Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 8

Sponsored Links

8……*
Kamar an dasa Abraham haka tsaya jikinsa na rawa kansa ya sara sosai, wannan shi ne karan farko daya yi mata kyakkyawan kallo, kallon da ba zai taɓa shafewa a cikin ƙwaƙwalwarsa musamman yanzu da yake cikin yanayin ciwon hauka, haukan kuma bai sanya ya manta wani kyakkyawan gurbi dake zuciyarsa ba.
Ko a baya bai san haka kyan jikinta da surarta yake ba. Malama Majeederh na tsaya gaban mirror ta ɗauki wani body lotion tana dubawa ɗago kan da za ta yi taga mutum tsaye a bayanta ta cikin mirrorn.
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ta furta cikin tsoro ta rufe Idanunta domin bata gama tantance waye ba, ta ƙara buɗe idanu ta cikin madubi ga mamakinta hawaye ta gani kwance cikin idanunsa sai a lokacin ta kalli cikakkiyar fuskarsa.
“Little?” ta ce da mamakin domin ita ta gama sanyawa a zuciyarta baya raye a duniya. Yana tsaye bai motsa ba, hawayen idanunsa bai tsaya ba, abubuwa ne da yawa suke son dawowa cikin tunaninsa wasu tsofaffin memories na gilmawa ta cikin jijiyar dake motsawa tunanin ko wanne ɗan adam a cikin ƙwaƙwalwa.
Su yake ya tambayeta “Me take a nan? Ya yaga ta take? Waye ya taɓa ta yanzu ya yanke hannun ko waye, me ta yiwa jama’ar gari? Shin daman haka addinin na su yake, mabiyansa basa yiwa kansa adalci, basu kyakkyawa na ciki ba ina ga bare?”
Bakinsa ya a yi masa nauyi, tunaninsa ya tsaya kamar yadda take kallon cikin idanunsa haka ita ma yake kallonta,irin kallon nan da ba kowa ne ya isa ya fassara ma’anar shi ba.
“Jee” Abraham ya faɗa tare da yin inda take, kafin ta juya da nufin matsawa ko ɗaukan hijabi gaba ta jita nan naɗe jikin mutum ya ƙanƙameta a ƙirjinsa kamar wani zai ƙwace ta, tamkar zakin daya shekara yana neman abin farauta bai samu ba sai yanzu.
Duk yadda da su ƙwace jikinta kasawa tayi, fargabarta ɗaya kada wani ya shigo zargin da ake mata ya tabbata, domin babu wanda zai yarda ba da saninta Abraham ya shigo ba.
“Ka yi hauka?” “No!”
Ya bata amsa, amsar data bata mamaki tasha ce masa “Ka yi hauka ne” kai tsaye zai ce mata “Yes, Mahaukaci ne ni Jee” amma yanzu ya bata amsa da “No!”
Hakan na nufin akwai wani abu a ƙasa.
A lokacin kuma ta lura da yanayinsa, shigarsa, sauyin tunaninsa da kamanninsa everything. Majeederh tsayawa tayi tana kallon Ikon Allah, ba zata iya ciwon baki ba, ba zata iya kokawa ba don haka ta ja idanunta ta runtse ƙirjinta na ɗagawa a saitin nasa ƙirjinsa sosai kuma hakan ke taɓa Abraham, tun tuni ta san Abraham bai san wani abu mai kama da tsoro ba, bai san haƙuri ba, balle ace kayi haƙuri ya yi, bai ladama ba, bai san ya yi laifi ba, taurin kai ba zai taɓa abinda bai niyya ba. Abu ɗaya ne da shi yana da tsananin tausayi baya ƙaunar ganin hawayen mace yanzu zai riki ce.
Mamakin ganinsa kuma ya sata kasa ɗaukan mataki.
“Am not crazy Jee, ni ba mahaukaci ba, am not bad, an kai ni gidan mahaukata, kada ki bari wallahi zan kashe kowa”
Jeederh ta tattara ƙarfinta ta hankaɗe Abraham tare da nufar wajan wardrobe zata ɗauki hijabi cikin saur ya biyo ta tare da riƙe hannunta ya sa ƙafa ya daki wardrobe ɗin nan take ta tsage murfin ya faɗo. Ta sanya hannu ta zabga masa mari, ta ƙara zabga masa mari rai ɓace irin ɓacin ran da ko a gaban Abbu bata nuna ba lokacin daya koreta daga gidansa Idanunta ya kawo ruwa ya kwanta ta nuna shi da hannu tama kasa cewa komai.
Murmushi Abraham ya yi yana shafa fuskarsa wane yatsun hannunta ya kwanta sosai cikin gurɓatacciyar Hausar shi maganar a rarrabe da ƙarfi kuma ya ce..
“Beat me, beat me…If that will make you happy” ya cije baki tare da sanya hannunsa ya hargitsa kansa da zafin nama ya dinga kaiwa ko’ina duka hannunsu ya fara zubar da ji ni ya juya zuwa inda take kamar zai shigeta ya ce
“Idanunki ya bayyana laifina,ni na ce maka I’ll be back, sooner or later, bana da laifi Jee babu laifi wajeni” duk ya dagula hausar tashi wacce yasan ta fahimta. Ya kama hannunta ta ƙwace da sauri cikin kakkausar murya da riƙe kanta ba tare data bari ya fahimci halin da take ciki ba ta nuna masa ƙofa ta ce “Out, ka je can kayi haukanka mahaukaci”
“No, am not”
“You’re Mad” da ƙarfi ya ce “Am not, you stop listening to me” ya faɗa yana matse kafaɗarta idanunsa kamar za su faɗo ƙasa ya zaunar da ita saman gefen gado, tare da zubewa a gabanta ya ɗora kansa saman cinyarta kamar yadda ya sama, wani irin raunataccen kuka ya ƙwace masa, ya dinga yi kamar wani ƙaramin yaro tunda take bata taɓa ganin hawayensa ba balle kuka yau gashi yana rusa mata kuka kamar ance masa Denial ya mutu ko David ko Kiristi. Ba zata iya tantance lokaci daya shafe yana kukan ba, zuciyarta motsa rauni irin na ɗiya mace ya so kamata tausayi irin na uwa da ɗanta ƙwance akan fuskar Malama Majeederh.
Tana son bashi baki akan ya tashi ya tafi, ya ƙara yin nesa da ita fiye da yadda ya yi ta bashi labarin halin da itama take ciki, tasan faɗa ba zai taɓa yiwa Abraham ba, ko mutanen duniya ne za su taro a nan babu abinda ya dame shi.
A hankali ta sanya hannu zata ƙara ɗaukan hijabi caraf ya riƙe hannun tare da ƙwace hijabin ya zuba mata narkakkun idanunsa wanda sukai jajir while he’s still crying.
Hannunta ta sanya duk biyun a fuskarsa ta riƙe cikin kyakkyawan lafazi ta ce “Why? Why?”
“Am sorry!”
Ta dube shi ya ce mata sorry baya yi masa wahala, ya ce Sorry ga jama’a kuma babu uban wanda ya isa.
“Why?” Ta sake tambaya.
“Don’t judge me, because of your barracks that I have been doing for years”
Ya fesar da numfashi yana kallon jikinta sosai ba abinda ya dame shi mamakinta yake sai yanzu ya fahimci dalilinta na kwasar tarkace ta zuba a jikinta.
“Jee ban ji komai a small marin da ki kayi mini ba, da gaske Mahaukaci ne ni? Dad ya ɗaukeni sun kai ni gidan mahaukata kullum ana mini injection suna sayawa ina jiwa kai ne ciwo, suna son fasa tunani na” ya sunkuyar da kai kafin ya ce.
“Jesus”
“Ki yarda this time around mu tafi, muyi auren Choci” Sai a lokacin ta share hawayen idanunsa ta ce.
“Little ina cikin masifa, ina cikin jarrabawar Ubangiji, don Allah ka tafi leave me alone”
“I knw everything, Abbu ya barki zuwa waje right? Jama’ar addininki sun wulaƙantaki right, Uhm where’s is the baby?” Bata ce masa komai ba har yanzu yana durƙoshe gabanta ya ce
“Meye abun damuwa? Ni nayi miki cikin fa, ni ne baki cikin ke da babyn duk nawa ne barsu kawai” cikin razani tana fito da ido ta ce
“Abraham fita, ka fita na ce kabar bedroom ɗin nan” ya ɗaga ƙafa shi bai ga abin damuwa ba ya ce
“I mean my words ni ne na baki cikin, kawai bani da tabbacin yaushe cikin ya samu tunda al’amarin shekaru biyu baya ya faru kenan kuma yanzu ki ka fito da babyn waje, kawai nayi believing babu wani namiji da zai samu sa a irin tawa balle ya baki ciki”
“Ka cika Mahaukaci”
Gabaɗaya suka kalli bakin ƙofa Abu-turab ne tsaye yana tattara hannun riga, Abraham Daniel David ya miƙe tsaye Malama Majeederh ta tayi toilet cikin sauri ta zura abayar data cire ta ɗora rolling.
“Zan nuna maka Banbancin mai hankali da mara hankali, zan nuna maka tazarar dake tsakanin mai mulki da kuma wanda ake mulka” Abraham dai na tsaye can ya girgiza kai ya ce
“Oh, Go ahead”
“Kasan waye ni a jihar nan?” Cikin shan ƙamshi Abraham ya ce
“Governor Abu-turab Alƙasim” sosai His Excellency Abu-turab ya yi mamaki kafin ya ce
“Haukan ƙarya ka ke yi kenan?” Idanunsa akan ƙofar toilet ya ce
“Daman ai bance Mahaukaci ba ne ni, let me warn you kada ka takura kada ka matsanta,kada ka zurfafa domin You can take it”
“I love her” cewar Abu-turab.. “I am the one who raped her” Abraham ya bashi amsa, yana matsowa dab da shi.
“Zan iya komai a kanta” Wani irin murmushin mugunta Bad boy ya yi kafin ya ce.
“Ita ne dalilin ya sa aka kai ni gidan mahaukata”
Abu-turab ya faɗa shi ma yana matsowa wajan Abraham suka haɗe ko wannensu yana huci.
“Mara tsafta, wanda ya dulmiyya cikin yadanci ha zai taɓa samun Malama Majeederh ba”
Wata dariya sosai Abraham ya yi yana ɗora hannunsa a shoulder ta Abuturab ya ce.
“Ƙarshen samu ni na amshi budurcinta, na ɗauka abinda nake kwaɗayi ne sai dai ko mintuna arba’in ba ayi ba na fahimci ba budurcinta nake so ba,I want to end my life with her, I want to take my last breath on her shoulder,I lived with her love, I will die on her lap with a smile on my face”
Abraham ya faɗa a hargitse. Abu-turab ya ce “Idan ka dauwama a gidan yari har ƙarshen rayuwarka, sai mu gani ko zaka sameta”
“Kai ka ke tsoron prison, ka duba record, da report na Abraham Daniel David ni criminal nan”
Abu-turab ya ɗaga hannu zai mari Abraham kafin His Excellency ya sauke hannun ji ka ke ƙasss! Abraham ya ƙarya hannun. Wata ƙara ya saki da sauri kuma ya danna wani abu daman Hammad na waje don kada ya shigo ne, yana jin ƙarar ya shigo da sauri ganin Abraham ya sa ya ja da baya.
Securities ɗin da suke cikin gidan gabaɗaya suka shigo part ɗin Malama Majeederh daidai lokacin itama ta fito Idanunta jajir da alama ta saurari komai dake faruwa.
Zufa ce ta dinga yankowa Abu-turab, Majeederh ta tsaya tana kallon Abraham day taso ya tsaya a gaban baki ya buɗe ya ce.
“Malumana, shi ne….,”
Marin data sauke masa yasa ya kasa magana, ta ƙara sauke masa.
“Ka tarwatsa mini farin cikina, jin daɗina kwanciyar hankalina, ka rabani da iyayena i hate you” Abraham ya zare ido domin shi ya ɗauka for now bashi da wani laifi, idan har ta karanta saƙon daya bari before he leave the country.
“Na raineka da hannuna, na baka kulawa kamar yaron dana haifa,daga baya na rasa ka, nayi kuka na shiga damuwa, ban cancanci haka ba, kaci zarafina ka ci mutumcin addinina, ban san ya akai hakan ta faru ba amma zan so ka bayyanawa duniya gaskiya domin na samu sassauci, Abraham Daniel David…”.
Ta ɗauke kai shi dai yana tsaye gabanta kamar idanunsa za su faɗo ƙasa, yadda ƙirjinsa ke ɗagawa kai sai sanya a gane zafi da tasirin maganganunta a zuciyarsa.
“Allah ya isa, na tsaneka adadin tsanar da mahaifina ya yi mini zan so ka samu tabbataccen taɓin hankali na har abada” sai a lokacin Abu-turab ya zo ya kifawa Abraham mari amma ko motsawa bai ba Malama Majeederh kawai yake kallo.
“Ku kakkarya mini shi a kuma kai shi prison har ending rayuwarsa”
Securities suka rufe Abraham da duka ta ko’ina da ƙasan bindiga. Da ace babu Majeederh wajan ko kalamanta ba su yi tasiri a zuciyarsa ba da tuni dambe ake da shi. Ana dukansa yana kallonta. Ya miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabinta yaje har gabanta ya sanya mata, shi kansa bai san dalilin sanya mata hijabin ba, amma yana lura da idanun Abu-turab akanta. Wani securities ya sakarwa Abraham ƙasan bindiga akansa nan take kan ya fashe, Majeederh ta runtse Idanunta.
Daidai kunnenta ya ce.
“Jee kin jima da sanin Abraham baya giving up, azabar nan babu inda zata, idan baki yafe mini mun daidaita har mun yi aure babu shakka zan baki ciki na biyu, i don’t care” “take him out”
Cewar Abu-turab, Hammad tausayin Abraham ne ya kama shi.
Da ƙyar yake jan numfashi sbd wahala amma bai fasa kallonta ba, har suka isa bakin ƙofa za su fitar da shi idanunsa ya kawo ruwa sai kuma ya yi dry domin ya hango rauni a cikin idanunta kawai bata sani ba ne, da ƙarfi ya ce
“I love you Malumana, I’ll be back”

Not editing.
Littafin MIJIN MALAMA na kuɗi ne, kuyi magana a wannan number domin biyan kuɗin 08119237616… Na kusa gama free pages

 

Related Articles

*Ina Mata ‘yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_ *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*
We have
*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su
*Atampha of all kinds*
*Veils*
*shadda*
*shoes*
*qualitative handbags*
*Jewelries* etc
Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181*
Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu

https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo*🌈MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button