Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 6

Sponsored Links

Page 6*

★★★~~~★★★~~~★★★

Tashi yayi daga tsugunnon da yayi yana sauke wata ajiyar zuciya me ƙarfi ya juya ya nufi hanyar da zata sadashi da masaukinsu, Saida yayi nisa sannan ya juyo yaga ta miƙe tsaye tana me binsa da kallo,
Juyowa yayi ya dawo ya tsaya a gabanta ya zubanta idanu tare da numfasawa ya kira sunanta da wata irin murya da tasa ƙirjinta bugawa da ƙarfi ta ɗago idanunta da suke tsiyayar da hawaye yasa hannu ya kama fuskarta yana goge mata idanun ya buɗe bakinsa da yayi masa nauyi yace “zaki auren…..” Janyewa tayi dukan ƙirjinta na ƙaruwa tace “Aure….” Matsowa yayi gabanta ya damƙi hannunta yace “Yeah Beebah Aure zaki aureni koda danginki duka basu amince ba koda nima nawa bazasu amince ba kiji a ranki ke matata ce soon”
Sakin hannun nata yayi ya juya da sauri yabarta da sakakkiyar gwiwa data kasa turata ta kaita ko ƙofar gdansu saima guri data samu ta zauna ta zabga uban tagumi hannu biyu tanaci gaba da sharar hawayenta.

Related Articles

 

Ji tayi an daka mata tsawa ta zabura ta miƙe da sauri jikinta ya dauki rawa ganin Baba Uda tsaye a kanta taja baya da sauri ya kuwa tusota yana surfa mata ashar yana cewa “wato ke kunnen ƙashi ke gareki bakijin mgn ko to muje gdan uban naki naji daga inda kika samu ɗaurin gindin kula wannan ɗan iskan yaron me siffar munafukai”
Da gudu ta shiga gdan kamar an jefota Jumme da Jimo dukkansu suka miƙe ganin Baba Uda yasa Jumme shigewa ɗaki yaci gaba da sababinsa yanata kundume² ashariya.

 

Cikin girmamawa Jima ya ɗago ya dubesa yace “Nifa yaya ban fahimci abinda kake nufi ba” “Eh ai dama bazaka gane ba nasani bazaka gane ba Jimo ka saki yarinyar nan sasakai abinda taga dama shine takeyi kaƙi matsa mata ta fitar da miji bare batun aure yanzu gashi garin sakacinka taje ta janyo mana abinda zai kashem” da bayannaniyar rashin fahimta Jimo yace “menene Yaya ka sanar dani” numfasawa yayi yace “wai har gida akaje akace min yarinyar nan Bibo anganta ita da ɗaya cikin bakin nan da dagaci yasa akayi shelar zuwansu ƙauyen nan haƙar ma’adanai….”
Tafa hannuwa Baba Jimo ya shigayi yana girgiza kai kawai sai yayi wuf ya cafko Habibah ya rufe ta da duka ta saki ihun daya janyo hankalin mutanen da suke wuccewa gidan ya cika da mutane daƙyar aka kwaceta hannun Baba Jimo yana haki yace “Ni zaki tozarta Habibatu kwana huɗun can nayi Miki kashedi akan wannan yaron da labari yazo min yana binki gona shine ya sake canza salon yaudararsa to na rantse da abar dogaro kasheki zanyi Habibah yankaki zanyi da wuƙa na jefaki a rijiyar jeji domin bazaki zamemin haihuwar asara ba….”

 

Kuka takeyi tana matsawa daga inda take tsaye tana shirin fita Baba Uda ya cafko ta ta rushe da kuka tace “kada ku kasheni bansan meye yasa bana iya bijire masa ba yana kalaminsa da hankali kalaminsa na nutsuwa ne komansa a nutse yake bashi da hayaniya ku fahimceshi da gaske ba irin Jami….” Zubewa tayi ƙasa hancinta da bakinta suna zubar da jini tsallaketa sukayi suka bar gurin dukkansu da bayyananniyar damuwa a fuskarsu kai tsaye gdan dagaci suka nufa idan ka gansu zaka zata korarru ne.
A ƙofar gida sukaga dagaci tare da baƙi suka tsaya a nesa dashi suna tattaunawa bayan dagaci ya gama sallamar baƙinsa ya ƙarasa garesu suka gaisa yayi musu iso zuwa fadarsa ya dubesu yace “yanayi ya nuna kuna cikin damuwa meye yake tafe daku?”
Numfasawa Uda yayi yace “damuwa babba ma kuwa ranka shi daɗe wato tun farko Saida mukace bamasan sauke baƙi a garin nan aka nuna mana bamu isa ba saboda baku abin yake shafa ba yanzu ga abinda hakan yake neman haifar wa wani a cikinsu yana neman lalata mana tarbiyyar ƴar wajen ɗan’uwana Bibo nasan dai kasan Bibo….”

 

Nan suka kwashe duk abinda aka faɗa musu ƙarya da gaskiya suka zayyane masa ya jinjina abin yayi shiru yana tunanin mafita can ya ɗago ya dubesu yace “yanzu dai zamu kira yaron gobe da safe jimo Uda kuje gda zamu nemeku”
Miƙewa sukayi sukayi bankwana suka tafi ranar kwana sukayi suna saƙa irin matakin da zasu ɗauka akan Habeeb.
Kwana tayi jikinta yana ciwo tana kuka Jumme nayi mata faɗan dalilin da yasa bataji kashedin da iyayen nata sukayi mata ba, cikin kukan tace “Nifa bani nace yazo ba kuma bani nake kulashi ba shine yake kulani sannan Jumme kece kike cemin babu kyau wulakanta mutum bare sh…..” Katseta tayi da cewa “naji banason ji nidai na faɗa Miki indai kinason naci gaba da sanya Miki albarka to ki fita daga harkar wannan ɗan birni ba sonki yakeba cutar ki zaiyi ina me tabbatar Miki duk dariyar da ɗan birni zaiyiwa na ƙauye cutarsa zaiyi saboda haka ki kula da kanki”

 

******

Washegari da safe a fada Baba Uda ya miƙe ya zabgawa Habeeb Mari Najeeb ya miƙe da sauri yayo kansa Habeeb ya riƙe shi da sauri, nunashi Baba Uda yayi yace “Ƙarya kakeyi yaro baka isaba kayi kaɗan ka koma gurin munafukan da suka turoka ka faɗa musu kaidai baka isa mu baka aure ba kai bakai ba wani ma da yafika kama da galihu muddin daga birni ya fito bai isa mu ɗauki jininmu mu bashi ba haba! haba!! Yaro aikai tawayar ma tayi maka yawa gaka musulmi kuma a zuri’ar mu kaje ka nema dai a wani gurin Habeeba tafi ƙarfinka”
Ɗagowa Habeeb yayi ya dubi Uda yace “kayi hƙr Baba bani na jarabci kaina da son Beebah ba Allah ne ya jarabceni inasonta kuma itama alama ta nuna ta karɓeni duk abinda kuke tunani bazaku sameshi daga gareni ba”
Dariya Uda yayi yace “ƙaryar banza to bazamu bayar ba son ya kasheka in yana kisa mune sai muka haifi Habeeba munce bazamu bayar ba”

 

Miƙewa sukayi suka fice daga fadar suna ƙunkuni suna Harbin iska suna zuwa gdan kuwa suka gindaya mata sharruɗa tare da sanya mata sarka a ƙafarta gabadaya sun haramta mata fita daga gda hakan bai wani dameta ba tayi jinyar jikinta kwana biyu ta warke kullum saidai su Kande suzo su bata lbrn abinda ya faru a dandali da kuma halin da Habeeb yake ciki na irin damuwar da yayi da rashinta saidai tayi murmushi kawai ta share don tasan ajalinta ne kawai zaisa tayi karambanin fita daga wannan gida.
Kullum sai Habeeb yazo ƙofar gidansu Bibo haka Baba Uda da Baba Jimo zasuyi masa korar kare gashi da baƙin naci yaƙi hƙr haka yayita zarya tsakanin masaukinsu da gdansu amma ganinta yafi ƙarfinsa saidai ya gaji da aikensa da magiyarsa ya hƙr ya koma ya zama kamar wani zautacce cikin abinda bai rufa wata guda ba ƴa macen da yake ɗauka ba’a bakin komai ba macen da abaya yake ganin bazai iya sanyata cikin rayuwarsa ba sai gashi cikin lkcn da bai shirya ba bai tsammata ba ta faɗo rayuwarsa tana sauya masa taswirar rayuwa.

 

Sosai Najeeb ya mayar dashi mahaukaci baya bawa duk wani abu daya shafi Habeeba muhimmanci ko zama sukayi suna tattaunawa abinka da abinda ya damu ruhin mutum indai Habeeb zai sako shafin Beebah cikin hirar to zata ƙare domin Najeeb zai kama faɗar maganganun da in yayi wasa ranar ko ɗaki ɗaya bazasu kwana da Habeeb ba wannan tasa suka raba tsaki da Najeeb mgn ma sai ta zama dole Habeeb ke tsayawa suyi da Najeeb haka dai lkc yayita tafiya duk wata hanya da yake ganin zata zame masa me sauƙi wajen haɗuwa da Habeeba ya rasa dole yaja ya dangana da gdan hakimi da rasa masa kuka yana roƙonsa ko nawa sukeso kome sukeso matsayin sadakin Habeeba a sanar dashi zai bayar kuma yayi alƙawarin matukar ba ita taso musulunci ba bazai rabata da addininta ba.
A zahiri Mati Dagaci yaji matukar tausayin Habeeb musamman dake yana yawan kawo masa gaisuwa yasanshi yana lura da yanda ya susuce ko aikin daya kawo shi garin ya dainayi shikenan daga ka sameshi a bakin kogi ya zubawa ruwa idanu saidai ace anganshi a jeji a zaune ko kuma yana gda yana karanta wasiƙar jaki.
Ɗagowa Mati Dagaci yayi yace “Yaro hakikanin gaskiya duk da bambanci addini naji tausayinka matuƙa domin so mugun ciwo ne da bashida magani sai saidai samun abinda zuciya ta kwaɗaitu dashi Habibu banida maganin matsalarka na rantse da Allanku da Bibo ƴata ce nice na haife ta a yau bazaka bar gurin nan ba saina bawa Limamin Hayin Fulani damar ɗaura muku aure bisa tsarin addininku amma kash banida wannan damar”
Numfasawa Dagaci Mati yayi ya sake duban Habeeb da idanunsa suka rine suka koma jajaye yace “duk da haka bazan kashe maka gwiwa ba kaje kaci gaba da addu’ar kasa malaman addininku su tayaka Habeebu inda rai da rabo”

 

Miƙewa yayi cikin mutuwar jiki yace “Shikenan Baba Dagaci na gde amma bazan iya ci gaba da zama a garin nan ba zan koma Garinmu saidai inason kafin na tafi kayimin alfarma ɗaya” da sigar tausayi Dagaci yace “Wacce iri ce Habeebu” sunkuyar da kansa yayi yace “Ka aika a kira Habeebah nasan idan Baba Jimo yaji kiran nakane zai barta ta fito inason magana da ita kalma ɗaya tak nakeson ji daga gareta wlh indai har Habeebah tace bata sona zan hƙr da ita domin nasan ƙaddarar sai soyayyarta ta wahalar dani ce tasa na zaɓi wannan garin matsayin inda zanzo idan kuwa ta amsa min tanasona to ko duk dangina da nata zasu ƙare saina mallaketa domin itaɗin mahaɗin raina ce”
Shiru Dagaci yayi yana jinjina kalaman can ya ɗago yace “shikenan Sarkin zagi tashi kaje ka sanar munason ganin Bibo yanzu a gabanmu” babu ɓata lkc sai gata tun daga nesa ya kafeta da manyan idanunsa da suka rine da damuwa itama shi take kallo ganin ya zabura ya miƙe yasata tsayawa a inda take jikinta ya ɗauki ɓari saboda tuna mugun kashedin da Baba Uda yayi mata.
Ji takeyi kamar ta juya amma batada ƙarfin gwiwar hakan domin Zuciyarta tana kwaɗayin ganin ɗan birni ko ba komai tasan zata samu sauƙin abinda take ji a ƙasan ruhinta.
Takowa yayi gabanta ya tsaya ta gyara tsayuwarta cikin dakiyar zuciya ta dubesa kafin yayi mgn ta rigashi da cewa “Dan birni meye ya sameka ka rame kamar kayi jinya?” Tana mgnr tanakai hannunta fuskarsa ta shafa ƙasumbarsa da ta kwana biyu bai gyarata ba hakan yasashi lumshe idanunsa ya kamo hannun nata yayi kissing nasa yace “Ha… Habee..bah kina iya rayuwa me daɗi batare da kinsan halin da nake ciki ba?” Da rashin fahimta ta dubesa zatayi mgn ya ɗora yatsansa a saman bakinta yace zo muje inason tambayarki ne a gaban Dagaci duk amsar da kika bani ita ce zatayi aiki wajen sama mana mafita Ni dake baki ɗaya”

 

Kama hannunta yayi suka isa gaban Dagaci suka zauna Dagaci ya dubeta yace “Habeebah kwana biyu kin ɓuya ɗan goron ma da ake siyowa a kawomin na toshi an daina kodai an daina auren dani ne?” Murmushi tayi tayi ƙasa da kanta tace “Aa su Baba ne suka tsareni suka hanani fit….” Girgiza kai yayi yace “to ai shikenan dama Habeebu ne yakeson ganinki zai koma garinsu yanaso kuyi sallama” ɗagowa tayi tace “Habeeb!”
Ɗagowa yayi tare da jinjina mata kai yace “Sunanan kenan Habeeba don Allah ki nutsu ki bani amsa ɗaya tak ita kaɗai nake buƙata daga gareki kada ki cutar da kanki ki faɗa min iyakar gskyr abinda ke ranki game dani Habeebah kinaso na?”

 

Ɗagowa tayi da sauri ta kalleshi shima itan yake kallo cikin tsoro ta kawar dakai gabanta na faduwa ta miƙe ya riƙe Rigarta ta baya yace “Wlh bazaki bar gurin nan ba saikin amsa min tambayar nan don itace hadafin mafita ta Habibah kalma ɗaya ce eh ko a’a zata cireni a zullumi sannan zata ƙarfafamin gwiwa Please ki faɗamin matsayin da kika ajeni kinasona zaki aureni ko baki sona?” Ido ta zubawa Baba Uda sake shigowa zauren majalisar dagacin shima ya kafeta da idanu yana nufosu tana ƙoƙarin ture Habeeb ta kasa saima riƙon tsauri daya ƙara yima damtsanta wata ƙara kakeji kau… Kau… Abinda yasata saurin sauke idanunta kan babanta Jimo dake tsaye da wani yaro Lanti ya zare wuƙa yayi kan Habeeb Najeeb ya taso da gudu ya nufosu ya riƙe wuƙar ta yanke shi hakan yasa ya saki ya sake nufar Bibo da Habeeb ya ɗaga wuƙar zai cakawa Habeeb Bibo tayi hanzarin tureshi wuƙar ta soke ta a gefen cikinta take ta saki wata ƙara me nuni da irin azabar da taji hakan yasa Habeeb juyowa don shi kwata² baima lura da dalilin tureshin da tayi ba.

 

Ganinta a ƙasa a zube cikin jini yasashi sakin ihu da dira kanta ya ɗagota yana jijjigata yana kiran sunanta yana cewa “Habeebah wayyoh matata don Allah kada ki mutu bamu cika burinmu ba wlh in kika mutu nima mutuwa zanyi…..” Sunkutarta Najeeb yayi suka fice da ita da mugun gudu suka nufi gdansu Dagaci yana biye dasu saboda haukan iyayen Habibah ya wucce tunaninsa baitaɓa tunanin da gaske sukeyi zasu iya kashe ƴarsu da hannunsu ba.
Tun a hanya suka rinƙa kiran James dake babban likita ne shine yake kula da lfyrsu suna zuwa ya dira akanta ya fara treatment nata sai bayan ya gama sannan su Jimo suka shigo Jumme ta shiga ɗakin da sauri ta faɗa kan Habeebah da take farfaɗo wa yanzu tana faɗin shikenan nikam rayuwata ta lalace Jimo zaka kashe mana ƴarmu ɗaya tilo akan wani bare meye yasa kukeson kubawa zuciya dama ta barku da nadama….”
Ajiyar zuciyar da Bibo ta sauke ce ta sanya Habeeb saurin tashi daga inda yake ya nufeta ta kuwa buɗe idanunta akansa ya riƙe hannunta yana jera mata sannu ta sake ƙanƙame hannunsa cikin kuka da Muryar jinya da wahala tace “Meye ribata idan banbi wanda naji a raina zan iya sadaukar da rayuwata don kare tasa ba? Habeeb bazan zauna dasu Baba Uda ba inka tafi kasheni zasuyi ka tafi dani garinku na amince zan aureka ina sonk…..” Tsalle Jimo yayi ya haye ruwan cikinta ya naushi bakinta jini yayi tsartuwa zuwa sama ……..
[4/7, 9:16 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button