Munayamaleek 7
🍇MunayaMaleek🍓
_by NoorEemaan_📚✍️
Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks@nooreemaan
https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link
(Kuyi following sabon account dina please)
https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32
(Follow my WhatsApp channel domin samun update )
*Gaisuwa ta musamman zuwa ga makarantar NoorEemaan, bazan iya rubuta yawan ku ba, amma ina muku son so*❤️
Vii
(7)
A ranar da Munaya ta sanar da likita cewa budurcin ta ta siyar Kafin ta samu makud’an kuɗaɗen nan bai runtsa ba, sosai zuciyar sa ke kuna tamkar ciki daya suka fito da ita, a ransa kuma yana ji tamkar har da laifin sa yasa hakan ta faru, a matsayin sa na likita ya kamata yayi la’akari da cewa Munaya karamar yarinya ce, bai kamata kai tsaye ya sanar Mata cewa komai zai iya faruwa da Amnah idan ba’a yi saurin yi mata aikin ba, yana ji a ransa cewa har da kalaman sa gareta yasa ta tsorata har tayi saurin bada budurcin ta, Amma yanzu ya ɗauki darasi a rayuwa, zai kiyaye yanda zai yiwa duk wanda ya Kawo patient magana da ma patient ɗin, zai kwantar musu da hankali ko da yasan cewa shi Mara lafiyar na dab da rasa ransa, ko dan gudun abinda ya faru da munaya ya sake faruwa ga wata, kila daya kwantar wa Munaya hankali duk da halin da kanwar ta ke ciki na halin rai ko mutuwa da kila bata rasa abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a rayuwar ta ba, da kila ta tsira da daya, amma abin ciwo da takaicin, babu Amnah, Babu budurcin Munaya! Ya sake juyi kan gadon sa cikin damuwa, yana ji kamar yaga mara imanin daya aikatawa Munaya haka da tabbas sai inda karfin sa ya kare, qwarai abin ya tsaya masa a zuciya.
***
Bangaren Maleek kuwa tun bayan da suka dawo daga neman Munaya ya rasa meke damun sa, mintina daya zuwa biyu tunanin ta ya fado masa rai, sai dai ya alakanta hakan da managar da Munaya ta faɗa masa bayan ta watsa masa 3.9 million din sa, yayi tunanin zata dawo aikin bayan wasu kwanakin zuwa goma haka amma sai ya ga lokaci na dada ja ba tare da ko mai kamaninta ya gani ba, shi dai yasan bai bata muhimmanci ba saboda ita din ba komai bace a gareshi, kawai yana takaicin abinda ya aikata da karamar yarinyar da take basa kyama, sai kuma maganar mutuwar yarinyar (Amnah) da ya dake sa sosai, sai yake jin wani *quilty conscience*, bai taba nadamar shan giya ba sai ranar daya kusanci Munaya cikin maye, ko da yana cikin maye shi din tsayayyen namiji ba, sai dai bai san abinda yasa a ranar ya kasa controlling kansa ba har ya afka mata, ya mike tsaye hannun sa sanye cikin aljihu ya taka zuwa ga dogon window’n glass din office din, tarr yake ganin mutanen da suke wucewa kan ababen hawa da masu haɗa haɗar su cikin kwanciyar hankali, ya jima a tsaye idanun sa a wajen yana kallo, sai dai ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani ne, sai daya bata lokaci tsaye a wajen kana ya dawo ya zauna kan kujerar sa, can kuma kamar an tsikare shi ya mike zuwa dakin hutun sa ya shiga, tun ranar da abin nan ya faru ya daina barin masu aiki shiga Wajen, daya tashi zai rufe kofar da kansa, yana shiga jinin daya bata farin sofan na nan bai goge ba, ya sauke idanun sa masu rikitarwa kan sofan yana kallo, ya dauke idanunsa daga kallon jinin ya sauke kan mataciyyar ribbon din ta daya tsufa sosai ya ga har da silin dogon gashin ta daya manne da ribbon din, ya dauke idanunsa daga nan ya zauna kan kujera, ya dawo da cctv Cameran baya zuwa ranar da abin nan ya faru, ya dinga kalla daya bayan daya, sai dai daya zo kan inda komai ya kankama sai ya yi saurin kashe wa, domin haushin kansa yake ji, he hate his self for what he did, Sam baya nadamar zinar daya aikata, sai haushin kansa da yake ji da aikata hakan da yarinyar da ya tsana, ya furzar ga iska mai dumi daga bakin sa ya shaki kamshin mouth spray ɗin a hancinsa.
***
_8:00pm_
Cikin farin ciki mummy take yau, zata samu cikar burinta, motsa coffeen dake cikin kyakkyawar wani mug take, bayan ta gama ta nufi hanyar dakin ta, ta san Maleek yana shigowa zai shanye coffeen, domin baya wasa da coffee, Shakur ba sha yake ba tunda shi ba masoyin sa bane, yafi ganewa shayi, ta shiga daki ta shirya cikin had’add’en nighty tana jiran sa, domin an tabbatar mata da kansa zai shigo ya neme ta bayan ya shanye.
Munaya!!!
Har ila yau komai baya yiwa Munaya dadi, taji duniyar ta tsaya mata cak, gata dai tana rayuwa cikin mutane sai dai kallo daya mutum zai mata ya fahimci tana fuskantar kalubalen rayuwa, ta zama shiru shiru, bata fita ko ina, bata zuwa ko ina, kayan kwalaman da likita ya bata har yanzu bata gama cinye su ba kasancewar ta rasa apetite din ta, sai ta ji y’a’yan hanjin ta sun motsa Sannan take neman abu ta saka a cikin ta, ta sake ramewa sosai tamkar zata ɓalle idan an mata kyakkyawan riko.
Tana kwance idanunta na kallon farin wata wanda hasken sa ne ya haskaka dan tsakar gidan, domin ta daina rayuwa da fitila ko wani abu da zai haskaka gidan idan dare yayi, daman ba’a zancen nepa, takun mutum taji zuwa cikin gidan kana ta ji Muryar wani yaro na fadin “Assalamu alaikum, wai ana kiran Munaya in ji wani a waje” yana gama fadin haka ya juya ya fita bai jira amsa ba, kamar ko ya san da cewa ba amsar zai samu ba.
Tsawon mintuna biyar kana Munaya ta yunkura ta mike tsaye, taji jiri zai kada ta tayi saurin dafa bango, ta saka takalmi hadi da zura hijab din ta, a hankali ta nufi hanyar fita, she thought as much doctor ne kuwa tsaye jikin motar sa.
***
Cikin nutsuwa Alhaji Dawood ya buɗe karamin gate din gidan ya shiga hannunsa rike da karamin trolley, sanye yake cikin wasu hadaddun suit ash color, kallo daya mutum zai masa ya hango cewa shi din business man ne, kana ga kwarjini, wayewa, hadi da kamala a tare da shi, mai gadi daya sallame sallah yayi saurin juyowa sakamakon motsin mutum da ya ji, fara’a ta wadatu kan fuskar mai gadi, cikin sauri ya tashi zuwa gaban Alhaji ya ɗan durkusa cikin girmamawa yace “Barka da zuwa Alhaji, ya hanya?”
“Cikin murmushi Alhaji Dawood yace “lafiya Lou alhamdulillah Audu, mun same ku lafiya?”
“Wallahi alhamdulillah Alhaji”
“Masha Allah!” Alhaji Dawood ya fada yana barin wajen bayan ya hana mai gadi karban masa trolley din sa, kansa tsaye ya shiga cikin had’add’en falon inda ba kowa sai motsin plasma dake bango yana aiki shi kadai, ya saki murmushi yana hango farin cikin da iyalansa zasu yi idan suka gan shi, hakan yasa yayi musu zuwan bazata, tunda waccan zuwan daya ce musu zai zo bai samu zuwa ba shi yasa this time ya shirya musu surprise, sai dai su gan shi, har ya gota dinning din ya dawo da baya saboda kamshin coffee daya daki hancin sa, ya dauki mug din mai dauke da coffee ya kurba kadan, ya ji ya masa dad’i sosai, sai ya shanye duka, bayan nan ya dire mug din, ya ajiye trolley din gefen kujera, ya nufi dakin mummy domin yayi kewar ta sosai.
Mummy kam data ji motsin bude kofa ta wani lumshe ido cikin jin dadi fuskar ta dauke da murmushin nasara, Finally dai yau zata kashe ƙishirwar da ta daɓe shekaru masu yawa tana jira, cikin wani salo ta buɗe idanun ta tarr ta sauke su cikin na Alhaji Dawood dake mata murmushi, ta zabura hadi da mikewa kirjinta na ludugan bugu, ta murza idanun ta da kyau ta ga dai still Alhajin take gani a tsaye, take fuskar ta ya Sanja har bata san sanda ta furta “haba Alhaji, ya zaka dawo yau?” ta karasa cikin dacin murya.
Kalaman sun dan bawa Alhaji Dawood mamaki, ya kalle ta da kyau yace “ban gane da ban dawo ba yau, akwai matsala ne Sa’adah?”
Sai a lokacin ta fahimci subutar data yi, cikin kissa ta karasa gareshi hadi da rungume shi tace “ina nufin daka sanar min ai, ya kamata a shirya maka tarba mai kyau tunda baka taba dadewa irin haka baka dawo ba” ta karasa tana share hawayen takaicin daya zubo mata cikin dabara, tana jin kamar ta shake Alhaji Dawood ta huta.
Murmushi bai gushe a fuskar Alhaji Dawood ba, ya rungume ta da kyau yace “karki damu matata, ko me kuke da shi zan ci, besides na Sha dadd’ad’an coffeen da kika yi, kamar kin san zan dawo, kodai kin ji hakan a jikin ki?” Ya karasa cikin wani salon soyyaaya irin na su na Manya.
Wani tukikin abu ya kara tsaya wa mummy a makoshi, ta danne ta hanyar sakin murmushin yake, yanzu haka tana ji tana gani duk tanadin data yi domin Maleek sai Alhaji ne zai more shi, bakin ciki kamar ta mutu amma haka ta daure gudun kada Alhaji Dawood din ya gane.
***
A hankali Munaya ta karasa wajen doctor da sallama ciki ciki, ya kuma ji ya amsa, kana cikin wasa yace “na zata sarautar ce ta motsa bazaki fito ba” bata ce komai ba, duk da ta lura yana daga cikin mutane masu yawan fara’a da wasa.
“Ina yini” tace ba tare da ta bashi amsar waccen maganar da yayi ba.
Bai hakura ba ya sake cewa “lafiya kalau, ai yau sai kin budi baki munyi hira sosai, tunda na ga rowar magana kike min, na gano wayon ki”
Still bata ƙara cewa komai ba, shi ma bai damu ba, domin har yanzu yana mata uzuri, shiru ya ratsa tsakanin su kana ya fara Mata fada mai haɗe da nasiha “ina kara baki hakuri kan abinda ya faru, Allah kuma ya jikan Amnah da Rahama, amma abinda kika aikata Munaya ba karamin laifi bane, kinyi wauta sosai, ki sani cewa shi Allah ke bada lafiya ba Mutum ba, haka zalika mutum bazai iya kara wa bawa lokaci ba, matukar lokacin sa yayi zai mutu ne , what you did was very bad, and i prayed Allah subhana wata ala ya yafe Miki, Bazan boye Miki ba naji haushi sosai kan abinda ya faru, shiyasa kika ga ban dawo ba sai yau, daga yanzu idan zaki yi abu ki nemi shawara ta kinji tunda na dauke ki matsayin kanwata, karki kara gaban kanki kin ji ko?” Ta jinjina kai hawaye na cika idanun ta.
“Good girl” ya fada yana mata murmushi sannan yace “kafin mu yi hirar da nake so ya kamata ki san sunana, tunda bazaki tambaya ba, ni zan fada Miki”
Ya kara motsawa kusa da ita yace “sunana Abbas Muhammad, Ni dan asalin garin Kano ne, nayi karatu a Kano, nayi bautar ƙasa a Katsina, sai dai aiki ya kawo Ni Abuja, ina da kanne biyu mata Amina da Zainab, suna tare da mahaifiyata a Kano, Allah yayi wa mahaifina rasuwa 4years back, wanna shine takaitaccen tarihina”
Munaya jinjina kai kawai take domin babu abinda ke Mata wahala yi kamar magana yanzu, likita bai damu ba, ya mata uzuri mai yawa amma so yake ya zama silar dawowar ta daidai, ko da bai yi nasara duka ba, amma at least ya rage wani abun.
Ya dan kara matsowa kusa da ita, ya rage murya yace “wacece Munaya, Tell me?”.
*Ayi hakuri da Page din yau, nayi busy ne*
_Akwai sanarwar da zan yi saboda mutane na ta tambaya ta, na so bari sai na kammala free pages kafin na sanar amma yawan tambayar ya sa na sanar, tambayar da ake min shine “littafin kuɗi ne ko free?” TOH littafin MunayaMaleek paid novel ne, amma muna kan free pages ne har yanzu, thanks for your support, Allah ya ƙara muku budi ya biya bukata_
07082281566
#MunayaMaleek 2023
#NoorEemaan
#Heartouching
#selffishness