Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 52

Sponsored Links

Aisha Baby Novel: *Ku shiga wannan link ɗin domin cin gasar Arewabooks a facebook👇🏼*
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0FmezASrxXqPu36esVQepCtpQo8kQa3YDTRg86S35nuLfyEH4MQkuRExrgvZxsaxal&id=100067047050886&mibextid=Nif5oz

Ta zare Idanu tana riƙe numfashinta saboda gabaɗaya nauyinsa ya sakar mata,ta rufe bakinta da hannu yadda yake kallon idanunta zuwa bakinta tasan tana buɗe baki da niyyar magana akwai abinda zai biyo baya, Khalil yaƙi tashi sai bin fuskarta zuwa dogun wuyanta da kallo yake a hankali yana sake sauke mata nauyin nasa ya ɗora fuskarsa akan tata ya sauke numfashi da wani ƙaramin voice ya ce “Kin zalunce ni…” Tayi saurin zare ido ya manna mata kiss a Idanun ya ce “Ina nufin zuciyata” Majeederh dai bakinta a rufe ya saka hannunsa da ƙarfi ya fisge hannayenta yana ɗaga su sama kamar mai shirin caje ta ya kalli yadda ko’ina na jikinta ke shinning ga wani ƙamshin kwalacca mai kwantar da hankali da sanya nutsuwa, hannunsa ɗaya riƙe da hannun ɗayan kuma yana murza cibiyarta ya ce “Lallai yarinya, Ibrahim zaki ma wayo?” Ta haɗe fuska ta ce “To tunda yarinya ce sake ni” Ya yi wani kalar murmushi yana kashe mata ido ɗaya da ɗaga mata gira ya ce “Na isa, tunda har kin lalata ni lokaci guda kika haifi twins” Ya ci-gaba da murza abinda yake ya ce “Lalata Ibrahim abu ne mai wahala but it’s very easy to my wife, sexy Mama” Majeederh ta haɗe fuska tana tura bakinta a hankali muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce “Bad boy” Yana cire ribbon ɗin kanta ya ce “Yhhhh, but untill on bed” Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta, gabaɗaya ya manta azumi ya kai ya gama kunce masa lissafin kansa, gently Jee ta zura hannayenta a ƙasan hannayensa ta rungumesa sosai ƙirjinsu manne a hankali ta ce “Man” Bai ce komai ba, sai dabara da ya yi mata yana ɗagota a hankali ya fara unhooking bra ɗin tayi saurin riƙe shi tace “Not now” A hankali ya ce “Saboda ke kika biya sadaki?” Da sauri ta ce “Sadakin da ba a bani ba?” Ya yi saurin sakinta tare da ja baya ya yi zuru domin da gaske shi bai bada sadaki ba ya yi kalar tausayi ya ce “Don Allah?” Ta hararesa tana miƙewa tare da ɗaukan abayarta sai a lokacin ya fahimci dabara take masa ya miƙe yana shafa kansa kamar zai nufi upstairs sai ya sunkuya gabaɗaya ya yi sama da ita ya ce “Yaushe ki kai wayon yiwa Ibrahim dabara? Ke kina jin idan nayi niyyar abu zaki hana? Shuka sai da ban ruwa” Ta yi murmushi kawai ya ce “I love you, and I’ll always love you Jee” Ta mintsine shi ta ce “No is the man without a woman” Ya girgiza kai kawai can ya ce “Muje mu gaisa da wannan mala malan naki, naga how big they are yanzu?” Jee mamakin rashin kunyar Khalil take gabaɗaya baya jin nauyin sakin magana. Suna shiga bedroom ɗinsa ya saketa ta zauna saman kujera ya nemi waje a gabanta ya durƙusa hannunsa akan cinyarta yanayinsa ya sauya a hankali ya hargitsa sumarsa ya ɗago kai ya kalleta itama shi take kallo ya ce “You didn’t tell me Hawwa’u?”

“Me?” Ya kwaɓe fuska yana ƙara haɗe hannayensu waje guda ya ce “Kina so na, tun sanda bana ji” Tayi dariya mai kyau ta ce “Oh, yanzu ji kake?” Ya ɗan yatsuna fuska ya ce “Be serious Maa” Ta zame hannunta ta ɗora a kansa a hankali ta shiga tura hannunta cikin tulin sumarsa cikin murya mai laushi sosai ta ce “Me ya sa zan faɗa? Bayan lokacin ko auren baka san ma’anar shi ba? Kana ji da rigima, dukan jama’a haura katangar Abbu?” Ya yi shiru kamar mai nazari while he keeps his eyes on her, tasan kuma dole ya karanto gaskiya a hankali ya yi dariya sosai yana girgiza kai ya ce “Kawai kina tunanin ban isa gona ruwa da ƴa ƴa shuka ba, kina tunanin kayan aikin noman sun yi kaɗan ko?” Ta zare ido sosai ta kasa cewa komai ya zauna sosai saman carpet yana lumshe idanunsa jin tana yamutsa gashinsa kamar babu laka a jiki ya ce “Da gaske kin zalunce ni, kuma ki gaggauta neman yafiya” Ta ranƙwashe shi a ka ya ɗaga mata gira ya ce “Ni nasan ko niyyar gado ne ni, ko motsi lafiyayye ne wlh, kuma da kin faɗa mini komai I’ll fight don na aureki, I’ll fight for my love, zan iya sadaukarwar da komai just to be with you Sexy mama, ni nasan ban cancanta da ke ba, bani da qualities na mazan da suke so…,”
“Stop, bana so” Ta furta muryarta na rawa sosai ta kalle shi ta ce “Me ake buƙata a zaman auren Man? So da ƙaunar juna, yarda da amincewa, riƙe gaskiya da amana, kishin juna, kulawa, kyautatawa, i love you, and you love me too, ci, sha, sutura, magani duka kana bamu ka faɗa mini Qualities ɗin da suka fi wannan?” Kallonta kawai yake without blinking,yana jin kansa wani daban Majeederh ta shafi fuskarsa zuwa gemunsa ta ce “The most important thing in your character is your honesty” Shi a ransa yake jin bai yarda ba kawai taimaka masa tayi da kuma ƙarfa ƙafan da ya yiwa rayuwarta “Are you sure?” “Yes, of course Aby-Alhassan” Ya kwaɓe fuska ya ce
“Ni ban so” Ta ce “Sai me?” Calmly yana saka idanunsa cikin nata ya ce “Say my name, ina son ji” Ta ɗauke ido tana miƙewa tsaye sai kuma ta juya sosai ta ce “I can’t” Ya miƙe tsaye shima yana riƙe ƙugu kamar yadda tayi yadda yake sakin jiki da iyalinsa ba zaka taɓa yarda yana da azababben miskilanci ba ya ce “Kina son ɗaukawa kan ki zunubi, yanzu dai ki zaɓa” Ta juya Idanu alamar tana ji ya ce “Ko kice Ibrahim, ko yau a casar bugun dawar da zamuyi Kiyi riding nawa” Ta zare ido sai kuma ta yi saurin ɗauke kanta ya juya ya kalleta sai kuma ya nufi waje ya ce “Zoki ban abinci”
Washegari da safe Khalil ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda gezner dark blue ɗinkin jamper da babbar riga, bai saka hula ba sai sumar kansa daya ɗaure zuwa ƙasan wuya, bai saka babbar rigar ba ya bar iya half da wando hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗayan kuma yana danna wayarsa da ɗan sauri yake sakkowa daga kan steps ɗin benen sumar kansa na tashi sbd iskar dake kaɗawa ta Main parlour, yana sakkowa Alhassan ya miƙe da sauri ya ce “Aby” Al’hussain ma ya miƙe baby khalil na tsaye gabaɗaya shaddar jikinsu iri ɗaya ce, Baby Khalil ya fara miƙawa Abyn nasu hannu yana durƙusawa ya ce “Assalamu alaika Aby” Khalil ya amsa yana bashi side hug twins ma suka miƙa masa hannu har sun saba da gaisuwar musabaha, yana tsaye da yaran yana jin abubuwan da kowa ke cewa bugun zuciyarsa da ya ji ya sauya yana tafiya da sauri yasan she’s here, tana tsaye kuma shi take kallo ya ɗago kansa suka haɗa ido, farar lafaya ce a jikinta mai bala’in tsada ta kwanta jikinta sosai, ta ɗaura wani siririn liƙab hatta flat shoe ɗin ƙafarta fari ne, har wayar hannunta wacce Khalil ya sauya mata fari, gabaɗaya tayi shigar da Khalil ke so yana ƙaunar farin abu, a fili ya furta “Allhamdulillah!” Ya yi saurin ɗauke tunanin da yake sanda ya tuna azumi suke, ya sunkuya ya ɗauki Al’hussain, Alhassan ya fara kuka ya ce duk kukansa ba zai ɗauke shi ba wlh, yau mai halin matarsa zai ɗauka Majeederh ta yi murmushi ta ɗauki Alhassan tana rungume shi, a tare ita da Khalil suka kama hannun Baby Khalil, Alhassan ya ce “Baby” Khalil ya buɗe ido ya ce “What? Baby?” Ya juya ya kalli Majeederh ya ce “Mimi ɗanki ake cewa Baby fa?” Ta ce “Haka suke faɗa, amma zasu koma faɗin Yaya K” Ya jinjina kai suna fita driver ya buɗe musu jibgegiyar mota yaran a tsakiya, Kspider da Jee suna baya, suna ɗaukan hanya yaga tana buɗe Azkar a hankali ya ce “Ki faɗa a fili, I’ll repeat after u” Haka akai har suka nufi gidan Abbu, suna zuwa suka samu Aaliyyah da cikinta ya fara girma sosai suka gaisa da Mami Abbu kuma baya nan, kasancewar jirgi baya jira suka tafi gidan Uncle Bello tunda Uncle Isma’il ba kowa a gidan, Jawaad ya dawo gidan Uncle B da zama, Sona kuma tana gidan Abbu. Tun a ƙofa suka fara jiyo maganar Innati

“Ku kawo ruwa mai ɗan iskan sanyi, ina ƙara Saa guda macewa zan yi, wannan azumin Allah ka yafe Ubangiji ka cika kabarina da gwala-gwalan lada Allah ka yafe mini zunnubaina, a bani ruwa ana taɓa cikina lotsewa zai ƙwaranƙwasa” “Karya azumi kuma?” A hargitse Innati ta ce “Waye wannan kamar ana tashin hankali zai shigo kai tsaye ba sallama?” Majeederh ta ƙarasa shigowa ta zauna tana cewa “Ina yini Innati?” Innati tayi banza ta sake cewa “Ina yini?” Tana ƙanƙance Idanu ta ce “Ibro ka rabani da munafukar matarka, bani ba ita ni ta munafurta” Khalil dai na tsaye idanunsa zube akan majeederh shi har yanzu ya kasa fahimtar wanne kalar so yake mata? Innati ta miƙe tare da ɗaukan kwano ta kwaɗawa Majeederh aka ta ce “Algunguma, irin wannan ranar nake jira gashi tazo, babu tashin hankalin da bamu gani ba akan bakya so da ƙaunar Ibro” Majeederh ta runtse Idanunta cike da baƙin cikin kalamanta a baya kuma tayi nadama yanzu duk wanda ya furta haka ma haushinsa zata ji wallahi Innati ta ce “Ba dole ki runtse ido ba? Wannan azababbiyar ƙaryar ta bugawa a jaridu a haɗa? Ina har Aljanu ki kayi wai Allah ya kashe Ibro ki huta, kika dinga suma kin tsane shi baki son shi? Yanzu ubanwa kika bajewa tika tiki ya ƙunsa miki ciki? Ɗan gwaninin yaron ko? Shi ne ya buga miki iska?” Majeederh ta rasa me zata ce sai kawai ta fashe da kukan takaicin Innati, Khalil ya dinga riƙe murmushin shi ya ƙarasa kusa da matarsa yana bata side hug ya ce “To ke ina ruwanki ne? Idan ta tsane ni ina son ta ai?”

Innati ta fashe da matsanancin kuka hankali tashe ta ce “Asstagafirullah! Allah na tuba bana iya bacci idan na tuna a gidan nan aka bunka iska ta biyu, a gidan nan aka dinga lalata, bani da nutsuwa ana tsokala tsinke a kunnena wuta za a tsokano saboda tashin hankali” Uncle Bello da yake shigowa ya ce “Ibrahim ku tashi ku tafi kar ku yi missing Flight ɗinku” Majeederh dai kuka take, Alhassan ya cika ya yi fam ya kafe Innati da ido, Baby Khalil ya kalli Abynsu ya ce “Aby mene buga iska?” A harzuƙe Innati ta ce “Ubanka Ibro shi ya bugawa babarka iska, ya ƙunsa mata ciki wallahi tallahi” Da wani sauri Majeederh ta miƙe tana yin waje domin Uncle Isma’il ya ce har yanzu Alpha na asibiti kuma karta kuskura ta je, ta jima tsaye kafin taga Khalil ya fito shi da Jawaad da yaran tana ganinsa ta buɗe ƙofa ta shiga saboda wata matsananciyar kunya data lulluɓe mata jiki, bata taɓa jin kunyar mijin nata Dr Ibrahimul-khalil irin yau ba, bata son ma haɗa Idanu da shi, shigowa motar ya yi bayan ya saka yaran tana ganinsa ta rufe ido sarai ya ganta ya share, a haka suka nufi airport, Uncle Isma’il tuni ya sanya ayi masa binciken gidan su Zuleehart a can Ghana accra ɗin. Zuwan su airport ba wahala bayan an musu komai passengers sun fara shiga, Khalil na sallama da John yaga wani ya tsaya kusa da Majeederh kallon su yake, a tsorace Majeederh take kallon mutumin fuska rufe ya miƙa mata envelope babba fara tas sai wani ƙaramin rose dake maƙale a jiki ta ce “Waye kai?” Ya ce “Sanin ko waye ni bashi da muhimmanci, domin bani ne wanda yake zuwa gareki ba, ni ɗin Manzo ne, bi ma’ana ɗan aike, Boss Ubangida shi ne wanda ya aiko ni…..,”
“Ok da kai da ubanka yake ko wa?” Khalil yama kasa ƙarasa maganar ya nufi kan mutumin “Ni fa ɗan aikene, ko a zamanin jahiliyya ɗan aike baya laifi kuma..,” Wani mugun naushi da Khalil ya sauke mutumin shi ne ya hana shi ƙarasa maganar, ya damƙi wuyansa tare da yi masa gware nan take jini ya ɓalle, Alhassan me zai yi ba ihu ba yana tsalle yaga ubansa na faɗa, mutumin ya ɗaga hannu ya ce “Ka saurare ni please, zan faɗa maka ko waye” Bai bashi damar magana ba ya damƙi hannun ya karya Ihun azaba ya saki da wani irin fitsarin wahala, ya ce “Ka tsaya ka ji” Khalil ya sake kaiwa bakinsa naushi haƙori ɗaya ya fita ya saka hannu ya zare ribbon ɗin kansa a kausash ya ce “Bana buƙatar reasons, ka zama shaiɗan mai raba aure ko?” Ganin Khalil na ƙoƙarin yin kisa yasa majeederh cewa “Man…,” Wata masifaffiyar tsawa ya daka mata tare dayi mata nuni ta kama yaran su nufi jirgi, polices ɗin wajen suka tsaya domin babu wanda bai san waye Khalil ba, ya kalli mutumin ya ce “Kai kayi kaɗan wajen siyan soyayyar Matana, Ubangidan naka ya fito muyi gaba da gaba, zan tafi Saudiyya idan ɗan halak ne shi cikin uwarsa da ubansa ya biyoni zuwa Palace ga i.d card nan” Yana faɗin hakan ya cilla masa I.d card ya nufi cikin jirgin bai yarda ya nufi wajen Jee ba domin sai yanzu yake jin nauyin tsawar da ya yi mata, yana shiga cikin jirgin mutumin ya nufi mota jiki jina jina da jini, yana shiga wanda ke cikin motar ya ajiye azkar ɗin hannunsa ya ce “Sorry” Mutumin ya ce “Boss Ubangidana Akeeth ni zan baka haƙuri” A hankali Akeeth ya girgiza kai ya ce “Ka yankar mini ticket na zuwa Saudiyya now, I’ll follow him….
[10/12, 2:09 PM]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button