki zuwa wajen ba ko da na minute biyu ne gashi duk kiran sa da yake yaki dagawa abinda ya kular dashi kenan.
Da sauri ya daga wayar yana ganin shine be jira wata magana ba ya fara mita.

“Ka kyauta! Sai yanzu kaga daman kirana, kana ina?”

“I’m so sorry bro, wallahi abun ne yafi karfin kai na, ina Apo”

“Me ya faru? Naji muryar ka haka haka, are you sick?” Ya fada cikin kulawa jin muryar Rafeeq din kasa kasa.

“I’m fine lafiya ta kalou, wani babban al’amari ne ya faru but alhamdullillah yanzu, I’m ok.”

“Huh! Shikenan ka huta sosai, gobe zan dawo nima. Zan yi wa Mummy bayani dan duk ta damu. Please ka kula da kanka. Na sanka da saka damuwa, gobe zan dawo sai mu duba matsalar muyi maganin ta.”

“Ok thank you. Sai ka dawo.”

Ajiyar zuciya ya sauke me karfi, bashi da kamar dan uwansa a duniyar nan kaf, Asim shine kadai wanda ya gane shi, ya fuskanci yanayin sa yake kuma kaunarsa. Akwai shakuwa me karfin gaske a tsakanin su. Sai dai shi yana da dannewa da nuna halin ko in kula ba kamar Asim din ba. Openly yake nuna kulawar sa ga duk abinda yake so din. Har yanzu be gama sanin challenges din rayuwa ba tunda be taba fuskanta ba. He’s so lucky yana da duk abinda yake bukata a tare dashi, Kuma duk tsaurin AJI baya cika takura masa kamar Rafeeq din.
Abincin ya dauka ya soma ci sai wani tunani ya fado masa. Idan har ita din househelp ce kenan abincin da zata ci ne ya zube dazun, yasan kuma ba lallai ta sake samun wani da zata ci ba, duk sai yaji ya damu sosai. Wayar sa ya dauka ya kira Saddam lokacin tara har da rabi. Suna compound din gidan suna hira da gateman da driver dan tunda suka ajiye shi basu tafi ba dama driver a gidan yake Saddam ne dama yake tafiya shima yau din be tafi ba tunda be san yanayin da Rafeeq din yake ciki ba. Yana ganin kiran sa ya daga da sauri.

“Ka tafi ne?”

“No Sir, ina nan.”

“Ok, come inside please.”

Yace masa ya kashe. Tashi yayi ya haura balcony din ya tura kofar ya shiga falon.

“Kayi min order same food da kayi order dazu.”

“Ok sir.

” Yace ya dauki wayar sa ya shiga yayi order din, suka ce zai iso nan da 15min. Yana zaune rider din ya kawo suka tashi a tare suka fito, Saddam ya karba yace driver ya fito da mota suje Asokoro.

***Noor na zaune ta gama dukkan night routines dinta tana mammatsa kafarta dake mata ciwo saboda tsabar tsaiwar da tasha yau, ga wata irin yunwa dake nukurkusar ta bata da abinda zata ci dan ko da rana bata ci komai ba saboda aiki gashi dan abincin nata ya watse a kasa dole haka zata hakura ta kwanta. Ruwa ta mike ta sake debowa a sink din toilet tazo tasha sannan ta kashe wutar dakin ta kwanta a kasa kan sallayar ta dan mafiya yawan lokuta a kasan take kwanciya dan ta riga ta saba ma. Mintuna kadan da kwanciyar tata taji kamar ana mata knocking a jikin kofar ta, firgigit ta bude idon ta, ta sake kasa kunne ta tabbatar knocking din ake yi.

“Na shiga uku.” Tace tana dafe chest dinta. A hankali ta mike ta matsa jikin window din dakin ta leka ko zata ga wanda ke knocking amma bata iya hango kowa ba. Hijab dinta ta dauka ta saka sannan ta matsa jikin kofar a hankali tace

“Waye?”.

 

#thelovetriangle💕

 

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
08030811300

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button