Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 20

Sponsored Links

Husnah suka kalli junansu da sauri ganin Khalil ya juya motar xai bar layin, Amina ta dawo fuska a daure tace “Wai wani zai je ya yanko wani makullin” Husnah ta rike kugu tace “Tashin hankali, lallai wannan mutumin dan iska ne, karya fa yake yi wllh, mu din dai ne baxai bude ma gidan mu shiga ba” Nihad ta taso da sauri ta tsaya jikin gate din tace “Me ya faru?” Naf dai ta kasa cewa komai tun da ta bi motar da ido baki bude, Zully tayi wani dariya ta rike ha6a tace “Kan uban can… Amma gayen nan daga ɗan iska sai shi, but don Allah ku baku ji kun kagu kuna son ganinsa ba? It’s the gut for me” Nihad dake ta zaro ido ta kasa fahimtar abinda suke cewa tace “Don Allah ku min magana mana, ya dawo ne?” Husnah ta sauke wani uban ajiyar zuciya ta koma bakin flower ta zauna tana girgiza kafa, Naf da wani bakin ciki ya isheta tace “Amma idan ban tara yan sara suka da yan da6a sun ma drivern nan mugun bugu ba ku ce bani bace, don kaza kazansa da uwar me yake takama xae walakanta mu haka da girman mu, wa ye shi xai dinga feeling kansa haka yana fama da talauci…” Tuni Nihad ta fara fahimtar abinda ya faru hawaye ya cika idonta, ita dai ta shiga uku da abinda wannan yaron ke yi mata, Husnah ta kara sauke wani axababben ajiyar xuciya ta mike tace “Nihad mu xa mu tafi, ashe da gasken gaske tsinanne ne mutumin nan sai yau na sake tabbatarwa, wato tantirin ɗan iska ne na bugawa a jarida, har mu zai walakanta ya juya kan mota ya bar mu uwa yan iska a tsaye bakin gate? Who the hell did he think he is” Nihad ta sakar masu kuka tace “Ba ina gaya maku ba kun zata exaggerating nake, ai wallahi zai iya yin abinda ya fi haka, ina Amina?” Amina tace “Ga ni” Nihad tace “Ki kira Umma da wayarki ki gaya mata abinda dan iskan yayi maku” Amina ta fiddo wayarta a jaka ta hau kiran Umma, Umma na dagawa ta larabta mata abinda khalil yayi masu a bakin gate, Umma ta rike ha6a bayan ta gama sauraron Amina tace “Yau ga shegen mutumi, kuna nan har yanzu bakin gate din kenan a tsaye?” Amina tace “Wallahi” Umma tace “Ina wayar Nihad din?” Amina tace “Ya karɓe wai xai ajiye mata” Umma ta wani mulmulo zagi ta lafta mata tace “Uban wa yace ki basa? Wajensa na aiko ki xaki basa waya? To wallahi duk inda xaki nemosa ki nemosa ki amsar min wayata, kaji min doluwar yarinya kawai” Amina ta turo baki tace “To wai ba karbewa yayi a hannu na ba, ni me xan ce masa” Umma ta kara kunduma mata zagi tace “Ubanki ne ya siya min wayar da xa ki ba wani ɗan iska can? Na dai gaya maki kar ki kuskura ki dawo min gida babu wannan ledar wayar, shashashar banza kawai doluwa” Daga haka umma ta katse wayar tana huci, Nihad tace “Ban gane ba, wayar kika basa Amina?” Amina tace “Toh wai ba amshewa yayi a hannuna ba yace xai ajiye maki” Nihad ta kunduma mata zagi ita ma tace “Wallahi maza ki bi sa ki amso min wayata, meye hadina da shi da har xai amsar min waya yace xai ajiye? Munafuki kawai” Amina tace “Ni dai wallahi ku daina min masifa tunda ba ni na mika masa ba” Husnah tace “Toh wannan takadirin ai ko bata basa ba xai iya fizgewa a hannunta, don naga kamar ya ta6a dabanci, ni dai wllh bai walakanta banza yau din nan ba, xai san ya ta6a Clique dinmu…” Naf duk ta fi su shiga takaici a wajen, she really wants to meet with Khalil ya ga karshen rashin mutunci da tijara, Zully tace “Ni anya ma ba shi yaje ya samu Abban yace a basa auren Nihad din ba kawai don ya samu hanyar dinga walakantata?” Nihad na tafe hannu tace “Ai ko da kansa xai tafi ya samu Abban yace masa yayi hakuri ya fasa auren, i am going to make life miserable for him, xai san cewar ni ba sa’ar zama waje daya da shi bace balle uwa uba aure, shi har ya isa ya aureni? Wallahi da wuri wuri zai koma gun Abba yace ya fasa” Husnah tace “Atoh, duk wannan koke koken da kike yau kwana da kwanaki babu abinda xai tsinana maki sai ma 6ata lokacin ki da kike ki ji in gaya maki, yanzu kamata yayi ace kin zauna kin nutsu kin fara nazarin ta yanda zaki fara musguna ma shege, kar ki kuskura ki raga masa daga cikin tijara da iskanci da muka iya a Clique dinmu, In his next life ko million daya xa a dinga basa ya zo gidan masu kudi yayi driving wallahi baxai zo ba, shi din banza shi din hofi” Sosai hudubar Husnah ke shigar Nihad da taji daga wannan moment din ta daina kuka, baxata kara asaran hawayenta ba akan Halilu, sai dai ta fara daukan action a kansa, kuma da ƙafafuwansa xai gudu ya bar mata gidan ya koma kauyensu na har abada, Husnah tace “Kuma gidan nan ko da uban wa yake yawo sai mun shiga gobe, balle daga shi sai talauci yake yawon ma, wallahi kamar mun shiga gobe, Allah ya kai mu goben, kuma ina fatan Allah Ubangiji ya hada mu da shi face to face goben” Nihad ta sauke ajiyar xuciya saboda sosai ta samu kwarin gwiwa, tace “Amina ki ɗan ara min wayarki mana zuwa gobe” Amina tace “Toh ni sai in yi amfani da wanne?” A fusace Nihad tace “In za ki ara min ki ara min malama, banza kawai ba ke kika je kika mika ma wawan can wanda Umma ta baki ki kawo min ba? Dallah bani wayarki ai ba cinyewa xan yi ba” Amina tace “Ban ga xan iya ba, ni islamiyya ma xan yi tafiyata daga nan, duk an bata ma mutum lokaci ansa na makara kawai a banxa, sai da nace ma Umma ni islamiyya xan tafi amma ta ki” daga haka ta juya fuuu ta bar su wajen a tsaye, Husnah tace “Ke rabu da wani aran waya, gobe ni da kaina xan kawo maki waya, screen touch kuwa” Nihad tace “Toh ta yaya, bayan kina ganin abinda yake yi da gidan kamar na ubansa” Husnah tace “Baki yi trusting dinmu ba kenan?” Naf tayi wani Murmushi tace “Ai kamar mun shiga gidan nan gobe idan Allah ya kai mu, ki saurare mu idan mun tashi test” A hankali Nihad tace “Toh shikenan, Allah ya kai mu” Zully tace “Toh wai ya sunan wannan tatattcen mutumin ne?” Nihad tace “Halilu naji ana kiransa” Duk suka kwashe da dariya Husnah tace “Za mu haliro masa gobe kuwa” Daga haka suka yi mata sallama, tana jin suka shiga motarsu suka bar layin, ta sauke wani ajiyar xuciya ta juya ta koma cikin gidan. Sai bayan magrib Nihad ta ji shigowar Khalil gidan, nan da nan taji bacin ranta ya ninku a kan na da, tana jin sa ya shigo parlor ta mike ta fito parlon, bai ko kalleta ba ya ajiye ledan hannunsa ya zauna saman kujera ya dau remote yayi powering tv, a fusace ta karaso cikin parlon ta fixgo ledan da ya ajiye don a tunaninta wayarta ce, da ido ya bi ta har ta gama bincika ledan ganin fruits ne ta cillar a gefe, tana tafe hannu cike da tsiwa tace “Ka buda kunnenka da kyau ka saurareni, yau ya zama first and last day da xaka sake kulleni a gida idan xaka fita don ni ba akuyarka ko tinkiyarka bace, kuma ka bani wayar da Ummata ta aiko min” Kallon Tv kawai khalil yake, tayi masa wani tsawa tace “Baka ji na ne ina maka magana?” Still bai kalleta ba balle ta sa ran xai amsa, a mugun fusace ta tafi ta kashe socket din gun Tv din gaba daya tana kallonsa tana huci, Khalil ya kalli karamar wayarsa dake ring, dagawa yayi ya kai kunne yace “Idan na gama abinda nake xan kira ki Hajiya” Huci kawai Nihad take tana kallonsa, yana katse wayar ya mike ya nufi bedroom, wani bakin ciki ya kara rufeta ta bi sa da sauri ta shige gabansa tana cewa “Ni ce ma zan dinga maka magana zaka tashi ka bar wajen, to wallahi baka isa ba….” zata cakumosa kamar yanda ta saba ganin kallon da yake mata sai ta fasa kai hannun nata kwalarsa, Cikin kakkausar murya yace “Matsa ki bani waje” Duk da yanda gabanta ke faduwa tace “Baxan matsa ba, ka bani wayata tunda ba kai ka siya ba….” Irin kallon da taga yake mata yasa ta fashe da matsanancin kuka ta durkushe wajen don can kasan xuciyarta a tsorace take da shi, ya bi gefenta ya shige daki abunsa ya kulle kofar. Mikewa tayi tana kuka tana bubbuga masa kofa tace “Ni wallahi ka bani wayata tunda ba da kudinka aka siya ba, ina ruwanka da sakon da aka kawo min da xaka sa hannunka ka amsa” Banza yayi mata, ita kuma bata fasa bubbuga kofar ba, bayan kusan minti biyar taji ya bude kofar sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri amma kuma bata fasa fadan abinda take fada ba, taga ya sa ma dakin makulli ya cire sannan yayi hanyar kitchen ya shiga, bin sa tayi har bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kuka tace “Wallahi idan na maka Allah ya isa sai ya bi ka har generation dinka, ka bani wayana nace” Gas ya kunna ya dau karamin tukunya sabo ya dauraye ya sa ruwa a ciki ya daura saman gas din, bata fasa masa fitsaran da take ba a bakin kofa, ya juya ya ɗan kalleta, ta wani maka masa harara tace “In kuma siyarwa kaje kayi sai ka gaya min in cire rai” Shi dai bai ce mata komai ba ya rungume hannunsa yana jiran ruwan ya tafasa, ta rushe da kuka ta hade kanta da kofa tace “Wayyo Allahna na shiga uku” Ya daga kai ya ɗan kalleta, juyawa yayi yana kallon ruwansa dake saman gas, ta dago kai cikin kuka tace “Koma me kayi da wayar ban yafe ba….” Ko rufe baki bata yi ba taga ya cire hannunsa da sauri daga handle din tukunyar alamar ya kona sa, ya koma baya yana kallon tukunyar, wani shegen dariya ta saki har da kyakyatawa ta durkusa a wajen, yanda take dariyar kai kace bata da sauran damuwa a duniya, ya ɗan kalleta sai kuma ya shafa kansa ya juya yana murmushi ya kalli inda ya tukunyar ta kona sa, ruwan da bai juye ba kenan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ya bar ta a ciki, bayan ta ci dariyarta ya isheta sai kuma ta mike ta hade rai, a hankali ta dauke tukunyar shinkafar da Aunty Jamila ta girka, ta dau na miyan ma duk ta kai dakinta da plate da spoon sannan ta koma ta jawo kofar kitchen din ta saka makulli ta zare, sai ta ga ta yanda xai sha shayin yau, infact forever and ever, don ta kulle kitchen din kenan har abada, Dakinta ta wuce ta bude akwatunta ta binciko duk kayan ta ajiye makullin karkashin akwatin sannan ta mayar da kayan ta kulle akwatin ta koma gefen gado ta zauna. Tun kafin tayi sallan magrib tayi wanka, don haka ta zuba abinci ta ci, ta tashi ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala, tana yin sallan isha’i ta sa ma dakinta makulli ta ta dawo ta kwanta. Washegari bayan Nihad tayi wanka ta wanke bandakinta, she can be lazy in all aspects but not when it comes to her bathroom and Bedroom, bayan ta fito sai da ta fara gyara dakinta sannan ta saka kaya, sbda mugunta haka ta zuba sauran shinkafar da sanyi ta ci, ta koma bandaki ta kuskure bakinta da mouth wash ta fito, Hijab har kasa ta daura saman kayanta, sannan ta dau jakar da take xuwa makaranta da shi ta bude kofa a hankali ta fito parlor, yana kwance saman doguwar kujera, ta galla masa wani harara ta karasa cikin parlon, ta tsaya bayan 2 seater, ta dake tace “Makaranta xaka ajiyeni malam” Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune yace “Ohk, wace makarantar?” Babu yabo babu fallasa tana juya ido tace “Wanda ka saba kai ni” ya gyada kai yace “Ohk” Sai kuma ya koma ya kwanta, a mugun fusace tace “Kana bata min lokaci lectures din safe gareni, ko kuma ka bani makullin motarmu inyi tafiyata” Khalil yace “Ki jira duk sanda Allah ya nufa kin koma can gidan naku da xama sai ki ci gaba da xuwa makarantar, amma a nan gidan kam ke da fita ko nan da gate sai wani ikon Allah, na soke xuwa wannan makarantar har abada” Da mamaki take kallonsa baki bude, sai kuma ta hadiye abu da kyar tace “Kai kuma a uban wa xaka gaya min haka? Kai a wa xaka soke min xuwa makarantata?” Ya kalleta yace “Kira Abbanki ki tambayesa” Bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba tana kallonsa, yace “Allah ya amfana ɗan wanda kika samu” Yana kai wa nan ya mike ya shige daki ya bar ta wajen, sulalewa kasa tayi tana kuka sosai, wai yau common driver ne yake ce mata baxata je makaranta ba wai ya soke, whatttt??? Nihad ta ci kuka ta gode Allah a wajen kafin ta shiga daki, komai na duniyar ta ji ya isheta…. Throughout ranan haka ta yini a kwance tana hawaye, tana mugun son tayi magana da Umma amma babu dama, don babu wayar da xata yi kiran, she needs to tell Umma this, bayan Umma bata da wani wanda xata gaya ma, tana jin an kira la’asar ta mike zaune, sosai kanta yayi mata nauyi, ga magungunanta rabon da ta sha tun jiya, kuma bata jin xata sha, shiru shiru bata ji alamar ya fita gate ba gashi har an tada sallah, mikewa tayi a hankali ta fita parlor, ta dinga bin parlon da kallo ta kalli bakin kofa taga ba takalminsa, to har ya fita kenan bata ji ba, komawa corridor din dakunan tayi ta kai hannunta handle din kofar dakinsa ta murda a hankali kofar ya bude, ta leka cikin dakin ta ga ba kowa, kallon karamar wayarsa dake saman gado ta dinga yi, dai dai nan ya bude kofar bandaki ya fito, tayi masa wani tsinannen harara ta juya ta koma dakinta. Bayan ya dawo masallaci yana zaune compound bai shigo parlon ba yaji an kwankwasa gate, ya dinga kallon gate din kafin ya mike ya tafi bakin gate din, har sannan ba a fasa kwankwasawa ba, yace “Waye?” a fusace Umma tace “Malam xaka bude min kofa ko kuwa? Ji wani tambayar walakanci wai waye, shi dama talaka ai bai iya samun waje ba, ka tashi ka garkame gida kamar na ubanka, da an kwankwasa kuma kace waye, to masu shi ne sai ka bude ko?” Khalil na tsaye yana sauraronta, sai da ya dau kusan 40 seconds kafin ya bude gate din, Umma ce tsaye da su Husnah a bakin gate din, Yayi kasa da kansa yace “Ina yini” Umma tayi mitsi mitsi da ido tace “Ban yini ba, nace ban yini ba, ɗan marasu mutunci” Ya so juyawa ya bar wajen amma ya kasa sbda girma da mutuncin da Abba ke da shi a idonsa, Husnah, Naf da Zully suka dinga kallonsa babu kwakkwaran kiftawa, duk tambaya daya ce ke yawo a xuciyarsu, wannan shi ne dreban, is he the driver? Husnah tace “Umma wai shine driver din??” Umma tace “Gashi kuwa kin gansa” Duk suka kalli junansu, Husnah ta tafe hannu tana kallon khalil tace “Wato kai ne ɗan rainin wayon da ya barmu bakin gate jiya? Kai ga ka shafaffe da mai ko?” Naf na nuna sa da yatsa tace “Kai kana buzu har xaka zo kasar mutane kana bubbusa hanci kamar algaita? Waye kai? Kuma uban me kake takama da shi? Kasan mu su waye da kake tunanin zaka mana walakanci ka kwana lafiya?” Zully tace “Ai ni na ma rasa ta cewa, wato wannan dai shine driver me ba kawar mu though time, toh hasken naka kake takama da shi kake tijara ko me?” Nihad ce ta taho da gudu ganin Umma ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Sai kuma ta sake Umma ta rungume su Husnah gaba daya har da hawayenta sbda tsabar farin ciki, juyawa khalil yayi ya bar wajen kamar zai tashi sama, Husnah tace “Sai ga mu ga ɗan rainin wayon nan yau” Nihad ta sauke wani ajiyar xuciyar takaici, Umma tace “Wato bai baki wayar ba dai” Nihad tace “Wallahi kuwa, ya ki bani” Umma tace “Mu je ciki, sai na ci kaxa kazansa, wato yanxu baya ganin kowa da gashi sbda Alhaji ya gama bada mu gabansa yayi mugun raina mu, yo ya bada mu mana tunda har xai dau yar sa ya basa, idan ma hadin yake son yi ina ‘ya yan abokanansa?” Duk suka dukufa xuwa cikin parlon Umma na ƙare ma Khalil zagi su Husnah na tayata, shi kam tuni ya shige daki ya sa makulli, sabuwar waya dal Husnah ta siya ma Nihad har da sim card a ciki, murna wajen Nihad ba a cewa komai, gaba daya ta mance damuwar da take ciki, Umma tace “Kinga shikenan sai ki kwantar da hankalinki yanxu, tunda sun ga gida kullum kya gansu, kafin dai su dawo nan din gaba daya” Nihad ta marairaice tace “Umma fa kulle gate din yake yi kuma makullin na jikinsa” Naf tace “Amma fa kamar a jikin gate din ya bar makullin yanxu da ya bude mana fa” Husnah tace “Idan ko haka ne kawai cirewa xa mu yi mu je a yanko mana spare” Zully tace “Bari in duba” Mikewa tayi ta fita, sai ga ta ta dawo rike da makullin tace “Ai ko dai gashi” Umma tace “Toh Alhamdulillah, tunda dare bai yi ba yanzu me xai hana ku je inda ake yankan spare din a yanka maku?” Naf ta mike tace “Yanzu kuwa, kawai kudi za mu cika masu yau yau din nan xa a yanka a bamu” Naf da Zully ne suka tafi da makullin wajen yankar makulli, Nihad ta dauko ma Husnah makullin kitchen xata dafa masu taliya wai, Nihad na kallon Umma ta marairaice tace “Umma yau na shirya xan je makaranta ya hanani wai ya soke” Buda baki Umma tayi tana kallon Nihad, sai kuma tace “Toh ba a haifi ubansa ba balle shi, shi har ya isa ya soke maki karatu? Bari dai su yanko makullin kawai, ki kwantar da hankalin ki, ai indai da raina babu me cutarki a duniya Nihad, sannan nace maki ki wani manta da batun dreba kiyi rayuwarki yanda kike so, ga makulli nan xa a kawo ai, rayuwarki kawai za ki dinga yi yanda kike so kanki tsaye” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh Umma” Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Yanxu shkkn har yau Aliyu ba neme ki ba ko?” Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta girgiza kai hawayen na sauka fuskarta tace “Ai blocking dina yayi Umma, kuma sim din ma na karya ai… Umma ban san waye yayi min haka ba kilan don a rabani da Aliyu ne.” Kuka take yi sosai kamar ranta xai fita, cikin rawar murya tace “Wallahi ina sonsa Umma, gashi yanxu an rabani da shi” Umma tace “Aa ki daina cewa an raba ku, kina fara xuwa makaranta duk yanda xa ayi ki nemi numbersa ki nema, ba kince min a kawayenki akwai me numbersa ba?” Nihad ta gyada kai hawaye na gangarowa fuskarta tace “Naf tana da numbersa, dama can sun san juna a Uk” Umma tace “Toh ko wajenta ki amsa, kar ma ko da wasa ki wani ce ai Abbanki ya maki aure ko da xa ku fara magana da shi” Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, har kusan magrib Umma na parlor da Nihad, Husnah ta kawo taliyar duk suka ci, all this while kuma khalil na kwance daki ko masallaci bai fita ba, Karfe bakwai su Naf suka dawo da makulli, Umma tace “Yauwa yan albarka, gasu nan kuwa har uku, toh sannunku, Allah ya maku albarka” ta mika ma Nihad daya, ta saka daya a jakarta sannan ta basu su ma daya, tace “Toh kun ga dare yayi ni xan koma gida, ku sai anjima ko? Ko dai a nan xa ku kwana kawai?”

 

Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Related Articles

Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button