Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 8

Sponsored Links

Free Page 8*

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Related Articles

Koda ya fito tsakar gdan Saida ya bawa Marka kasonta sannan ya ƙara mata wasu masu tsoka da zata kula masa da habibansa kafin ya dawo duk da ya ƙudurce a ransa bazai daɗe ba hakan bai hanashi jin kewar abar ƙaunar tasa ba,
Cikin ƙaramin lkc yayi sabo da ita sabon da yake jin zagawarta a cikin jininsa yanajin zuciyarta na bugawa daidai da bugun tasa zuciyar, yana shiga masauki jakar kayansa kawai ya ɗauka drivern campanyn simintin na mahaifinsa ya ɗauke su suka ɗauki hanyar Dutse tsakanin Tsaunin gawo da Birnin Dutse tafiya ce ta gaske kasancewar Tsaunin gawo cikin ƙasar Kano take a rankin wata babbar ƙaramar hukuma.
Sun gajiya lkcn da suka shiga Dutse dare yayi nisa wannan tasa ba kowa ne yasan da dawowarsu ba, kai tsaye sashinsa ya nufa ya watsa ruwa yayi sallar magrib da Isha ya kwanta yana hucce gajiya amma zuciyarsa taki barinsa a Jigawa ta ɗauke shi ta mayar dashi Tsaunin gawo, hakanan ya wanzu yanata murmushi yana tunano irin wani yanayi da ya tsinci kansa ɗazu da yana kissing kyakkyawan bakin Beebansa tabbas akwai nutsuwa a cikin kasancewa da abinda zuci take muradi dole yayi bakin kokarinsa yaga ya mallaki Beebah bada jimawa ba ko ya samu zuciyarsa ta samu salama.

 

Da waɗannan tunane² bacci ya ɗauke shi me sihirtaccen daɗi cike da mafarkin abar ƙaunarsa cikin kyakkyawan yanayi wanda ya sanyashi jin shauƙin kasancewarsu tare aikam yana tashi da asuba ya watsa ruwa ya sanya doguwar riga ya nufi masallacin cikin gdan sarautar sai lkcn ƴan’uwa barori da kuyangi suka fahimci ashe autan Kilishi ya dawo Auta me dakawa maza gumbar wuya a hannu.
Kaffatan duk wani ma’aikaci dake cikin wannan gda yana masifar shayinsa bawai don tsabar zalumcinsa ba a’a saidai don masifar kwarjininsa ko kusa baya ɗaukar raini da wargi tun ma yana ƙarami bare yanzu da yake jinsa sama da kowa a duniya.
Bayan idar da sallah kamar yanda al’adar gdan take Saida suka gama gaisawa da juna ƴan’uwansa sunata yi masa sannu da zuwa yanata jin daɗi duk da kacokan hankalinsa yanaga Mai martaba domin shine dalilin zamansa so yakeyi ya samu damar magana dashi a yau ɗin nan.
Shi a burinsa ma baya fatan maganar aurensa da Beebah ta wucce wata guda saboda ji yakeyi kamar zai iya zautuwa idan bai sameta ba.

 

Mai martaba yana karɓar gaisuwa fiye da rabi na hankalinsa yanakan Habeeb tabbas da yanayi ya fahimci ɗan nasa yana cikin damuwa domin ya rame sosai ga wani duhu da yayi kamar wanda ya tashi daga jinya, Saida Sarki Khalil ya sallami kowa sannan yayi gyaran murya yace “Habibullahi an dawo lfy ya aikin muna fatan komai ya tafi yanda muka tsara?”
Ƙasa yayi da kansa yace “Muna fatan hakan Allah yaja kwananka…” Shiru ce ta ɗan ratsa har yanzu mai martaba kallonsa yakeyi can ya numfasa yace “Kayi rashin lfy ne?” Da sauri ya ɗago yana duban kansa ashe dai da gaske Najeeb yakeyi ya rame ɗin shi rabonsa da duba madubi har ya manta bare yaga yanayinsa.
“Muna sauraronka Habibullah” abinda mai martaba ya faɗa kenan hakan ya bawa Habeeb damar karkacewa cike da faɗuwar gaba ya lankwashe kafa kamar me neman gafara yace “Allah ya taimakeka dama mgnr da kuka daɗe kunayi min ce ta taso game da aure….” Sai kuma yayi shiru kamar me jin tsoron furtawa, murmushi Mai martaba Khalil yayi yace “Masha Allah ai dama hakan muke fata Habibu naji daɗin wannan labari a ina take, ya sunanta kuma ƴar waye a ƙasar nan sannan meye matakin karatun ta ɓangaren Islama da boko?……”

 

Dam gabansa ya buga kwata² ya manta da dokar gidan nasu na cewa macen aure sai saukakkiya wacce ta karanta ƙur’ani kuma ta haddace koda uzufi talatin ne a kanta matakin karatun boko degree sannan ba ƴar kowanne mutum ake kawowa gdannan ba sai wanda aka san sunansa a ƙasar, itako Beebah batada komai gata ba ƴar kowa ba gata ba musulma ba bare ayi maganar karatun Kur’ani boko kuwa ba itaba duk garinsu ma baiga wanda yayi ko gaba da primary ba.
Wani gwauron numfashi ya sauke lkcn da mai martaba ya katseshi da cewa “ka samu a gaba kayi mana shiru ko abin faɗarka ya ƙare ne?” “Ba musulma bace…..” Ya faɗa cikin son arowa kansa dakiya, wannan kalma ta sanya mai martaba saurin ɗagowa yace “Wht? Ya Salam subhanallah Habeeb wannan ai zancen banza da wofi ne da bazai yiwu ba kafira kuma kakeso zaka auro mana cikin zuri’armu don taɓewa da lalacewa….”

 

Da sauri ya ɗago kalmar kafirar nan na mugun taɓa zuciyarsa miƙewa Mai martaba yayi ya saɓa babbar rigarsa ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga masallacin Habeeb yayi saurin miƙewa yasha gabansa ya zube yace “Kayimin rai ka fahimceni wlh Mai martaba inason Habeebah itama tanasona nasan zata iyayin komai donni bana ko tantama zata musulunta duk abinda ake nema zata samu nidai burina ku yarda na aurota Allah ya taimakeka ka taimaka min wajen wannan jihadin wlh saboda Ni Beebah har gdan iyayenta ta bari yanzu haka tana gdan Sarkin garinsu…..”
Ɗaukeshi da mari Mai martaba yayi ya nunashi da yatsa zaiyi mgn takaici da bakin ciki ya hanashi iya cewa komai ya fice da sauri daga masallacin ya sake binsa yana masa magiya bai saurareshi ba ya shige sashinsa ya datso ƙofarsa take Habeeb ya zube a gurin zuciyarsa na tafasa tabbas wannan shine ake cewa yaƙi saida uwa shikam baiga laifinsa ba cikin son farantawa zuciyarsa na auren Beebah ba kuma baiga dalilin da zaisashi janyewa daga ra’ayinsa a faɗin duniyar nan ba.
Da wannan ya juya ya koma ɗakinsa ya rinƙa zagayashi yana dukan iska zuciyarsa tana masa wani mugun tuƙuƙi daya kasa samawa sassauci.

 

Wanka yayi ya sanya kayansa ya nufi cikin gdan fuskar nan kamar hadari saboda damuwar dake danƙare a ƙasanta Saida ya shiga ko ina suka gaisa yanayinsa yasa babu wanda ya tankasa sunsan yanzun rai zai ɓaci, ɓangaren Kilishi ya nufa ya ƙwankwasa ƙofar tana zaune saman sallaya da ƙur’ani me tsarki a hannunta tana muraja ya shigo ya samu guri ya zauna ta dubeshi ta mayar da hankalinta ga karatun ta.
Saida ta ida inda takeson tsayawa sannan ta ɗago ta dubeshi tace “Autan maza Ina ka shiga ne tun jiya naji lbrn dawowarka sabanin ko yaushe baka zomin ba” ajiyar zuciya yayi ya ɗago idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya sauke ajiyar zuciya da tasa gaban Hajiya Kilishi faɗuwa tace “naga ta kaina Ni Ummusalma Habibu na meye ya sameka ne naganka a ɗefare a lalace kamar kayi jinya?”
Sunkuyar da kansa yayi yana wasa da yatsansa ta kafesa da idanunta tana mamakin ramar ɗan nata tace “Habibu! Ɗagowa yayi ga mamakinta sai taga hawaye sharrrr a idanunsa gabanta ya faɗi tace “Ina dalilin hawayen?” Numfasawa yayi taja fasali tace “to tashi kaje bazakazo ka tayarmin da hankali ba bayan bankai sanin damuwarka ba….” Saurin ɗagowa yayi yace “Ba haka bane Hajiya kawai dai ina tsoron kema kada kiƙi fahimtata kamar yanda mai martaba yaƙi tsayawa ya fahimceni ne!”

 

Murmushinta na Dattaku tayi tace “Habibu kenan ai indai kaga ban fahimceka ba to yanayin da kazo dashi ne baiyi daidai da a fahimceka ba maza ina sauraronka” numfashi ya sauke nan ya zayyane mata komai taja wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske tayi kasaƙe tana tunana wannan gingimemen aikin da Habib ya kinkimo duk da bataji taƙi abin a ranta ba duba da dalilin daya zayyana mata amma ta hango hargitsi na gaske a tafiyar tabbas kafin aci Zomo sai anci gudu tunda mai martaba yaki fahimtar Habeeb to batasan kuma waye zai samu nasarar fahimtar dashi ba, tunda yaki wannan lamari bataga wanda zaisa yasoshi ba saidai in Allah yayi to ikonsa sai yasa ya rusuna yabi ko bayaso.
Sosai jikin Habeeb ya ƙara sanyi lakwas yace “Hajiya kinyi shiru don Allah kice kuma kisa albarka da bakinki me albarka inada tabbacin indai kika yarda kuma kika bani goyon baya Allah zai amince kuma zamu samu lada in har Habeebah ta yarda ta karbi addinin Musulunci Hajiya ki duba ladan da zaki samu ki aminta ki cire kokwanto”

 

Taguminta ta janye ta ɗago ta zubansa idanunta tayi masa murmushi na karfafa gwiwa tace “Na baka goyon baya Habib kaje ka nemi auren Habibah ka aurota ku rayu cikin aminci amma fah ina horon ka da kabi komai a hankali Kuma kayiwa mahaifinka biyayya shine kawai zaisa nasarar ka ta ɗore”
Numfashi yaja cikin jin daɗin wannan nasara daya samu gurin mahaifiyarsa yayi mata gdy yanajin wani haske ji yake yama samu Habeebah ya gama, da wannan ya miƙe ya fice daga gdan ya nufi gdan babban yayansu da yake da yakinin idan ya samu Mai martaba da mgnr zai ɗauketa seriously ya ishe shi yana shirin fita gurin aiki suka gaisa tare da nufar office din tare suna tattaunawa akan abinda ya shafi fam ɗin nasu.
Bayan sun huta komai ya lafa ne Alh Ahmad ya dubi Habeeb yace “Kace kanada mgn dani Habeeb ina sauraronka” sosa kansa yayi sannan yayi masa bayanin komai Alh Ahmad ya ɗago yanayi masa kallon bashida hankali yace “Wannan shine tabbatar da har yanzu lissafinka ba daidai yake ba tunaninka ya goce nikam bazan iya shiga maganar nan mara yiwuwa ba mai martaba yaci mutuncina gara kai dama kaine ka siyawa kanka da kanka, Habeeb idan shawara kake nema nikam ina baka shawarar ka hƙr da wannan aure da kakeson yi kazo ka zaɓa a matan Fam ga ƴammata nan duk sun gama karatu wasu ma daga wasu ƙasashen suka dawo amma kai kasan ba’a fara ba kuma bazaa fara akanka ba Bamagujiya Habeeb haba wannan faɗuwar daraja tayi yawa da yawa to ka a musulmi Mai martaba baya aminta da ƴar talaka bare kuma ƴar maguzawa……”
Miƙewa yayi ya dauki wayoyinsa ya zuba a aljihunsa ya fice daga office ɗin da takaicin meye yasa ma zuciyarsa ta raya masa yazo gurinsa bayan ba mafita zai bashi ba? Tsaki yaja ya nufi inda yayi parking motarsa ya shiga yaja ya fice daga harabar ma’aikatar.

 

*Share please*
[4/11, 7:44 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button