Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 55

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Majeederh na ƙoƙarin ambatar sunan “Mr No name” Da Uncle Isma’il ya furta ta ji ya ce “Yana ƙofa ai, izini yake nema a cewar shi ni ɗan gida ne dole zan iya shigowa duk da cewa shima zuwan nasa akwai babban dalili” Ta kasa magana ganin Khalil ya miƙe yana nufar ƙofa tasan halinsa daman kuma yau mulki yake ji da shi tunda ya zauna ko cikakken tari baiyi ba, balle magana, ba zaka ce yana wajen bama, hango shi yayi a tsaye sai dai ya juya masa baya, hannu ya dunƙule da nufin kaiwa ƙeyarsa naushi yaga ya juyo Khalil ya ware fitinannun idanunsa yana kallon Akeeth laɓɓansa na rawa wajen furta “Uncle Akeeth? You? Mr no name” Akeeth ya yi murmushi ya ce “Yes, ni ne ranar wanka ba a ɓoye cibi Dr Ibrahimul-khalil, ka ce idan ni ɗan halak ne na biyoka so I’m here don na tabbatar da cewa ɗan halak ɗin ne…,”
“Kana son rabani da matata why?” Khalil idanunsa rufe yake maganar yana dunƙule hannunsa saboda ba zai iya dukan Akeeth ba, ya masa halarci a rayuwa Akeeth ya ce “Muje ciki, ba zuwa kuma na yi domin na rabaku ba, i am here to ask of your forgiveness friend” wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya khalil ya sauke ba tare da ya yi magana ba suka shiga ciki, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya miƙe ya rungume Akeeth ya ce “Marhaban bika ya Ahki” Ajlaal da Akeeth abokai ne sosai,suka zauna, mamaki ya hana Majeederh motsi, kenan Akeeth shike bibiyarta da sunan Mr no name? Yake son lalata mata rayuwa haka kurum? Da farin cikin aurenta? Me ta yi masa idan ta fahimta dalilin daya kawo shi gidan t.v Arewa24 kenan? (Wonders shall never end). Abin mamaki baya ƙare wa.

“Dr Khalil, Malama Majeederh na san na ɓata muku amma ni kai na ban jima da fahimtar kuskurena ba sai kwanan nan, Allah ya gani ina son Majeederh so bana wasa ba, tun kina kawo Khalil wajena gidan marayun nan Matsayin Little ɗinki, ban san menene ya hanani tun kararki ba, a ranar da jarrabawa ta sameki kika haihu a sannan na faɗi a sume na yi jinya kafin na dawo daidai na samu labarin aurenki da Tsohon Gwamna Abuturab, bayan nan kuma na samu labarin kin auri Khalil, na kasa jurewa wannan ƙaddarar hakan yasa na dinga bibiyarki da sunan Mr no name, burina wai ko hakan zai sanya Khalil sakinki na aura, amma kamar ƙara muku fahimtar juna ake, duk da cewa ko tsakanin harshe da haƙori ana saɓawa, yanzu na fahimci ban kyauta ba, idan zan kashe aure to zan iya kashe mutum kuma na raunata zuciyarku ne, al’amarin shafin soyayyarku ko Romie da Juliet zasu shafa muku lafiya, bambancinku da Layler da Majnoon kaɗan ne, shi ne Khalil bai haukace ba saɓanin ƙais, Majeederh na raye bata mutu ba saɓanin Layler, mai zai sanya na raba wannan zuciyoyin? Lallai Ubangiji ba zai barni ba dole zunubaina su zama jarrabawa a gareni, na yarda ita ɗin ba rabona ba ce, she’ll just be my first love and my destiny” Ya yi shiru sai kuma ya kalle su da kyau
“I am sorry, i knew I made a mistake nayi shirme na cika mai son zuciya, kuma faɗin Allah da Manzonsa ne; ka so wa ɗan uwanka abinda ka so wa kanka, Dr Khalil ka yi haƙuri ka yafe mini don Allah, and you too Malama Majeederh” Majeederh ta kalli Miskilin mijin nata kamar yadda tayi zato waya yake dannawa abinsa, tana so tayi magana bata son damuwar shi
“Don Allah Khalil, ba zan samu nutsuwa a zuciyata ba idan baka yafe mini ba, ni da kaina, nasan na yi kuskure” A taƙaice Khalil ya ce “It’s okay” Akeeth ya gane ya yafe kawai faɗa ne ba zaiyi ba, ya ce “Saura ke Malama” Khalil ya miƙe tsaye yana kame fuska ba walwala ya ce “Yafiyarta kake so ko muryarta kake son ji?” Idanunsa zube akan Akeeth ba shakka a jikinsa ya yi maganar can ya ɗan buɗe kafaɗa ya ce “Idan yafiya ne an yafe” Yana faɗin hakan ya yi gaba tare da cewa “Madam kawo mini Mac book” Ta miƙe tabi bayansa Uncle Isma’il ya bisu da kallo cike da burgewa ganin yadda Khalil ke nuna son matarsa da kishinta a gaban kowa. Gaisawa suka shiga yi Ummie ko inda Uncle Isma’il yake bata kalla ba, shi kuma kamar maye sai binta yake da kallo zuciyarsa a bubbuɗe da sabon yanayi. Bayan ansha ruwa Fatymerh ta kaiwa Akeeth kayan buɗe baki tana ƙoƙarin tafiya ya ce “Zahraah” Ta yi cak sunan ya soki zuciyarta tunda daman an mata bayani akan sunan Faɗimatu ta juya ta kalle shi, a hankali ta ce “Kana son wani abu ne?” Akeeth ya ɗan langwaɓar da kansa ya ce
“Are you going to leave me?” Ta kasa cewa komai ya ɗan sauke murya ya ce “Zauna, let’s eat together, ki fanshi Nene” Ta kasa yi masa musu saboda ƙwayar idanun Akeeth akwai wasu abubuwa na ban mamaki. Maimakon ya ɗauki spoon sai taga ya wanke hannu a bowl tare da saka yatsu ya fara cin abincin yana kai na biyu ya ce “Identify yourself” Tayi shiru shi kuma ya ce “Ni ga sunana kin gani, ina tare da Nene (My mother), bana da wa ko ƙani, i lost my Papa when i was little, so Nene ta fanshe shi na yi karatu sosai, Nene cikakkiyar Hausa ce babana kuma Yoruba ne, so na kan ɗan juye Yarabawa some times, Business man ne kamfanin takalmi bag shoes kai many things, bana ɗaukan raini but i am friendly to everyone, i am simple like 1,2,3… kuma difficult to understand, I love sakwara da miyan egusi ina son nama sosai”

“Ohho, that’s nice”
Fatymerh ta ce tana lumshe sexy eyes ɗinta, hakan ya ƙara jirkita zuciyar Akeeth Yoruba demon ya motsa daman su basu da kunya akan Soyayya ya kasa cin abincin ya ce “Yanzu kuma ina son kiyi replacing Nene, kin ji Fatymerh Zarahh?” A hankali ta ce “Ina Saudiyya kana Naija? Taya zanyi replacing?” Calmly ya ce “By marring me” Ta waro idanunta sosai akansa sai kuma ta ɗauke kai, ya ce “Don Allah don Annabi karki ce a’a, say Yes Dear karki raunata zuciyar marayan Allah” Ta haɗe fuska ta ce “Yanzu ka ce wata ce Destiny naka? Kuma first love” Akeeth ya ce “Na tuba, na bi Allah da Manzonsa da Nene na biki” Ta miƙe zata fice ya yi saurin kamota yana dawo da ita jikinsa duk a rikice yake da sauri kuma ya saketa yana cewa “Aahh.. Asstagafirullah i am sorry” Bata amsa ba ya ce “Jeki, kina cigaba da zama a nan da matsala we’ll talk on phone” Ita mamaki ma yake bata wallahi ta juya tare da barin parlourn.
Ummie na ƙoƙarin fitowa daga ƙofa zuwa waje domin fita Masallaci suka ci karo da Uncle Isma’il ya yi saurin ja baya, yana cewa “Afuwan, ban kula ba” Idanu kawai ta ɗan zuba masa kafin ta ɗauke ido ba tare data tanka ba ta nemi shigewa ya yi saurin cewa “Ina son magana dake ki bani dama” Ta sake kallonsa fuska a haɗe domin taga take taken shi, kamar za ta yi magana sai kuma ta shige, tun daga ranar kullum Uncle Isma’il sai ya takura Ummie, dake daman oumara yazo sai ya fara zaman palace gabaɗaya ba wanda bai fahimci Uncle Isma’il ba, Gimbiya ta tattara shi ta watsar a gefe.
Ana washegarin sallah Majeederh ta sha ƙunshi bini bini Khalil sai ya kama hannunta ya tsura masa ido da sun haɗa ido sai ya marairaice ya ce “Da gayya ki kayi” ta ce “Kamarya?” A hankali ya sake damƙe hannun kamar yana so ya zura yatsun a bakisa ya ce “Ina so, nawa ne farashin?” Ta kwanta saman cinyarsa tana wasa ya ƙirjinsa ta ce “Bazaka iya biya ba” Ya buɗe gajiyayyun idanunsa sosai ya ce “Faɗi kawai”
“Ka rayu dani, har zuwa numfashin ƙarshe bana son kishiya ba zan iya jure ganinka da wata mace ba a duniya Man” Ya yi zuru yana kallonta sai kawai ta fashe da kuka ta ce “Farashin ya yi girma ko?” Ya jinjina kai ya ce “Gaskiya, sauya wani dai” Ta ce “Oh aure zaka ƙara?” Ya girgiza kai ya ce “Bana ce ba”

“Ba zaka sake aure ba?”
Still ya sake girgiza mata kai ya ce “Bana ce ba” Ta kai ƙarshe wasu hawayen na bin ƙuncinta ta ce “What do you mean by that?” Ya kashe ido ya ce “My jealous cat, bani da tabbaci ne zan ƙara ko a’a” Majeederh ta sake fashewa da kuka tana shagwaɓe fuska ya yi saurin rungumeta ya ce “Mijin mace ɗaya kike so na zama? Ko mijin ta ce, ko kafin ta ce?” Ta yi shiru bata kula shi ba, ya sake matseta a ƙirjinsa ya ce “Kin Isheni daga nan duniya har jannatul fir’daus, you’re my one and only wife” Ta ƙanƙame shi tana sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce “Wallahi Khalil mutuwa zan yi idan na ganka da wata na tabbata” Ya yi mata dariya ce “Ni mutuwa na yi da ake ta tururuwa a kan ki? Jee” Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa bugun zuciyarta na ƙaruwa daidai kunnenta ya ce “You are a gift from God, kin wadata ni da komai musamman a…..,” Ya raɗa mata a kunne tayi saurin rufe ido tana cewa “Uhm uhm ni dai!” A hankali ya furta “Hawwa’u” Ta ɗago kai da sauri ta kalle shi cike da tsoron jin sunanta ya ce “I love you, i so much love you Sexy mama” A tare suka rungume juna cike da soyayya.
Uncle Isma’il na zaune idanunsa akan Ummie dake duba Alkyabbar da aka kawo mata ya juya ya kalli Majeederh ya ce “Hawwa’u na je Gombe, Hajiya Luba ta faɗa mini dukkan abinda tayi muku ke da mahaifinki, abinda ya shige ya shige ba sai na faɗa miki ba domin hakan zai iya ƙara rusa farin cikin da kike ciki, halin data tsinci kanta kaɗai abin tausayi ne, ta gane yawon gidan boka bashi da wani amfani ko rana, ita data dogara da shi gata nan cikin wuta, domin babban tashin hankali ne ace mutum ya rasa ƙafa ga tsutsotsin da suke bi mata al’aura, zuwa gidan boka sallar kwana 40 bata karɓuwa balle ka yarda da abinda ya ce? Ke da kika dogara da Allah ki kai imani da shi ba gashi kina cikin kwanciyar hankali ba? Idan ba labari aka bayar ba waye zai ce wata ƙaddara ta faɗa miki? Shi yasa ake cewa watarana sai labari, don Allah don Annabi taci albarkacin Sona da Jawaad ki yafe mata please” Majeederh ta girgiza kai ta ce “Na yafe mata, wallahi na jima da yafe mata duniya da lahira” Uncle Isma’il ya yi murmushi ya ce “Alhamdulillah, Ubangiji ya albarkaci aurenki da zuciyarki ya ci-gaba da baku kwanciyar hankali na har abada” Ta yi shiru Ƙhulud ta ce “Amin” Ummie dai ko tari ba ta yi, sabgar gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Ranar daya kama ɗaya ga watan Sha’aban dubban jama’a suka halacci masallacin idi, Dr Khalil ya fita cikin wata fitinanniyyar Alkyabba milk mai yafin golden idan ka ganshi zaka ɗauka shi ne sarkin Makka gabaɗaya, a hankali yake fitowa idanunsa lumshe bakinsa na motsawa ana zikirin tafiya masallaci, Alhassan da Al’hussain da Yaa K gabaɗaya sun saka Alkyabba Ummie ta ce “Mene haka?” Ya buɗe ido alamar me? Ta nuna kayan jikinsa ya kwaɓe fuska bai ce komai ba a karo na farko tayi dariya mai gamsarwa akan idanun Uncle Isma’il hakan ya ƙara gigita shi ta ce “Ibrahim kenan, ai sarauta ke zaɓar mutum ba shi ke zaɓar ta ba” Shi dai ya yi shiru, ya nufi bedroom ya samu Majeederh na tsaye ta saka haɗaɗɗan farin lace mai manyan zane ɗinkin Buba ta kafa ɗauri ture kaga tsiya sai baza Ƙamshin da ya yi masifar missing take, jin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya tabbatar mata shi ne ta juya suka haɗa ido kallonta kawai yake ya kasa magana sai kawai ya juya. Ana idar da sallah Khalil yaga an cika a fada kuma an kira shi wai ashe Mai martaba Ajlaal Sultaan ne ya yi murabus saboda baya da cikakkiyar lafiya, Rohaan baya sha’awar sarauta shi ne ake ƙoƙarin sanya sunan Khalil matsayin wanda zai zama sarkin Makka, ai kuwa ya rufe ido ya ce bai san wannan ba, ya dinga surfa bala’i a ranar har Ummie ido kawai ta saka masa, ya gaji ya yi shiru ba wanda ya kula shi aka sanya ranar naɗa shi wanda yake daidai da cikar Edd ɗin Majeederh, Mijin Malama ya ce garin ma zai bari ya koma Naija daman duk a wahale yake a nan. Kafin tafiyar Akeeth suka daidaita da Fatymerh soyayya suke sosai ya gabatar da kansa kuma aka bashi Ita, Uncle Isma’il ya nema ma Jawaad auren Zizi shi ma aka bashi.
Khalil na zaune ya rasa inda zai saka kansa don farin ciki, Mami ta ce “Allah ya shirya ka Khalil, kwana shida da haihuwa gobe suna amma kamar yanzu aka haihu? Ko kunyar idanunmu baka ji? To kwashe yaran naka kayi gaba” Khalil ya shafa kansa idanunsa zube akan tagwaye yaran nasa mata, babu inda suka bar matarsa Mimi kuma Malama Majeederh, soyayyar duniya ya ɗorata akan yaran da suka kasance mata, Majeederh ita kunya ma yake bata Aaliyyah dake riƙe da Baby boy ɗinta mai sunan kakansa mahaifin Barrister Aliyu wato Sufyan ta ce “Ni matsalar ma yadda ba kunya yake ƙanƙame matarsa a idanunmu, kai dai baka data surukai” Khalil ya juya ya kalleta sai ya ce “Bani da ita wallahi, kuma na fi lusarin mijinki, jinin Ibrahimul-khalil daban yake ki duba haihuwata ta farko tagwaye, Alhassan da Al’hussain, yanzu a ta biyu ma tawaye ne Noha da Soha, Ma’ana Gimbiya da Fulani” Aaliyyah ta riƙe baki ta ce “Au kai ka haihu ma?” Ya ɗage mata gira ya ce “Yes, saboda ni ne mijin Malama, malama kuma tawa ce menene bambancin wanda ya bada ciki da wanda ya haihu?” Da sauri Mami ta ɗaga waya tana karawa a kunne cike da kunya ta ce “Hello magana kike ok gani nan..” Majeederh ta yi murmushi kawai domin tasan halin mijinta sak abinda zuciyarsa ta raya masa yake faɗa sai dai haƙuri, shi yasa kafin ya yi magana zai daɗe. Aaliyyah tayi sak ta juya tana kallon Innati dake firfita hankali tashe ta ce “Innati lafiya?” A gigice Innati tana fashewa da kuka ta ce “Gobara ake a kunnena, buɗe firiza ki ɗakko mini ruwa mai ɗan iskan sanyi idan da ƙanƙara mai kwantar da tashin hankalin ki haɗo, batsa ƙarara” Ta ƙara fashewa da kuka tana girgiza ta ce “Wallahi tallahi batsa ce wannan yanzu don Allah meye yin ciki kuma? Kamar wani ɗan iska?…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button