Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 40

Sponsored Links

XL…

*MunayaMaleek is Five hundred naira only, via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, send evidence of payment to 07082281566*

Idanun Munaya a kasa yayinda suke tafiya, duk wani taku daya da ta yi daidai yake da digar hawaye a kasan interlock din farfajiyar gidan, yanxu dukkanin jama’ar da suka taru a nan domin zaman makokin ya Shakur suka zauna? Ya Shakur baya duniya yanxu, ya tafi ya bar su, gani take kamar mafarki ne, gani take kamar zata gan shi yana mata barkwancin sa, gefe daya kuma ga uban surutun little Amnah daya ishe ta, sai cewa take “mummy biki muka zo, mummy bikin wa ake yi?”

Related Articles

Kallo daya da barrister tayi wa matar dake zaune sanye da hijabi hadi da carbi da yadda idanun ta ke kumbure suka tabbatar mata da cewa itace mahaifiyar su Shakur, barrister tayi sallama matan dake zaune suka haɗa baƙi wurin amsa wa, har lokacin tana rike da hannun Munaya, dayan hannun na rike da little Amnah, ta samu waje suka zauna sannan ta ce.
“Ina kwanan mu, ya karin hakurin mu?” Matan suka haɗa bakin amsa wa da cewa “hakuri sai ma’aiki”
Barrister ta kara cewa “Allah ya jikansa da rahama, halin sa na gari ya bi…”

Kukan da Hajiya Sa’adah ta saki ya saka barrister dakatar da addu’ar da take, a hankali munaya ta dago kanta ta sauke su kan Hajiya Sa’adah, sai ita ma wani sabon kuka ya kufce mata, Hajiya Sa’adah ta tsagaita da kukan da take ta kura wa Munaya ido Tsawon lokaci kamar mai nazarin wani abu ta kara maida idanun ta kan little Amnah tana kallon ta sosai
“Yaya dan Allah karbi ki sha shayin ko kadan ne, tunda aka yi rasuwar nan baki ci wani abin kirki ba” kanwar ta mai bi mata data zo daga Katsina ta fada, hakan ya katse Mata tunanin da take kan Munaya da yarta.
Matan dake wajen suka haɗa baƙi wurin lallaba ta kan ta sha.
Hajiya Sa’adah ta karɓi cup din hannun kanwar ta ta saboda bakin mutane ba dan tana sha’awar saka komai a cikin taɓa.

“Ni kam ruwan da aka saka yaron nan Abdul Maleek ya kare kuwa?” Wata dattijuwar mata ta fada da alama daga dangin Alhaji Dawood take saboda kammanin su.

Wata matashiyar mata tace “eh an cire masa tun dazu, sai dai abinci ne yaki ci”

Nan mutane suka shiga tausaya masa kowa da irin abinda ya ke fada.

“Allah Sarki… Maleek din na ciki kenan?” Inji barrister Abrar.

Dattijuwar nan tace “eh yana ciki, bayin Allah bamu shaida ku ba, daga ina kuke?” Sai kuma tace “ko da yake Abdulshakurr na kowa ne, Allah ya jikansa da rahama, ku shiga ku masa gaisuwa shi Maleek din, yana can dakin” ta nuna musu da hannu.

Barrister Abrar ta mike ta nufi dakin, a tunanin ta Munaya zata biyo ta, bayan ta fito, ta dawo ta zauna, kasa ƙasa tace “je ki mai gaisuwa Munaya kinji yi hakuri” hakurin da Barrister Abrar ta kara ambata sai ya sanya wasu sababbin hawaye suka zubo mata, ta mike a hankali, Amnah ta kama hijab din ta, matan dake cike a falon suka bita da kallo ganin yadda idanun ta suka kumbura
“Allah Sarki, kodai budurwar sa ce? da alama sun Shaku” dattijuwar matar nan ta kara fadi da alama tana da surutu.

Barrister Abrar ta girgiza kanta kawai, Hajiya Sa’adah kuwa ta bi Munaya da ido, har suka bacewa ganin ta.

A hankali munaya ta tura kofar, little kuwa ta ruga a guje ta dane jikin sa tayi ihun “yeeeeeee Daddy na”

Munaya dake tsaye bakin kofa taji Zuciyar ta ya kara karye wa ganin hotunan sa ne da Shakur a baje kasan tiles, yayinda shima ke zaune a kasan, sumar kansa a hargitse kamar wani Maraya daya rasa komai da kowa haka ya dawo, yayinda cannula da aka manne da salletape na hannun sa har yanzu, a yau sai taji wani mugun tausayin sa, tabbas mutuwa ta wuce wasa, domin duk haushi, kiyaye ko gaba da kake wa mutum matukar maganar mutuwa ta shigo ciki ana mantawa da ita ne a wanna lokacin, a halin da take ciki na jijjigar da mutuwar Shakur tayi mata ta manta abinda ya shiga tsakanin ta da Maleek, ta samu ta tsugunna da kyar saboda wani jiri jiri take gani, ta zauna dab da shi, cikin Muryar ta dake rawa sakamakon kukan da take tace “ya karin hakuri?”

A hankali ya dago rinannun idanun sa masu kama da gauta ya zuba mata cikin kankance su, hawaye shar shar suka ƙara zuba wa Munaya, ta kara cewa “ya karin hakuri?”

Kawai ji tayi ya haɗe ta da little Amnah dake jikin sa ya rungume, ya daura kansa a kafadar ta ya shiga hura iskan bakin sa, numfashin sa na sama sama cikin son shanye kukan sa, hakan ya gagara kukan mai sauti ya kufce masa da wani irin masculine voice, kukan na sa ya kara raunata zuciyar Munaya ta saki kukan ita ma, kamar yadda kukan sa ke kara sanya ta kuka haka shima, kukan ta na kara tuno masa wanene gudan jinin sa dake binne a gidan da suka taso tare amma ya tafi ya barshi.
Kukan da suke ya sanya little Amnah itama fasa nata kukan, su ka hadu su uku suka dinga rera kukan gwanin taba zuciya tsawon lokaci.

_BAYAN SATI DAYA_
*9:00pm*

Tsaye yake bakin window yana kallon garden daidai inda kabarin Shakur yake, bai damu ya dinga kwana kusa da wajen ba kullum, amma Daddy ya hana shi, duk da ba Shakur ɗin a raye a doran kasa amma wata kaunar sa dake binne can Kasan zuciyar sa ke taso masa a kullum, yaji karar buɗe kofar dakin sa amma bai juyo ba.

“AbdulMaleek!” Ya ji Alhaji Dawood ya kira shi da cikakken sunan shi, abinda ya manta rabon daya kira shi da hakan, amma hakan bai saka ya amsa ba, illa dan waiwayo wa da yayi, waiwayowan ba yana nufin ya gan shi bane kasancewar bai juyo duka ba, ya ɗai waiwayo din ne domin Alhaji Dawood ya san cewa ya ji kiran da yayi masa.

Alhaji Dawood ya girgiza kansa, kana cikin sanyin jiki ya tako har bayan sa ya riko hannun sa yace “zo ka zauna”
Ba musu ya bishi suka zauna a bakin gadon.

Alhaji Dawood ya numfasa ya ce “Maleek! Har zuwa yaushe Zaka cigaba da tsaye a wajen nan a duk dare?”

“Har zuwa lokacin da nima zan kasance a inda yake kwance yanzu Daddy” ya karasa da kiran Alhaji Dawood da irin yadda Shakur ke kiransa, ya daga kansa sama zuwa bango inda hoton sa dana Shakur ke manne, sui dauki hoton ne wata ranar Lahadi ba zai manta ba, sun haɗe bayan su waje daya yayinda hannun su dake daure da tsadadden agogo ke kan gemun su, Shakur na dariya yayinda fuskar Maleek ke sake amma bai yi ko da murmushi ba hoton yayi matukar kyau, ya taune labbansa kana ya ɗauke idanunsa daga kallon hoton ya mayar kan Alhaji Dawood ya cigaba da cewa “ina jin kamar na tauye kaunar dake wa Shakur idan har ina kwance a gado a well furnished room yayinda shi kuma ke kwance a karkashin kas..”

“Maleek! Shakur baya bukatar dukkanin wani abu daga gare ka yanzu sai addu’a, babban kaunar da zaka masa shine addu’a, kamar yadda muke kyautata zato da cewa Shakur dan aljanna ne, idan zaton mu ya zama gaskiya toh lahirar Shakur tayi kyau, ya kuma samu ninkin jindadi daya fi na duniya sau ba adadi, You know you can’t forever continue like this, kaima kana da rayuwa da buririkan da kake son cimma, dole Zaka ɗauki dangana shine cikakken imanin ko wani Muslimi”

“Dad duk wani buri da nake da shi ya fice min a rai, taya zan cigaba da jin dadin rayuwa bayan ba Shakur a labarin rayuwa ta” ya ce yana rufe hannun sa kan fuskar sa.

Alhaji Dawood ya cire hannun na sa sannan yace “manta Shakur a kundin rayuwar ka dama rayuwar mu ba abu bane mai yiwuwa, Shakur is unforgettable a Rayuwar mu, idan rayuwa ta bai kai ba, ina son ka bawa har jikokin ka da za’a samu daga yarka Amnah, kuma jika ta fari a gareni labarin sa, su san kyawawan halayen sa da nagartan sa, ko sayi koyi da shi”

Tun lokacin da little Amnah ta shigo cikin maganar da Alhaji Dawood ke yi Maleek ya dago kansa kusan a firgice, domin abu ne daya zo masa a bazata ya Kuma bashi mamaki kasancewar bai taɓa tunanin ya san da ita ba, ya zuba masa ido har ya kai karshen maganar sa, so yake ya tambayi Alhaji Dawood din kan taya ya sani amma ya kasa.

Alhaji Dawood ya mike tsaye kana ya ce “Shakur told me what I suppose to know, check you phone I sent you the massage, abinda kayi babban kuskure ne Maleek, wanna ba tarbiyyar Muslunci bane, banso na samu jika ta wanna hanyar ba, amma bazan kyamace ta ba, domin ita din bata da laifin komai, raina ya sosu da faruwar hakan, wanda da a normal days ne daka fuskanci mummunan ɓacin rai na, amma darajar Shakur, Shakur kadai ya saka zan kyale maganar iya nan”
Yana gama fadin haka ya fice daga dakin.

Da kallo ya bi Alhaji Dawood din har ya fice daga dakin, sannan ya janyo wayar sa da bai kara bi ta kanta ba tun ranar rasuwar Shakur, ya buɗe ta sakwanin na rige-rigen shigo masa, bai bi ta kan su ba kai tsaye wajen inbox ya shiga, nan ya ga sakon da Alhaji Dawood ya tura masa.

Hawaye ne suka ciko idanun sa sosai tamkar zasu zubo a lokacin da yake karanta sakon, dama daga lokacin da Shakur ya kwanta asibiti Ya fahimci cewa ashe shi din mai rauni ne, bakomi zuciyar sa zai iya dauka ba.

Wanna dalilin na ɗaya daga cikin Abin yasa bazai taba manta Shakur ɗin sa ba, Baya raye, amma ya yaye masa matsalar da yake fargaban taya zai tunkari Alhaji Dawood da shi.

Ya shiga chat din su da mahaifin sa ta sms ya tura masa cewa _dad nasan na aikata ba daidai ba, na san nayi kuskure, but it wasn’t my fault, ban yi da gangan ba wallahi, kawai na dauki hakan a matsayin part of my destiny ne, ƙaddara ta ce hakan, dan girman Allah ka yafe min, hakan bazai sake faruwa ba_

Duk da cewa Shakur ya riga daya rokon masa gafara amma shima ya kamata ya kara bada hakuri.

_ka nemi gafarar Ubangijin ka_ shine amsar da Alhaji Dawood ya tura masa.

Tsawon lokaci yana kallon amsar, tabbas bai taba tunanin neman yafiyar Ubangiji ba tun bayan daya aikata zunubi dake cikin zunubai masu girma.

Ya mike ya koma window’n ya tsaya, ya zura hannun sa daya cikin aljihu a hankali yace _”dear Shakur! Ina so na bayyana maka irin godiyar da zuciya ta ke maka bisa kauna da hadin kai da kake bani tun yarinta har izuwa yau da baka raye, kai ɗin ba iya dan’uwana bane, kai din abokina ne very long time ago, thanks for being amazing, the bond we share is truly exceptional, and I’m so grateful for you presence in my life, and I’m so hurt and heartbroken with your absence in my life, I pray Allah grant you jannah, may your gentle soul rest in peace, Allah ya sa kana kwance cikin salama, rest on kid bro, Maleek loves you_”

*Hajiya Sa’adah*

Kamar mai tsoron tunkarar abu haka ta nufi wajen Alhaji Dawood dake zaune a falo shi kadai, kana kallon sa kasan yana cikin kadaici, yanzu ma sanye take da hijab, tunda aka yi rasuwar nan shigar ta kenan, hakan Kuma bai boye ramar da duhun data kara ba.

Daga dan nesa da kujerar da yake zaune ta rabe, ta hadiye wani yawu mai kauri kana ta iya buɗar baki tace “Alhaji ina wuni, ya karin hakurin mu”

Alhaji Dawood yayi shiru ya tsayar da idanun sa waje daya, ba tare da ya kalle ta ba, ta fashe da kuka sosai tace “Alhaji kayi haku…”

“Dakata!” Yace a dan kausashe yana daga hannun sa na hagu sama, kana ya fuskance ta yace “dama baki wahalar da kanki ba, domin baƙi da kalaman da zaki wanke kanki da su a wajena, domin ni ganau ne, me na miki Sa’adah, me na miki da kika zabi tarwatsa zuciya ta, mena rage ki da shi da kika zami kuntata min ta wanna hanyar, Ni Muslimi ne, na dauki ƙaddara, Allah Kuma ya ƙaddara cewa iya zaman Shakur kenan a duniya, amma ke ce sila, ki sani, wallahi zan dinga kallon ki a matsayin hakan har karshen numfashi na”

Hajiya Sa’adah ta kara sautin kukan ta tace “Alhaji dan Allah kayi hakuri ba laifina bane Ni kadai, kai ma kana da laifi, tun bana damuwa da tafiye-tafiyen da kake har na zo ina damuwa, amma baka yi komai a kai ba, Rashin ka a kusa ya sanya na fara kwadayin Maleek, bana samun nutsuwa da kai, baka da lokacin mu, kasuwanci kawai ka saka a gaba, tarbiyyar yara da komai ka tsakar min, shaidan ya ribaci zuciya ta har na aikata hakan, amma wallahi nayi nada….”
Gwanin tausayi yace “Sa’adah bana gamsar dake? Amma baki taba gayamin na nemi magani ba, shine sai kan Marayan yarona zaki sauke bukatar ki, tsawon wani lokaci kika ɗauka kina cutar da Ni da yarana? Tsawon wani lokaci kike cin amana ta!” Yace Cikin fada.

Hajiya Sa’adah ta cigaba da kuka, bata ce komai ba, ya ɗauke kansa daga gare ta yace “Sa’adah na sake ki saki daya, na sake ki saki biyu, na sake ki saki uku!!!”

Ya numfashi jikin sa na rawa yace “abu ɗaya ne ya saka bazan ce ki fita daga gida ba, saboda Shakur, darajar Abdulshakurr ne zai cigaba da riƙe ki a gidan nan ba aure na ba, domin na datse halakar dake tsakanin mu, zaki iya yin komai da kike so a gidan nan, kuma kome kike bukata zan yi miki darajar Shakur, ki fada min abinda kike bukata ta text message zan tura miki kudin, amma kada ki zo ko kusa da inda nake”

Hajiya Sa’adah da tun sanda ya ambaci saki ta daskare a zaune, domin abu ne wanda ya zo mata a bazata, duk da a da tana bukatar sakin, amma Yanzu data samu bata farin ciki, fargaba take yayinda zuciyar ta ya shiga rawa domin rabuwar bashi da Amfani a gare ta kuma.

Alhaji Dawood kuwa duk cikin maganganun ta babu wanda ya tsaya masa a rai kamar data ce baya sauke nauyin dake kansa da kuma tsakar mata tarbiyyar yaran data ce, so yake yayi figuring out, shin da laifin sa kamar yadda ta fada? Hawaye suka ciko idanun sa amma basu da alamar zuba yana kallon waje daya cikin tunani, Hajiya Sa’adah ta dinga kuka tana rokon sa amma ya yi kamar baya jinta, karshe ya mike domin barin wajen saboda yana bukatar nazari sosai kan maganar , bai yi sammani ba ya ganta gaban sa ta rike mai ƙafafuwa cikin son rokon sa, ya kwace kafar sa da karfi har ta buge habar ta sannan ya mata wani kallo da fuskar sa mai cike da ɓacin rai, kana ya tsallake ta ya wuce, Hajiya Sa’adah ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita.

_kuyi hakuri, kuna raina wallahi, nayi azumi ne yau_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button