Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 7

Sponsored Links

7…….*

_Complete story Arewabooks👇🏾_
https://arewabooks.com/chapter?id=6219d7896c0de838cd360960

Duk yadda Jeederh ta kai da son kamewa waje guda da riƙe kanta amma ka sawa tayi ta miƙe tsaye hannunta riƙe da Khalil, amma ta kasa motsawa sbd bata ƙara jin saukar sautin da kunnuwanta suka jiye mata ba. Shiru shiru sai kawai ta juya zata koma saman bed ta ƙara jin ance “Jee, Jee Malumana” a wannan karan muryar da aka kira sunan bata fita sosai kamar bai kiran yana cikin wani hali, ƙirjinta ya yi kyakkyawar bugawa, bugawar da sai data runtse Idanunta, me ya sa muryar ke yi mata tsananin kama data Little Son? Me ya sa hatta sunan ya zo ɗaya da wanda ya laƙaba mata sbd bashi da hausar da zai iya kiran complete sunanta Majeederh kamar yadda kowa ke faɗa, iya ƙoƙarinsa da faɗar sunan sai dai ya furta kalmar _Jee_ a sauƙaƙe?
“Yaa Allah” ta furta domin tasan har abada har gaban abada idan akwai he never comes to her, amma meke damunta har haka me ya sa muryar ke mata amsa kuwwa a kunne? “Jeeeee!!!” Ya sake furtawa muryarsa bata fita sosai kamar wacce aka tsikara tayi wajan ƙofa tare da sanya hannu ta murɗa handle, tsaye ta gashi yana zabga ƙamshi daga shi sai wata kyakkyawar Arabian jallabiya brown kallo wacce tayi masa kyau sosai, ya ɗan sakar mata kyakkyawan murmushi kafin ya ce
“Kina buƙatar wani abu ne?” Tayi masa kallo ta ɗauke kai ba tare data amsa shi ba, domin bata da yawon magana Majeederh nada matsanancin aji sosai, wanda kuma halittar ta ce hakan. Gani ya yi tana leƙa waje shi ma ya leƙa yana cewa “What are looking for? Me ki ke kallo?” A raunane wanda kuma ba kowa take son yaga raunin nata ba ta riƙe kanta sosai tana sake rufe jikinta da hijabi ta ce “Allow me to go”
“Where?” Ya amsata da sauri. “Ban son zaman nan, kuma ka bari na leƙa waje” Abu-turab ya ware idanu yana shafa sumar kansa ya ce.
“Me Jiddo zata yi a waje yanzu? 2 saura ok” tayi shiru ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin tayi saurin ƙanƙame jikinta waje guda lokacin Khalil ya fara kuka..
Sosai Abu-turab ya rufe ƙofar kana ya nemi waje nesa da ita ya zauna saman kujera ya harɗe ƙafa. Malama Majeederh hankalinta ya rabo wajan kashi uku, ɗaya na waje, ɗaya na kan Khalil dake kuka, ɗaya na kan Abu-turab daya sanyata a gaba tare da kafeta da idanu. Sai ta zama ira bata ƙaunar kallo yana takura ta ainun.
Abu-turab yana ƙoƙarin magana su ka ji an daki ƙofar ya miƙe tsaye tare da kallon Jeederh ya ce
“Sorry, na ce a kawo mini abin shur ina da azumi” bata ce komai ba ita dai.
Ya nufi ƙofa yana fita ya rufe ta, kokawa ake sosai da Abraham Daniel David wanda yake son ta ƙarfi sai ya ɓalle ƙofar, gadai securities da yawa amma sun kasa controlling nasa ya jiwa kansa ciwo amma yaƙi ya yi giving up, wani irin ƙarfi ke zuwar masa. “Abraham” Abu-turab ya kira shi,ya juya kalli Abu-turab.
“Me ka ke buƙata?” Da hannu ya nuna masa bedroom ɗin da Malama Majeederh ke ciki, kana ya nuna ƙirjinsa wajan zuciyarsa ya ce.
“Jeena, nan” Abu-turab ya fahimci Abraham na son shaida masa Jee na cikin zuciyarsa ita kuma yake nema. Cikin nutsuwa yana murmushi ya ce
“My friend zo ka ji” Abraham ya kafe waje guda domin babu na biyunsa a taurin kai. Cikin tattausa harshe ya ce “Ita Jee ɗin bata nan, amma ka dawo gobe zan kaita wajanta” ya faɗi hakan cikin harshen Ingilishi yadda Abraham zai fahimci mai yake nufi.
“Promise?” His Excellency ya ce “Promise” Abraham ya sanya hannu a tsakiyar rigarsa inda ya yage ya zaro wata kyakkyawar flowers sai ƙamshi take ya miƙawa Abraham yana wani irin buɗe ido ya ce “Malumana”
Ma’ana the flowers is for her. His Excellency ya amsa deep down na zuciyarsa cike da mamakina Abraham who is he to her?.
Securities ɗin za su kama shi ya girgiza musu kai tare da yin gaba yana ɗan tangaɗi yana yin gaba ya ji saukar muryar Khalil na kuka ya tsaya cak, sai ya juya kawai sai su kaga ya yi murmushi ya ce
“My pregnancy”
“An samu matsala” In ji Khamal. Abu-turab ya saka hannu ya tsige flower ɗin tare da zubar da ita ya ce
“Make sure baku sake sakaci ba, i hate noises”
“We’re sorry Sir, Hakan ba zai sake faruwa ba, wallahi ta sama ya hauro mahaukaci ne daya kama hannun Captain sai da ya ƙarya shi,ya sha duka sosai wajanmu amma bashi da haƙuri yana da zuciya ban san wani abu giving up ba” His Excellency bai ƙara magana ba ya buɗe bedroom ɗin har yanzu tana zaune saɓanin ɗazo Madara take bawa Khalil, Abu-turab ya jima yana satar kallonta da tayi ƙoƙarin ɗago kai sai ya janye idanunsa ya basar
“Jiddo, we need to talk please” yadda ta ƙara nutsuwa ya san cewa ta bashi dama cikin nutsuwarsa ya ce
“Majeederh kina da hankali, ko ban girmeki ba zamu iya zuwa age mate don haka duk abinda zan faɗa miki ba zai zama cutarwa a gareki ba” ya sauke numfashi ya ɗora da “Don Allah kada ki ji zafinki akan hukuncin da ya yanke miki, iyaye ba a taɓa fushi da su ki ɗauki hakan matsayin jarrabawa kuma ƙaddara wacce babu yadda zaki iya dole sai ta kasance, ba zan miki nasiha akan yarda da ita ƙaddarar ba domin kusan kin fini sani, sai dai na nemi ta barraki a wajanki” ya ƙara yin shiru ya ce “I feel your pain, kafin na zama gwana na sha wahala,ina rayuwa da mahaifiyata after my father’s died, dangin mahaifina they are so selfish sun ƙwace komai dana mallaka wajan Abbana, filaye, kadarori all the properties, mun fara yawo yawo a dangi kowa yana gudunmu sbd babu ran mahaifina sun manta alherin da ya yi musu, dangin Mamana basa kusa, na fara dako ina garuwa ban taɓa yarda ba zan iya ba, burina Mamana ta ji daɗi na zama wani abu” ya ɗan sauke numfashi kamar lokacin abin ke faruwa kafin ya zuba mata Idanu ya ce “I was thinking mene ya sa mutane suke manta alheri? Kuma da yawan mutane suke sawa ka zama mutumin banza, ko dana fito takarar House of assembly kin me ne ya faru?” Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalle shi some seconds kafin ta janye ganinta daga gare shi, tana ɗan ɗauke numfashi sbd abubuwan da suka tukare mata bata san ranar faɗawar su ba. Abu-turab smile yana jan idanunsa zuwa sama kafin ya ce
“Cewa akai kada a sake a zaɓeni wai bani da uba, ba wannan ya daman ba familyna sune kan gaba wajan ganin na fasa kujerar da nake nema, kamar yadda suka so ban samu ba, gabaɗaya deligate suka juya mini baya, cikin ikon bayan an cinye tenuwa huɗu cif na sake fitowa takara i won the election, nayi shekara huɗu a lokacin ne na haɗu da ƙaddarata, wacce ta zame mini Dafi a zuciya, ta zame mini wani tabon da bana tunanin zai taɓa gogewa da jikin zuciyata sai dai idan zuciyar ce ta samu abinda take buƙata, Jiddo ban faɗa miki haka domin ki tausaya mini zuwa gaba ba, shi ya sa ma ba zan baki labarin cikakkiyar ƙaddara tawa ba, amma ki sani ko wanne mumini idan har amsa sunansa dole Ubangiji ya jarabce shi da jarrabawa, bafa don ya son mutum yake jarabtar shi ba, sau tarin wanda Ubangiji ya fi jarabta to ya fi samun kusanci da shi, kiyi haƙuri ki ɗauka haka zanen taki ƙaddarar yake, babu mamaki mahaifinki ya fiki jin zafin abun da ya faru kiyi masa uzuri, ki addu’a cikin sauƙi komai zai zama labari” ruwa ya ɗauka ya sha yana sauke numfashi.
“Thank you!” Ta furta cikin kamewarta da nutsuwarta a koda yaushe, da nuna cewa ita ɗin babba ce mai ƙiba da daraja wacce a yanzu ta rasa ko wanne daga ciki.
“It’s my pleasure, an kawo Raguna na raɗin sunan baby” “ba buƙata”
“Akwai” ya furta cikin tsare gida.
“Kada ki zama mai son kan ki Jiddo, kada ki zama mai musu after all this am elder than you na je 42 ke kina 35, kin ga akwai respect na girman dana baki” shi kansa mamakin surutunsa yake a yanzu ya manta rabon da ya yi magana mai tsayi, lallai zuciya bata da aji ga abinda take muradi da kwaɗayin zama da shi..
“Khalil na godiya”
“Mamin Khalil fa?” Bata ce komai ba ya watsa hannu ya ce “Alright, i don’t need your thanks”
Ganin yadda take kallo agogo ya sa ya fahimci tana son kwanciya ya miƙe tsaye yana shafa sumar kansa ya ce
“Ya Rabb! Good night”
Har ya je bakin ƙofa ya sake juyawa ya zuba mata idanunsa ya ce
“Lailatan sa’ida” ta bisa da kallo har ya fice.
Majeederh Yaronta Khalil ta zubawa idanu wanda yake barci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bata da sanya damuwa a rai, amma kunnuwanta sun kasa manta sautin Abbu da yake cewa
“Allah ya isa Majeederh”
Ta rufe ido da sauri ta buɗe data tuna kalmar “Tamkar gawa haka ki ke a waje na” “Fasiƙa!”
Ƙirjinta ya fara ɗagawa numfashinta na tsayawa ta fara kokawa da iskar dake kaiwa zuwa hunhunta ta miƙe da sauri tare da shigewa Bathroom tana daga tsaye ta sakarwa kanta ruwa mai sanyi shower ta dinga ratsa tsakiyar kanta jikinta ya jiƙe ta mance ciwonta sam, ita da ace ciwon zai zama sanadin tafiyarta lahira da wallahi sai tafi kowa murna da kan ta yarda ta koma wajan wanda ya halicceta ya bata ikon kare mutuncinta amma wani mugu azzalumi ya rusa wannan ƙimar, ya shiga gonar da bashi da ikon ko mallakarta bare ya yi tunanin yin noma ya zuba iri. Ana cewa sai ƴa mace ta bada dama ake cin mutuncinta, kamar yadda kalamar sai bango ya tsage ƙadangare yake samun damar shiga.
“Wata bawa dama?” Zuciyarta ta tambayeta. A fili ta furta “Ba zan yafe ba, ko waye na tsane shi Allah ya hana shi kwanciyar hankali”
Ta cire kayan jikinta tare da ɗaura towel jikinta sai sheƙi yake ko’ina yana glowing tunda hutu take samu. Dirarriyar mace ajin farko, kyawun Majeederh na iya sanya ayi raped nata balle Mutum ya yi arba da surar jikinta. Fitowa tayi ta ɗauki wata push pink ɗin abaya ta sanya tayi rolling kanta tare da tsayawa gaban window tana kallon waje tare da shaƙar fresh air, a hankali ta ƙara buɗe Idanunta domin daga bayan ɗakin da take gate ɗin bayan gidan ne idon ba gizo Idanunta ke mata ba babu shakka mutum take hangowa zaune shi ɗaya ya zuba uban tagumi…
Washegari ta shirya tsaf ita da Khalil tana cikin wata blue black ɗin Abaya tayi rolling kanta da babban mayafi fuskar nan fara fat kamar wacce jini ya ƙarewa ga yawon jiri da take yi da ciwon kai duk dare, ta ajjiye cup ɗin hannunta Mama dake zaune ta ce
“Ko ke fa, ai jego ba zai yiwu babu cin abinci ba, shi ya sa babu ko ruwan nono a jikinki, ina tunanin zan yi wa Haseenatou magana ta zo ta tayaki zama kyafi sakewa”
“Na gode sosai Mama, am ina son tafiya”
“Tafiya zuwa ina? Kina kallon yadda jama’a suke fakon ki kamar kin kashe rai wani bai san meke faruwa ba, kawai jita jita zai ji ya kama ya ɗorawa kansa, Ƴata duk wata daraja mace gidan mijinta idan babu shi ne ake rayuwa cikin gidan iyaye, yanzu an shige zamanin da idan ƙaddara ta faɗawa ɗan ka zaka gujesa, a lokacin ma zaka jawosa jikinka, Malama Majeederh baki da wajan zuwa sama da nan kiyi zamanki ki raini ɗan ki har ki samu mijin aure” Majeederh jin Mama kawai take domin ita ba aure yanzu a shafin rayuwarta, babu ma namijin da zai iya sha’awar zama da ita matsayin miji. Suna zaune aka buɗe ƙofa wata kyakkyawar yarinya ta fara shigowa da gudu hannunta riƙe da teddy tana zuwa ta haye jikin Mama ta ce.
“Uncle ba ni”
“To ƴar gatan Uncle”
P.a Hammad ya shigo da murmushin tare da zubewa ya ce “Ina kwana Mama” Mama tayi murmushi ta ce “Allhamdulillah ya mutum gidan” ya amsa da “Suna lafiya” ta miƙe tsaye ta ajjiye Jidda ta ce
“Bari na shiga na kalli labarai” ya yi mata adawo lafiya cike da ladabi da girmamawa domin yana da tabbacin Malama Majeederh ta girme shi ya ce
“Barka da Safiya Anti Majeederh” idanunta akan Khalil a kullum shi ne abokin wasanta, ya zame mata t.v
Ta jima tana kallon Khalil kafin ta ce “Kana lafiya?”
“Allahamdulillah ya baby” ta juya idanunta kawai bata ce komai ba.
“Jidda ce Mami good morning” ta kalli Pa. Hammad ta ce “Mami ce?” Daga bakin ƙofa aka ce “She’s your Mother, jeki gaidata” His Excellency Abu-turab ya furta yana shigowa cikin wata dakakkiyar shadda mai kyau sai zabga ƙamshi yake sosai nutsuwarsa ta gama bayyana kamalar shi.
Jidda tana tsalle da murna ta ce “Mamina”
Ta faɗa tana leƙa fuskar Malama Majeederh.
Jeederh ta yi wa Jidda murmushi tana shafa kanta, P.a Hammad ya yi waje ya bar daga His Excellency sai Malama Majeederh da Jidda.
“Is my daughter, mun rasa mahaifiyarta wajan haihuwarta honestly sunanki na saka mata” da mamakin sosai Majeederh ke jin abun ina ya santa har ya sanyawa yarinyarsa sunanta? Lallai karamcin Abu-turab daban yake, kamar yadda ya ce haka aka yanka rago tare da ƙara yiwa Ibrahimul-khalil huɗu ba da sunan daya samu. Tun daga nesa yake danna horn cikin sauri mai gadi ya buɗe masa ya shigo, a hankali ya sako kan motar cikin harabar gidan nasa, mamakin ganin motoci daban daban a parking lot ya kama shi.
Ya buɗe ya fito yana sanye cikin wani tattausa brown ɗin yadi mai laushi ya ɗora hula jaddara, hannunsa ɗaya ya saka cikin Aljihu har zai tambayi mai gadi baƙi akai ne? Sai kawai ya buɗe ƙofa ya shiga, shiru gidan babu motsin komai sai wani slow music dake ta shi, ga parlourn kaca-kaca sai wari da ƙaurin abinci yake, kwalayen exotic birjik plate ɗin abinci har a saman kujera, nan da nan cikin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya fara juyawa ya toshe hanci da sauri yana haurawa sama tare kiran
“Latifa, Latifa”
Yana ƙoƙarin buɗe Ƙofar bedroom ɗin ta tayi saurin fitowa, ya shiga kallonta frm head to toe, towel ne a jikinta iya qiwwa gashin kanta duk a har gitse ya dubi gefen bakinta ya ga jambaki.
“Lafiya?” Aliyu ya ce
“Su waye a gidan?” Ta ce “Friends ɗina ne, yanzu zasu bar maka gida” ya yi jim kafin ya ce “Yanzu dake da friends ɗin mahaukatan ina ne Wife? Ki kalli gidan nan kamar bola wanne irin abu ne, kema kalleki babu tsafta ba komai irin ƙamshin perfume ɗin nan ma babu, babu mamaki part ɗina ba haka yake ba gyara a haka ki ke ihun kada nayi aure? Ko son ki zai kasheni idan har zaki dinga gallaza mini da ƙazantarki wallahi tsanarki zan yi” ya juya rai ɓace bai taɓa ganin ƙazanta irin ta Latifa ba ta rasa yadda za tayi amma tayi farin ciki domin ita tunaninta ya manta da batun Latifa… Gidan ya yi shiru Mama tana part ɗinta, His Excellency Abu-turab ya fita zuwa Wajan meeting a Government house, securities ɗin na bakin ƙofa. A hankali ya dinga leƙo kansa ta wajan gate ɗin dake kusa da bedroom ɗin Jeederh, shigar yau ta musamman ce gashin kansa ya ƙarya hargitsewa ya kwanto gaban goshinsa, hannunsa riƙe da wani teddy da flower mai kyau rabin faffaɗan ƙirjinsa a bayyane sbd yagewar da rigarsa tayi wandon jikinsa 3gauter ne, ga ƙatuwar sarƙa a wuya. Ya kama gate ɗin tare da dirowa cikin gidan, da sauri ya nufi bedroom ɗin cikin sa a yana kama handle ɗin bedroom ya jisa a buɗe, Abraham ya lumshe idanunsa masu cike da kewa ba sallama ba knocking ya tura kansa cikin bedroom ɗin daidai lokacin ta fito daga toilet tana sanye towel iya cinya…

Not editing
Jiya na yi Busy na je unguwa ga wajan aiki🙏🏿.

An fara biyan kuɗin littafin tuni… Yi magana domin biyan naka 08119237616

 

*Ina Mata ‘yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_ *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*
We have
*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su
*Atampha of all kinds*
*Veils*
*shadda*
*shoes*
*qualitative handbags*
*Jewelries* etc
Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181*
Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu

https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo*🌈MIJIN MALAMA🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

_Please ayi following Acct na sister na👇🏾_
https://arewabooks.com/u/ayshadansabo

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button