Munayamaleek 3
🍇MunayaMaleek🍓
_by NoorEemaan📚✍️_
iii
(3)
*MALEEK*
Bayan ya gama aikin da bai samu karasa wa a office ya rufe system din sa hadi da ture shi gefe, ya kwanta rigingine, yana fatan bacci ya dauke shi, amma ya san baccin bazai zo ba, domin duk daren duniya ya kan so yayi bacci, kamar yadda ko wani dan adam ke yi, amma hakan baya yuwa, saboda an riga an raine shi da Barasa tun yana dan shekara uku a duniya, har ya girma ya fara nema da kan sa, har ya zamana he’s so addicted to it da idan bai sha ta duk dare kafin ya kwanta ba, ya kan ji kamar ya haukace.
Kamar yanzu yana kwance idanunsa tarr babu alamun bacci, duk da kasancewar yanzu karfe biyun dare, ya mike kamar an tsikare shi ya nufi wardrobe din sa ya bude ya dauko wani box madaidaici, ya dawo bakin gado ya zauna, ya daura box din a cinyarsa ya danna wasu numbers, dan akwatin sirrin sa ya bude, take kananun kwalabe masu ɗauke da giya suka bayyana, ya mika hannu ya dauki guda daya mai suna *Mr dowell’s whiskey* ya kafa baki ya shanye duka, sannan ya kara daukan Wani ya shanye, take idanun sa suka kada suka yi jajur, ya rufe dan akwatin kana ya mike ya mayar da shi cikin wardrobe ya dawo ya kwanta rub da ciki, ya lumshe kyawawa kuma rikitatun idanun sa, cikin abinda bai fi mintuna biyar ba bacci ya dauke shi.
***
*MUNAYA*
_5:30am_
Abu mai dumi data ji ya zuba a kirjin ta, ya ratsa ta rigar ta har ya taba fatar ta shi yayi sanadiyar tashin ta daga baccin daya dan dauke ta.
“Amnah!” Ta faɗa cikin sauri ganin tana amai sosai, sai dai zallar ruwa take amayar wa, Amma ta kasa ko da motsi, saboda mutuwar jiki, sai aman dake fita a bakin ta, ta tashi da ita a jikin ta cikin sauri, ta jinginar da ita jikin gini, Amnah ta tafi luuu zata kwanta domin babu kwari a jikin ta ko daya, Munaya tayi saurin tareta ta kwantar da ita, kana cikin sauri ta fita zuwa tsakar gida ta dauro alwala ta dawo cikin daki ta sanja kayan jikin ta, ta yi saurin tada sallah, tana jin yanda amnah ke fitar da nunfashi da kyar, sam ba a nutse tayi sallar ba, ko azkhar bata iya yi ba, ta saka ɗaya daga cikin hijab din ta data siya, ta lalubo wa Amnah atamfa doguwar riga daya kode ta sanya mata, kana ta dauki ragowar kuɗin da Shakur ya bata dubu goma sha huɗu ta dauki Amnah rungume a jikin ta, cikin sauri ta fito daga gidan, ko rufe kofar langa langan su da kusan rabi ya cire daga bango bata yi ba saboda sauri, burinta ta kai Amnah asibiti, domin jikin kara rikicewa yake a ko wani dakika daya na agogo, gudu-gudu sauri-sauri, ta dinga tafiya har ta iso bakin titi, ta ga babu wasu ababen hawa, kasancewar garin bai ida wayewa ba gashi lokacin sanyi ne, ta tsaya har na mintuna biyar bata samu ba abin hawa ba , sai ta fara tafiya cikin sauri, tana yi tana kallon fuskar Amnah da yayi fayau, idanunta sun shige ciki sosai, ramar ta ya fito muraran, kiris ya rage basu zube a kasa ba, sakamakon kallon da take wa Amnah, ta yi saurin jan tunga ta tsaya, ta cigaba da tafiya tana waigen bayan ta ko zata ga abin hawa, ta ɗan jima tana tafiya sannan ta ji dan sahu na mata horn daga baya tayi saurin juyowa, ta shige dan sahun, cikin rikicewa, fuskar ta a kacame da hawaye tace “muje asibiti ɗan Allah”
mai dan tsahu yace “wani asibiti?” ta kira sunan asibitin da Umma ke kai Amnah ya ja suka tafi, mintuna daya biyu ta kira sunan Amnah, amma shiru ba amsa, Munaya na tsoro, tsoron rasa tilon kanwar ta, bata son rasa Amnah, kaf duniya ita kadai ta rage mata, ita ce sanyin idaniyar ta, Amnah bata ko iya magana, sai numfashin ta dake fita da sauri tamkar zai fasa dan kirjin ta ya fito, sai juyi take a jikin Munaya alamun tana cikin zafin ciwo, wanda hakan ke saka kirjin Munaya lugudan bugu.
“Mun iso asibitin” mai dan sahu ya fada yana waiwayo ta, cikin sauri Munaya ta sauka, ta bashi dubu daya cikin kudin dake hannun ta, ya girgiza kai da cewa “ki barshi, Allah ya bata lafiya” ta kasa ko da magana balle godiya, ta yi cikin asibitin da gudu, mai dan sahu ya girgiza kan sa, tayi matukar bashi tausayi, domin ya hango damuwa mai tarin yawa a tare da ita, a bayyane yace “ko ina iyayenta suka bar karamar yarinya da wanna wahalar, domin ko shakka babu wanna yarinyar bazata iya haifar mara lafiyan ba” ya sake Girgiza kai, yana tada Babur din sa, ya Kuma gode wa Allah daya wadata shi da lafiya, Domin idan kana tunanin kana cikin halin kunci ko kana fuskantar wani kalubalen rayuwa, toh idan ka ga wanda kafi sai kayi godiya ga Allah da yayi maka wanna ni’imar, ba dan kafi wasu ba,sai dai ko wani bawa da tashi kalar ƙaddarar.
Cikin asibitin kuwa a gagauce suka karbi Amnah, aka mata fixing drip, domin babu karfi ko daya a jikin ta, Munaya na gefe tana kuka sosai, bayan likita ya gama duk wani abu daya dace yayi wa Amnah ya juyo ga Munaya yace “ina maman ku?”
“Ta mutuuu” tace cikin kuka.
“Baban ku fa, ko wani daga dangin iyayen ku?”
“Doctor bamu da Kowa, bamu da Kowa sai kan mu”
“Ya Salam!” Likita ya fada cikin rashin sanin abin yi, domin bai san yadda zai mata wanna bayanin ba, gani yake tayi kankanta da yawa, ya kara kallon munaya yace “muje office dina” ya karasa yana barin dakin cikin sauri, Munaya ta kara kallon Amnah dake kwance kamar mara rai, sannan ta bi bayan likitan a sanyaye.
“Zauna” likita ya fada yana nuna wa Munaya kujera.
Kamar mai zama kan wuta haka ta zauna, a tsorace take matuka, likita yayi gyaran murya yace “am…i believe kin San cutar da kanwar ki ke dauke dashi ko?”
Cikin sauri ta daga kai alamun “eh”.
“Good! A yanzu dai ta kai stage na karshe wanda take daf da rasa rayuwar ta matukar ba a mata aiki cikin gaggawa ba, domin shi Cancer yana undergrowing kullum ne, because is a disease in which the cells of a tissue undergo, uncontrolled (and often rapid) proliferation, it’s Something damaging that spreads throughout something else, So the best shine a mata aikin, sannan sai ta cigaba da shan magunguna, domin shi karin ruwan nan da aka mata babu abinda zai kara mata a fanin cutar, sai dai ya kara mata karfi data rasa sakamakon aman da tayi, amma cutar na cin ta ta ciki, shiyasa dazu nake tambayar ki ko ina dangin ku, saboda kudin aikin ba kananu bane, I know you can’t afford it alone, million uku da dubu dari tara ba wasa bane baby girl”
A firgice Munaya tace “do..doct….doctor! million uku da dubu dari bakwai aka ce wa Umma na last time”
Likita yace ” gaskiya a da kenan, domin maganar da kike shekara daya data wuce kenan, yanzu kudin ya karu” daga nan bai kara cewa komai ba ya cigaba da aikin sa.
Munaya ta rufe idanun ta da tafukan hannayen ta ta fara rera kuka, ta mike zuwa gaban likitan ta tsugunna tace “dan Allah likita ku taimaka ku mata aikin nan, wallahi Allah zan nemo kudin duk inda yake na biya, Ni dai fatana ta rayu, wallahi zan biya, idan ma baku yarda ba muyi yarjejeniya, ku rike ta a wajen ku har sai na gama biyan ku sai ku bani kanwata, Ni dai ina so ta warke, dan Allah likita ka taimaka, ita kaɗai gareni…” Ta karasa cikin Muryar kuka mai narka zuciya.
Likita ya girgiza kai, yana kara tabbatar da yarintar Munaya, saboda abubuwan data faɗa bazai taba yuwa ba, tsari da dokar asibitin bazai taba yarda da hakan ba.
“Hakan bazai yu ba, ki Sani cewa ko iya kudin gado da karin ruwan nan dana yi wa kanwar ki aka barki dashi bazaki iya biya ba, You re even lucky kin samu ina duty ma da kika zo, da baza su karbe ta ba har sai kin ajiye dubu saba’in, which i know baki da irin wanna kudin, amma na dauki nauyin Hakan tunda baki da su, kuma kanwar ki na Cikin mayuwanci hali, abu daya dai zan iya taimaka muku dashi yanzu, magani za’a siya mata, wanda zai dan taimaka mata kafin a samu kuɗin aikin, but note kada a dauki lokaci Kafin a mata aikin nan, domin komai zai iya faruwa da ita” ya karasa maganar da rubuta mata maganin a farar takarda hadi da cewa “gashi bashi da tsada sosai i think bazai wuce dubu goma sha biyu da dari biyar ba, so ki siyo mata a pharmacy’n cikin asibitin nan a bata, but i repeat, aikin nan shine abinda sister’n ki ke bukata, magani bazai mata abinda ake so ba, so ki sa wanna a ranki”
Jinjina kai Munaya tayi, ta lashi busassun labb’anta kana ta fita daga office din likitan, cikin sauri taje pharmacy din, luckily kamar yadda likita ya fada 12,500 aka siyar mata, ta duba hannun ta ta ga saura 1,500 ta fita wajen asibitin ta ga wani provision store ta siyi yoghhurt mara sanyi sannan ta dawo cikin asibitin, direct dakin da aka kwantar da Amnah ta nufa, ta buɗe Kofar a hankali, idanun ta suka sarke dana Amnah dake kwance, tadan ji sanyi a ranta ta lumshe idanun ta cikin sakin ajiyar zuciya, ta kara buɗe idon, and then she saw Amnah smiling at her, ta karasa wajen gadon da sauri ta dago ta zuwa jikin ta tace “sannu Amnah, ya jikin ki, kin ji sauki ko?” Amnah ta gyada kai, Munaya ta sumbaci goshin ta da kumatun ta, sannan ta bude yoghurt din ta bata, Amnah ta kau da kai gefe, Munaya ta marairaice tamkar zata saki kuka tace “ki sha ko kadan ne ki sha magani kin ji” ta karasa cikin rarrashi.
Amnah ta buɗe bakin ta ta sha kadan, sannan Munaya ta ballo yan kananan maganin ta, ta dinga zuba mata a baki da daddaya ta sha, har ta ɗan sha yoghurt din kadan, Amnah ta kwantar da kanta a jikin Munaya, tace “mu…na….za..ki..mun…kitso ko?”
“Zan Miki mai kyau ma, da zarar kin warke”
“Yau..she…zan…War…ke mu…naaa?” Amnah ta tambaya tana kallon Munaya.
“Nan kusa da yardar Allah, nan kusa Amnah” dakin ya kara daukan shiru na wasu mintuna, suna rungume da juna abin tausayi, Amnah ta kara breaking shirun da cewa “ina… son…ki munaaa…, Ku…ma ina… son Umma, Am…ma na..fi son ki a…kan kowa, sa…bo…da baki ta..fi kin barni ba, ku…llum ki..na ta..re da ni, amma ita Um…ma ta ta..fi ba…ta da..wo ba”
Zafaffan hawaye mai tafe da murmushi ya wanzu a fuskar Munaya, ta ji mutuwar Umma ya dawo mata sabo, yayin da tsanar mahaifin su ya cika zuciyar ta, domin bata taɓa ganin mutum mara tausayi irin sa ba, ya tafi ya bar su, a kan dalilin sa mara tushe.
Cikin Muryar ta ɗaya dan shake sakamakon kukan da ta sha tace “Amnah ina son ki sosai nima, ina matukar kaunar ki kanwata, Umma ma na son ki sosai, amma bata da zabi ɗaya wuce ta tafi ta barmu”
Dakin ya sake daukan shiru, can Munaya tace “kwanta Amnah, bari nayi fitsari”
bayan ta kwantar da ita ta mike zuwa toilet, tana cikin gyara skirt din, ta ji karar faduwar abu kamar karfe kan tiles, tayi saurin buɗe Kofar toilet din ta fito, ta ga karfen da ake rataye karin ruwa ne ya fadi, ta kalli gadon taga Amnah ta fisge karin ruwan da aka Mata, hannun ta tallafe da kanta tana jijjiga hadi da mika sosai, cikin sauri ta nufi gadon tana kiran sunan ta cikin tashin hankali, amma ba amsa, ta fara kiran sunan doctor da karfi, tun daga office din sa ya jiyo Muryar ta, haka zalika nurses ɗin, cikin sauri suka shigo dakin, likitan baya bukatar ta mai karin bayani, he knows something is wrong.
Tsawon mintuna goma kafin likita yayi nasaran laffar da jijjigan da take, sai dai bata fasa rike kan ta ba, hakan yasa likitan yayi mata alluran bacci domin ta samu sauƙin radaddin ciwon kan, ya mayar mata da karin ruwan, cikin k’ak’arwan murya Munaya tace “likita, ya take yanzu?”
“Likita ya saka hannu a aljihu, ya sauke numfashi sannan yace “as you can see, she’s unconscious, kamar yadda na fada Miki a baya mafita daya ce a mata aikin nan cikin gaggawa, domin za ki iya rasa ta a ko wani lokaci, I’m sorry to say, Amma cutar ya dai gejin da komai zai iya faruwa” yana gama fadin hakan ya fice daga dakin, nurses ɗin ma suka rufa masa baya.
Munaya ta bi likitan da kallo, tamkar ta ga sabon Hallita, gaba-daya ta rude ta firgice, ta dawo bakin gadon ta rike hannun Amnah, ta fara rera sabon kuka ƙasa-kasa, can kuma kukan ya dauke dif sakamakon tuno da *AA DAWOOD MOTORS* ma’ana wajen aikin ta, shaf ta manta da cewa tana aiki a wani waje banda yanzu, ta tuno kirkin Shakur, zata je wajen shi domin ya taimaka mata da kuɗin asibitin Amnah, ta yarda ko a albashin ta ne a dinga Zara, zata cigaba da musu aiki har ta gama biyan kudin da suka ara mata, koda shekaru goma sha biyar hakan zai dauke ta, wanna tunanin da ta yi ne yasa wani ƙarfi yazo mata, ta sumbaci hannun Amnah, tamkar wacce Amnah ke jin ta tace “in Sha Allah za a dace, Bara na je yanzu nan zan dawo kin ji” ta saki hannun ta a hankali ta nufi Hanyar barin dakin, har ta ɗora hannun ta a kan handle na kofar ta waiwayo tana kallon fuskar Amnah data yi fayau ta kuma kara fari, ta ji wani abu da bata san menene ba ya daki zuciyar ta, tayi saurin dauke idanun ta daga kanta ta bude dakin ta fice da gudu.
****
*MALEEK*
Tun zuwan sa office ya kasa gane kansa, wani irin mixed feelings da bai taba jin makamantansa ba yake ji a yau, ya mike zuwa dakin da yake hutawa, Bayan dan madaidaicin fridge dake dakin ya dauko irin box din da yake ajiye barar sa a gida ya dora kan doguwar sofa ya danna password ya ciro Barasa guda biyu ya zauna ya shanye tas, kana ya mayar ya rufe, yana ganin tunda ya sha barasan nan zai dawo normal, da wannan tunanin ya mike ya mayar da box din ya fita zuwa cikin office din sa, ya zauna, yana son taba aiki a system amma har wani biyu-biyu yake ganin rubutun screen din, ya kifa kansa da yayi masa nauyi a kan table glass.
Cikin sauri-sauri, gudu gudu take taka matatakalar benen domin isa office din Maleek, sai haki take saki domin ko da hawo saman kaɗai aka bar mutum zai gaji, bare ita dake zirga-zirga tun safe, bayan ta zo kofar shiga office din maleek sai ta tsaya tana sakin numfashi, sai data yi seconds biyar a haka kana ta tsaya bakin kofar ya buɗe ta shiga, ta fara neman Shakur, sai dai baya office din, hakan ya tabbatar mata da cewa bai zo ba yau, sai Maleek data gani ya kifa kansa a table, ta ma kasa magana sai ido data zuba masa.
*Maleek*
Shigowar mutum da ya ji ne ya sanya shi dago kansa, ya zuba wa Munaya rikitatun idanun sa, Wanna karon ba kallon tsana yake mata ba, kallon sosai yake bin ta da shi, tun daga kasa zuwa sama, a hankali ya motsa labb’ansa yace “You! Duk lokacin da kika ga dama kike zuwa aiki huh?”
Duk da bada fada yayi mata magana ba, amma sai da sautin Muryar sa ya bawa Munaya tsoro, domin amon ya fita da wani irin kalar tune da baki bazai iya furtawa ba, sai dai a bar wa zuciya, cikin rashin sanin abin yi ta durkusa tace “dan Allah dan Annabi kayi hakuri, wallahi Amnah kanwata ce ba lafiya, yanzu haka tana asibiti unconscious, tana da brain Cancer, likitoci sun ce kudin aikin da za a mata 3.9 million ne, Dan Allah dan Annabi ka taimaka min, kada na rasa kanwata, wallahi na yarda ko a albashina ne kana cire wa har na gama biyan ka, dan Allah kaji” ta karasa tana fashe masa da kuka mai ban tausayi.
Maleek ya cigaba da kallon Munaya, sai k’awata masa surar ta ake, yana ganin sabanin abinda yake a zahiri, gani yake bai taba ganin kyakkyawa kuma cikakkiyar mace kamar ta ba, ya saki wani shu’umin murmushi yana ganin zai yi amfani da damar sa, zai yi amfani da abinda ta roke shi ya kawar da abinda yake ji, domin shi kadai ya san balai’n da yake ji a marar sa, daurewa kawai yake, cikin takama da isa yace “ina da kudi fiye da abinda kike bukata, akwai wasu ma a drawer nan, zan baki million hudu ma, amma on one condition, zaki bani kanki” ya faɗa cikin gushewar tunani.
Murnan da Munaya take ya koma ciki, tashin hankali ya maye gurbin murmushin data fara yi, sam bata taɓa sammanin irin wanna maganar Daga bakin Maleek ba, duk da karancin shekarun ta amma ta fahimci abinda yake nufi, ta fara girgiza kai tana komawa da baya, har ta jingina da bango, tasa hannun ta ta share hawayen dake zuba a idanunta tamkar an balle famfo tace “dan Allah ka taimaka min, kaji tausayi na, , I’m only 15 year’s, and I’m a virgin, karka lalata min rayuwa ta please”
“Hey shut up! ban yarda baki san namiji ba, a zamanin nan bana jin akwai mace da zata ce min tana tare da budurcin ta na yarda, don’t pretend to me, ba dole na miki ba, zaɓi na baki, if you truly love your sister Zaki iya komai domin ceto rayuwar ta, so the choice is yours” ya karasa cikin Murya da zuwa yanzu mutum zai fahimci cewa ba a hayyacin sa yake ba, Munaya ta dinga ji tamkar mafarki take, daman haka boss din ta yake bata sani ba? Sam bai yi kama da wanda zai iya furta kazaman kalaman nan ba, bare Kuma ya aikata su , ga koshi ga kwanan yunwa, tana tuno nasihar Umma kan rike mutuncin ta, ta kuma tuno halin data bar Amnah a asibiti, tamkar zararriya haka ta fita daga office din tana fadin a’a Bazan iya ba!” Har ta sauka kasan bene, taji Muryar likita tamkar yanzu yake mata magana _”as you can see, she’s unconscious, kamar yadda na fada Miki a baya, mafita daya ce a mata aikin nan cikin gaggawa, domin za ki iya rasa ta a ko wani lokaci, I’m sorry to say, Amma cutar ya dai gejin da komai zai iya faruwa_”
And then taji Muryar Umma tamkar yanzu take gaya mata _”Munaya ga amanar kanwarki nan na baki, ki kula da ita, karki bari tayi kukan maraice, ke ma ki kila sosai, ki kula da mutumcin ki na diya mace domin shine darajar ki, kar ki bari wani rudi na duniya yasa ki rasa wanna tsadadden darajan naki”_ kalaman Umma na karshe a gareta kenan.
Sai ta zama so confused ta rasa ya zata yi, ta zube nan karkashin stairs din tana fashewa da kuka gwanin tausayi, ta toshe kunnen ta saboda ta daina jin maganar Umma dana likita, domin sai amsa kuwwa maganar su take a hannun ta, ta tuna duk minti daya data bata daidai yake da rasa Amnah, ba kuma zata so ta rasa tilon kanwar ta ba, ta mike cikin sauri kamar an tsikare ta ta koma saman cikin gudu, wanna karon bata ji wahalar hawa benen ba saboda tashin hankalin da take ciki, har gaban sa taje tana jin mugun tsoron sa da take ji na barin zuciyar ta, a raunane tace “na amince, na yarda ka kwanta da Ni, na amince zan baka kaina, na amince ka karbi budurcina, matukar zaka bani kudin asibitin kanwata, i don’t want to lose her please” ta karasa cikin wani sanyin murya tana runtse idanun ta, amma hawaye bai zuba ba, sai jaa da fuskar ta yayi tamkar tumatir.
Maleek ya mike, yana haɗa hanya har ya zo gabanta, ya watsa mata idanun sa da suka yi mugun ja, domin abu biyu ne ya hade masa, sha’awa da gushewar hankalin (maye), ya saki wani shu’umin murmushi, Cak ya dauki Munaya kamar yar tsana zuwa dakin da yake hutawa, Munaya da jikin ta ke k’ak’arwa ta fashe da kuka, duk yanda ta so dakewa kasa wa tayi.
#Share
#MunayaMaleek2023
#NoorEemaan
07082281566