Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 68

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

68

Inna bata ba Husnah chance din magana ba ta daka mata wani tsawa tana kara toshe hanci tace “Don Allah ki fita ki bamu waje, wacece kuma Nihad, Nihad da ke gidan mijinta ɗan Janar Jikamshi, meye hadinki da ita” Umma da zuciyarta ke bugawa sosai tace “Turai don Allah ki fitar mana da ita zuciyata tashi take….” Husnah ta marairaice tace “Ko number….” Hajiya Turai ta mike da sauri cikin daga murya tace “Fita ki bamu waje, fita” Juyawa Husnah tayi da sauri ta bar bakin kofar ganin Turai ta yo kanta gata jibgegegiyar gaske, Nihal ta bi Husnah da kallon mamaki, Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ta koma da kyar ta kwanta har sannan gabanta na faduwa, Inna tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Da kyar idan ba wani cutar bane ya kamata, amma wannan doyin gaskiya ba na lafiya bane, a bude mana window a kara Ac….” Mumy ta ji kamar ta bi bayan Husnah taji neman me take ma Nihad, tana ta nazarin maganan nata amma ta kasa tashi sai kallon kofar dakin take. Ana idar da magrib Mami ta shiga dakinta, tun yamma take da baƙi a gidan basu tafi ba sai dab da magariba, tana kallon Nihad dake kwance saman darduma tace “Me yasa kika kwanta a kasa?” Cike da karfin hali tace “Sallah nayi” Mami tace “Toh koma saman gadon” Nihad ta mike ta kwanta kan gadon, tun dazu zazzabin ya dawo mata sosai amma a haka ta daure ta tashi tayi sallah, Mami ta dauke darduman ta ajiye inda yake sannan tace “Me kike son za ki ci yanzu?” Nihad ta girgiza mata kai kawai, Mami ta kashe Ac din dakin ganin kamar sanyi take ji, sannan tace “A kawo maki Custard za ki sha?” Nan ma Nihad ta girgiza mata kai kawai, Mami ta juya ta bar dakin, Bilkisu ta kira ta sa ta dama Custard din, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta shigo da shi a cup Mami ta amsa ta kai cikin dakinta tana kallon Nihad ta ajiye Cup din a kasa tace “Bari ya ɗan huce sai ki tashi ki sha” Daga haka ta tafi ta gyara curtains din dakin sannan ta rage hasken wutan ta fita…. Bayan minti goma Mami ta sake komawa dakin, ganinta still a kwance tace “Ai ya huce haka, tashi ki dauka ki sha” Nihad ta mike zaune, Mami ta dau cup din custard din ta mika mata, amsa tayi amma tana kallon cikin cup din taji zuciyarta ya fara tashi, ta kauda kai tace “Bazan iya sha ba” Mami tace “Toh me za ki ci?” Shiru tayi bata ce komai ba, Mami tace “A kawo shayi?” Nan ma dai girgiza kai tayi, Mami tace “Kin dai san baza ki kwanta da yunwa ba ko? Think of anything you want to take ayi a kawo maki yanzu” Hawaye ne ya cika idonta, Mami ta karasa kusa da ita cikin kwantar da murya tace “Shayin ma baki so?” Ta gyada mata kai, Mami tace “Toh a siyo maki abu a waje zaki ci?” Nihad ta gyada mata kai, Mami ta juya ta fita daga dakin, wayarta dake parlor ta dauka tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga tace “Eatry zaka je yanzu ka siyo abinci ka kawo min” Yace “Abinci? Wani irin abinci?” Mami tace “Idan an samu pounded yam ko Semovita with vegetable soup” Yace “Ohk” Katse wayar tayi ta zauna saman kujera. Ba a dau lokaci ba Khalil ya dawo rike da ledan takeaway din abincin, ya ajiye parlon Mami yana kallonta, tace “Na manta ban ce ka hado da fruits ba” Yace “Yanzu komawa za ayi a siyo fruits din?” Mami tace “Ehh” Juyawa yayi a hankali ya fita daga parlon, ta dau abincin ta shiga dakinta da shi, ta kira Bilkisu ta kawo mata plate, tana gama zuba pounded yam din a plate ta kalli Nihad tace “Sauko kasa ki ci” Nihad ta mike zaune ta sauko kasa ta zauna kan rug da ta shimfida mata tana kallon pounded yam din, it looks so enticing kuma bata ji zuciyarta na tashi ba, Ta kalli ruwan wanke hannu da aka ajiye mata ta wanke hannunta sannan ta fara cin pounded yam din, Mami tace “Do not rush it, idan kin ci kadan ki rufe anjima sai ki ci sauran” Nihad ta gyada mata, Mami ta dauko mata magungunanta ta ajiye gabanta sannan ta juya ta fita, Nihad bata wani ci da yawa ba kamar yanda Mami tace mata, ta dau maganinta ta sha sannan ta rufe abincin ta tafi bandaki ta wanke hannunta, ta dauro alwala ta fito tana idar da sallah ta kwanta bacci ya dauke ta. Wajen karfe sha biyu saura Mami ta shigo dakin ganin idonta biyu tace “Za ki sha kankana a kawo maki?” Nihad ta girgiza mata kai Mami ta dau abinda zata dauka ta fita daga dakin…. Da kyar Nihad ta bude ido ta sauko daga saman gadon Mami ta durkusa saboda daure mata da mararta yayi, Mami dake zaune saman darduma ta kunna wutan dakin tana kallonta tace “Ya aka yi?” Tana yarfe hannu cike da karfin hali tace “Cikina ke min ciwo” Mami ta mike da sauri tace “Ciki kuma?” Kallon agogo tayi taga karfe uku saura na dare, ta zagayo side din da take tace “Sannu, tashi zauna gefen gadon” Mami ta dagota zata zaunar da ita gefen gadon taga stain din jini a rigar jikinta, cikin tashin hankali tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Nihad ta koma ta durkusa saboda murda mata da maran ke yi sosai, Waya Mami ta dauko da sauri tayi dialing number Khalil, sai da ya kusa katsewa ya daga, Tace “Ka taho part dina yanzu yanzu” Daga haka ta katse wayar, ta kara dago Nihad tana mata sannu, duk ta rikice ta rasa abinda zata yi… Khalil na shigowa dakin ya nufosu da sauri ganinta rike da Nihad yace “Me ya faru Mami?” Mami tace “Wai cikinta ke ciwo and she is bleeding ko za mu tafi asibiti ne?” Ai bai san sanda ya amshi Nihad daga hannunta ba hankali tashe yana kallonta yace “When did u start bleeding?” Ta kasa ce masa komai sai sai hawaye ke sauka idonta, tuni Mami ta dauko makullin motarta, ganin yanda ya tsaya shi ma ya rasa abun yi duk ya rude, ta masa tsawa tace “Dallah ni ka fito min da ita mu wuce asibiti” Daga haka ta fice daga dakin da sauri zata kai ma drivernta makullin mota kafin ya fito da ita, Asibitin da ya fi ko wanne tsada a Abuja Mami ta sa suka tafi, kuma har suka isa asibitin bata daina bleeding din ba, duk iya dauriyarta sai da ta fashe da kuka sosai, likitocin suka shiga da ita emergency, tsabar rudewar da Khalil yayi har mancewa yayi ashe shima fa likita ne, ya jinginar da kansa jikin bangon asibitin with throbbing heart, he just cant say why he is bleeding that way, Mami ma ta kasa zaune ta kasa tsaye a corridor din emergency ward din, she looks so disturbed, lokaci daya Khalil jikinsa yayi mugun sanyi, he just can’t imagine Nihad loosing the pregnancy, ya kasa ci gaba da tsayuwa ya zauna kan kujeran dake wajen ya rike kansa zuciyarsa na bugawa, bayan kusan minti arba’in wani baturen likita ya fito, Mami na ganinsa ta nufesa da sauri, gabanta na faduwa da turanci take tambayarsa ya ake ciki, yace ta samesa a office, sosai taji gabanta ya fadi, Khalil ya daga kai yana kallon likitan har ya bar wajen, can ya kalli Emergency ward din, wani bahaushe ne ya fito, Mami ta kara bin sa, cike da karfin hali tace “Likita ya ake ciki don Allah??” Ya tsaya yana kallonta yace “Ki kwantar da hankalinki Hajiya, she will be fine da izinin Allah, mu je office” Bin bayansa tayi zuwa office dinsa, suna shiga ta zauna saman kujera ya kunna Ac din babban office din nasa ya zauna yana kallonta kamar yanda ita ma take kallonsa, yace “Ki kwantar da hankalinki, bleeding din ya tsaya amma there is high chances of her miscarrying the pregnancy gaskiya” Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, sosai taji hankalinta ya tashi, tayi karfin halin cewa “Cant anything be done about it pls Dr?? Babu abinda za a iya yi?” Likitan ya girgiza kai yace “Kawai dai yanzu zan baku shawarwari ne ta yanda za a tafiyar da cikin nata har Allah ya sa ta wuce stage din nan, she is just 4 weeks pregnant now, and she is having a cervical insufficiency kinga idan ba abi a hankali ba sannan kuma ba wani iko na Allah ba she is going to loose the pregnancy at anytime, bazai zauna ba…” Mami tayi shiru tana kallonsa ta ma rasa abinda zata ce masa, he could see how worried she is, yace “Nan da sati biyu ya kamata ku yi mata pre natal Ultrasound saboda its likely yan biyu take dauke da….” Mami ta bude ido sosai tana kallonsa, ya gyada kai yace ‘Yeah mun ga alamar hakan but it’s not as if we are 100% sure don at this stage ba a gani, Allah ya bamu ikon gano hakan ne base on experience and how good we are” Yana murmushi ya kare maganar, Mami dai ta kasa ce masa komai, Cikin kwantar da murya yace “In sha Allah everything will be fine Hajiya, kar ki wani daga hankalinki, but nan dai da sati biyu ayi Ultrasound din don tabbatarwa, by then she is 6 weeks pregnant” a hankali Mami tace “Amma babu abinda ya samu cikin yanzu ko Dr?” Yace “Cikinta na nan har yanzu, kawai dai yanzu zan baki measures da za a bi don gudun miscarrying cikin, sannan we will keep her here for some days, Da farko well balanced meal, kuma duk wani abu da zai dameta ya daga mata hankali da fargaba a gujesa gaskiya, sannan she should be on bedrest, shi yasa nace za mu yi admitting dinta a nan na yan kwanaki…” Sosai Mami ta basa attention dinta tana sauraronsa har ya kai karshe, Bayan ya gama Mami tace “Idan aka bi duk abubuwan nan da ka fada ai shikenan babu wani abu da zai samu cikin kuma ko Dr?” Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Hajiya to be sincere to u… the chances of keeping this pregnancy, and the chances of loosing it is just 50/50, that’s just the plain truth” Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tace “Muna bukatar sallama zuwa da safe Dr” Ya daga kafada yace “Alright then, Allah ya kai mu goben” Tace “Zan iya shiga in ganta yanzu?” Yace “Sure, ai an maidata ward yanzu haka” Tace “Nagode” Daga haka ta fita daga office din, wani likita ta tambaya ya gaya mata ward din da aka kai Nihad, tana isa kusa da ward din ta tsaya ta ciro wayarta a jaka tayi dialing number Janar, hoping he is going to pickup, yana fara ring kuwa ya daga, daga bangaren yace “Why are you awake by this time??” Tace “Fatima ce bata da lafiya” Har Janar zai tambayeta wacece Fatima kawai sai ya tuna warce take nufi wato Nihad, yace “Hasbunallah what’s wrong with her?” Mami tace “Na kira Dr Rukayya ta zo jiya ta dubata da na fahimci bata da lafiya, bayan ta dubata ta tabbatar min tana dauke da ciki” Janar ya ɗan yi shiru, can yace “Maa sha Allah, that’s a good news, Allah ya bata lafiya, maa sha Allah” Mami tace “Toh dazu Ina sallah wajejen karfe uku ta fara bleeding, cause she is in my room” Janar yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, kuna ina yanzu?” Tace “Muna asibiti, and they are telling me nonsense, that there is high chances of her loosing the pregnancy, sannan cikin ma na yan biyu ne” Janar yace “Take her away from that hospital immediately, i will make some calls now zuwa gobe za ki fita da ita America…..” Mami tace “Shi yasa dama na kiraka” Janar yace “Ina khalil din?” Tace “Tare muka zo asibitin da shi, amma ni ban ga amfanin ma zuwa da shi ba, yanzu na fito office din likitan wanda nake tunanin bai san abinda yake ba gaskiya, har yana bani assurance akwai high chances of loosing the babies who does that, i dont think he is okay” Janar yace “Ku koma gida ku fara shiri kawai” Mami tace “Shikenan sai anjima” Daga haka ta katse wayar ta shiga ward din, Khalil na zaune kusa da Nihad yana rike da hannunta yana kallonta, ita kuma tana bacci, gaba daya ya zama wani iri kamar shi ne babu lafiyan, yana ganin Mami ya juya yana kallonta, he doesn’t look himself at all, gaba daya a sanyaye yake, Mami ta nufi gadon tana kallonta ita ma, a hankali ya mike ya fita daga ward din zai je gun likitan don jira yake ta fito dama. Da asuba Mami ta bar masu asibitinsu tare da Nihad bayan ta biya bills din, dama sojan da ya kawota da motar soja guda daya da ya biyosu suna cikin asibitin giving dem security tun a jiyan, gari ya fara haske suka isa gida, Mami ta sauka daga motar tana kallon Nihad dake kokarin saukowa tace “Ki fa yi a hankali” A hankali ta sauko daga motar Mami na biye da ita a baya making sure ba sauri take ba suka shiga gidan, shi dai Khalil ya bi su da kallo, Mami ta ajiye mayafinta ta shiga bandakinta ta hada mata ruwan wanka a bathtub sannan ta fito dakin tace “Shiga kije kiyi wanka, and be careful as u do so” Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta koma parlonta ta tadda Khalil a zaune tace “Ka hada mata kayan sakawanta da duk abinda zata bukata a jaka za mu tafi asibiti…” Da mamaki yace “Asibiti kuma?” Wani asibitin?” Mami bata tsaya basa amsa ba ta koma ciki ta dau wayarta, kanwarta Hamidah ta kira, yana fara ring Hamidah ta daga, bayan sun gaisa Mami tace “Flight din naku yau din ne still Hamida?” Hamida tace “Ummi fa bata gama siyayya ma jikokinta ba in gaya maki Yaya, shi yasa ma bamu yanki ticket ba har yanzu” Mami tace “Toh ku bari ko nan da 2 days ne don nima zan fita zuwa US yau” Hamida tace “Ohk me zaki yi a Us?” Mami tace “Matar Khalil ce bata da lafiya za mu kai ta asibiti” Aunty Hamida tace “Ayya to Allah ya bata lafiya, yarinyar da Aunty Maryam ta bani labari?” Mami tace “Ehh” Aunty Hamida tace “Toh shikenan Mami zuwa jibin in sha Allah, Allah ya tsare hanya ya shirye shirye?” Mami tace “Lafiya Alhamdulillah, ki gaida Ummi” Daga haka ta katse wayarta. Ba laifi Nihad ta sha shayi har da dankali da safen kuma bata ji amai ba, Mami dake dakin sai take ga kamar ko wani abu ya samu cikin ne tunda she isn’t looking sick anymore, ga kuma abinci ta ci sosai, this thought make her palpitate, jiran kiran Janar kawai take duk da it’s still 9am, Har ta gama hada jakan kayanta ga na Nihad da ta ajiye a gefe bayan Khalil ya kawo mata, Nihad na gama cin breakfast din sai bacci, Mami na ta zaune dakin bata fita ba har karfe goma, sai ga kiran Janar Mami ta daga yace “Za a kawo mata B-2 Visa nan da karfe sha biyu, zuwa da yamma za ku bar kasar in sha Allah” Mami tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ya jikin nata?” Mami tace “Toh da sauki, but i am hoping Allah ya sa ba abinda ya samu cikin, yanzu dai bacci take” Janar yace “In sha Allah everything will be okay” A hankali Mami tace “I hope so”Janar yace “Za mu yi magana zuwa Anjima” Daga haka ya katse wayar, Mami ta juya tana kallon Nihad dake ta baccinta. Mimi ce ta shigo dakin wajen karfe sha daya tana kallon Nihad da ke bacci har sannan ta zauna gefenta tana kallonta, can ta kalli Mami tace “Mami tun baccin dazu ne bata tashi ba?” Mami tace “Toh dole sai kusa da ita za ki zauna kiyi magana Mimi, what if u wake her?” Mimi ta mike ta bar wajen ta koma kusa da Mami, Mami tace “Kice ma Bilkisu da Sarah su gyara kajin nan Hajiya Safeenah zata zo anjima” Mimi tace “Toh” Daga haka ta fita daga dakin… Bayan Azahar Hajiya Safeenah ta iso gidan, Mami ta fito parlonta tace “Ni fa nayi tunanin tun dazu da kika kirani zaki fito” Hajiya Safeenah tace “Sai da na fara biyawa wani waje kafin in zo nan” Mami tace “Ya gajiya?” Hajiya Safeenah tace “Alhamdulillah, ya yaran?” Mami tace “Lafiyansu Lau” ina Nadeeyah?” Hajiya Safeenah tace “Tana gida” Mami tace “Toh maa sha Allah, wani magana kika ce za mu yi jiya kuwa” Hajiya Safeenah ta gyara zama, bayan ta sauke ajiyar zuciya tace “Jiya da daddare dangin Baban Nadeeyah suka kirani with different complaints…” Mami tace “Tohh, ikon Allah, me aka masu?” Hajiya Safeenah ta girgiza kai tace “Wai mijin da Nadeeyah zata aura da babansa basu je sun gaishesu ba anyi al’adun can, kawai ina ta iko da yarinya” Mami tayi shiru tana kallon Hajiya Safeenah, can tace “Amma lokaci bai kure ba kuwa Safeenah?” Hajiya Safeenah tace “Na gaya masu bikin saura sati daya suka ce ae kawai a daga” Mami tace “Ikon Allah, to tun da basu fadi haka ba sai yanzu?” Hajiya Safeenah dai bata ce komai ba, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace “Ina ce mahaifin Nadeeyah a Nigeria ya rasu?” Hajiya Safeenah tace “Toh yaushe rabonsa ma da Yemen din kafin ya rasu, shekaransa kusan talatin a kasar nan, to idan ba tashin hankali suke so ba meye na cewa sai anje an gaishesu bayan yana da ran ma ba damuwa suka yi da shi ba” Mami ta sauke ajiyar zuciya tace “Toh zan sanar ma Janar in sha Allah, sai kawai a bi su a yanda suke so don a samu zaman lafiya” Hajiya Safeenah tace “Wallahi ko bacci ban yi ba jiya, sun daga min hankali sosai, karamar magana ce suka mayar babba” Mami tace “Kai, Allah dai ya kyauta” Hajiya Safeenah tace “Toh Ameen” Mami tace “Dama dazu ce maki zanyi za mu je US ganin likita sae kuma kika ce min ai zaki shigo yau ma” Hajiya Safeenah tace “Wa ye ba lafiya?” Mami tace “Matar Khalil din ce ba lafiya” Hajiya Safeenah tace “Subhanallah, Allah sarki, Allah Ubangiji ya bata lafiya, karfe nawa za ku tafi?” Mami tace “Zuwa la’asar in sha Allah” Hajiya Safeenah tace “Toh Allah Ubangiji ya bata lafiya, tana ina yanzu?” Mami tace “Tana ciki tana bacci” Hajiya Safeenah tace “Allah ya sa kaffara ne” Mami tace “Ameen” Sun ɗan taɓa hira, Hajiya Safeenah ta ci abincin da su Bilkisu suka kawo mata sannan tace ma Mami zata koma gida tana da baki, Mami ta rakata har Main parlor, Hajiya Safeenah tace “In dai kun fita zuwa airport ki sanar min, sai in hadu daku a can mu yi sallama Hajiya” Mami tace “Toh in sha Allah” Daga haka Hajiya Safeenah ta bar gidan, Mami na komawa parlonta sai ga Khalil ya shigo, Ya zauna yana kallonta yace “Ya me jikin Mami?” Mami tace “Alhamdulillah, ai kun yi waya da Abbanka ko?” Khalil ya girgiza kai yace “Aa” Mami tace “Toh anjima za mu je USA da ita a dubata da kyau” Ya sauke idonsa yayi shiru, can yace “Mami Visa fa?” Mami tace “Yayi sorting komai out an kawo mata dazu” Yace “Amma na ganin likita ko?” Mami tace “Ehh” Yace “Ohk” Mami tace “Yanzu Hajiya Safeenah ta fita gidan nan, wai dangin mahaifin Nadeeyah sunce sai kai da Janar kun je sun sanku” khalil ya buda ido sosai yana kallonta, Mami tace “Toh abinda suka ce kenan wallahi, ina ma son in kira Janar din yanzu in fara gaya masa kafin mu fita kasar” Khalil dai bai ce komai ba, can ya mike ya nufi dakinta ta bi sa da kallo, har sannan bacci Nihad take, ya karasa kusa da gadon ya zauna gefen ya kamo hannunta, a Hankali ta bude ido tana ganinsa murya can kasa tace “Yunwa nake ji?” Shima yayi kasa da murya yace “Me za ki ci Dear?” Tace “Pounded yam” Yace “Ohk let me get u immediately” Da sauri ya fita daga dakin Mami dai ta bi sa da kallo, kiran Janar ne ya shigo wayarta, tana dagawa bayan sun gaisa yace “Ya jikin nata?” Mami tace “Alhamdulillah, bacci dai kawai take yi” Yace “Toh Allah ya sauke, you should be cautious of time pls, kar kuma kuyi missing jirgin” Mami tace “Ina duba agogo wllhi” Yace “Good” Tace “Kana ji Janar?” Yace “Ina ji” Nan ta sanar masa abinda Hajiya Safeenah ta zo gaya mata dazu, Janar yace “Waye zai kama ya tafi Yemen yanxu? Don’t i have what to do??”

Related Articles

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

 

Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba’a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da ‘Nihad pack’ 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button