Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 10

Sponsored Links

10

 

A tsaye ta sameta cikin kitchen din riqe da cup tana shan yoghourt,fuskar nan a hade,fridge din ta bude ta ciro mata kayan,saidai bata ga dambun kazar ba
“Ina dambun?” Ta tambayeta tana duban kayan
“Ban sani ba nima cikin freezer din na ajjiye”
“Wacce iriyar banzar magana kike fada,banson iskancin banza waye zai dauka?” Ta fada a dan zafafe,da alama dai akwai wata a qasa,cikin sanyin muryarta kamar yadda yake a halittarta tace
“Wallahi ban sani ba anty asma’u,dana gama na saka a ciki mummy ta aikeni gidan mummy laraba”, shigowar mummy cikin kitchen din shi ya katse muhawarar
” hayaniyar me nake ji?”ta tambayesu tana aje warmers din abincin da daddy ya gama ci
“Wannan yarinyar mummy nason ta fara rainani,sumumu kasau macijin sari ka noqe,na sata ta hadamin kaya amma tace wai bata ga dambun da nace ta yimin ba?”
“Banson tashin hankali da daren nan ki kira mana hankalin babanku,ta sake miki wani,wancan nayi baqi na basu” ta fadi tana ficewa a kitchen din,shiru tayi kafin ya kwashe kayan ta fice itama bayan ta aje mugun tsaki.

Related Articles

A qalla ta shafe kusan minti goma kafin itama ta soma takawa a hankali tana ficewa daga kitchen din,bata san me ya taba zuciyarta ba batasan tana hawaye ba saidata shafi fuskarta,tana goge hawayen tana addu’ar bacci da haka ta kwanta bayan taja bargonta zuwa kafadunta.

Ta jima a kwance tana nazarin rayuwa kafin ta tattara dukka lamuranta ta sake miqawa Allah.

Ya dan jima tsaye shida drivansa yana qarewa gidan kallo,haka kawai yaji zuciyarsa ta nutsu ta aminta da gidan,yana jin gamsuwa da nutsuwa har cikin zuciyarsa,yana son mace mai kamun kai da jan aji,yana ganin kamar akwai alamun hakan tattare da ita,yanayin arziqin gidansu yana ganin kaman bazai sanyata qyamatar mai qaramin qarfi ba,kamar zata amsheshi haka yakeji,amma hakan bazaizama dalilin da zai sanya ya kasa jarraba ta ba kamar sauran,a nutse ya yiwa drivern nasa umarnin su wuce.

????????????????

Qarfe biyu na rana suke takowa zuwa cikin layin nasu daga bakin titi zuwa gidansu ita da asma’u dake qunquni kamar zata fashe,taci alwashin bata sake hawa motar,duk da ba tsufa ne yasata yin hakan ba,uban motar da take ci ne kawai da kuma halin tsiyar qarfen nasara,inda Allah ya taqaita saida sukazo kwanar gidan nasu ta kakare musu a nan,itakam aysha na gefanta,baki daya bata ga abun bacin rai ba,don dai yau kadai.

“Malam ka cikani,Allah bazan biya ba”
“Wallahi saika biya kaji na gaya maka,ba inda zan sakeka kaje” hayaniyar mutum biyu kenan data cika kunnensu gab da zasu qarasa qofar gidansu,hayaniyar na tashi ne daga wani dan case dake maqale da gidan maqocinsu dake kallon nasu gidan,case ne da mai gadin gidan ya bude yana saida katin waya da sauran ‘yan qananun abubuwa da ba’a samu cikin unguwar sai sunje waje mai nisa saboda yanayin unguwar tasu,dukkansu hankalinsu yakai wajen,asma’u ta ganeshi tsaf,yayin da aysha taso ta shaida fuskar,da sauri asma’u ta dauke kanta,hakanan taji gabanta na faduwa,ta yaya akai yasan gidansu?,me yake a layinsu?,fatanta daya kada Allah yasa ya nuna ya santa,don ta fuskanci yana da wata zarra da rashin fargaba.

Saidai ko daya addu’arta bata ci ba,don kafin tayi qwararan taku guda goma ya samu isa gabansu,murmushi yake jifanta da shi wanda ya haddasa mata faduwar gaba,babu shakka ba qarya yana da kyau wanda ko gasa ya shiga idan baizo na daya ba zaiyi na biyu,saidai baida makamin da zai tayashi yaqin shiga inda yakeso
“Ranki ya dade….ashe nan ne gidanku?” Ya fadi yana qarewa gidan nasu kallo kamar da gaske yau dinne ya soma tozali da shi,itama gidan ta kalla kaman yau ta soma gani sannan ta maido dubanta gareshi,cikin tsiwa da tsaurin ido tace
“Nan ne,sai yaya?” Murmushi ya saki sannan yace
“Nayi farinciki sosai…..hakan ya nuna Allah yana sona” tana niyyar maida masa habu mai trader da suka tarar suna taqaddama ya qaraso yana sakw fadin
“Mallam ka sallameni ka biyani kudina zan koma bakin aikina”
“Karka damu yanzu za’a biyaka….” Sai ya dubi asma’u dake dubansu galala tana tabe baki
“Ranki ya dade taimaka ki ranta min wasu kudi mana ‘yan kadan ba masu yawa ba” kallon banza tayi masa,wani bacin rai na tokare wuyanta,yanzu ita asma’u har tayi arahar da saurayi mai cin bashi wajen masu qananun akurkin shaguna zai tsaya kafada da kafada da ita yana magana?,baqinciki yasa ta kasa magana illa dogon tsaki da taja ta wuce zuwa bakin wangalelen get din gidansu kamar zata saki kuka,koma meye motarsu ce ta jawo mata,da bai isa ya ganta ba bare ya tsaya da ita.

Binta sukayi da kallo duk su ukun har ta shige cikin gidan kafin kowanne ya maido idanunsa inda suke,idanu suka hada shida ayshan,sai kuma ta danyi turus cikin rashin sabo ganinta gaban maza har biyu abinda bata saba da shi ba,sai a sannan ta soma tuhumar kanta name ta tsaya yi a wajen,a hankali ta ciro jakar ta dake rataye a kafadarta ta bude tana fatan samun wani abu a ciki,cikin sanyin muryarta ta daga idanunta ta dubi habu mai trader
“Nawa ne kudin naka?”
“Eh…ammm….dari biyar…..dari biyar ce” dubu daya ta ciro ta miqa masa
“Gashi bani da canji….ka bashi canjin dari biyar din ya riqea hannunshi” tana gama fadi ta maida jakarta kafadarta ta nufi cikin gidan,tana ganin rashin kyautatawarta qarara,tana gani tunda har ya karya billensa ya tambaya buqata gareshi,bai kamata kana da shi ka hana wanda baida shi ba,batasan dalilinsa na tambayarta ba.

Tun kan ta isa parlour din take jiyo banbamin fadan asma’u,tsaye ta sameta gaban mommy sa’adah da alamu labari take bata da kuma nuna bacin ranta
“Sannu da gida mummy…” Aysha ta furta tana dan rusunawa cikin girmamawa
“Yauwa…..ina ke kuma kika tsaya?” Ta tambayeta tana dubanta
“Ta tsaya tana kallonmu salon ta sake samun damar rainani…..munafuka….waya sani ma ko kin sanshi….koma kece kika turoshi?” Bata ce komai ba ta juya ta nufi bangaren da dakinta yake,tana iya jiyo muryar asma’un tana ci gaba da cewa
“Banza baqauya kawai….Allah mommy cikin satin nan indai daddy bai sauya min mota ba Allah na bar zuwa school,ai ba girma na bane a ganni mota tana bani matsala…haba don Allah mommy…sau biyu fa tana min haka” kai ta kada kawai,sau tari tana mamakin halayya irin ta asma’un,itakam har yau cikin duniyar nan bata ga wani abu da zai burgeta ya shiga zuciyarta da yawa har irin haka ba,me ta nema?,meta rasa?,amma ko yaushe qari take nema,ko yaushe so take taga ta zama perfect,ko yaushe so take taga komai nata yafi na kowa,ko yaushe yadda ta tsara ma kanta haka takeso taga ya kasance,tafi dukkan sauran ‘yan uwanta mata uku buri da kai kanta can wata uwa duniya,duniyar da ma’abota buri da hangen duniya da tsaho suke yunqurin isa.

Dukka tana wannan tunanin ne tana cire kayan jikinta don wanka take da buqatar yi saboda tsananin ranar da ake kodawa,da wannan tunanin ta shiga bandaki ta sakarwa kanta ruwan shower mai sanyi ba tare data sirka da ruwan dumi ba,koda sanyi ake indai ba tsananta yayi ba tana iya wanka abinta da ruwa mai sanyi,saboda sabo da tayi da wata iriyar rayuwar da tayi can a baya.

Dari biyar din habu mai gadi ya miqa masa yana cikin rusunawa tamkar bashi ya gama cin kwalarsa dazu ba yana cewa
“Gashi yallabai….” Daga kai khalipha yayi ya dubi kudin sannan hannayensa zube cikin aljihun wandon jeans din jikinsa ‘yan gwanjo wanda ya ara wajen habun ya dora kan t.shirt dinsa da ainihin wandon jikinsa
“Bakai aikin da kyau ba habu” cikin fargabar ko kada yadda ya ringa cacimarsa ne ya bata masa rai yace
“Tuba nake yallabai….” Murmushi khalipha yayi ya amshi dubu dayan da yake miqa masa yana cewa
“Nan gaba kayi da gaske,ka daina tuna waye ni,kayi kaman ka kama mutumin da yaci bashinka shekara guda ya tsere yau ka kamashi” dariya ya bawa habun har sai daya dara,yana mamakin sauqin kai irin na khalipha,dama akwai masu kudin dake da sauqin kai haka,amma mamakinsa meye dalilin da yasa khaliphan ya maida kansa talaka a idanuwansu?.

Isowar wani matashi cikin shigar coat baqaqe dauke da briefcase wajen ya sanya habu tsagaita dariyar da yake,briefcase din mutumin ya zuge ya miqowa khalipha,dubu dayan daya karba ya jefa cikin sabbain bandiran kudin dake cikin jakar,sannan ya zaro bandir din ‘yan ashirin ashirin ya miqawa habu,cikin rawar jiki da murna yace
“Duka wannan nawa ne yallabai?” Kai ya gyada masa sannan yace
“Next term zanci bashin credit….karka manta”
“Allah ya kaimu yallabai…yaushe zakazo”
“Ba lokaci….saika ganni kawai” ya fada yana amsar wayoyinsa daga hannun matashin tare da duba miscal din daya tara zaman da yayi wajen habun,sannan ya soma takawa a hankali zuwa wajen motocinsa dake can bakin layin suna jiransu.

Mai kawai ta shafa ta zura doguwar rigar atamfa a jikinta,bacci takeji sosai saboda jiya bata samu tayi isashshen bacci ba,tayi karatu sosai hakan ya hanata bacci da wuri,kan gadonta ta koma ta janyo wayarta ta soma lalubar lambar aliya wadda bata jin dadi bata samu ta shigo ba,ringing uku aliyar ta daga tana fadin
“Yanzu nake zancanki cikin raina” murmushi ta saki mai dan sauti,tana jin dadin yadda aliyar ke nuna mata qauna
“Nima kina raina,lactures ne yau sunyi zafi da yawa aliya,kaina har ciwo ciwo yake wallahi” ta qarashe maganar da sanyin muryarta,dariya aliya tayi
“Tofa….alhuda huda yau da kanta take fadin haka?,lallai yau kun gasu” ‘yar dariya itama tayi
“Eh lallai jiki yayi kyau tunda har kike da bakin tsokanata….to Allah ya qara lafiya”
“Amin sashin(haka take kiranta wasu lokutan),naso na shigo makarantar yauma,mama ce tace na bari na qara jin dama zuwa jibi da muke da lacture”
“Allah sarki mama…ki gaidamin ita don Allah”
“Keee….wai me kike nufi?…banfa dauke miki dubiya ba” dariya ce ta qwacewa aysha ba tare data shirya ba
“To kuma me kika ji nace?”
“Baki ce ba amma i know you in and and out eesha….bakyason zuwa gidanmu bakison zuwa gidan kowa….bansan me yasa ba..ko kina tantamar qaunar da nake miki” tabbas ba qarya aliya take ba,hakanan take jin kaman bata dace data rabi kowa ba,bata kai matsayin hada alaqa da kowa ba tunda har uwarta mahaifiya ma bata da buqatarta
“Kiyi haquri sashin…gobe zan shigo in sha Allahu”zaro ido aliya tayi kaman tana gabanta cikin mamaki da doki
“What…da gaske kike?”
“Na taba miki qarya?” Ta amsa mata cikin dariya dariya
“Heee….Allah ya nuna mana gobe….breaking news yau a kunnen mama…kinga bari naje na soma shiri tun yau…sai anjima” ta fadi cikin zumudi gami da katse wayar tabar aysha da dariya,tasan dole aliya taji dadi saboda yadda take qaunar ayshan,bugu da qari tunda suke zuwanta gidansu daya sanda mamanta bata da lafiya wannan shine na biyun.

Wayarta ce ta sake ruri a karo na biyu,sake jawo wayar tayi tana tsammanin aliya ce ta sake kira,idanunta ta zaro zuciyarta na bugawa ganin sunan wadda ke yawo saman screen din wayarta,a zabure ta miqe ta zauna sosai saman gado bugun zuciyarta na qaruwa,UMMI NA sunan data yi serving number mahaifiyarta dashi shike yawo saman wayar,tunda take karo na farko da lambar wayar ummin ta soma yawo akan wayarta ba tare da ita tayi gangancin kiranta ba,cikin zumudi farinciki cakude da wani irin tsoro ta amsa kiran tana mai cike da fatan ummin tata ce da gaske.

Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke sanda tajiyo muryar Basma

“Anty indo…basma ce” ta fada cikin zumudi
“Wai…yau kin tuna ni basma” ta fada tana jin dadi cikin ranta,ko banza yarinyar na sonta cikin ‘yanuwanta
“Anty bani da waya shi yasa bana kiranki…..yanzu ma ummi na wanka na dauka bata sani ba”
“Ina ummi basma…tana tunawa da ni?…tana zancena?….” Ta fada cikin karyayyiyar murya
“Ummi bata son ana………”
“Basmah!” Aysha ta jiyo murya ummin na kiran sunan basman cikin tsawa,da alamu ma kusa da ita take
“Uban wa kike kira?”ta sake tambayar yarinyar cikin hargagi
“Kiyi haq….haquri um…mi…” Abinda aysha ta jiyo kenan wayar ta katse,sauke wayar itama tayi daga kunnenta cikin fargaba,muryar mahaifiyarta Kawai data jiyo da fadanta ya sanya jikinta yin laushi tare da tsoro tamkar tana gabanta,zuciyarta ta karye sai hawaye ya soma sintiri saman kuncinta
“Ya Allah” ta furta a sanyaye tana kwantar da kanta saman pillow,fatanta daya Allah yasa kada ta yiwa yarinyar irin mugun dukan data saba,bata taba mance yadda dukan ummin nasu yake,bata mancewa da irin fushinta,bata manta yanayin hukuncinta,gefe daya zuciyarta na saqe saqe kala kala irin wanda ta saba,tasha qaryata mutane da kanta cewa ummin mahaifiyarta ce,saidai an sha gaya mata,kowa ma hakan yake gaya mata itace mahaifiyarta sau shurin masaki,ita ta tsugunna ta haifeta,saidai garin yaya?,me yasa?me ya faru?me tayi mata?,Allah masani har yau bata samu wannan amsa tata ba,ta dade tana kuka saman gadon ita daya har baccin data kwanta dominsa yazo ya sureta

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARINH,IDAN KINA DA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*

 

*HUGUMA*

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button