Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 33-34

Sponsored Links

 

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Related Articles

Abu kamar wasa Saida Beebah tayi kwana goma sha uku a asibitin sannan ta samu ƙwarin da aka sallame ta, a zaman nan nata babu wani daga gidan sarautar da yazo dubata in ka ɗauke Hajiyan soro da tazo itama don ta fahimci kowa ma a gidan fushi Habeeb yakeyi dashi ne kuma ta fahimci da gaske ya damu da damuwar yarinyar fiye da yanda ya damu da kansa sannan zuwa lkcn anyi walƙiya a cikin gidan sarautar duk wanda ya isa yasan Habeebatullah matar Habeeb ce mai martaba ne har yanzu zancen baije masa ba yaketa sha da gwiɓa.
Wani abu da yaso ya ja masu samun saɓani da Kilishi lkcn da aka sallami Habeebah daga asibiti fir yace bazata koma Emirates House ba gdansa zata wucce domin kuwa baiga dalilin da zaisa Khausar ta tare a cikin gidan daya gina da sunan Beebah ita kuma taci gaba da zama a inda ba don ita aka tanadeshi ba.
Kilishi taƙi yarda shikuma ya kafe itakam data gaji hakanan ranta badon yaso ba ta raka Habeeba har Prince area inda gdan nasa yake ita kanta Beebah bata amince da wannan hukuncin ba saidai batada mafita tunda Kilishi ta amince haka zata hƙr shikam ransa har kunne zuciyarsa fari tas haka suka shiga gidan yana riƙe da hannun Beebah da gabaɗaya jikinta babu ƙwari.

 

Kilishi ce tayi sallama babu kowa a parlourn farkon sai ƙamshi da yaketa fitarwa na amarci Beebah ta lumshe idanunta ta sauke kan wani babban hotonta da sukayi kwanakin baya lkcn bikin naɗin Maje Dutse, neman gurin zama takeyi ya hanata ya ja hannunta ya buɗe wata ƙofa suka shiga parlour ne madaidaici da aka kashe masa manyan kudade wajen haɗashi sai wasu ƙofofi biyu dake facing juna a cikinsa.
Kilishi ya kalla yace “ya kikaga gurin Kilishi?” Ajiyar numfashi tayi ta zauna tace “gurin yayi kyau Habibu ina Khausar ɗin?” Nandanan fara’ar kan fuskarsa ta ɗauke ya bagarar da zancen da cewa “Da alama kinajin yunwa Wyf ki kwanta naje kitchen na dafo Miki Indomie” murmushi Hajiya Kilishi tayi ta miƙe tace “sai ayita hƙr da kai zuciya nesa zaman mata biyu Habeeb sai ansa lura saboda abokan adawar junane ko dariya babu wacce keso taga kayiwa wata fiye da wacce kayi mata, to nidai ina horon ka da adalci domin shine hanyar tsiranka”
Miƙewa tayi tayi musu sallama ta fice ya rakata ya dawo har yanzu baiji motsin Khausar ba bai wani damu ba ya shige kitchen ya fara dube-dube yayi Sa’a ya tarar da shinkafa da wake ga salat da cucumber da Bama an haɗa an yanka masa kwai gefe kuma ga soyayyen nama nan ya taɓe baki yasan bai wucce baƙi zatayi ta girka musu ba ya kuwa ɗauki flat ya zubawa Beebah ya haɗa mata komi ya ɗauka ya nufi part ɗin nata tana zaune inda ya barta ya zauna yana hilatarta da hira taƙi kulawa saboda har yanzu zuciyarta bata sauka dashi ba.

 

Abincin kawai taja ta fara ci tana jin daɗinsa sosai rabonta da taci abinda yayi mata daɗi haka harta manta, aikuwa taci abincin sosai sannan ta miƙe batare data kulashi ba ta nufi ƙofa ɗaya cikin ƙofofin dake cikin parlourn, ta kuwa yi saa ta buɗe nata ta mayar ta rufe tanabin dakin da kallo tashin farko wani ɓangare da aka jera akwatuna guda goma sha takwas ta fara bi da kallo sannan ta sauke idanunta kan gadon da aka gyara shi yaji kayan ƙawa yayi kyau na sosai.
Ajiyar zuciya ta sauke lkcn da taji ya bude dakin ya shigo ya mayar ya rufe ya kamota jikinsa ya janye tare da kallonsa da kallon akwatunan lumshe idanu yayi ya sake janyota jikinsa ya haɗata da jikinsa sosai cikin sanyin murya ta bawan da yake neman tuba gurin ubangidansa yace.
“Kiyi afuwa a gareni Wyf ki daina yimin rowar kalaminki ko mara daɗi ne ki rinƙa furtamin zan jure wlh nasan kallon da kikemin ki daina zargina ba laifina bane babu yacce zanyi ne amma kinsani duniya ta sani ke nakeson……” Rufe masa baki tayi ta dago manyan idanunta zatayi mgn ya toshe mata bakin da cewa “Karki ce don Allah babu amfani mu rinƙa jayayya Beebah wasu hakan sukeson gani ki manta da komai muyi rayuwa me daɗi kinga mun samu ƴanci inason mu raini bbynmu da kulawa”

 

Ƙwacewa tayi taje ta kwanta yayima Kofar key ya rage kayan jikinsa ya haura gadon tayi saurin tashi ya cafke ta ya haɗata da ƙirjinsa ya ɗora lips ɗinsa a goshinta ta saki masa wani kuka da ya sanyashi saurin janyewa ya zubanta idanu tanata ƙoƙarin ƙwacewa sake matseta yayi yace “Ke wai ya kikeso nayi ne Wyf wannan wanne irin kishi ne daya hanaki tsayawa ki fahimceni ki bani dama mu tunkari abinda ke gabanmu?” Magana takeson yi ya hanata dama saboda ya lura sai ya saita mata tunani akansa da gaske sannan zasu daidaita idan ita taƙi fahimtarsa waye zai fahimceshi bayan ya ɓata da kowa akanta Mai Martaba har baki yayi masa lkcn da yaji lbrn Habeeba matarsa ce itace bamagujiyar daya hanasa aure, sunyi baram baram har yana iƙirarin janye masa tallafi idan bai rabu da itaba shi kuma ya amince ya ajiye masa komai daya shafeshi ya yarda ya rayu da ita, yanaji a ransa indai da ita to bashida wata damuwa.
Hajiya Kilishi ita kaɗai ta rage masa kuma ita ta haneshi yanke igiyar aurensa akan Khausar tunda ita ce ta tona masa asirinsa itace burmawa cikinsa wuƙa, duk da yasan komai daɗewa gsky zatayi halinta amma yaso ace shine ya tone komai in yaso komai za’ayi ayi lkcn ya shirya.
Haɗe bakinsu yayi suka rinƙa kokawa tana kuka tana tureshi shikuma yaƙi barinta kuma yaƙi rarrashinta Saida ya rabata da komai na jikinta yaja musu bargo babu abinda ke tashi sai shassheƙar kukanta tanayi masa magiya shikuma yaƙi sauraronta tunda ya fahimci itama bata sauraron uzurinsa Saida yayi hani’an sannan ya ɗaga yana ajiyar zuciya.

 

Taja masa tsaki tare da jan blanket ta rufe jikinta tana ƴan ƙunƙuninta shidai bai kulata yayi wanka ya shirya ya fice tare da ja mata ƙofar.
Ta daɗe tana juyi kafin ta ƙarfafa kanta ta tashi tayi wanka tayi sallar la’asar ta rinƙa jiyo hayaniya a babban parlourn itadai ranta bai bata ta fita ba tayi zamanta a parlourn ta tana kallon wani series Film da ake haskawa a MBC Bollywood wayarta tayi ruri ta janyota ganin numbersa yasata ajiyewa taci gaba da kallonta tana nan kwance taji an buɗe ƙofar an shigo ta ɗago kanta sukayi ido biyu da ƙannen mijin nata su miemie Miemie ce ta iso gareta tace “Sannu Aunty Beebah ya jikin ya fetus ɗin mu?” Tashi tayi zaune a gajiye idanunta akan Khausar da Allah ya sani Beebah ko kaɗan batason ganinta.
Ganin itama Khausar ɗin idanunta akanta yake yasata kawar da nata tare da cewa “Alhmdllh Mimi ya amarci ku baku tare bane naga kuna yawo?” Murmushi miemie tayi tace “Wlh kinsan itama Khausar rikicin aurenki yasata tarewa babu shiri kinsan ita matar cushe ba daraja ta cika ba….”

 

Jin ƙanwar mijin nata na ƙoƙarin cin mutuncinta a gaban kishiya kishiyarma Beebah yasata juyawa ta fice badon ta rasa abin faɗa ba saidon tuna kashedin da mijin nasu ya kirata yayi mata.
Cikin ranta tana raya matakin daya kamata ta ɗauka akan wannan wulaƙanci da akeyi mata akan macen da bata fita komi ba zama tayi ranta na suya ta rasa meye yasa dangin mijin nasu suka rabu biyu wasu suna ƙin Beebah wasu suna ƙinta, ajiyar zuciya tayi ta kwanta tana kwancen duk sun shigo sunyi mata sallama amma banda Miemie haka suka tafi itakam Miemie gurin Beebah aka barta sunata hirar su har dare Mijinta yazo ya ɗauketa ya kaita gda, bayan sallar Isha ne Beebah taji tanajin yunwa ta mike ta fito ta nufi kitchen ɗin dake babban parlourn ta shiga, komai akwai a cikinsa hakan ya bata damar daukar doya ta fere tayi fatenta da wake da busasshen kifi ta zubo a flat tana shirin fitowa taji an shigo ta ɗago sukayi ido huɗu ta sunkuyar da kanta ganin yanayin fuskarsa babu walwala yasa tsoro shigarta cikin in…ina tace “Sas…sannu da shigowa” ajiyar zuciya yayi ya karɓi abincin ya ɗauki juice din data dauko ya fita daga kitchen ɗin cikin tsoron yanayinsa tabisa a baya suka wucce Khausar tsaye a babban parlourn tana danne-danne da waya.

 

Babu wanda yace da ita itama babu wanda tacewa suka wucceta ta bisu da kallo tare da taɓe baki, suka shiga ciki ya mayar da ƙofar ya kulle yace “Waye yace kiyi girki?” Kujera ta zauna batare da tayi masa mgn ba ya matso gabanta yace “tambayarki nakeyi” cikin alamun ƙosawa tace “Ji nayi inason yi” yanayin data bashi amsa yasashi ajiye mata flat ɗin ya zauna kusa da ita ya ɗebo yakai mata bakinta ta karɓa ya sauke ajiyar zuciya yana bata yana kallonta tayi ƙasa da idanunta yaja numfashi tare da kiran sunanta, ta ɗago idanuwanta da suka cika da ƙwallah yasa hannu ya tallafe kuncinta yace “Idan kikaci gaba da kukan nan zaki iya sawa zuciyata ta buga Please Wyf kiji tausayina ki daina kinji?”
Ɗaga masa kai tayi alamar eh ya ɗora bakinsa a nata yace “Ina zamuje honey moon?” Kwantar da kanta tayi a ƙirjinsa a hankali damuwarta na yayewa tanajin wani farin ciki da nutsuwa na shigarta, tabbas ta amince Habeeb shine duniyarta bazata iya barinsa ba….
Tunanin ya katse mata da cewa “Idan ina tare dake dukkan wata damuwa tawa takan ɗauke na nemeta na rasa Wyf muyiwa juna halarci rayuwa mu rayu dake mu mutu tare wlh kinyimin halaccin da babu wata mace da zata sha gabanki a duniyata ke ko a lahira nasani kina saman kowacce mace cikin matana”

 

Hannu yakai ya shafa cikinta yayi murmushi yace “Zan kaiki Tsaunin gawo idan kin haifamin Bbyna nasan ganinsa zaisa su amince ba butulce musu kikayi ba ƙaddarar rabo tasa muka kasa control zuciyoyinmu har Saida muka mallaki juna Beebah inasonki”
Murmushi tayi wanda rabonta da tayisa har ta manta ta ɗago ta ɗora lips ɗin ta kan nasa tayi kissing nasa tace “Nima inasonka Hero kawai idan na tuna…..” Shiru tayi walwalarta ta ɗauke kuka na neman kwace mata yayi saurin girgiza mata kai yace “Me kike tunawa?” Da rawar murya tace “Bani kaɗai nake ikon ka ba Hero bani kaɗai ke mallakar ka ba wannan yana saremin gwiwa inajin kamar na mutu saboda baƙin ciki komai yakanyimin baƙi harda kai, Hero meye yasa dangin mahaifinka sukaƙi sona ne shima yaƙi sona? Meyesa bazasu karɓeni matsayin da mahaifiyarka ta karɓeni ba?”

 

Zubanta idanu yayi yana murmushi yace “Ke kaɗai kike mallakar Price Habeeb ɗinki Wyf Hero naki ne ke kaɗai” girgiza kai tayi alamar rashin yarda ya tsuke fuska yace “Da gaske” murmushin dole tayi masa nan sukaci abincin ya ɗauko ledar daya shigo da ita dadai ita ba ma’abociyar son tsire bace amma tunda ta samu cikin nan kullum sai taci hakan yasa baya gajiya da siyoshi aikuwa tana gani ta sauka ta ɗora kanta a cinyarsa tace.
“Idan na tuna da masoyi sai inji ƙwallah nata kwarara……
Idan na tuna da masoyi sai inji tamkar In saka ƙara…..
Idan na tuna da masoyi sai inji mutuwa bamuda tazara…….”
Nishaɗi abin ya bashi sosai ya sauko shima ya ɗauka yakai mata bakinta yace “Nayi kewa… Nayi kewa…. Nayi kewar me mini hira…..” Dariya duka abin ya basu ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tace “Kasan me?” Lumshe idanuwansa yayi yace “Me me kenan?” Dariya ta farayi tana rufe idonta ta zame ta fara ja da baya, sosai yake nishaɗi ya biye mata suka rinƙa zagaye parlourn daƙyar ya kamata ya matseta yace “saikin faɗa” ƙara tayi tace “Wayyo Boobs ɗina Hero mugunta ko ahhh wlh zan faɗa maka…”

 

 

Sakar mata nipples ɗinta yayi yace “Uhm inajinki” turo baki tayi tace “Yaune kawai na ɗan ji daɗi da kanayi kadan…..” Hannu yakai zai ƙara cafkarta ta kwasa da gudu ta shige bayan kujera yayi murmushi yace “Ina gdy da yabo yau zakiji yafi haka zo kici namanki na ka’ida kar yayi sanyi”
Zama tayi taci gaba da cin tsiren Saida ta ƙoshi ta tura masa gabansa tace “Kuma na ƙoshi gobe da safe kafin na tashi ka dumamamin shi” kama kunnensa yayi yace “Angama gimbiyata”
Da wannan suka tashi sukayi ciki tare sukayi wanka suka shirya kamar basu da wata damuwa suka kwanta sun raya daren cikin nutsuwar da cikinsu babu wanda ya taɓa samun irinta suka kwana manne da juna, ita kuwa Khausar tayi kwanan haushi, cikin kwanaki bakwai ɗin da yayi mata ko ɗaki basu taɓa haɗawa ba amma yau tanajinsa sunata nishadinsu da matar sonsa tabbas da aiki ja a gabanta.
[5/12, 8:10 PM] AM OUM HAIRAN:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button