Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 48

Sponsored Links

Aisha Baby Novel: Latifa ta dinga kallon Mr President da mamaki fal zuciyarta, a yadda take ta sani kuma take ji tasan cewa baya duniya, ƴaƴan shi biyu sun yi silar mutuwar shi ta hanyar caka masa wuƙa? Why is he still alive? Latifa asked herself da wani irin confusion at the same time shocked, yadda Latifa ke kallonsa ya sanya ya ɗan kalleta kaɗan tunda ba wani saninta ya yi ba, kuma daman fito da shi akai suke tattaunawa da Chancellor.
“Sir!” Latifa ta kira shi yana kallonta ba tare daya amsa ba, ta ɗan sauke numfashi ta ce “Abraham’s father?” Mr president ya sake ware idanunsa jin ta kira sunan babban ɗan shi daya mallaka kuma yake tsananin so, dukiyar da yake so kuma da son mulkar ko’ina ya danne son da ya kewa Khalil ɗin, Mr President bai sake kallonta ba ta zube a gabansa tana wani irin kuka, ta ce “Sir; don Allah ka bawa Khalil haƙuri ya yafe mini ya saka a sakeni wallahi nayi nadamar aikata abubuwan da na yi, nasan ban kyauta ba, ban kuma zama aminiyar ƙwarai ba ka saka baki na koma gidan mijina” Baiyi magana ba wani Babban Gandiroba ya daka mata tsawa ya ce “Tashi ki bamu waje, keda kike da babban case kike tunanin barin gidan nan?” Jikinta na rawa ta juya ta ce
“A big case? What case? Aminiyata na yaudara, ni ba kisa nayi ba, ba sata ba, ba fashi ba balle kidnaping!” Marin da aka kai mata ya haddasa yin shirunta bisa dole. Aka tisa ƙeyarta zuwa sashin mata na babban gidan yarin mai tarin tsaro wanda manya ake zubawa kawai a ciki. Chancellor ya dubi Mr President ya ce “Tun bayan jinyar da kayi a ƙarƙashin kulawar jami’an Pakistan nake ƙoƙarin ganin na samu ganawa da kai al’amarin ya faskara, na kasa yarda ko gasgata laifin da ake tuhumarka da shi Mr President, nasan ba zaka taɓa yaudarata kaci amanar yardar da nayi maka ba” Chancellor ya yi shiru for some seconds kafin ya ce “Bayan laifin daka aikatawa Pakistan, Germany ma sun makaka a Court a bisa dalilin cin amanar siyasa (Democracy) da kayi ka zama kura da fatar akuya, a fuska mutumin kirki a zuciya saɓanin haka, a zahiri Mr President Daniel David a ɓoye Ddmaster bom” Mr President bai amsa ba, domin bashi da wata kalma da zaiwa Chancellor ɗin bayani, abu ɗaya ya sani shi ɗin mugu ne, mai tsananin son kansa da son duniya da kuma son ƙarfin iko!
“Wacece Debeka? Mene manufarka na bani ita matsayin ƴata bayan kasan bana haihuwa? Ina son yarinyar, tana ina yanzu?” Chancellor ya tattaro duka abubuwan dake damunsa ya zayyana, ya ware idanunsa akan Mr President yana jiran jin amsa wacce zata gamsar da shi, kamar daga sama a karo na farko Mr President ya ce “Debeka is Dead! Ta mutu” A gigice Chancellor na miƙewa tsaye ya ce “What! Mutuwa garin yaya?” Mr president ya ce “Calm down, aiki zata ɓata mini ni kuma na rabata da duniya, abinda baka sani ba akwai manufar data sanya na dage akan aurenta da Abraham, ita ta sani ai, da farko hankalinsa nake so ta jawo zuwa gareta, abu yaƙi, bani da wani zaɓi wanda ya shige ta aure shi, ta aure shi da nufin tayi masa allura wanda zan iya control ɗinsa, sai kuma ta faɗa soyayyar shi, har ta kamu da ciwon zuciya, soyayyar ta sanya ta kasa aiwatar da burina wanda shi ne ya saka suka kasance tare da Khalil ɗin, Khalil ya kamata ni kuma ban shirya ya san waye ubansa ba, wannan ya sanya nayi amfani da ɗan ƙaramin bom ɗin da aka sanya mata a jikinta ba tare da saninta ba, na kawo ƙarshenta”
Chancellor ya share zufa yana kallon Mr President cike da tashin hankali wanda ya kusa sanyawa zuciyarsa tsayawa da aiki a kiɗime ya ce “Bom; a landmine!” Mr president ya ce “YES, an anti-personnel landmines” Chancellor ya ce “Bom! How?” Mr president ya miƙe tsaye yana murmushi ya ce “Sorry Chancellor, na yi wasa dakai da yawa, Debeka na ɗaya daga cikin yaran da mukai safarar su, bani da yarda ko kaɗan idan nayi lissafi to daidai yake tafiya no mistake from Denial David, duk wanda zan aiki da shi sai na saka an manna masa ɗan ƙaramin bom wanda iya shi zai illata sai wanda yake more closer da mutum irin wanda suke rungume da juna, shi yasa ake cewa Ddmaster bom ma’ana Denial David master bom” Kafin Chancellor ya sake magana wani mutum dake tsaye ya ce “Time off” Yana faɗin hakan ya nunawa Mr President hanya zuwa sashinsa na Vip.. Yana shiga ya tsaya cak yana tunani bayan wani lokaci wani Gandiroba yazo kawo masa abinci mai kyau irin nasu na masu arziƙi ya kalli mutumin ya ce “Ina buƙatar magana da wata, ko kai mata saƙo” Gandiroba ɗin ya zare idanu ya ce “Sir kasan kuskure ne, komai muke akan ɗari ɗari muke fa, kuma muna taka dokokin cikin gidan prison ɗin nan” Mr President ya ce “Kana da 1.5m” “Naa…na..na amince wace?” Mr president ya ce “Ka bincika yau aka kawota ƴar kano ce” A taƙaice ya yi masa bayanin kamannin Latifa Omar “Me kake so?”
“Is Abraham still alive? Mom ɗinsa? Tare da sister ɗinsa Clara”

A hankali Khalil ke driving yana sanye da wani Kashim fari tas mai laushi da taushi ya kwanta a jikinsa tare da kama shi, hula ce zanna bukar a kansa hakan kuma bai hana kwantaccen sumar kansa bayyana ba, ta kwanta a wuyansa, idanunsa a ɗan lumshe yake driving ɗin zuwa Tukur Road da zai kaisa Arewa24, hannunsa ɗaya akan steering ɗaya kuma a jingine da cinyarsa yana ɗan shafa fuskarsa zuwa gemunsa, ya ɗan kwanta a kasalance yake gudanar da komai, a hankali ya saka hannu ya zare hular, ƙira’ar Sheykh Sudais na tashi a motar wacce Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ta saita, jin shiru ya saka Majeederh ɗago kanta daga kan Azkar ɗin da take dubawa ta kalle shi sosai sai kuma tayi gyaran murya “Uhm uhm” Bai kalleta ba idanunsa na sake lumshewa cikin ƙasa da murya sosai ya ce “Maluma” Ta girgiza kai ta ce “Malama kuma?” Ya juya kaɗan yana buɗe idanunsa ya kalleta calmly cike da nutsuwa ya ce “Watan Ramadan muke har ya shige ke maluma ce” Ta buɗe ido ya ce “If you look so romantic, ki amsa sunan Sexy mama, idan na kalli su Alhassan sai ki amsa sunan Blessing Woman, idan kina kishi kuma My jealous cat, harkar ilimi Maluma, idan ki kai mini kyau sosai ƴar madara idan sunanki nake son kira Jee, idan kin hanani bacci kuma My dream girl” Kallonsa kawai take ya sake ɗaga mata gira yana yin ƙasa da murya ya saka kai kamar zai taɓa ta sai ya janye hannunsa ya ce “Idan kina kunya akan gado kuma “Blush machine”
“Man! Azumi kake fa” Ya kashe mata Idanu ɗaya ya ce “Na taɓa ki ne? Ko taɓa ki na yi ban jin komai” Ta harare shi ta ce “Ah, haba dai?”
“Of course wifey” Ta ce “To mutum dai maza yana azumin jemage wlh kana iya bakinka, kalaman ka su rusa azumi dole kayi sittin” Ya dai kalleta bai ce komai ba, shi ya riga yasan ya saka niyya ba komai ke sawa ya ji wani abu ba sai iya abinda ya saka a ran shi. Horn ya yi a gate ɗin Arewa24 wani security ya buɗe, Majeederh ta ɗan sauke glass ɗin dake kusa da ita, baka ganin komai sai fararen Idanunta ya ce “Madam wajen wa kika zo?” Ta ɗan yi jim sai ta ce “Sashin Mata a yau, su Hafat da A’isha….e.t.c” Ya ce “Suna?” Calmly ta ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan” Securityn ya yi saurin buɗe idanu sosai, yana leƙa motar yaga waye mijin Malama ɗin kamar yadda jita jita ke cewa ɗan shugaban ƙasar Jamani ne, sai dai kuma ance ya mutu shekaru biyu da wajen wata bakwai da suka shige baya, ya ce “I am coming” Sashin Mata a yau ɗin ya kira suka tabbatar da zuwan nata, ya koma ya yi musu jagora daga bakin gate ɗin suka saka suna, time, date aka masu i.d card Khalil dai fuska a ɗaure babu walwala hannunsa zube cikin Aljihu hakan yasa security ɗin ya ji shakkar shi, a jere suka nufi ciki a bakin ƙofa suka ci karo da Zuwairiyya Gere shugaban sashin marubutan kwana cassa’in da daɗin kowa, kafin su gaisa da uwar marayu ta ƙaraso Fauziyya D Sulaiman suka gaisa Majeederh bata taɓa yarda da karamcin marubuta irin yau ba, tuni Khalil ya bar wajen tunda ba wani saninsu ya yi ba, Majeederh ta nufi ɗakin watsa shirye-shirye tunda ba wai live bane recording ne, bayan ta shiga suka gaisa sosai aka bata waje ta zauna bata ji ko ɗar a ranta ba, sabida ta saba da camera bayan nutsuwa da saita komai Hafsat ta kalli camera sai kuma ta ɗauke Idanu ta ce “Yau fa jama’a mun yi babban kamu”

“Kafin na faɗa muku ko wacce ku shirya turo tambayoyinku ta shafukan sada zumunta dake facebook, Instagram da twitter, na ce ina matan da suke tara ƙawaye? Wannan shirin naku ne, ina wanda basu yarda da ƙaddara ba wannan shirin naku ne, wacce baƙuwarmu? Wakuke zaton gani?” Sai kuma tayi murmushi ta ce “Bari musha ruwa mu dawo” Jajere tayi murmushi burinta kawai Majeederh ta ɗaga liƙab ɗin fuskarta, a hankali ta cire liƙab ɗin daman kuma wata dakakkiyar abaya ce a jikinta mai masifar kyau, tayi rolling kanta kyakkyawar fuskarta zubin ta half-caste ta bayyana duk suka zuba mata Idanu, ko wanne zuciyarsa na bugawa saboda ba suyi tunanin kyanta ya kai haka ba, Hafsat ta ce “Are you ready? Kin shirya?” Ta lumshe idanunta ta buɗe a hankali ta ce “In sha Allah” Da hannu Hafsat tayi alama kafin ta ce.
“Barkanmu da dawowa cikin shirin Mata a yau, yau shirin zai yi duba na tsanake akan gurɓatattun ƙawaye, da kuma illar jinkirin aure da abubuwan da suke kawo su, a tare damu akwai….,” Duk suka faɗi sunayensu kana ta ɗora da “Sai kuma babbar baƙuwarmu Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Babbar Malamar nan da tayi shura da fice a jihar Kano, kuma ita ce wacce ta dawo da martabar uwa ƙasa Nijeriya na ƙwato kambun gasar zakarun Alkur’ani na duk duniya, wanda har yanzu mune muke da wannan kambun, idan mai kallo bai manta ba shekarun baya akwai zancen daya dinga trending a social media wanda muma mun tattauna akai na cikin da Majeederh ta samu ba tare da aure ba, me ya faru? Duk yanzu zamu ji” Sukai ɗan murmushi Hafsat ta sake cewa “Kasancewar watan Ramadan Malama zata fara buɗe mana wannan shirin da addu’a, Malama Majeederh Abdul’aziz Khan Bismillah” Majeederh ta rufe Idanu ta buɗe, a daidai wannan lokacin kuma Abuturab na zaune ya yi jigum idanunsa akanta zuciyarsa na tsananin bugawa yana mamakin yadda ta sauya kyanta ya ƙaru wanda yake da alaƙa da shigar cikinta, ta yi gyaran murya a taushashe kafin ta furta “Bismillah” Addu’a tayi ta gyara zama tana ɗorawa da “Allahumma Taqabbal siyamana, Allahumma Tagabbal Siyamana, Allahumma Taqabbal Sujudana, Waá Ruku’Ana-Birahmatika Ya Rabbul ‘Alamin. Allahumma Innaka Afuwan Tuhibbul Afwa Fa’fu Anna, Allahumma Innaka Afuwan Tuhibbul Afwa Fa’fu Anna Fa’fu-Anna Ya kareem- Fa’fu Anna Ya Raheem- Fa’fu Anna Ya Akramal Akrameen- Allahummaghfirlana Maa Qaddamna Wamaá Akh’kharna- Wamaá arsalna- Wamaá A’lanna- Wamaá Anta ‘Alamu Biha minna- Innaka Antas Sami’ul Kareeb- Birahmatika Ya Rabbul ‘Alamin” Hafsat dake jan ragamar shirin ta ce “Malama Majeederh ba rayuwarki zamu shiga ba, muna son ƙara koyi da riƙon da ki kaiwa ƙaddara kika amsheta da hannu bibbiyu mene gaskiyar lamari na abinda ya faru?” Majeederh tayi ƙasa da kanta na wani lokaci sai kuma ta ɗago kanta a daidai lokacin kuma idanunta ya sauka akan wanda ba tayi zato ko tsammanin gani ba yana zaune wajen da ƴan bayan fage suke na ɗaukan shirin kamar yadda yake kallonta itama shi take kallo gudun zuciyarta na ƙaruwa…..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button