Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 22

Sponsored Links

*22*

Jameel sosai yayi mamakin ganin Hammad a daidai wannan lokaci,,dan zaton shi ma ko zahran ce ba lfy.

Bayan sun samu guri sun zauna ne,jameel yakai dubansa gun Hammad yace a sanyaye,”me ke faruwa ne abokina?”

Related Articles

Jajayen idanuwanshi ya ɗago ya dubi jameel ɗin sannan ya fesar da iska,yace a raunane”captain na rasa taya zan sanar da zahra ɓarnar da nai mata abaya,kullum cikin tsinewa soja me ulcer take ina tsoron ranar da tsinuwarta zata bini,so nike in nemi yafiyarta,amma na rasa taya zan ɓullo mata ta fahimceni”ya ƙarasa maganar kamar zeyi kuka.
Shuru ce ta biyo baya na ƴan daƙiƙu kamin jameel ya nisa yace”kuskure de ya riga ya faru,zahra kuma tabbas bazata mance komai ba,sede muyi adduar Allah ya kawo mana abun da sauƙi,”

Asanyaye hammad ya amsa da “Amin”

“yanzu muyi breakfast,se kaje ka sameta ka faɗa mata komai,sabida zuwa dani ze ƙara dagula abun sabida zata ga abun kamar tonon asiri”jameel ya faɗi yana kallon hammad ɗin.

Haka sukayi breakfast ɗin gaba ɗaya jikin hammad ɗin ba ƙwari,ya nufi gida zuciyarshi cike da tsoro da zullumin me faɗar gaskiyar tashi zata janyo masa

Zahra ko tunda ya fita bata ma san baya gidan ba tana ɗaki tana shirga baccinta,shiyasa koda ya dawo gidan beji motsinta a falon ba,ɗakinta ya wuce kai tsaye.

Can ya hangeta kwance tsakiyar gado ta ƙudundune da bargo tana baccinta hankali kwance.

A hankali ya taka ya isa kan gadon,zama yayi ya ƙureta da ido gaba ɗaya nauyi da kunyarta yakeji,a hankali yasa hannu ya janye bargon dake jikinta,a zabure ta mike tana ruƙo bargon,kukan shagwaɓa tasa mishi gamida faɗawa jikinshi tace,”kai yaya bacci fa nikeyi,kuma sanyi nike ji shine zaka buɗeni”tayi maganar cikin shirin kuka.

Murmushi yayi sannan ya kwantar da ita akan gadon yabi bayanta yay mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,yace yana kallon idonta”zahra ta iyayen rigima,to ayi haƙuri yayanki yazo kuyi wata magana me muhimmanci ne shiyasa ya tasheki,amma kamin nan maza kije kiyi wanka ki kimtsa kiyi breakfast,gashi can naga mummy ta ayko,se ki sameni a ɗakina kinji ko?”ya faɗi yana jan dogon hancinta.

Murmushi tayi sannan tace”to yaya yanzu kuwa zanyi duk abinda kace,ɗagani”ta faɗi tana ɗan tureshi.

Ɗagatan yayi ta sauko ta shige toilet,shi kuma ya miƙe ya fice daga ɗakin zuwa nashi,zuciyarshi fal tsoro da firgici.

zahra cikin gaggawa ta kammala komai da yayan nata yace tayi,sannan ta nufi ɗakin nashi harda ɗan gudunta,dan ta ƙosa taji maganar da zasuyi.

Da sallamarta ta shiga ɗakin yana kwance akan gado,yayi rigingine yana kallon silin,shigowarta ce tasa ya maido idonsa kanta,

“yaya gani to na gama” ta faɗi tana ƙoƙarin zama a gefen gadon,
Hannu ya miƙa mata alamar tazo gunshi,ba musu ta isa kusa dashi ta kama hannun nasa,yajata jikinshi.
Mirginata yayi ta koma ƙasan sa,shi kuma yay mata rumfa,cikin dauriya yace”zahra ni me laifine agareki,hasalima ni ne wanda ya ruguza rayuwarki abaya zahra in baki gafarce ni ba zahra ina cikin damuwa”ya ƙarasa maganar hawaye na bin idonsa.

Cike da rashin fahimta zahra tasa hannu ta na share masa hawayen idonsa sannan tace”yaya ka faɗamin me kayi min,da har kake neman yafiyata?nayi alƙawarin yafe ma insha Allahu”ta faɗi cike da tausayinshi.

A hankali ya furta”zahra nine sojan nan abokin jameel wanda yay miki fyaɗe acikin bukka ana ruwan sama lokacin da kika nemi jin ɗumi daga gareni,zahra nine soja me ulcer da kike kukan faɗi lokacin da nike keta mutuncinki”ya ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.

Zahra jin kanta takeyi yana juyawa,wani zazzaɓi ne me zafi ya kamata nan take,wasu irin hawaye ne ke biyo idonta, duniyar juya mata takeyi,yayinda numfashinta ya shiga yi mata wahalar ja,dan haka runtse idonta kawai tayi ta dena kallonshi,

A jikinshi yaji zafin da jijinta yayi,a tsorace ya ɗagata,yana taɓa wiyanta,zafin da yaji sosai ya gigitashi,ga wasu jijiyoyi da suka fito a goshinta raɗo raɗo,alamun ciwon kai.

A gigice yake jijjigata amma ko motsi batayi,agigice ya kinkimeta yayi waje da ita zuwa mota.

Kwantar da ita yayi a kujerar baya sannan ya zaga ya tada motar ya fincika da gudu me gadi ya buɗe masa ƙofa yayi asibiti da ita.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button