Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 2

Sponsored Links

🍇MunayaMaleek🍓

 

_by NoorEemaan_📚✍️

I dedicate is page to Nanarh, a.k.a kanwar Abba ali.❤️

 

ii
(2)

 

Kankame jikin ta tayi waje daya cikin tsananin tsoro. “Maleek!” Shakur ɗaya shigo yanzu ya yi hanzarin kiran shi, hakan kuma ya hana Maleek isa wajen Munaya da niyyar huce haushin sa, domin ya ki jinin kazan ta, sam baya kaunar ganin datti, ya kuma lura yarinyar nan is fun of abinda baya so.

A zafafe ya juyo ga Shakur yace “kaga abinda ka janyo ko? You see what I’m telling you”

“Relax Maleek, calm down please” Shakur ya fada yana dan bubbuga kafadun sa.

Cikin bacin rai Maleek ya cire hannun Shakur yace “don’t tell me to calm down, who knows ko ta zuba min infection da germs a toilet”

Shakur ya juyo ga Munaya da jikin ta ke rawa yace “meyasa kika shigar masa toilet?”

“Al…alwal alwala na shiga yi” tace Cikin k’ak’arwan murya.

Ya Girgiza kai, sanna ya taka zuwa cikin toilet din ya danna wani madanni yayi flushing fitsarin da ta yi, sannan ya fito, ya nufi wajen tebur din Maleek ya dauki *pager* Wanda wireless telecommunications ne da aka yi connecting da loudspeaker, musamman an tanade shi Domin sanarwa ma’aikata wani abu, a maimakon a je kiran wani. “The cleaner to the CEO’s office, the cleaner to the CEO’s office urgently” Shakur ya faɗa kana ya ajiye telephone din.
Munaya da ta ji yanda Muryar Shakur ya karade ko ina tayi wiki wiki da ido, kanta a kasa ko dagowa ta kasa yi.

Mintuna biyu kacal ma’aikaci mai sanye da fararren kaya ya shigo dauke da mopping stick da mopping bucket ya shiga aikin sa, shakur kalli Munaya yace “biyo ni na nuna miki wajen sallah” kafar ta na hardewa ta bi shi, yayinda take jin idanun Maleek na bin ta da kallo na wulakanci da idanun sa masu kaifi”

***

“Kin ji aikin da nace zaki dinga masa ko? don’t cross your limit ki kula, Zaki zo karfe tara na safe ki tashi hudu na yamma, albashin ki dubu talatin da biyar duk wata”

Cikin farin ciki mara mistaltuwa Munaya ta washe jerarrun haƙoran ta, sosai taji dadin samun wanna aikin, ko aikin dubu goma bata taɓa saka ran samu ba, amma gashi Allah ya dube ta, ya Mata fiye da abinda ta saka ran samu.

Ta saci kallon Maleek dake danna system cikin kwarewa fuskar sa a dinke tsaf, har ranta ta so Shakur zata yi wa aiki, domin Maleek kam na bata tsoro, musamman kallon da yake mata a duk lokacin da suka haɗa ido, tana hango rashin haɗuwar jini ko tace tsanar ta a idanun sa, amma zata yi matukar kokarin ta wajen kiyaye abinda zai sa ya kara jin haushin ta, ko yasa ta rasa aikin ta.

” Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Munaya ta faɗa tana dan rissinawa.

“Ameen ga wanna, ki samu wasu kayan ki siya saboda zuwa aiki, always look good and neat” Shakur ya fada yana mika mata kudin

“Thank you, Allah ya saka maka da gidan aljanna” ta faɗa wasu kwallan dad’i na zubo mata, wanna shine karon farko data fara rike kuɗi masu yawa a rayuwar ta.

“Zaki iya tafiya, but make sure kin yi resuming aiki at 9:00am gobe”

“In Sha Allah, Nagode sosai” ta ce tana barin office din domin zuwa gida.

“Mtsss, i don’t think zan iya aiken yarinyar nan ko ina, zan dai bar ta ne saboda farin cikin ka, amma maganar gaskiya, bana son ganin ta” Maleek ya fada cikin iyakar gaskiyar sa.

“Tana da shiga rai, You will like her One day, zaka ce na fada maka Maleek”

Maleek ya dago kansa ya zabga masa harara, Shakur ya kwashe da dariya.

***
*MUNAYA*

Cikin kuzari data rasa rabon data samu irin sa tayi sallama cikin gidan su, hoping to see Amnah ta zo yi mata oyoyo, amma shiru, ta kara yin sallama, ta nufi dakin su, nan ta tarar da Amnah a kwance, cikin sauri ta karasa wajen ta, tace “Amnah! Amnah!!”
Cikin zafin ciwo Amnah ta fara lalube da hannun ta har ta taɓa fuskar Munaya kasancewar idanun ta na lumshe ne. “Muna, kaina ciwo sosai”

Munaya ta runtse ido saboda zafin data ji hannun Amnah yayi, ta ware idanun ta,
Cikin tausaya wa tace
“sannu, bari na siyo Miki magani”
Cikin tabe baki kamar zata yi kuka ta ware hannunta tace “ki tafi dani”
MUNAYA ta rungume ta a jikin ta suka fito, suna cikin tafiya Amnah tace “Muna nayi kuka sosai da kika tafi” Munaya tayi Murmushi tace “ai gashi na dawo, ke kiyi murna na samu aiki, in Sha Allah zan fara tara kudin aikin da za a miki, Zaki warke kinji” gama maganar ta yayi daidai da zuwan su Chemist din, ta siya mata magunguna har dana zazzaɓi domin ta ji jikin ta da zafi.

“Muna zan ci kifi” Amnah ta faɗa tana nuna kifin dake jere cikin show glass a gefen mai Chemist din.
“TOH bari na siya Miki” Munaya ta faɗa tana mikawa mai kifin dari biyar, dadi sosai taji da data samu kuɗin siyawa kanwar ta kifin, ba kamar da ba da zata ce “kiyi hakuri Amnah, ba kudi” maimakon su wuce gida sai suka zarce titi, Munaya ta siyi dinkakun hijabai guda biyar, kaloli masu kyau, ta kuma siyi takalmi kala biyu, ta siyawa Amnah ita ma, sauran kudin kuma zata ajiye suna cin abinci kafin a biya ta.

***

*SA’ADAH*.

A karo na ba adadi matar mai kimanin shekaru arba’in da takwas ke kallon kanta a madubi, ta sha makeup sosai tamkar budurwa, kara fashe jikin ta tayi da designer turare, sannan ta dawo bakin gado ta zauna, tana fatan a yau, a yau daya ya kalle ta a matsayin abin so, ba wai a matsayin mahaifiya ba, tun daga lokacin daya zama cikakken namiji take kwalliya musamman domin shi, duk kwalliyar da zata yi ba dan Alhaji Dawood take yin sa ba, sai dan Maleek domin shine muradin ranta, da kwadayin mallakar sa ta raine shi har ya zama cikakken saurayi, sai dai kash, har yanzu bata kai ga kashe ƙishirwar ta ba.
Numfashi mai zafi ta fesar daga bakin ta, ta mike hadi da barin dakin ta sauko izuwa kasan bene, ta samu daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana jiran dawowarsu, mintuna goma da zamanta ta ji tsayuwar motor su, ta mike cikin sauri ta bude labulen window ta hango zaratan samari biyun da kan su daya sun taho, idanunta kyar kan Maleek domin shine damuwar ta, ganin suna daf da kofar falon yasa ta koma cikin sauri ta zauna, tana gyara zaman rigar ta.

 

Sanyayar Muryar Shakur ce ta fara sallama cikin falon, yayinda Maleek ke bayan sa, ta mike cikin rawar jiki tana fadin “oyoyo my boy” Maleek ya saki wani tsadadden murmushi domin ya san da shi take, Shakur kuwa ya samu waje ya zauna, domin ya saɓa ganin hakan, domin tun suna yara kulawa ta musamman mummyn ke bawa Maleek, Sa’adah kuwa ta rungume Maleek cikin tsananin so da bukatuwa, Maleek kuwa sam bai kowa komai ran sa, kasancewar ta mahaifiyar sa, ya yi hugging dịn ta back kana ya raba rungumar da fadin “mummy ya gida?”

Sa’adah taji ranta ya sosu, musamman mummyn daya kira ta, ita tafi son yace mata Sa’adah, saboda idan yace Mata mummyn nan sai ta ji kamar yana mata kallon tsohuwa ne, amma a azahiri sai ta kirkiri murmushi tace “lafiya Lou my boy, ya aikin?”

“Fine mummy” ya amsa yana zama kusa dan’uwan sa..

“Mummy barka da yamma” Shakur ya fada looking at his mother, hoping wata rana, ko da sau daya ne ta nuna masa soyayya tamkar yanda take nuna wa dan uwan sa Maleek, sam baya kishi da Maleek, amma yana bukatar soyayyar uwar sa shi ma, baya ga soyayyar uba, bai san Wata soyayya kuma ba sai na jinin sa, dan’uwan sa Maleek dake kaunar sa, kauna Bata wasa ba.

 

A sake Sa’adah ta amsa masa, sai dai hankalin ta na ga Maleek, har tana jin dama ya rage su biyu kacal a gidan, ita fa gani take Shakur daya zama cikon na ukun su ya takura musu, tunda Alhaji Dawood baya nan, har wani haushin Shakur din take ji, ta ja tsaki a ranta, tana kokarin daidaita kanta, domin zata iya subutar fallasa kanta, shirin ta ya lalace.

Tun daga sama zuwa kasa yake kallon ta, musamman katon hijab din ta dake kokarin jan sa, ransa ya ƙara ɓaci, taya zata zo masa aiki a haka da wanna uban hijab din? Ya bugi table din gaban sa cikin fushi daya bayyana a fuskar sa..

Munaya ta hadiyi wani yawu mai kauri, kana cikin rawar murya tace “ina…kwa…na”

“Out of my office, dirty thing” maleek ya faɗa cikin tsawa, cikin rawar jiki har hijab din ta na harde ta ta nufi kofa, hawaye na zubo gidan ta…

“Shakur, Shakur, Shakur!!! You cost all these, duk kai ka janyo min wanna ciwon kan” ya fada as if taking of himself yana dafe kan sa.

Munaya ta samu kujera dake can nesa da office din sa ta zauna, ta sanya kanta cikin hijab ta yi kuka sosai, kana ta fito da kanta ta gyara zaman hijab dinta, ta kwantar da kanta jikin kujerar tana tuno Amnah kanwar ta, ta san yanzu haka kuka take, ga jikin ta da ya soma rikicewa, da tana da hali wallahi bazata fita ta barta cikin halin da take ciki ba, ta kara share hawaye tana lumshe kumburarrun idanun ta.

*BAYAN SATI BIYU*

*MUNAYA*

_12:00am_

Hankalin ta a tashe take shafa bayan Amnah dake kwarara amai a jikin ta, ga jikin ta da yayi zafi sosai, rabon da ciwon ta ya tashi haka tun Umma na nan, cikin rashin sanin abin fada tace “Amnah dan Allah ki daina aman haka, ya isa, kin san bamu da Kowa ko? Ya zan yi yanzu” ta fada tana fashewa da kuka, Amnah kuwa ta gama amayar da abinda ke cikin ta gaba-daya, har ya zamana yunkurin aman take babu abinda ke iya fita, har Tsawon mintuna biyar sannan ta daina, Munaya ta saki ajiyar zuciya mai tafe da shesheka, kana ta ajiye Amnah gefe, ta cire kayan jikin ta daya ɓaci da amai ta saka wasu, sannan ta dauko wa Amnah wasu kayan itama ta Sanja mata, sannan ta dauki kayan su data cire ta goge wajen aman tunda ya riga daya ɓaci, tocilan su da bai cika haske ba ta ɗauka ta haska zuwa dan tsakar gidan su ta ajiye kayan amai, sannan ta koma ciki, ta zube gaban Amnah tace “Amnah!”

Cikin maganar Amnah mai rarrabewa hadi da rawa tace “muuu…naaaa….. Z….zan…mutu, ki…min addu’a….. kai…na ci..wo so….sai” ta fada tana tamke hannun Munaya cikin zafin ciwo, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo wa Munaya, ta riko hannun Amnah cikin nata da kyau tace “ba zaki mutu ba Amnah, bazaki tafi ki barni ba, zaki warke da izinin Allah”
Addu’a ta shiga tofa mata, tsawon rabin awa ta ji saukar numfashin Amnah alamun bacci ya dauke ta, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta dauki Amnah ta kwantar da ita a kirjin ta, taji dama dama a ranta ganin bugun zuciyar amnah na fita da kyau, ta shafa kanta dake kyalli sakamakon babu gashi ko daya, ta lumshe idanun ta, tana tuno ranar da Umma ta aske yalwattacen sumar Amnah kamar yadda likita ya bada shawara, ta tuno irin kukan da amnah ke yi a lokacin da ake mata askin tana fadin “a’a ba…na so Um..ma, ki bar min ga…shi…na, i…na son ga..s..hi”

Hawaye suka zubo wa Munaya, tuno kukan da Umma ta sha a ranar da likita ya shaida musu cewa “ya kamata tuni kun lura da cewa yarinyar nan na da *brain Cancer* domin duk wani symptoms na brain tumor tana da shi, kamar yadda kika lissafa min tana yawan amai, tana yawan ciwon kai , sannan maganar ta na rarrabewa hadi da rawa, ganin ta na dishashewa, sannan tana zama kullum a rikice, sannan bakomai kwakwalwar ta ke dauka ba, duka wanna yana cikin symptoms na brain Cancer, kuma test da aka mata ya tabbatar da Hakan, shi wanna cutar yana da matukar hadari, musamman da ita karamar yarinya ce, abin ya mata yawan ɗauka, domin a kullum kara undergrowing yake, ma’ana yana kara tsirowa ya mamaye mata ƙwaƙwalwa, so the earlier a mata aiki, the better for her”

Ta tuno yanda Umma ta rikice da kuka tana tambayar likita kudin aikin na iya kai wa nawa, likita ya ajiye biron hannun sa yace ” toh a yanzu dai aikin na kai wa million uku da dubu dari bakwai, yeah 3.7″ ya karasa cikin tabbaci.

Ta tuno yanda numfashin Umma ya dauke na wani lokaci kana cikin raunin murya mai balai’n tausayi ta maimaita “3.7 million kake nufi likita?”

A ranar Munaya ta ga Umma cikin tashin hankali mara mistaltuwa bayan sun dawo gida.

Daga kuma wannan ranar Ummu ta fara neman hanyar samun kudin aikin Amnah, har ta sa wanna gidan na su a kasuwa, sai dai ko miliyan daya ba a taya ba, daga masu cewa dubu dari uku, sai masu cewa dubu dari biyar domin gidan karami ne sosai, tsahon gini, ga shi daki daya ne da toilet da karamin kitchen Wanda gefe daya ya zube, ganin ko kwatan-kwatan kudin aikin Amnah gidan bazai yi ba, Umma ta hakura da siyar da gidan ta fara aikin neman yi, wankau, da duk wani aikin karfi Umma nayi, a kuma kullum sai ta ajiye ko da dari ce, na aikin Amnah, ita kanta Umma tana ajiye kudin ne, amma bata san har zuwa shekara nawa zata haɗa million uku da dubu dari bakwai ba, tana dai fatan su yi tsawon rai da har zata tara kudin aikin ayi wa Amnah, daga lokacin suka rayu da burin samun kudin aikin Amnah, sai dai kana naka Allah na nashi, nashi ne kuma gaskiya, domin ko dubu talatin Ummu bata tara ba ta bar su…

Juyin da Amnah tayi a jikin Munaya ne ya katse mata tunanin da take, ta share hawayen fuskar ta, sosai take tausayawa rayuwar su, amma tafi tausayawa Amnah, Allah kadai ya san zafi, ciwo, da radaddin da take ji a kullum, idanun ta biyu har aka yi kiran sallar farko, sai a lokacin wani wahalallan bacci ya dauke ta.

 

07082281566

Share❤️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button