Mijin Malama Book 2 Page 43
Aisha Baby Novel: Khalil bai dawo da Alhassan ba sai ƙarfe biyu na dare, kamar yadda ya fita dashi, yanzu ma yana goye a bayansa ya kama windown bedroom ɗin Jee ya hauro, gently ya kwantar da yaron a tsakiya shi kuma ya zauna gefe, wani irin kyakkyawan murmushi Khalil ya y, wani irin nutsuwa na saukar masa, a ransa yana jin ya samu abokin hira da cin kai, domin basu baro Orphanage ba sai da sukai kaca-kaca da parlon part ɗin John, suka sauya masa kama su ice-cream, chocolate, tea butter cookies komai suka watsar a parlorn a hankali kuma ya ɗauke Alhassan suka gudu jin John yana fitowa ya san kuma Faɗimatu ya bari da aiki for sure.
Khalil raya daren ya yi yana kallon Matarsa da kuma fitinannan ɗan shi Alhassan, idan ya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan, deep down na zuciyarsa yana son ganin biyunin Alhassan wato Al’hussain yaga ya yake shi kuma? Idanunsa zube a fuskarta yaga tana ɗan marairaicewa kamar bata jin daɗin kwanciyar, ya ɗan matsa kaɗan tare da sanya hannunsa a saman goshinta yaji zafi sosai, cike da tausayawa ya ɗan rausayar da kansa gefe guda yana kallonta da wani sabon yanayi ga wani so da ƙaunarta da a kullum yake ƙara narkar masa da zuciya, a yanzu kuma idan ya ce zai taɓa ta to wlh ba zata iya kwatar kanta ba, kuma dole asirin shi ya tonu duk da ashirye yake da hakan, but not today dole ya riƙe kansa.
“My everything, ƴar Aljanna” Ya yi mata peck a goshi a hankali ya ce “Thank You,for everything” Gently ya miƙe har zai fita ya sake ɗaukar farar powder ya shafa a fuskarsa, a nutse cike da kamala hannunsa zube cikin Aljihu ya nufi waje, luckily yaga ƙofar part ɗin General a buɗe, ya ɗan tsaya yana tuna maganganun General da Zaleehat yana ganin rashin adalci ƙarara, domin tun a asibiti jikinsa ya bashi akwai wani abu a ƙasa yadda Zaleehat keta kallon General kuma yana fita harabar asibiti yaga Bilal, a hankali ya nufi cikin part ɗin yana shiga bedroom General na fitowa daga bathroom ɗaure da towel a ƙugun shi, idanunsa ya sauka akan Khalil dake sanye da farar kaya ga farar powder a fuskarsa, jikin General ya fara rawa, domin yasan Khalil is dead already, babu mai kama da shi, idan ba Aljani ba to fatalwar Khalil ce. Yadda jikinsa ke ɓari da kyarma ya sanya yaji cikinsa na juyawa, cikin rashin sani towel ɗin ya zame ya faɗi ƙasa, neman abin kare jikinsa yake amma tuni towel din ya yi nasa wajan, Khalil duk miskilancin shi ji ya yi kamar ya tuntsire da dariya ganin General Alpha Bello khan! Tsaye a gabansa kuma naked.
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!! Kai da kake kabarinka me ya fito da kai?” Khalil ya buɗe baki yana zare ido kansa a hargitse ya ce “Matata!” General ya ce “Mata kuma? Ina matacce ina mata?” Khalil yana matsawa wajan Alpha tare da miƙa hannu kamar zai kama shi ya ce
“A wajanka nake matacce, a gurinta mutum ne mai numfashi, ka aureta amma ruhina yana tare da ita dare, rana,safe, yamma, ba zan barta ba” Zufa ta dinga yankowa Alpha yana jin kamar ya saki fitsari ya saka hannu ya daddafe mararsa ya ce “Amma ba adalci bane, ka riga da ka zama matacce kake bibiyar matata?”
“Matarka ko tawa? Bari ka zama matacce sai mu yi daidai da kai” Ya miƙa hannu zai damƙo shi, Alpha ya saki ihu yana “Na yarda matarka me kake so nayi yanzu?” Khalil ya karkace baki ya ce “Ka cire wannan pictures ɗin na Matata a bedroom naka, hakan zai sanya ruhina cikin salama, ƙamshin su da naji ya jawo fatalwa ta nan” Ya kai maganar da ƙyar ƙirjinsa na bugawa saboda yadda maganar tayi masa tsayi sosai.
“Yanzu Insha Allahu zan cire” Yana faɗin haka ya fara cire all frames ɗin hotunan Majeederh dake bedroom ɗinsa. Idanunsa jajur ya zube gaban Khalil ya ce
“Ka tausaya mini, wallahi wallahi ina son Malama Majeederh, ina son zama mijin malama na har abada, da soyayyarta na rayu shi ke ɗawainiyya dani, ban taɓa son wata a duniya irinta ba, ba kuma zan taɓa so ba don girman Allah ka bar mini ita i so much love her!” Kau! Khalil ya ɗauke General da wani irin mahaukacin mari wanda ya sake tabbatar masa wannan ba hannun mutum bane, without allowing him to recover ya sake sauke masa wasu tagwayen maruka, nan da nan idanunsa ya yi wani jaa gefen baki ya fashe, jini ya kwanta fuskar ta yahe tare da kumbura Khalil ya fara loosing control ɗinsa a lokacin jin yadda wani ƙato yake cewa yana son matarsa ta sunna uwar yaransa? Alpha ya ce “kiyi komai fatalwa, amma karki azabtar da zuciyata ta hanyar rabani da wacce nake muradi, na ƙaryata matata Zuleehart gudun kada Majeederh ta ji ina da aure taƙi accepting nawa as her husband” Khalil ya wargaza kansa, yana juya rinannun idanunsa a hankali ya nufi wajen General ya kama hannunsa kamar zai miƙar da shi tsaye, wani irin ihu da kururuwa ya yi lokacin da ya ji ƙarar karyewar hannunsa biyu! Wani fitsarin azaba ya shiga zubo masa, ya taɓa jin harbin bindiga har babu adadi, saran maciji a daji, amma bai taɓa jin azaba irin wannan ba, jikinsa ya jiƙe sosai da zufa, Khalil ya ce “Uwar data haifeka nagartacciyya ce, baka san darajar mace ba, ka gaggauta ƙaryata kanka ka wanke zunubanka da gasgata zancen Zulee” Yana faɗin hakan ya saka hannu ya kashe wutar ɗakin, General ya fara ihu yana faɗin “Ƙarya nake, matata ce ita ɗin uwar yarana,Bilal, Waheed da Dina ce, nine mijinta ƙarya nake muku…,” Daidai nan aka kunna wutar bedroom ɗin, tuni kuma Khalil ya haura ta window ɗakin Alpha. Halin da Uncle Bello yaga ɗansa ya gigita shi fuskarsa ta wani irin kumbura bakinsa ya karkace, Maman Alpha tayi tsaye tana mamakin me ya same shi? “General lafiya?” General ya girgiza kai ya ce “Abba ba lafiya ba, matata ce ita ɗin matata ce” Uncle Bello ya ce “Wace matar taka?” Ya ce “Zuleehart, wallahi Allah kenan she’s my wife, Bilal, Waheed, Dina ƴaƴana ne su” Wani irin bahagon mari Uncle Bello ya zubawa General ya nuna shi da yatsa ya ce “Ka bani mamaki, dama zuciya nata raya mini akwai wani abu, sai dai baka cuci Zuleehart ba kanka ka cuta, ka sheganta yaranka na cikinka da bakinka” Alpha ya ce “Ban sheganta su ba Abba” A hargitse ya ce “Ka ce baka son su, baka da haɗi da su, ba yaranka bane hakan daidai yake da sheganta su, shashasha kuma sai ka saki Majeederh” General ya runtse idanunsa abubuwa da yawa sun haɗe masa zuciyarsa kamar zata fito waje ya ce “Abba kayi mini komai banda raba zuciyata da ƴar uwata, banda rabani da matata” Uncle Bello ya saki tsaki tare da ficewa daga ɗakin, Maman Alpha ta nemi waje ta zauna tana kallon shi a hankali kafin ta sauke ajiyar zuciya.
Tsirgen da Alhassan ke yi a gadon shi ya tilasta mata miƙewa zaune tana jin wani irin kasala a jikinta, bata da kuzari ko kaɗan ga masifaffen ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious da take mutuwar so da ƙaunar shaƙa a hancinta, ta kifa kanta bakinta ɗauke da addu’a, jin motsi da ƙarar sun yi yawa ya sanya ta juya idanunta ya sauka akan Alhassan dake zaune ɗare-ɗare akan window yana ƙoƙarin dira ya haura ƙasa, ta miƙe da sauri tana zaro kyawawan idanunta waje wanda suka ƙara yin laushi sosai, tana zuwa ta ce “What are you doing my love?” Alhassan ya lumshe idanunsa masu laushi yana girgiza kai ya ce “Aby” Majeederh tayi shiru sai kuma ta ce “Aby kuma Love?” Ya sake nuna mata ƙasa ya ce “Nan Aby” ta ce “Get down, zaka ji ciwo” Ya zuba mata ido kamar yadda Khalil yake idan ya san zai aikata abu bata ankare ba taji ya dirga ƙasa ya faɗi, wata ƴar ƙara ta saki “Na shiga uku” Ina Alhassan ya gane haura katanga? Daga ita sai Lingerie night wear white colour cinyoyinta a waje ta ɗauki hula mai gashi gashi ta saka, ƙafarta cikin Scuff faux-shearling slippers ta nufi main parlour.
“Majeederh ina zuwa haka?” Ta juya ta kalli Yaya Bilkisu sai kuma ta ce “Alhassan ya kama window ya haura, zan ɗakko shi ne” Maman Alpha ta riƙe haɓa ta ce “Wanne irin haura window ni ƴar nan? Mun shige su” Ta girgiza kai ta ce “Daman yana yi?” A hankali ta ce “A’a” Yaya Bilkisu ta ce “Khalil ya tafi Khalil ya dawo” a mamake Majeederh tayiwa Yaya Bilkisu wani hargitsatsen kallo sai kuma ta nufi waje, daidai nan Alpha ya fito daga mota fuskarsa jajur saboda azabar ɗorin da akai mata, ga fuska a kumbure. Ya zubawa Majeederh Idanu cike da ƙauna, ga wani irin masifar kyau da tayi ta ciko sosai ba zaka ce ta shayar da yara har biyu ba, fatar jikinta sai glowing take da wani shinning. Sam bata kula da shi ba ta nufi bayan window ɗinta, amma ba Alhassan babu mai kama da shi a tsorace ta dinga dubawa amma ko inuwar shi babu, ta fara kuka tana kiran sunan shi Maman Alpha da Yaya Bilkisu suka fito, haka Uncle Bello da yake ƙoƙarin fita wajen aiki, suna tsaye sai ga Al’hussain ya fito da sauri Yaya Bilkisu ta ce “Ɗan banza gashi nan ai” Majeederh ta kalli ƙwayar idanun Al’hussain sam ba irin ta Khalil bace Alhassan kuma komai nasa irin na Khalil ne ta ce “Al’hussain ne wannan, na shiga uku where is my son” Mamakin yadda bata ɓoye son yaran a fili suke, suka shiga dubawa lungu da saƙo amma baya nan basu ankare ba su kaga Majeederh ta sulale tare da faɗuwa a sume, da hanzari Uncle Bello ya kira family Doctor. Jigum sukai kowa da tunanin da yake a ran shi, Yaya Bilkisu ta ce “Mun shiga uku ina wannan yaron ya yi?”
“Tunanin da nake ta yi kenan yaya, sai dai wani ya ɗauke shi bayan yaran ko entrance bata barinsu fita balle compound?” Maman Alpha ta furta cike da damuwa haɗi da zullumi na rashin sanin abin yi, da rashin gane takamaimai inda Alhassan ɗin ya shiga, saboda shi yaro ne mara yadda ba mutane, ba ruwan shi da kowa idan ba Majeederh ko Al’hussain ba. Yaya Bilkisu ta ƙara shiru ta ce “Ni kakannin yaron na masarauta ma nake ji, yadda suka ƙwallafa son duniya akan yaran nan musamman miskilar matar nan ai sai ta saka a ɗauremu” Uncle Bello ya sauke numfashi ya ce “Yanzu lafiyar Majeederh muke son fara gani tukun” Dr daya gama bincike da gwaje-gwaje ya ce yana zuwa wajan 20 minutes ya ɗauka kana ya dawo lokacin tuni Uncle Isma’il ya zo Dr na murmushi ya kalli Majeederh data farka ya ce “ku bata tea yanzu” A hankali ya juya ya kalli General Alpha dake zaune ya ce
“Congratulations General, your wife is pregnant na kimanin sati uku” General ya yi saurin kallon Majeederh ita kuma tayi saurin kallon cikin nata tana shafawa a hankali, lokaci guda wani irin sanyi da farin ciki ya fara mamaye zuciyarta ta san ba cikin kowa bane sai na ruhin mijinta Khalil, ta nemi dukkan wani ƙuncin ta rasa a zuciyarta a hankali ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suna zirarowa ta cikin idanunta. Yaya Bilkisu ta kalli Dr ta ce “Dr ciki fa? Na sati uku to yaushe Majeederh ta tare har ta samu nutsuwar ɗaukan ciki?” Innati tayi ƙasa da murya ta ce
“Bana faɗa miki maye bane? Gashi nan ya turmushe ƴar mutane ya ɗurka mata ciki, ita kuma dake kamar matar ayu take har ta ɗauki ciki? Yanzu zamaninmu ayi haka sai fa mace tayi shekara ɗari ko yatsa mijinta bai riƙe mata ba” Innati ta rushe da kuka ta ce “Ina zamu kai wannan zunubin Balkisa? Muna cikin gidan nan akai iskanci hadda ɗaukan ciki fa? Ba dole iyaye suke sakawa yara idanu ba? Allah na tuba ban san komai ba nikam” tsananin shock ya sanya Alpha kasa magana idanunsa har duhu suke a sanyaye ya ce “Thank you Dr”
“Ba cikinsa bane, na ruhin mijina ne” Duka suka kalleta Uncle Isma’il ya ce “Thank you Dr, you can go?” Dr ya ce “Ok, Allah ya inganta” Dr na fita Uncle Isma’il ya ce “Kika ce me?” Ta ce “Ba cikinsa bane, na ruhin mijina ne shi ya yi min ciki” Tsit Innati tayi ta raƙube bayan Yaya Bilkisu, Uncle Isma’il ya ce “Majeederh kina da hankali? Kin san me kike cewa? Mutum ya rasu tun tuni amma kice wai cikin ruhin mijinki ne? Shin daman yanzu akwai fatalwa ne? Anya ƙwaƙwalwarki bata samu matsala ba wajan sarrafa tunaninki ba kuwa?” Ta dinga kallon Uncle ta girgiza kai sai kuma tayi murmushi ta ce “Lafiya lau nake, believe me Uncle wallahi cikin Khalil ne, kullum yana zuwar mini a mafarki, yana cewa daga kabarinsa ya fito yana faɗa mini ba zai iya barina ba, wallahi cikin Khalil ne” Kafin Uncle Isma’il ya yi magana wayarsa ta fara ringing baƙuwar number ya gani but a special digit number ya ɗauka ya miƙe da sauri ya ce “Alhamdulillah! Yanzu kuna compound tare da Alhassan ɗin?” Majeederh tayi saurin miƙewa tayi waje, gabaɗaya suka rufa mata baya har Alpha, tama riga ta mance kayan bacci ne jikinta gashi yanzu ko hular babu, gashinta ya baje ya sauka a saman kafaɗarta da goshinta ƙafarta ko takalmi babu ta nufi compound ɗin, cak tayi ganin wanda ta gani tsaye kamar ta gane shi, John ya yi murmushi yana ƙasa da kansa saboda yanayin kayan jikin nata, Uncle Isma’il ya ce “Kai ka kira? Ina Alhassan ɗin?” John ya matsa jikin mota tare da buɗe back seat, Alhassan ya fito da sauri yana sanye da wata farar shadda mai azabar kyau, hadda babbar riga an ɗora masa babbar riga da hula, Majeederh ta dinga kallon Alhassan gabanta na dukan uku-uku ya washe mata fararen haƙoran shi ya langwaɓe kai ya ce “Aby” Ya faɗa yana nuna mata ƙofar mota daidai nan Khalil ya sako ƙafarsa waje wacce take sanye da Derby shoe black colour, hannunsa dake ɗaure da Rolex ya riƙe ƙofar motar da shi, gently ya fito yana ɗan yatsuna fuska, sanye yake da dakakkiyar shadda gezner, ya ɗora jaddara a kansa, ya ƙara cikar haiba da kamala musamman ƙasumbar fuskarsa, ya tsaya a kan ƙafafuwansa yana zuba hannunsa a aljihu.
Innati da yaya Bilkisu suka kurma ihu tare da cewa “Wallahi ita ce, fatalwa, fatalwa” Innati ta ce “A’a ba fatalwa ba Fatale” Suka haɗa kai tare da yin gware, General wani irin fitsari ne ya kusa kufce masa ganin Khalil ya ƙara tuna masa da abinda ya same shi jiya, wani irin rikitaccen tashin hankali ya ruftawa zuciyarsa zufa ta dinga yanko masa, Uncle Bello da Uncle Isma’il salatin da duk yazo bakinsu suke furtawa a fili a kuma bayyane, Maman Alpha dai tayi tsaye tana son ganin ikon Allah domin wanda ya mutu baya dawowa. Kallon kallo ake tsakanin Majeederh da Khalil ko wanne zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, ita na ganinsa tsaye akan duga-dugansa yana sakar mata wani murmushi mai laushi, shi kuma bugawar zuciyarsa ta ganin shigar dake jikinta ne. Jee muryarta na rawa sosai ta shiga nuna Khalil da hannu “Ma…maa.. man?” Da gudu kuma tana ƙara fisge drip ɗin hannunta ta nufi wajansa, yana ganinta ya yi ɗan baya gudun kada su faɗi da wani irin ƙarfi ta faɗa saman ƙirjinsa tana ƙanƙame shi sosai tare da sakin wani raunataccen kuka, sukai baya kamar zasu faɗi ya yi saurin riƙo ƙugunta ya manne da nashi ya rungumeta da kyau a ƙirjinsa a hankali kuma ya tallafo fuskarta yana….[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: A zafafe cikin faɗa da wata dakakkiyar tsawa wacce ba a taɓa ji Uncle Bello ya yi ba ya ce “Kin yi kaɗan Barrister, baki da wannan ikon da hurumin, idan har ni na haifi Alpha, kuma Majeederh ƴata ce to aure tsakaninsu ya haramta har gaban abada wallahi tallahi” Yana faɗin hakan yana saka hannu tare da miƙar da Khalil tsaye ya kama hannun Majeederh ya sanya acikin na Khalil, da sauri Khalil ya damƙe hannunta yana sauk’e wata ajiyar zuciya. Majeederh ma ta riƙe hannun mijinta tana Jin kamar ta rungume shi ko zata samu sauƙi a zuciyarta, bata da tension ɗin komai a kanta, ta yarda komai ya faru da bawa hukuncin Ubangiji ne, ba wanda ya isa ya ɗora maka abinda Ubangiji bai nufa ba, wani abun lesson ne a rayuwarka. Maman Alpha ta share idanunta tana kallon mijinta ta ce
“Damuwar wasu ka sani banda ɗan daka haifa? Ashe zaka iya zuba idanu ɗan daka samar da shi ransa ya salwanta akan abinda kake da ikon mallaka masa?” Uncle Bello ya ɗaga mata hannu ya ce “Look! Barrister ban iya son zuciya ba, ba zan fara saboda Alpha ba, idan a matsayinki na Barrister mai kare hak’ƙin ɗan adam da talakawa wanda aka cutar bai sanya kin gane illar abinda kike shirin yi ba, to nima ba zan mara miki baya ba, General musulmi ne yaci ace ya yarda da ƙaddara ya yi kuma imani da ita” Ya juya ya kalli Khalil da kansa ke ƙasa ya ɗora kansa a wuyan Majeederh idanunsa a lumshe Uncle Bello ya furta “Ibrahim ɗauki matarka ka je, yanzu ne za ku yi rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali” Khalil ya ware idanunsa a hankali yana mai jinjina kansa.
Uncle ya ƙara haɗe hannayensu waje guda ya ce “Ibrahim da ga yau ka zama tsaki kume gefe na rayuwar Hawwa’u, ka ɗauka bata san kowa a duniya ba sai kai, ka zama garkuwarta, duk sanda Majeederh tayi kuka saboda kai i won’t forgive you, idan Majeederh tayi kuka saboda kai to daga ranar zaka san waye Bello,kuje maza kuje daga yau yanzu babu wata matsala da zata sanya hankalinku tashi, ko da akwai zan yi maganinta ba tare da saninku ba, Ubangiji ya yi muku albarka ya baku zuri’a ta gari ya wadataku da arziƙi mai amfani” Idanun Majeederh cike da hawaye ta rungume Uncle Bello ta ce “Na gode Uncle” Uncle ya shafa kanta yana jin sonta har zuciyarsa ya ce
“It’s my responsibility dear, ki kula da mijinki kin ji? Duk son da kukewa juna hakan bazai hana ku samun saɓani ba, ki kyautata masa, kiyi supporting nasa always be by his side” Ta jinjina kai, Majeederh ta kalli Alpha dake kwance gefen idanunsa na zubar da hawaye ta miƙa hannu zata taɓa shi Maman Alpha tayi saurin cewa “leave him alone” Uncle Bello ya ce
“Majeederh bi mijinki, I’ll talk to her ” Khalil ya ɗan matsa kusa da Uncle a karo na farko ya ɗan rusuna with so much respect, saboda Uncle ya masa abinda ba kowa zai masa ba, ya dinga tattaro abubuwan da zai furta a wajen yi wa Uncle Bello godiya da bashi haƙurin dukan ɗan shi da ya yi amma ya kasa, can ƙasa muryarsa so Calm ya ce
“I am sorry” Uncle ya shafa kansa ya ce “I wish you all the best and happiness in your life Ibrahimul-khalil” Khalil ya miƙe ya kama hannun Majeederh suka fita, suna zuwa corridor ya ji ta sake shi ta tsaya ya juya yana zuba mata narkakkun idanunsa, wanda suke cike da gajiya a hankali ya ɗaga mata gira alamar “Miye?” Ta ƙarasa da sauri ta rungume shi tana kwantar da kanta a ƙirjinsa muryarta na rawa ta ce “I love you, I love you Man, na ji tsoro!” Ya riƙo fuskarta yana kashe mata ido ɗaya, yana jin zuciyarta na bugawa, sun jima a haka kafin ya kama hannunta suka nufi reception, Alhassan na ganinsu ya tafi da gudu ya nufi wajen Khalil yana faɗin “Aby” Khalil bai saki Majeederh ba ya ɗauki Alhassan ya ƙarasa inda su Innati suke da su Abbu, Innati ta riƙe haɓa hannunta riƙe da bottle water mai ɗan iskan sanyi sai turiri yake ta ranƙwashi Alhassan ta ce “Algungumi to kai dai ba abokin arziƙi bane a gaskiya, wani abu ne kuma Aby?” Majeederh ta yi murmushi Mami ta ce “Har kun fito?” Ta ce “Eh Mami” Innati tayi ƙasa da murya ta ce “To ya naji ban ji wani ihu yana tashi ba?” Abbu ya kalleta da mamaki a hankali ya ce
“Ihun me kuma?” Innati ta ce “Na mutuwar Soja mana?” Abbu ya sake kallon Innati da mamaki sosai ya ce “Wani ne ya ce ya mutu?” Innati ta ce “To jira nake a fito da gawa fa? Ashe bai mutu ba? Zaman me yake ba gwara ya margaya uban kowa ya huta da rashin tawakkalinsa ba? Wai da gaske yana raye?” Ba wanda ya ce mata komai ta fashe da kuka sosai tana zare gefen zaninta ta ce “Bafa ƴar iska bace ni da zanna magana ana mini kallon wata arniyar legas, kawai a kira dreba ya kai ni gida duk sanda ya mutu na dawo” Khalil ya ɗauke idanunsa wallahi kamar an masa dole dole wajan furta “Zamu tafi” Mami ta ce “Tafiya kuma? Yau ɗin nan Khalil ko can gidanmu ba kuje ba” Jee ta ce “A’a zamu” Ta ce “To shikenan” Majeederh ta amshi Al’hussain ta rungume, Khalil ya kama hannun Baby Khalil su biyar abinsu sukai waje, Khalil ya kalli Majeederh sai ya ɗan kwaɓe fuska ta haɗe rai itama ya miƙa mata key ya ce “Plx” karɓa kawai tayi ta nufi wajen driver, bayan ta ajjiye Al’hussain a baya, baby khalil ma na baya, Alhassan na cinyar Khalil tayi Bismillah tare da yiwa motar key tai reverse a hankali ta harba motar zuwa bakin gate ganin zata nufi hanyar gidan Uncle Bello a taƙaice ya ce “Hubb Lodge Road” Ta kalle shi waya yake dannawa ta ɗauke kanta4d, a jikinta take jin duk motsinta akan idanunsa, tayi murmushi kawai tana mai ci-gaba da driving.
Suna zuwa daidai ƙofar gidan Barrister Aliyu Sufyan Khalil ya ce “Stop the car” Ta juya da sauri ta kalle shi bai kalleta ba har zuwa lokacin gashinsa a zube yake a baya da gefen fuska ya fito, tana ƙoƙarin fitowa ya sakawa motar key ya nufi gate ɗin gidan Barrister Aliyu, ya ɗan tsaya, daidai nan kuma manyan motoci na ƴan sanda wanda Khalil yama IGP Latif Mahdi waya yana buƙata, kasancewar IGP yasan khalil ya kuma san ba zai iya cutar da kowa ba dole akwai dalilinsa na yin haka, ya sanya ya buga waya kai tsaye aka turo, Majeederh na cikin mota tana kallon ikon Allah tana addu’ar Allah ya sa ba wani abu Barrister yama Khalil ɗin ba, Khalil ya shiga gidan tare da knocking ba jimawa aka buɗe Aaliyyah ta yi wani fresh saboda cikin jikinta, ta zare idanunta ganin Khalil ta ce “Kspider, Yaya Khalil?” Ya ɗan fuske dole shi Yaya ne ta ce “Come in,ka shigo” Ya ɗan yi jim sai kuma ya shiga, banda wani irin ƙamshi babu abinda parlon yake komai gwanin sha’awa, ya nemi saman sabuwar kujerar dake parlon ya zauna, ta miƙe ta ce “Bari na kawo maka drinks” Ya ɗan murza yatsun yana ƙarewa parlon kallo ya taɓe baki speaking calmly ya ce “Ina…,” Sai ya yi shiru ta ce “Yaa Aliyu?” Ya zuba mata idanu bai magana ba ta ce “Latifa?” Ya lumshe idanu ya buɗe ta ce “Tana bedroom ɗinta ta kulle, ai police ne suka zo kamata Yaa Aliyu ya hana tun daga nan ta shige bedroom ta kulle” Khalil ya miƙe yana zura hannu a aljihu ya zaro wani master key ya buɗe bedroom ɗin dake ta dawo down strairs da zama, yana buɗewa ya ce “come in” ba a ɗauki lokaci ba polices ɗin suka shigo, wasu manya guda uku amma mata. Latifa na ƙuryar gado taga an faɗo ciki hantar cikinta ya kaɗa ganin police ta fashe da kuka ta ce “Don darajar Allah da Annabi kuyi haƙuri ku yafe mini kuji tausayina don Allah..,” ɗaya daga ciki ta daki bakinta da ƙasan bindiga nan da nan jini ya fara zuba, suka damƙeta zuwa waje, Barrister Aliyu dake sakkowa ƙasa ya bi Khalil da kallo domin da farko bai gane shi ba, sai ya yi masa kama da actor’s ɗin Nollywood, domin ko fuskarsa ba a gani sosai sai jajayen laɓɓansa. Latifa ta kalli Barrister Aliyu ta ce “Sweetheart don Allah don Annabi karka bari su tafi dani na shiga uku na lalace dame zan ji? Daman nasan hak’ƙin Majeederh ba zai barni ba, Khalil Oga sir kayi haƙuri saboda Allah Majeederh ta yafe mini itama” Khalil ya saka hannu ya tura sumar shi baya yana kallon Latifa ya ce “To bata yafe ba, idan ma haka ne ni mijin malama ban yafe ba” Ta dinga kuka tana turjewa tana kallon Zaki yaƙi kallonta ta juya ta kalli Aaliyyah ta ce “Aaliyyah ki taimaka mini idan na je gidan maza ni kaɗai kashe ni za su yi”
“Sanda kike zuwa wajen boka kina k’ulla sharri saboda kawai ki cutar da ɗan adam, ɗan adam ɗin ma wanda ya yarda dake kin nemi taimako ne?” Aaliyyah tayi dariyar rainin hankali ta ce “Kinci uban ɗan iska a rainin hankali, ai uban kuturu ya yi kaɗan balle na makaho, ita rayuwa daman juyin wainar tanda ce, kuma rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba, billahi tashi ko ɗumi ba zatayi ba, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, maza gidan ɗan kande na jira ko zaman can zai wanke miki zunubanki”
Latifa idanun na zubar da hawaye ta dubi Aaliyyah dasu ta ce “Aaliyyah ni kike faɗawa haka?” Aaliyyah ta saki dariya ta ce “Warr, ke awa karan kaɗa miya? Ina ruwana da girmanki? Ai Karen Bana Shi ke Maganin Zomon Bana, kin rufe idanunki kin cutar da rayuwar wacce take matsayin uwa mahaifiya , duniyata, kin raina wayonta saboda kina baƙin ciki da baiwar da Ubangiji ya yi mata, idanunki sun rufe kin manta Sara da sassaƙa ba sa hana gamji toho”. Lafita ta ce “Haba Aaliyyah sharrin shaiɗan ne na gane kuskurena ki bani dama na wanke laifukana, ni ban ɗauke ki kishiya ba, ki bawa Oga sir Yaya Khalil haƙuri muyi zaman amana ki yarda dani don Allah” Aaliyyah ta zare Idanu ta ce “Ina ganin Kura da Rana yaya zan yarda ta cije ni? Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo, uhm wannan falsafar taki bata samu tunani mai kyau ba” Barrister Aliyu dai na tsaye, Khalil ya juya baya domin zai iya kaiwa Latifa duka shi kuma duk jikin da yake ɗauke da najasa da datti ba zai taɓa saka hannu akai ba, police ɗin suka ja Latifa har zuwa waje, Khalil ya juya zai fita Aaliyyah ta ce “Yaya Khalil Anti Jeederh fa? Ka zauna kaci abinci mana” Ya ɗan shafa kai clamly ya ce “No Thanks” Yana faɗin hakan ya juya saboda bashi da business da Aliyu, yana zuwa motar ƴan sandan na barin wajen kai tsaye kuma state C.i.d Khalil ya ce a shige da ita daga nan a shige da ita prison saboda yana da d’aurin gindi. Hankalin Majeederh ya tashi taso ko albarkacin baby khalil Latifa taci, ta dinga buga ƙofar Glass amma a rufe kafin a fitar da Latifa Khalil ya yi waya da gidan ƴan jarida na t.v dana redion Latifa tayi bayanin abubuwan data aikatawa Jee har yadda aka samu cikin da wanda ya yi shi, voice ɗin ya dinga zaga ko’ina dake live ne, abin ya yi trending cikin ƙank’anin lokaci, laifin Majeederh ya wanke a idanun jama’a da wanda suka aibatata da masu tsine mata, suka shiga neman yadda zasu ganta idanu rufe aka shiga tsinewa Latifa da mahaifinta Alhaji Bashir. Khalil na kallon yadda jee ke binsa da idanu bai kalleta ba taja motar bisa direction ɗin daya saita mata, babu inda kuma map ɗin ya tsayar dasu sai gaban wani haɗaɗɗan gidan mai masifar kyau da tsari ganin sunan Orphanage ta juya da sauri ta kalle shi, kafin tayi magana yara da yawa farare da baƙaƙe sun taho da gudu sun rungume Khalil, daga mai ɗane bayan shi sai mai riƙe hannunsa suna “We miss you Daddy” Majeederh taji idanunta ya cicciko da hawaye ashe ta wannan hanyar Ubangiji ke buɗawa Khalil ta rasa yadda a kullum arziƙin Khalil ƙara yawa yake ashe ga dalili, ta ɗan yi baya tana tuna sanda take kaisa orphanage ɗin shima when he was little, a hankali ta ce
“I love you gwarzona” Ya juya ya kalleta domin ya ji me ta ce hawayen daya gani a fuskarta ya sanya ya saki yaran, Alhassan tuni ya shige cikin yaran ya fara dambe dasu har an yaga masa riga, ya ƙarasa inda take a hankali ya buɗe bayan mota bata lura ba ta ji ta faɗa ya bi bayanta yana rufe ƙofar ya ɗan yi tafi driver yama motar key, Khalil ya yi ƙasa da glass suka haɗa idanu da Faɗimatu Majeederh ta dinga kallon yarinyar tana tuna sanda ta ganta a Vidcall ɗin Khalil, John ya ƙaraso yana yin ƙasa ya ce “Ranka ya daɗe” Khalil ya zubawa John Idanu ya ce “Nace maka me?” John ya jinjina kai ya ce “Kace yau tarihi zai maimaita kansa, zaka nunawa Malama Majeederh yadda kake sonta?” Khalil ya lumshe idanunsa speaking calmly ya ce “I love my wife John, kamar bata yadda ba amma zan tabbatar mata yau ɗinnan” Ya sake sauke numfashi yana buɗe zuciyarsa ya ƙara kallon John ya ce “Mun ɓata time, Sexy mama When will fasting begin?” Sexy Mama Majeederh ta maimaita a ranta tasan da ita yake, bata kalle shi ba ta ce “Today” Khalil ya ware idanunsa yana ɗan dukan kafaɗarta “Sexy mama!” Ta harare shi ya ɗage mata mata gira ya ce “But you didn’t tell me” Tayi masa shiru ya saka hannu ya mintsineta a bombom da sauri ta ce “Ohh sorry!” Khalil ya juya ya kalli John ya ce “Kayi lists na komi ka turamin, ka bar su Alhassan wajen ka” Ya sauke glass yana riƙe numfashi da shafa ƙirji ya kalli Jee ya ce “Saboda na ɗan shafa ki?” Ta tura baki ta ce “Mintsinina kayi fa?” Ya damƙota yana ƙasa da murya ya ce “Bari mu ƙarasa yau za kiga asalin mijinki da yadda ake Mintsini”
[