Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 32

Sponsored Links

XXXII….
<32>

*MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, evidence of payment to 07082281566, thanks for your patronage*

Cikin sauri sauri Shakur ke taka matatakalar da zai sada mutum da office ɗin Maleek.

Related Articles

Tun kafin ya shiga yaƙe jin kukan little Amnah, Cikin sauri ya karasa, kofar ta bude kanta ya shiga, da a ce a yanayi barkwanci yake babu yanda zai hana shi dariya domin gaba-daya fuskar Maleek ta hargitse dalilin kukan da little Amnah take, jijjiga ta yake yana mata waƙoƙin ɗaya saba mata a duk lokacin da take rigima amma na yau kam bai yi tasiri ba.

Ya tako har gaban Maleek Yace “ka ga rayuwar ka? Meyasa kake da taurin kai ne, yanzu ma da take kuka bazaka mayar da ita ba?”

“Eh ba zan mayar da ita ba, na aika a siyo min Madara yara da komai da zata buƙata na shan Madarar, ina bata Zaka ga tayi shiru”

 

“Allah You re not serious Maleek, ta fi bukatar mama akan wanna Madarar, kawo ta nan”
Shakur ya fada yana kokarin karbar ta.

Maleek ya ƙara rike ta gam yace “Shakur You thought I’m joking right, ka zata wasa nake? I said angel is not back to that girl”

“Oh don’t just call her that girl, Amnah’s mother for Allah’s sake, ka bani Ita nace maka” Shakur ya fada cikin daga sauti yana kokarin janta.

“Nace bazan baka ba, leave her alone” shima Maleek ya fada yana ƙara rike ta, yarinyar data yi shiru tun lokacin da suka fara fadan su ta fasa kuka sosai ganin ana ta jani in jaka da ita.

A rude kana da ɓacin rai Maleek Yace “ka gani kana sata kuka ko? Ka sake ta nace!” Maleek ya ce yana janta.

Shima Shakur so yake ya karbe ta lokaci ɗaya domin yarinyar ta huta da wanna jan da suke mata, ya daddage ya kwace ta da karfi yana faɗin
“bazan sake ta din ba, Allah You re crazy” idanun sa sunyi luhuluhu kamar zasu fado, Muryar sa har rawa take abinka da wanna bai da hayaniya.

Kukan da little Amnah ta fasa har can cikin dodon kunnen sa yaji ta, wanna dalilin kadai ya saka bai kara karbar little Amnah daga hannun Shakur ɗin ba.

Yana sauke numfashin ɓacin rai yace “ni ne mahaukaci, Ni kake kira mahaukaci?”

“an faɗa maka din” Shakur ya ja saki kana ya nufi hanyar fita bayan kofar ta bude kanta ya fice da little Amnah yana rarrashin ta.

Maleek ya koma da baya ya zube a kujera hannun sa dake da kansa, wani mugun ciwo kansa ya dauka.

Sosai Shakur ke sharara gudu akan kwalta abinda bai taba yi ba.
Burin sa kawai ya isa gidan doctor Aaban domin ba ƙaramin kuka little Amnah ke yi ba, dan ma ya rufe glasses din motar sa ba’a jin kukan ta da sai ace sato ta yayi.

Munaya ta mike da kyar jin horn domin zazzaɓin ya kara rufe ta, ta yamutsa fuskar ta cikin jin ciwo ta zura hijab kana ta fito daga dakin ta.

Gabanta na faduwa ta nufi Kofar da zai Sada mutum da farfajiyar gidan, bata san waye ne yazo a cikin wadanda zuciyar ta ke raya mata..

Cikin sauri ta nufi motar ganin ta Shakur ce, shi ma Shakur ya fito da little Amnah data yi baccin wahala, hannun ta a bakin ta da alama tsotsar hannun take baccin ya dauke ta.

Ya sakar wa Munaya murmushi, kwalla mai haɗe da murmushi a fuskar ta itama, ta karɓi little Amnah daga hannun sa, a sanyaye tace “nagode ya Shakur”

“Bakomi, a bata abincin ta ɗan Allah, sannan a gasa jikin ta idan za’a mata wanka”

“Wani abun ne ya same ta ya Shakur?” Ta tambaya cikin damuwa.

“A”a no babu komai, na ga yau ta sha wasa dayawa ne”

“Toh” daga haka bata kara cewa komai ba ta koma cikin gidan, tana jin dadi da Allah yasa barrister Abrar bata dawo ba har Shakur ya kawo da little Amnah.

Ko dakin ma ta kasa komawa, ta zauna a nan falon, little Amnah ta bude idanun ta, ta tabe baki zata yi kuka, Munaya tayi saurin dage hijabi dinta ta fito da maman ta ta sanya wa little a baki, cikin wani sauri ta cafke ta fara sha, wani mugun zafi ne ya ziyarci ƙwaƙwalwar ta, ta daure ta cije, bata yi ihu ba, sai wasu hawaye Masu dumi da suka zubo kan kumatun ta, ta share hawayen ta kana ta bi kayan jikin little Amnah da kallo, a ranta take aiyana ko Meyasa ya cire mata kayan jikin yarta ya sanya mata wasu? Sai kuma ta tabe baƙi cikin kauda tunanin sa a ranta.

Little Amnah ce ta cire bakin ta da kanta alamun ta koshi ta saki gyatsa, Munaya ta sumbaci labbanta kana ta ɗora ta a kafadar ta, daidai lokacin kuma taji wani horn, da alama masu gidan ne suka dawo.

*MALEEK*

Har dare zuciyar sa a dagule take ya rasa abinda ke masa dadi, yau ma kin yi dinner yayi, Shakur ma yaso yaki yi amma bayaso iyayen na su su fahimci halin da suke ciki da dan’uwan sa, amma har ransa bai ji dadin abinda ya faru a tsakanin su ba dazu.

Maleek Kasa bacci yayi so yake yaji a wani hali yarsa take jiki domin wahalar da suka bata.
Ya shanye fushin sa ya dauki hanyar dakin Shakur.

Shakur yaji dadin ganin dan uwan na sa, amma bai nuna ba ya sha kunu shima.

Maleek ya jingina jikin sa da kofa, Muryar sa babu walwala yace “ka kira kaji ko angel ta yi zazzaɓi”

Shakur ya masa Banza kamar bai ji abinda yace ba

“I’m taking to you Shakur!”

“Yes, me kace?” Shakur ɗin ya fada.

Maleek ya datse labbansa da haƙoran sa, kamar bazai yi magana ba sai yace “nace ka kira ka tambaya ko my angel tayi zazzaɓi”

Cikin cigaba da raina masa hankali Shakur yace “Meyasa zata yi zazzaɓi?”

A wanna bigiren bazai iya cigaba da danne ɓacin ransa ba, Cikin kakkausar murya Yace “don’t ask me that silly question again, bayan ta ci kasa safe, da yamma Kuma ga abinda muka mata…, ya Salam yata ta sha wahala yau” ya karasa cikin jin ciwon abin.

Dariya ce take jin Shakur ya danne ta, Wato bai taba ganin wanda ke son yar sa kamar Maleek ba, abin nashi kamar hauka, in dai a kanta ne komai ma zai iya aikatawa ko ya fada.

“Ai na kira su, na tambaye ta, lafiyar ta kalau”

Ya saki ajiyar zuciya kana yace
“Ohhh, na manta maganin ta a mota” yace cikin dafe kai.

“Maganin menene kuma?”

“Na kai ta hospital dazu”

“Saboda me? Saboda Ƙasar data ci?”

“Eh! Saboda kasar data ci, ko ka ɗauki abin da wasa?” Maleek ya tambaye shi yana daura hannuwan sa biyu a kirji.

“A’a, kawai yanda kake yi ne kamar kafi kowa son ta shi…”

“hakane, Da me kake tunani?” Maleek ya katse shi.

“Har Munaya data haife ta kake nufi?”.

“Eh har ita din, ko kana da ja?”

“Ni na isa Allah ya ja da ran daddyn Amnah”
Shakur ya fada cikin barkwanci, sai ya ga lips din Maleek yayi curving alamun murmushi zai subuce masa amma yana danne ta, Maleek bai ce komai ba ya fice, yana fitowa ya ga Hajiya Sa’adah suka hada ido, ta taho wajen sa cikin sauri, “my boy daga dakin ka nake, bazaka gayamin abinda ke damun ka ba?” Hankalina ya gagara kwanciya” ta fada kamar zata saki kuka.

“Ba komai mum” ya fada yana Mata murmushi.

“Toh muje na zuba maka abinci kaji” ta fada tana riko hannun sa.

“No mum it’s late already, bana jin yunwa”

“A’a muje dai ko tea ne sai ka, taya zaka kwanta a hakan?” Ya kara nacewa, ta rungumo sa gefen ta, sai Kuma tayi saurin sakin sa tana rike hannunsa domin Alhaji Dawood zai iya fitowa Daga daki ya gansu.

****

*Bayan shekara biyu*

A cikin Wadannan shekarun abubuwa da dama sun faru, wani mai dadi wani akasin sa.

A Cikin shekarun nan aka samo wa Munaya kwararren lesson teacher ya koya mata karatu, kasancewar ta jima sosai rabon ta da makaranta, bayan nan aka saka ta a wani tsadadden makaranta sai dai daga Ss3 ta fara domin ta samu zana jarabawar waec da neco.

Bayan result ya fito, sakamakon data fito da shi was excellent.

Little Amnah ta yi wayo sosai domin saura watannin biyu ta cika shekara uku, hakan kuma yayi daidai da shigar Munaya shekaru sha takwas, tun ranar data sha marin nan kuwa bata kara haduwa da Maleek ba, illa iyaka ya zo ganin yarsa kullum kamar yadda ya sa6a.

Cikin nutsuwa ta buɗe kofar toilet din ta, sanye take da bathrobe fari kal, sai towel data daure kanta da fasalin dauri mai V shape, ta zo gaban madubi ta tsaya, ta kura wa kanta ido sosai, tayi mamakin yaushe ta dawo haka, ta cikin madubin ta ga yanda kugun ta yayi wani irin fadi, mazaunan ta basu da wani girma sosai, amma hips dinta ya fito sosai kamar an dasa ko kuma tayi ciko, ta Daura hannun ta kan lafaffen Cikin ta, kijrin ta sun kara girma, sai ta ga ma ta kara tsayi a madubin, ta kalli yanda fatar ta ke sheki sosai, ta lumshe idanun ta kana ta zauna a kujerar gaban madubin, ta cire towel din kanta, gashin ta mai yawa ya zubo ya rufe fuskar ta, ta mayar baya sannan ta yi oiling din sa, ta saka combo ta taje shi, ta kara parking din sa, jelar har bayan ta ta shafa mai, kasancewar bata son makeup kawai lipsgloss ta shafa a karamin bakin ta, ta zizira kwalli, idanun ta suka kara girma da haske, ta taje girar ta da bai da cika sosai amma a saite yake.
Ta mike ta bude wardrobe dinta ta fito da wani Turkish gown kalar *burnt orange*

Tana gama saka kayan ta aka kwankwasa kofar dakin ta, ta nufi Kofar ta bude ,Junior ne yana rike da hannun little Amnah, ta musu murmushi, little Amnah ta rungume ta, Munaya tace
“oyoyo kun dawo?” Ta fada tana shafa kan Junior yayi mata murmushi yace
“Eh, Mami ma tace kizo”

“Toh gani nan, munaya tace, ta koma ta dauko bakin hijab ta saka, kana ta riko hannun su duka biyun suka nufi ɓangaren barrister Abrar.

“Assalamu alaikum” munaya tayi sallama bayan ta bude dakin.

“Wa’alaikumu Salam, karaso ki zauna” barrister dake zaune a tangamemmen bakin gadon ta ta fada.

Munaya ta zauna a gefen ta, kanta a kasa.

“Result ɗin ku ya fito, kuma alhamdulillah bakida wata matsala, rannan kin ce min kina da burin yin karatu, shine yanzu nake so ki gayamin me kike son karanta domin a fara miki processing admission”

Wato doctor Abbas yayi gaskiya daya ce su barrister are the most kind hearted mutanen da ya sani, tabbas bai yi karya ba mutane ne masu mutumci, karamci da taimako, da fari ta ɗauka cewa idan ta haihu zasu nemi ta bar musu gida, amma sai ta ga ba haka bane, a lokacin da suka dawo daga asibiti ta ga an sanja mata komai na dakin ta. Sai ta kara tunanin kila sai Amnah tayi wayo zasu tafi, sai ta ga ba haka bane, suka dauko mata me lesson har gashi tazo ta zana jarabawar fita a Sakandire, yanxu kuma ta tabbatar da cewa lallai suna maraba data cigaba da Zama a gidan.

“Kin yi shiru Munaya?” barrister ta fada..

Hakan ya katse wa Munaya tunanin ta, ta dago a hankali tace “mami dawainiyar tayi yawa”

“Karki damu ba wani dawainiya, yiwa kai ne, fadi min ina jinki”

 

Munaya tayi jim kadan sannan tace “dentistry nake son karanta”

“Masha Allah, kice zamu samu likitar hakori a gidan nan”.

Munaya ta rufe fuskar ta cikin jin kunya, barrister tayi dariya tace “toh Allah yayi jagora”

“Ameen” munaya ta amsa sai ta durkusa zata fara kwararo godiya Barr Abrar ta dago ta tana hana ta godiyar .

***

“Hello maimoon, Alhajin ya tafi, yanxu drive ya kai shi airport wallahi, a’a bana jin zai dawo da wuri, Kano fa za shi, shi Shakur kuma tun bakwai da rabi ya bar gidan nan zuwa makaranta” Hajiya Sa’adah ta fada wa Hajiya maimoona.

“Sa’adah this is the perfect time, yanxu ne lokacin ɗaya dace ki aikatawar da nufin ki domin cikar Burin ki, baki gaji ba? Shekaru kusan nawa kina fama da abu ɗaya, toh wallahi muddin wannan rana ta cewa bata tunanin zaki sake samun yanda kike so”
Hajiya maimoona ta bawa Hajiya Sa’adah shawara.

“Haka ne maimoona, yanzu ne lokacin ɗaya dace, amma ina tsoron kada hakan ya saka Maleek jin haushina”

“Malama babu wani haushi, yaran zamani ne fa, idon sa a yake tarr wallahi in gaya miki, sai dai ma ya miki maraba, ba kin siyo desire tablet din nan ba? TOH maza ki zuba masa a abin sha, karki manta da yin video record din nan, hohohooo kawata yau zata amarce da sabon jini” ta fada cikin dariya tana katse kiran.

Hakan ya kara wa Hajiya Sa’adah kwarin gwiwa, musamman data lissafa tun bayan dawowar Alhaji Dawood din tayi iya yinta wurin cimma burin ta amma abu ya ci tura kullum bata samun nasara, tabbas wanna shine lokacin ɗaya dace, domin daga ita sai Maleek a gidan yanxu, kafin ta Fara waya ta sallami masu aiki su tafi sai ta neme su, mai gadi kuma yana can yana fama da redio a bakin gate, tayi murmushi sosai, sannan ta nufi kitchen, banana smoothie daya sha madara ta haɗa masa bayan ta zuba kwayar motsa sha’awa har uku domin ya yi saurin kama sa, ta daura a tray ta nufi dakin sa, ta tsaya Tsawon mintuna biyu ta sauke numfashi kana ta tura Dakin a hankali ta shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button