Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 15

Sponsored Links

WARNING❌*
_Only matured ahead🔞 idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don ƴammata ba idan kinga zaki iya go ahead._

 

Jikinta taji yayi mata mugun sanyi zuciyarta ta cika da tausayinsa gefe guda kuma da firgicin yanayin da zata ishe Baba a matsayinsa na wanda baya ƙaunar yaganta cikin damuwa. Ganin ta kasa fita a motar ne yasashi buɗe murfin ɓangaren da yake ya fito ya buɗe mata ya kamo hannunta ya haɗata da jikin motar ya matseta ya ɗago fuskarta ya ɗora bakinsa saman ƙaramin bakinta ya tallafo kanta ta zame a hankali ya sake riƙota ya haɗe bakinsu daidai lkcn da haske ya gauraye gurin sakamakon wutar lantarkin da aka kawo daidai lkcn kuma wata lumtsumemiyar mota me numfashi ta tsaya a gefen su Aneey ita ce me hayyaci Abdu tuni yayi nisa baisan meye yake faruwa ba saida yaji ta tureshi sannan yaja fasali ya sauke idanunsa kan Hasina dake tsaye a kusa dasu Tana musu wani kallo na asalin tuhuma.
Babu alamun damuwa ya kama hannun Aneey yayi kissing nashi yace “Kiyimin tanadin abunda zai burgeni ki tareni dashi idan na dawo” yana faɗin haka ya shige mota yabarsu tsaye tana kallonsa Hasina tana kallonta cikin tsananin bugawar zuciya, saida ya ɓacewa ganinsu sannan Aneey ta juyo ga ƴar’uwartata data kafeta da ido ta buɗe baki zatayi mgn Hasina ta katseta da cewa “Tun wajen huɗu na yamma kuka dawo daga shopping da Alh Mu’azzam bayan ya saukeki ina kikaje a ina kika haɗu da Abdu har kuka fita dashi sannan ina kukaje dashi?”

Related Articles

 

Saita tunaninta ta tafiyi don sanin abinda ya dace ta faɗa mata ta yarda da ita tace “A ƙofar gdannan na dawo na tarar dashi yace na rakashi unguwa so shine fa dare yayi mana haka sai yanzu muka dawo…..” Ƙarya kikeyi Hanisa ki faɗa min gskyr inda kukaje da Abdu me kikayi masa ya baki waɗannan manyan kuɗaɗen sannan meye yasa ya ganni ya watsar dani kamar bai ganni ba?”
Sosai kalaman na Hasina suke shigar Hanisa tsoro ya shigeta kardai ace ta fahimci wani abu ya shiga tsakaninta da Abdu…. Bata ida wannan lissafin ba taji Hasina ta riƙe hannunta tace “Wlh cikin kwanakin nan bansan laifina garesa ba Hanisa ya juyamin baya baya mu’amalantata ko wayata yanzun baya ɗagawa kinga yanzun daga yawona na dawo bayan fitarku maza biyu ne suka kwanta dani amma ban gamsu ba Abdu kawai nakeson naji a cikin jikina sannan……”

 

 

Dukan da zuciyarta takeyi mata ne yasata saurin rufewa Hasina baki tace “Nasani Yaya Hasina babu abinda kikayiwa Abdu kawai yana cikin tension ne iyayensa sun matsa masa yayi aure shine duk ya shiga damuwa ɗanzun yake faɗa min yanzun ma cemin yakeyi zai tafi Minna saboda yasan abinda ya dace game da mafitarsa”
Riƙe hannun Aneesah Hasina tayi tace “Amma shine ya kasa faɗa min yabarni a duhu Hanisa yaƙi sanar dani asalin abinda ke faruwa toni meye zai hana yazo muyi auren” cije leɓe Aneesah tayi ta kama hannun Hasina tace “kada ki sawa kanki damuwa nima na bashi wannan shawarar kuma nasan zai ɗauke ta nidai burina ki daina damun kanki Insha Allahu Abdul-Ahad nakine” murmushi Hasina tayi tace “har zuciyata tayi sanyi muje na baki lbrn irin cin da Alh Khamis yayimin yau”
Duk da zuciyar Hanisa ba cikin nutsuwa take ba saida ta harari ƴar uwartata tace “ke wai meye yasa baki rabo da sakarci ne malam me Ahlari yace duk wanda yake aikata laifi yake ɓoye laifinsa ga jama’a to akwai yuwuwar wannan bawan zai shiryu, duk kuwa wanda yake fallasa laifukansa ga jama’a to wannan babu sa ran shiryuwa a gareshi Yaya don Allah ki rinƙa ɓoye laifukanki inasa miki rai da shiriya”

 

Jinjina kai Hasina tayi tace “wannan hakane Rabin jiki muje kiga kayan da Alh Mu’azzam ya kawo miki” tama manta da sunje shopping da Alh Mu’azzam haka ta ƙaƙalo murmushi suka shiga Baba yana tsakar gidan yana zaune akan tabarma da Radio a gefensa yana saurare Hanisa tayi sallama Baba ya gyara zamansa sosai yace “Yawwa Aneesatu zonan” gabanta ya faɗi lkcn data matsa wayarta taga 10:40pm ta ƙarasa gabansa ta tsugunna ya kafeta da ido yace “Hanisatu Ina kikaje?” Ɗagowa tayi cikin zullumi da tashin hankali ta buɗe baki zatayi mgn yace “so biyu ina ganinki a motar maza yau ɗin nan da farko Mu’azzamu ɗan gidan Haji Liti yaron nan daya fitini kowa yazo ya ɗaukeki kun dawo kuma wani ya kuma ɗaukar ki yanzun ashe kema zaki zubar da nasihata dana ɓata tsayin lkc inayi muku Aneesatu ashe kema shaiɗan ɗin ya samu damar hudaki? To shikenan Aneesah kuje kuyi duk abinda kukeso idan baƙin cikinku dana uwarku ya kasheni kun huta Allah ya sani ina iyakar ƙoƙarina wajen ganin kun zama ƴaƴa na gari abin faharin iyaye amma abin ya faskara tashi kije Allah ya shirya min ku”

 

Miƙewa tayi jikinta a mace ta nufi ɗakinsu Mama ta tarar da Yaya Hasina sunata brush da naman kaji ta nemi guri ta zauna Mama tace “Kya raɓe matso kema ayi dake ƴarnan ina kikaje ne?” Ƙasa tayi da kanta tana matsar hawaye kalaman Baba sunyi mugun kashe mata jiki tace “Wlh Yaya banaso nakeyin abinda yake ɓata ran Baba Kullum nasiharsa garemu mu zama na ƙwarai” tsaki sukaja a tare Hasina tace “Sai kiyi ai Ni ki bani kwancan wayar hannunki ga sabuwa kinyi” karɓar wace take miƙo matan tayi ta dubata sosai tayi murmushi tace “Ai wannan ɗin tafi dacewa dake” zaro ido tayi waje tace “ni shegiya wannan ai saiku manyan yara”

 

Musu suka kama tsakaninsu mama nayi musu dariya Hanisa tace “kingane ko babe abinda yasa nace ki bani wannan kinga masoyi nane ya siyeta wannan kuma masoyinki ne zaifi kyau kowa ya riƙe ta masoyinsa” kafaɗa ta maƙale tace “Aa nikam banason wayon bar abinki” dole ganin bazata yarda ba Hasina ta kamata da kokawa suna dariya ta samu ta kwace wayar ta cire layin tasa a sabuwar wayar da Alh Mu’azzam ya siyo mata ta ajiye mata.
Ficewa Mama tayi tana cewa “kun daifi kusa Ni na tafi na kwanta” saida safe sukayi mata suka sauke katifar da suka siya suka zauna ƙirga kuɗaɗensu Hasina tace “kinga gobe zamuje banki mu buɗe account sai mu wucce waffer a canzo waɗannan dalolin a adanasu zasuyi mana amfani musamman ma da kikace Abdu yace miki aure zaiyi Aneey inason Abdu bazan taɓa yarda na rasashi ba gobe idan mun gama da wuri zamuje gurin wani malami da muka taɓa zuwa da Mama zaiyimin aiki akan Abdu so nake yaji a duniya ya tsani kowacce mace Indai bani ba”
Shiru Aneey tayi ƙirjinta na bugawa da ƙarfi tace “Malami kuma Yaya….” Rufe mata baki tayi tace “Karkicemin komai ke kin fiye bidi’a itafa rayuwa Aneey sai kana taɓukawa kanka wani abu” jinjina kai tayi batason su cika jayayya da ƴar uwarta ta shiyasa tayi shiru zuciyarta tayi ƙunci hakanan batasan dalili ba takejin Abdu a ranta yanata dawo mata kwanciya tayi kalamansa dana King sunata dawo mata tsoronta na nunkuwa a ranta takejin yanzu idan ya tabbata itace matar Abdu ya Hasina zataji saurin katse zuciyar dake raya mata haka tayi da cewa “Ina Bama zai yuwu ba”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button