Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 18

Sponsored Links

Xviii….
(18)
Tsaye tayi tana kallon haduwar toilet din, komai da ake bukata na wanka da amfani akwai shi, ta kara jinjina karamcin wandannan mutanen data shigo rayuwar su a yau.
Bata wani jima a toilet din ba ta fito, har zata mayar da kayan jikin ta, sai ta duba rashin dacewar hakan, saboda barrister Abrar zata ji ba dadi, at least ya kamata tayi appreciating din kokarin ta gareta a matsayin ta na wacce basu hada komai ba, amma suka taimaka mata.

Wata doguwar riga mai yalwa caramel color ta sanya hadi da mayafin sa, ta nufi inda ta ga sallaya ta kabbara sallah, a sujjadar ta ta ƙarshe ta shiga addu’o’i da neman gafarar Ubangiji Cikin zubar hawayen kamar yanda take yi tun lokacin da Abin nan ya faru tsakanin ta da Maleek, Bayan ta iddar ta kwanta kan sallaya baccin da bata shirya zuwan sa ba ya dauke ta.
A tsorace ta farka tana kallon dakin bakin ta na furta “umma!” Tabbas umman ta ta gani, kamar wancan karon wanna karon ma fuskar Umma ba babu fara’a ko digo, abinda yafi daga mata hankali shine hawayen dake zuba a idanun Umman, sosai ta shiga nazarin ma’anar mafarkin ta amma karamar ƙwaƙwalwar ta ya gagara bata haɗin kai, ta lumshe idanunta wasu zafafan hawaye suka zubo, cikin raunin murya tace “ya rabbi ka yafe min, na tuba, idona ya rufe wurin samawa Amnah lafiya har na aikata zunubi mai girman gaske, ya Allah ya yafe min, ka ji kan Amnah da umma na, Ummah ki yafe min dan Allah…..” Ta karasa tana sulalewa kasa cikin kuka, sai da ta ji kanta ya fara ciwo kana tayi shiru, ta bude kumburarun idanunta ta ga har magriba tayi domin gari ya yi duhu, ta mike cikin dafa kanta ta nufi toilet ta dauro alwala ta fito hadi da tada sallah, tana sallame sallah ta ji an turo kofar an shigo, ta dago kanta suka hada ido da Abrar, ta dauke kanta hadi da mayar da idanun ta kasa, Barrister Abrar ce ta shigo ta zauna a bakin gado tace “ashe kin tashi Munaya, na shigo dazu kina bacci, ki zo ku gaisa da mai gidan ya dawo”

“Toh” Munaya ta amsa a sanyaye, Abrar ta mike, Munaya ta mara mata Baya.

Kyakkyawan magidanci mai tarin kwarjini da haiba ke zaune a kujerar falon, junior na kan cinyar sa yayinda yake amsa waya, da alama wayar mai muhimmanci, musamman yanda ya tattara nutsuwar sa kan amsa wayar, daidai lokacin daya ajiye wayar su Munaya suka karaso inda yake zaune, sau daya Munaya ta kalle shi ta dauke kan yi saboda kwarjininsa, zata iya cewa bata taba ganin kyawawan ma’aurata da suka yi matukar dace wa da juna kamar Wadannan ba, a dan nesa da shi ta tsugunna tace “ina wuni, sannu da zuwa” sai a lokacin ya dago idanun sa ya kalle ta, a kallo daya ya gane Munaya mai karanci shekaru ce, sosai ya ji tausayin sa, cikin sakakiyyar Muryar yace “stand up please”

Ba musu Munaya ta mike, tana wasa da dogayen yatsun ta da suka kara sirrancewa yace “kina lafiya? Abbas told us about you, so feel free, nan ma gidan ku ne kin ji ko?”

Munaya ta jinjina kai ta furta “Nagode”

“You’re welcome” ya amsa.

Junior dake kan cinyarsa ya sauko ya nufi Wajen Munaya, ya rike mata riga, dama tunda ya farka yake neman ta ina zai kara ganin ta, Munaya ta rike hannunsa suka nufi hanyar dakin da ke matsayin nata, tana jin barrister Abrar na fadin cewa “pure heart ka san me yaron nan yayi dazu….?” Ta san labarin yanda ya manne mata dazu zata ba shi, bata tsaya ji ba ta shiga dakin hadi da rufe kofar.
Ta zaunar da junior kan gado tace “ya sunan ka?” Yayi mata shiru bai yi magana ba, sai kallon ta yake.

Sai ta dauka ko baya jin Hausa ne tace “what’s your name?” Nan ma yayi shiru ya kwantar da kan shi kan gadon, ta saki murmushi, Hadi da shafa kan sa, tana kokarin manta mafarkin da tayi da Umman ta dazu, amma sai dawo mata yake, ta saki ajiyar zuciya, a hankali tace “I’m sorry umma, i failed you, ban rike daraja ta ba kamar yanda kika koya min” ta fada tana jarumtar shanye hawayen dake kokarin zubo mata, junior ya dago kansa yana kallon ta jin tayi magana, ta sakar masa murmushin yake tana mayar da kansa ta kwantar.
Har tayi sallar Isha suna tare da junior da ya kara wani baccin, duk da ba magana yake mata ba, amma ta ji dadin zaman sa kusa da ita.
Barrister Abrar ta aiko miemie ta zo kiran su domin dinning, Munaya tace “miemie kice mata na koshi Nagode”
Miemie ta koma ta faɗa kamar yanda Munaya ta fada mata, ta kuma dora da cewa “junior ma yayi bacci”

Barrister Abrar bata ce komai ba, ta mike da kanta domin zuwa dakin,
Kwance ta tarar da ita kusa da junior tace “kina so mu yi fada ko? Dan me zaki ce bakya cin abinci bayan kina da bukatar sa ko dan lafiyar ki, tashi mu je, and if you will not be comfortable having dinner with us at the dinning table sai a Kawo Miki daki” ta karasa tana daukan junior a hankali gudun kada ya farka, bayan kamar mintuna biyu da fitar ta, Munaya ta mike ta bi bayan ta.

A sanyaye tayi sallama, duk suka amsa, ta zauna kusa da miemie, barrister Abrar tayi serving din ta abinci kana suka fara ci, da kadan da kadan take tsakura kamar mai cin magani, duk suna lura da ita amma basu mata magana ba, kada ya zamana suna takura ta, bazata suka ji doctor Aaban yace “ya sunan ki?” Ya tambaye ta ba tare da ya kalle ta ba, so yake ta saki jikin ta, ta rage yawan tunani ko dan lafiyar ta, domin idan ta cigaba a haka zai zama babban risk idan lokacin haihuwar ta yazo, musamman daya kasance tana da hawan jini.
A hankali tace “Munaya, sunana Munaya”
Doctor Aaban ya jinjina kan sa yace “sunana Aaban mijin pure heart Abrar” yaran tare da Abrar suka yi dariya saboda yanda ya haɗa kalaman was funny.

Munaya tayi murmushi kawai, ta cigaba da tsakurar abincin ta, hammad yace ” Ni baki tambayi sunana ba” ta kalle shi, har ranta son mutanen wanna ahalin na burge ta, duk fargabar data zo da shi ta neme shi ta rasa saboda yanda suka karbeta, tace “I’m sorry ya sunan ka?” Ya gyara zaman sa yana murmushi yace “Ni sunan baban abbinmu gareni shiyasa ake ce min hammad, shi kuma Junior sunan baban Mamin mu yaci, TOH ke miemie bazaki fada mata sunan ki ba” ya karasa cikin salon yarinta.
Miemie da ta kai lomar abinci tayi dariya tace “Ni sunan mummyn abbin mu na ci, shiyasa ake ce min miemie, kuma mummy tana sona sosai fiye da su Hammad”

“Wallahi A’a, Abbi kana jin ta ko” musu zai kaure tsakanin su doctor Aaban yace “is okay, don’t mind miemie, mummy love’s you all”

Hammad yayi wa miemie gwalo yana cigaba da cin abincin sa, miemie ta turo baki zata yi korafin hammad yayi mata gwalo Mami ta mata kallon kar ma ta soma, dole ta tsuke bakin ta, Munaya duk tana kallon su, murmushi na bisa fuskar ta, sosai wanna familyn suka burge ta.

Bayan sun gama, Munaya ta taya barrister kwashe kayan da suka bata zuwa kitchen, suka gyara inda suka bata, duk da barrister din ta hana ta amma taki.

****

Mami da Abbi ke zaune a bolcony wato doctor Aaban da barrister Abrar, Mami zata yi magana yace “na san me a ranki, just give her time, zata saki jikin ta, duka yau kwana ta biyar a gidan nan” murmushi kawai tayi bata jin baya ga ammin ta akwai wanda ya karance ta tsaf kamar mijin ta, shiru ya ratsa dakin nawasu dakika kana Abbi Yace “har yanzu kina nan kan bakan ki na kai shi yaron kotu”.

Mami ta tashi zaune Domin a tabo Mata inda yake mata kaikayi, tace “sosai ma, mun ma fara maganar da Hanan, sai na kwato wa yarinyar nan yancin da yake tunanin yaci banza” Abbi ya kura wa bakin masifar ta ido har ta gama kana yace “oh now i see where this is coming from, Hanan ce ta kara zuga ki, zan hadu da ita ne”
Barrister Abrar tace “Allah babu ruwan ta, tun kafin ma ta san da maganar nace zan kwatar mata yancin ta, na fada mata ne domin mu hada hannu tare”

Abbi wato doctor Aaban yace “zaki yarda da abin da zan fada Miki yanzu?”

Mami ta jinjina kai, yace “i know my barrister zata iya yin nasara a duk wani Shari’a da ta sa a gaba da yardar Allah, amma bazan so kiyi wanna ba, ba wai ina goyon bayan Abinda yayi wa Munaya bane, naji matukar kunci abinda ya same karamar yarinyar irin wanna da ya kamata a ce karatu ta sa a gaba ba kalubalen rayuwa ba. Ina da dalilin da ya sa ban so maganar nan ta fita duniya, na farko saboda jaririn cikin ta, ba a san me gaba zata haifar ba, zaki so jaririn nan ya taso ya san cewa shi din dan zina ne? Ki sani cewa yanzu an daina kiwon mutane dabbobi ake kiwo, matukar maganar nan ta fito duniya tabbas ko bayan shekaru nawa ne sai mutane sun zagi yaron ko yarinyar da shi, karki manta lokacin miemie na karama tace wani mutum yace ke ina maman ki da mijin ammin ta yayi wa fyade, kin san yanda kalamar nan ta min ciwo kuwa? Dan yarinyar bata da wayo lokacin da me kike tunani zai faru, duk yanda aka so boye maganar duniya bata boyuwa, baka bayyana wa duniya magana ba ta fita, balle ma ka bayyana ta, da a ce shi wancan yaron ya ƙaryata cewa ba shi bane yayi mata cikin wanna case is different, a yanda Abbas ya bada labarin, bai ƙaryata ba, illa girman Kai bai bar shi ya amince cewa shi mai laifi bane, ina son duk wani mataki ko wani abu da za a aiwatar ya biyo bayan ta haihu lafiya, amma banda kai maganar kotu, for now dai let’s wish her a successful delivery”

Mami ta sauke ajiyar zuciya, ita fa so take Maleek ya dandana kudar sa ko ya ya ne, domin jin Munaya take a ranta kamar sun hada jini, amma kalaman mijin ta ya sake mata guiwa, ta kalle shi tace
“Ban ki maganar ka ba pure heart, Amma na riga na shigar da ƙara kayi hakuri”

Bai ji dadin hakan ba, domin fuskar sa ta nuna hakan yace “amma meyasa baki sanar min ba kafin ki shigar da ƙaran?”

“Kayi hakuri” tace masa.

“Is okay, ba damuwa, but Please becareful, nasan yanda kike ji a ranki game da yaron, Kada ki biyewa zuciyar ki, kiyi abinda yake daidai, kamar yadda kike saba” Abbi ya faɗa mata cikin sigar bada shawara.
“In Sha Allahu” ta amsa.

***
Tun lokacin da doctor Abbas ya basu labarin halin da Munaya ke ciki hankalin Shakur ya garara kwanciya. Safe, rana, dare tsumayin kiran doctor Abbas yake amma shiru, gogan kuwa baka taba karantar halin da yake ciki saboda miskilanci, walwalar sa kadan ce, hatta ma’aikatan sa suna kaffa- kaffa da shi a yanzu, firing mutane yake, ba gargadi, gaba-daya ya zama so depressed.

Kamar yau bayan Shakur ya gama lecturing ya biyo ta companyn Maleek, ya tarar da shi zaune gaban system yana aiki, ciki ciki yayi sallama domin sosai yake jin haushin Maleek din musamman halin ko in Kulan da yake nuna wa kamar maganar Munaya.

Ya zauna babu wanda ya yi magana da dan’uwan sa, can Shakur ya gyara zaman sa, yace “Maleek anya kana da tausayi kuwa? after all that happen between you and Munaya da labarin halin da take ciki daka ji, yet baka ce komai ba, now I’m wondering if you re truly my brother, domin babu mai taurin kai da zuciya a zuri’ar mu sai kai”
Shiru Maleek yayi sai faman mirza hannun sa yake alamun bacin rai, shi ma Shakur ransa ya ƙara ɓaci jin shirun da Maleek yayi da shi, a dan kausahe yace “magana nake da Kai Maleek!”

“What did you want me to say?” shi ma ya mayar masa a zafafe.

Shakur ya kara cewa ” oh haka zaka ce? Wallahi Nayi nadamar daukan yarinyar nan aiki a companyn ka, da ranar daka ce baka bukatar ta na bari ta tafi da duk hakan bata faru ba, na san ka tsani yarinyar, amma meyasa baka bar ta ta tafi ba, meyasa baka kore ta ba,ka keta mata haddi, and now kace min me zaka ce, bayan ka gama yin abinda zata yi da ita, ta zama bata da sauran amfani a gare ka ko?”

A zafafe Maleek ya mike zai dauke Shakur da mari, saboda yanda kalaman sa musamman na karshen suka bata ransa, sai kuma ya tsayar da hannun sa, yana murzawa a zafafe.

Shima Shakur ya zagayo ta inda Maleek ke tsaye yace “mare Ni mana, mare Ni, meyasa ka fasa”

“Believe it or not, ban yi hakan da gangan ba, i don’t know what came over me har na kusanci kazamar yarinyar can, kar ka kara fada min cewa na yi abinda na yi da ita, as if nayi Dan jin daɗin kai na ne, da kula yanmmata dabi’a tace da babu kalar yarinyar da bazan samu ba, kai ka sani, na dauki shigowar ta rayuwa ta tamkar kaddara, in ba kaddara ba menene a jikin kwailar yarinyar can da zai ja hankalina? gaya min Ta ya bazan tsani yarinyar nan ba? Saboda ita kake ce min I’m not your blood, you can say whatever you like no problem, Amma cikin jikin ta, ba ruwana da shi, ta zubar da shi, i have no business with her” Maleek ya karasa maganar cikin murya mai cike da bacin rai da damuwa, ya ɗauki car key din sa zai fice daga office din, shakur ya riko hannun sa yace “what! Ta zubar da cikin kace?”
Maleek ya kalli Shakur da idanun sa dake ci da wutar bala’i yace “yes, I said she should abort the baby”
“Maleek what came over you, kasan hadarin dake cikin hakan kuwa, bayan yanxu cikin ya girma kake so a zubar,,” bai tsaya sauraran Shakur ba ya kwace hannun sa da karfi ya bar office din, Shakur saboda yanda maganar ta dake shi kasa cewa komai yayi ya bishi da ido”
Maleek bai san ina za shi ba, yawo kawai yake a mota, kadaici kawai yake bukata, yana son yin tunani domin ƙwaƙwalwar sa is on fire right now.

***
*Shakur*
Har ƙarfe bakwai yana zaune a office din hoping that Maleek will be back Amma shiru, hankalin sa yayi mugun tashi, domin yana matukar kaunar dan’uwan sa fiye da komai, ganin ma’aikatan companyn sun fara tashi ne yasa ya fito daga office din ya rufe masa, kana ya sauka kasa ya fada mota ya fice daga Company’n, yana aiyana cewa Maleek yana gida duk yanda aka yi, bai yi wata tafiya mai nisa ba ya isa gida.

A hankali yayi sallama, mummy dake zaune cikin kwalliya tayi saurin tashi tace “ina my boy yake na ga kai kadai”

Dum kirjin Shakur ya buga, kenan bai zo gida ba, TOH ina yake? Maganar mummy ce ta dawo da shi tunanin sa cikin nuna babu wata damuwa yace “ammm yana da wasu baki ne, yanzu ma wani abun nazo daukar masa”

Hajiya Sa’adah ta saki ajiyar zuciya tace “alhamdulillah tunda lafiya, toh maza kaje kuyi ku dawo hakan nan, oh my boy ya gama jigata yau” ko sauraran ta bai tsaya yi ba ya nufi dakin Maleek, a kimtse kamar yadda mamallakin dakin ba baya ba wurin tsafta, ya tsaya ya kura wa gadon ido, tamkar zai hango Maleek din a kwance a kai, sai kuma ya fice cikin gaggawa, yayi Sa’a babu mummy a falon, hakan yasa ya kara sauri ya fice daga gidan.

Dan nesa da gidan su ya samu wani waje ya zauna ta yanda zai hango tahowar Maleek…

Har aka yi sallar Isha bai ga shigowar sa Layin ba, jikin sa ya kara sanyi, ya nufi masallacin dake dan nesa da su ya gabatar da sallar da bai samu yayi ba, bayan ya iddar ya fito zuciyar sa na wasiwasin kila Maleek ya wuce a lokacin da yake Sallah, ya duba agogon hannun sa ya ga karfe tara da hamsin da uku, ya dawo inda ya zauna dazu cikin tunanin mafita, kamar daga sama ya hango tahowar mota a guje, kallo daya yayi wa motar ya san ta dan’uwan sa, hakan yasa ya karasa tsakiyar hanya ya tsaya, domin ba zai bari Maleek ya shiga cikin gidan su har sai sun fahimci juna, ya gane nufin sa, ya kuma gyara.

Maleek dake ganin komai biyu-biyu yayi saurin taka burgi ganin mutum a gaban sa, motar ta bada karar kurrrrrrrrrrrrrrr, ya dago jajayen idanun sa sai ya hango tahowar Shakur, duk da yana cikin gushewar tunani amma ya shaida shi, a nutse Shakur ya bude motar ya zauna, warin giya ya buge shi, ransa ya sosu, sai yaji kamar laifin sa ne daya bata wa Maleek har ya kai shi ga karya alƙawarin daya masa na ya daina shan giya, Maleek ya kalli Shakur da jajayen idanun sa daya tara ruwan hawaye yana kyalli yace “i failed you bro, na karya alƙawarin dana dauka maka, amma Bani da zabi ɗaya wuce na sha din, i was depressed at that moment, I’m sorry”

Shakur ya ji kamar ya saki kuka saboda tausayin dan’uwan sa, tabbas Maleek na bukatar sani kan addini, dabi’ar yahudawa ta shige shi, domin da yana sani kan addini, Alqur’ani da addu’a itace maganin damuwa ba wai shan maye ba, ya kasa gane laifin waye behind wasu halaye na Maleek da sai yanzu suke bayyana kan su? Amma ƙwaƙwalwar sa ta gaza ba shi amsa, domin iya sanin sa mummy da daddy sunyi tayi kokarin wurin basu tarbiyya, duk da daddy ba mazauni bane.

Ya rungume dan’uwan sa kana yace “zamu yi magana Bayan ka dawo hayyacin ka, yanzu bacci kake bukata, ka dawo dayan ɓangaren mu karasa gida” a hankali Maleek ya fita, yana haɗa hanya, Shakur ya matsa zuwa mazaunin driver, gwaram haka Maleek ya zauna kan kujerar mai zaman Banza har motar ta motsa saboda nauyin sa daya saki gaba-daya, cikin lokaci kankani suka iso gidan na su, Shakur ya kashe motar ya fito, domin so yake su shiga gidan kada mummy ta gan su, bakin gate din su ya karasa ya kwankwansa a hankali, mai gadi ya leko yace “ka buɗe mana karamar kofar zamu shigo, bayan mun shiga da kamar mintuna talatin ka shigo da motar nan ciki”

“TOH yallabai” mai gadi ya amsa yana bude kofar.

Shakur ya bude bangaren da Maleek yake har ya fara bacci, ya girgiza shi, a sanyaye ya dago lumsasun idanun sa.

“Fito mu je” Shakur ya fada yana kamo hannun sa, mai gadi ya dinga masa sannu a tunanin sa Maleek din ba lafiya, yana tangadi da hada hanya suka bi ta baya da taimakon Shakur din ya kai shi har dakin sa ya kwantar da shi, ko mintuna uku cikakke ba a yi ba bacci ya dauke shi, ajiyar zuciya Shakur ya sauke, ya cire masa sau ciki din takalmin sa kana ya bar dakin, yana fitowa suka yi kicibis da Hajiya Sa’adah.

“Yawwa Ni kuwa kamar na ji motsi, ashe kun dawo, yana ina?”

“Yana bacci Mummy, ya gaji sosai ne”

“Allah Sarki my boy, gaskiya aiki na masa yawa, shiyasa na kasa gane kan sa kwana biyu” ta fada cikin kawar jiki tana nufar dakin, Shakur ya bi bayan ta, ya tsaya daga bakin kofar, kan gadon ta zauna, ta shafa kansa, sai ta ga ya kara mata wani kyau da haske, ta hadiyi wani yawu kana ta shiga shafa fuskar sa cikin wani salo amma sai tayi saurin Ankara da Shakur dake tsaye ta mike, ta dauki remote dịn ac ta kara masa gudun sa kana ta bar dakin zuwa na ta, ko damuwa da cewa Shakur din bai ci abinci bata yi ba, a kodayaushe tunanin ta da komai nata Maleek ne a kan gaba, shi ma Shakur bai damu ba, domin ba yau farau ba, hasalima ba shi da appetite din cin abinci. Dakin sa ya koma ya yi wanka, ya saka jallabiya mai yankaken hannun, tunanin Munaya ya fado masa, Lallai yana so ya ganta, gashi kuma doctor Abbas ɗin bai kira shi ba, tun ranar ɗaya karbi lambar sa yake tsumayin Ganin kiran sa, ga lokaci sai ja yake.

 

MunayaMaleek is 500, contact 07082281566 to subscribe yours.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button