Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 27

Sponsored Links

XVII….
(27)

Arewabooks: NoorEmaan

Munayamaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya FIRST BANK.
Evidence of payment to 07082281566(Dan Allah idan baki shirya siya ba, don’t chat Me please).

Related Articles

 

“Bum bum bumm” haka karar buga kofar dakin ke tashi, sai dai dadaddan mafarkin da yake ya rinjayi bugun kofar, hakan yasa sam bai farka ba.

Ɗaga can bakin kofa ta waje Shakur ya murda kofar sai dai bai buɗu ba da alama daga ta ciki aka rufe, yaji liman ya tada sallah a masallaci hakan yasa ya ware murya Yace “Maleek! Maleek lokacin sallah zai fita” daga can cikin bacci
Muryar Shakur ya doki dodon kunnen sa, hakan ya katse masa mafarkin da baya fatan katsuwar sa, Meyasa Shakur zai masa haka? ya yamutsa fuska, kana ya ware idanun sa, ya mike tsaye bayan Shakur ɗin ya kara yi masa magana, a gaggauce yayi alwalar ya nufi kofa ya buɗe, ya yi wa Shakur irin kallon baya kyauta min ba, Shakur kuwa bai fahimci komai ba, daidai nan Alhaji Dawood shima ya fito yana fadin “yau wani irin bacci muka yi? duk mun makara”

Shakur yayi dariya, Maleek kuwa murmursawa yayi, kana suka haɗa baƙi wurin furta “Barka da asuba daddy”

“Yawwa Barkan mu dai, mu hanzarta” suna wanna maganar yayin da suka tafiya.

_8:30am_
Iyalan gidan Alhaji Dawood ke zaune bisa dinning table suna having breakfast.
Maleek! A hankali yake tsakurar cardamom banana omelette dake gaban sa, duk son yake yiwa wanna cimmar amma yau ya fita kansa, saboda yanda farin ciki ya cike zuciyar sa dama cikin sa, bazai iya tuna when last ya ji sa cikin farin ciki kamar daga daren jiya zuwa yau ba, mafarkin daya yi da yarsa ya tsaya masa a rai ainun, mafarkin da bai so farkawar sa ba, mafarki mai cike da annushuwa tare da yarsa data zo duniya a jiya, is it possible to be mad in love like this? Wato wani mahaukacin son yarinyar nan ne ya mamaye zuciyar sa cikin abinda bai kai kwana ɗaya ba, he just wish dama ya gansa a gaban ta yanzu, ya ɗauke ta zuwa jikin sa, ya ji dumin ta, ya lumshe ido, ba tare da ya sani ba, wani murmushin gefen baki ya subuce masa.

Hajiya Sa’adah dake Kula da dukkanin wani motsin sa, ta saki baki ganin yayi murmushi, murmushin ɗaya so sumar da ita, da tana da iko data bude zuciyar sa ta ga menene silar wanna murmushin na sa, ta kasa dauke idanun ta daga kansa domin wani kyau na musamman ya kara mata, ga wani annuri da fuskar sa ke fitarwa.

“Shakur jinjirar waye ka daura a status dinka jiya” Alhaji Dawood ya tambaya, hakan ya dawo da Sa’adah nutsuwar da take kokarin rasawa, Maleek kuma ya bude idanunsa cikin sauri yana kallon Shakur ɗin.
Shakur ya samu da kyar abinci daya kai baƙin sa ya wuce, da ba abinda zai hana shi kwarewa saboda yanda tambayar ta zo mai a bazata, a iya sanin sa daddyn sa baya tambayar abinda bai shafe shi ba, hasali ma mutum ne da ba ruwan sa da sabgar mutane.

Shi kanshi Alhaji Dawood bai san meyasa yarinyar daya gani a status ɗin Shakur ta tsaya masa a rai ba, hakan ne ma yasa ya kasa hakuri har ya tambayi Shakur ɗin.

“Ammmm…uhmm yar abokina ce Daddy”

“Masha Allah, Allah ya raya, ikon Allah kasan dana gan hoton yarinyar sun min kama sosai da dan uwanka Maleek lokacin yana jariri”

MALEEK da SHAKUR suka shiga kallon juna, Shakur ya ɗauke idanun sa cikin basarwa yana murmushi yace “Daddy ai ana samun kama irin wannan sosai ko da ba’a hada jini da mutum ba”

“Wanna gaskiya ne, that reminds me, when are you guys planning on getting married, ko irin in dan kama ku kuna waya da budurwar ku ban taba yi ba”.

Shakur yayi dariya sosai, Maleek ya shafa keyar sa kawai ba tare da Yace komai ba ya cigaba da tsakurar abincin sa.
“Im serious boys, yaushe zaku fito da mata? It’s time daya kamata nima na ga yan jikokina”

“Mun kusa in Allah ya yarda Daddy”

“Toh Allah ya sa, kai fa Maleek, You re not saying anything?.

Hajiya Sa’adah data cika tayi fam cike da haushi tun sanda Alhaji Dawood ya fara maganar aure tace “haba Alhaji, yara kamar Waɗannan kake wa maganar aure, dududu nawa suke saboda Allah fa?”

Cikin mamaki Alhaji Dawood yace “yara? Yara fa kika ce Sa’adah? A iya sanina babu wanda bazai iya Zama tare da Iyali ba cikin su, dukkanin wasu qualities da ake nema ga mijin aure alhamdulillah yaran nan sun samu, so what else are they lacking?”

Hajiya Sa’adah ta ƙasa magana Alhaji Dawood ya kara da cewa “tunda kin ki fada musu a matsayin ki na Uwar su, toh Ni na taya ki, ko bakya sha’awar ganin yan dagwai dagwai a gidan nan?” Wanna karan da zolaya ya karasa maganar.

Kamar Hajiya Sa’adah ta shake shi haƙa take ji, tayi murmushin yake tana daukan cup of tea din ta ta kai baki.

Shakur ya duba agogon sa ya mike, domin nan da 30mins yake da lecture da zai koyar.
Yayi musu Sallama ya fice.

Yana daf da karasa jikin motar sa ya jiyo takun kafar Maleek daga bayan sa.

Ya cigaba da tafiya ba tare da ya juyo ba ɓalle yace wani abu.

 

Hakan ya kara kular da Maleek, tun jiya yake jira Shakur ɗin ya masa magana game da yarsa amma shiru, da safen nan ma yana expecting Shakur din zai masa magana amma shiru, hakurin sa kam na daf da karewa.

 

“Shakur!” Yaji Muryar maleek.

 

Shakur ya gimtse dariyar sa kana ya juyo a nutse yace “Na’am, kai ma ka fito?”

 

“Eh, makaranta zaka je?” Sai bayan da yayi maganar ne yaji shi kamar wani soko, domin yafi kowa sanin cewa lecturing Shakur ɗin za shi, amma so yake ya ja Shakur ɗin da hira har ya masa maganar jaririyar sa daya mato kan soyayyar ta.

 

“Eh wallahi, sai na dawo”
Shakur ya fada yana bude motar sa.

 

“Shikenan abinda zaka ce, bazaka ce min komai ba Shakur?”

 

“What did you want me to say, ka ga I’m almost late, sai mun hadu?” Shakur ya nuna masa agogo, kana yayi saurin buɗe motar sa ya shiga Saboda sosai dariya ke cin sa ba Kuma ya son yi a gaban Maleek din.

 

Sai bayan ya fita daga gidan ne ya saki dariyar, domin ya gama gano Maleek din da abinda ke kunshe a zuciyar sa, Cikin nishadi yake tukin sa, domin he’s glad cewa Maleek yana so yarsa, ya sauke ajiyar yana fatan abubuwa su daidaita su kuma zo da sauki, domin ya san akwai matsala anyday su Daddy suka ji labarin Maleek na da ya, har bai son tunowa saboda tsoron tashin hankalin da yake hangowa zai faru.

***.

*Hajiya Sa’adah*

Yatsun ta take ciza, ba kadan ba maganganun Alhaji Dawood ya kona mata rai, lalle dole tayi abu, dan me zai ce su yi aure, ita dama Shakur kaɗai yace ko huɗu zai aura a rana bazata damu ba, Amma Maleek, ina bazata taba Barin wata mace can ta more wahalar da tayi ba, zuciyar ta ba zai iya daukar ganin Maleek da wata macen ba, ta jawo wayar ta zata kira Hajiya maimoona kenan, sai kuma ta fasa, maganar jaririyar da Alhaji Dawood ya fada ne dazu ya fado mata, tabbas jiya ta ga status ɗin Shakur, amma bata buɗe ba yanzu zuciyar ta na azalzalta da son ganin jinjirar da Alhaji Dawood ke magana.

Ta shiga WhatsApp kai tsaye kana ta shiga bangaren status.
Wata mahaukaciyar bugawa zuciyar ta tayi, tabbas Alhaji Dawood bai yi karya ba, wanna babyn na kama da Maleek matuka, duk da cewa sanda ta zo gidan ba’a jariri ta tarar da Maleek ba amma tabbas taga kamanin su musamman baƙin da girar su, tayi tsuru tana kallon, kana ta ajiye wayar, maganar da Shakur yace ana samun ma su kammanin irin daya ya kore wani tunanin dake kokarin zuwa zuciyar ta, ta sauke numfashi, tana ƙara yarda da kalaman Shakur ɗin.
Number’n Hajiya maimoona ta yi dailing, domin kanta ya kulle da maganganun Alhaji Dawood, tana bukatar a warware mata.

“Hello kawata an tashi lafiya?” Inji Hajiya maimoona bayan ta daga kiran.

“Ina fa lafiya, Alhaji zai kashe Ni da raina” inji Hajiya Sa’adah

“Ban gane ba, yi min bayani”
Hajiya maimoona ta fada tana tattara nutsuwar ta kan wayar.

“Ana zaune kalau in gaya miki Alhaji yasa yaran nan a gaba wai ya kamata su fito da mata ayi musu aure”
Da daci a Muryar Hajiya Sa’adah da alama ba karamin bata ranta kalaman Alhaji Dawood din suka mata ba.

“Toh shi wanna Alhajin naki sai a hankali, shi har zai gaya wa yaran zamani aure da zarar sun shirya da kansu basu furta”

“Gane min hanya maimoona, nifa tsorona Kada na tashi a tutar babu, ga lokaci na ta ja amma ban kai ga cimma burina ba”

“Me kike ci na baka na zuba, abinda zan gaya miki shine kada kiyi gaggawa domin zaki iya tashi a tutar babun da kike tsoro, ke dai yanzu abinda zaki yi, ki tanadi desire tablet din nan, da zarar kin samu dama komai kankantar ta kiyi amfani da ita, ba Lallai haɗuwar ku ta farko ta miki yanda kike so ba, amma video record da zaki yi dinan shine zai cigaba da baki dama da ikon samun sa yanda kike so a gaba”

“Wanna shawarar tayi, zan samu na fita na siyo desire tablet din na adana, nagode kawata”

Da haƙa suka yi sallama da juna .

Maleek na zaune a office ɗin sa, amma kamar bai zo ba, domin ya kasa tabuka komai, sosai yake son ganin ta a zahiri, amma ya rasa yanda zai yi domin ya cimma ma muradin sa, hoton babyn ya saka a gaba yana kallo, yanda yake jin yarinyar nan a ransa zai iya bada rayuwa da dukkanin abinda ya mallaka domin ta, sunaye kala kala na zuwa ƙwaƙwalwar sa, so yake ya zaba wa yarsa unique name, so yake Shakur ya dawo su yi magana, yana son yarsa a kusa da shi, yana son ganin ta a kowacce rana.

 

 

_Mu hadu gobe dan jin yanda kaya, team Maleek ya kasuwa?_

07082281566

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button