Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 11

Sponsored Links

11

 

Washegari kusan wunin kitchen tayi,tana yi tana duba agogo kar lokacin da ta yiwa Aliya alqawarin zata je ya wuce,duk wani snacks da sukeyi su ajjiye cikin freezer dinsu sai data yisu dama ita keyi,tayi packaging dinsu kamar yadda ta saba sai suya a duk sanda buqatar hakan ta taso.

Tana fitowa a kitchen din anty safiyya ta shigo,inna laraba dauke da yaronta al_amin,ba laifi duk cikin yaran mummy sa’adatu ta fisu kirki,tana da dadin mu’amala da son jama’a,tana da fadin gsky saidai tana da fada idan akai ba dai dai ba,cikin fara’a aysha ta qarasa ta karbe al’amin daga hannu inna,ta dosana kan hannun daya daga cikin kujerun falon ta zauna tanawa al’amin wasa ta basu dama su gama gaisawa da mummy sa’ada dake baje a falon cikin takardu tana lissafe lissafen business dinta
“Aysha indo ‘yammata….,ba’a ganinku sai anzo gidanku ko?” Cewar anty safiyya tana duban aysha cikin murmushi,itama murmushi tayi ta soma gaidata ba tare data amsata ba,tana cikin tambayarta sauran yaranta asma’u ta sauko daga sama,tayi kwalliya sosai cikin wani irin yadi wanda cikin tsarabar daddy ce,tayi masifar kyau,don dama itadin ba baya bace wajen kwalliya
“Mara mutunci” anty safiyya ta fadi tana gasa mata harara,narke fuska asma’un tayi tana cewa
“Mummy ki mata magana Allah,kinga daga zuwanta ko?”
“Hala wancan me shegen jin kanne yazo” ta sake fadi tana jifanta da harara
“Allah mummy kiyi mata magana…..duk yadda yake ganin mutuncinki shine zaki gaya masa haka?”ta fada cikin bacin rai shimfide saman fuskarta,miqewa aysha tayi ta miqa mata al’amin daya soma neman nono ta soma barin wajen sanda anty safiyya ke cewa
” to basai ki rama masa ba….tunda na zagi qanin mummy”
“Ya isa haka safiyya…ke kullum qorafinki kan hamid ne….kinsan kuma indai ita tana wajen baida aibu” fuuuu asma’un ta wuce ranta naci gaba da baci,babban takaicinta ma yadda anty safiyyan tayi mata a gaban ayshan,yarinyar da taqi jini,ta kuma qi jinin ta rainata ko a disgata agabanta.

Bayan komawarta daki wanka ta sauya ta soma shiryawa,madaidaiciyar kwalliya tayi,tayi kyau cikin laffayar data nade jikinta marron mai adon baqi,tana cikin fesa turare aka turo qofan,asma’u ce ta dubeta
“Ki tambayi lantana kayan da na saka a hada min ki dauko ki kawo min,muna gefan garden”
“To” kawai aysha tace ba tare data dubeta ba,saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta irin hamid din yazo asma’u tace taje ta kai musu wani abu,batasan me yasa takeson mata hakan ba,ko da yake hakan baya rasa nasaba da yadda ko yaushe bata da burin daya wuce taga ta qasqantar da ayshan ta kuma nuna cewa ita ba kowa bace a wajenta,hakanan ita din ba jininta bace iqirarinta kenan koda yaushe.

Harta tura qofar dakin sai kuma ta sake dawowa tace
“Ke” tana dubanta,fararen idanunta kawai ta daga ta dubeta
“in zaki zo ki nemi hijabi ki saka,karki zomin a haka” tana gama fadi tayi gaba,hakanan taga ayshan tayi mata kyau,yadda marron din laffayar ta zauna saman fatar farar bufalatanar mace hakan ya sata qyashin ganinta a haka.

Sai data gama komai ta dauko jakarta ta fito baki daya sannan ta qarasa kitchen ta amshi kyakkyawan farantin da aka cika da kayan motsa baki ta nufi inda ta gaya matan.

Suna zaune daf da juna kan fararen kujerun da aka aje a wajen saboda zama da shan iska,isowarta wajen baisa sun gyara zamansu ba,idanun hamid jifa jifa nakan asma’un rabi na kan wayarshi,yayin da asma’un ta tattara dukka nutsuwarta da idanunta a kansa,sallama tayi ta dire sannan tace
“Ina yini” kai ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar kafin ya amsa,juyawa tayi tana qoqarin wucewa
“Sai yanzu kika ga damar kawo wa?…” Ta fadi da saigar tambaya,tsaiwa kawai tayi ba tare data amsa kota ce wani abu ba,tsaki ta saki sannan tace
“Me kika tsaya kuma yi….aisaiki wuce ko malama” nan bata tanka ta ba ta juya tabar wajen,halayen asma’un ba baqo bane wajenta,koma waye tana iya masa haka idan taso,abu daya ta sani kome mutanen gidan suke mata suna da qima a idanunta,na farko koba komai sun riqeta suna zaune da ita,ta samu ingantuwar rayuwarta wadda abaya bata zaceta ba bakuma ta tsammaci samunta ba,na biyu kuma girma da qimar daddy ya shafe komai,ya danne duk wani abu da za’a mata,karamcinsa a gunta ba abune mai yiwuwa a manta da shi ba.

Ciki ta koma kawai tayiwa mommy sallama ta amsa mata,tana shirin juyawa zata fita a falon sukayi karo da ahmad dan gidan hajiya laraba,murmushi ya sakar mata itama saita maida masa tana matsawa gefe
“Ina zuwa haka da wannan yammacin?”
“Ina yini” ta zabi gaidashi maimakon amsa mishi tambayarsa
“Mu qarasa ciki saimu gaisa ko?….ko zan bata miki lokaci?” Ba haka taso ba,amma sai ta kada kanta kawai tana juyawa zuwa cikin.

Da fara’a mommy ta tarbeshi,aysha na gefe ta gaidashi sannan ta miqe
“Shiga ciki ki samo masa wani abun” cewar mummy,duk da cewa ko cikin kitchen din akwai masu aiki dake aikin abincin dare.

Miqewa yayi ya soma yiwa mummy sallama sanda aysha ta sake ficewa da niyyar tafiya
“Saurin me kike haka ina zuwa?” Tajishi daga bayanta yana fadi,ahmad ne,murmusawa kadan tayi tana noqewa baya kadan saboda qarasowa da yayi yana niyyar jerawa da ita
“Zani dubiyar wata qawata ne” ta amsa masa
“Ohk…muje na saukeki mana” kai ta kada
“A’ah…na gode….zan qarasa na hau napep”
“Amma ina duka drivers din gidan?,bansan gidan nan ana hawa abun haya ba…”
“Wataqila basa nan”ta fada cikin zaquwar ya tsaya daga nan,don sun kusa isa wajen aje motoci,ga asma’u data hango daga nesa idanunta na kansu
“Fine….tunda wataqila basa nan muje ni na saukeki”
“Allah ka barshi”
“Bakison na samu ladar gaida mara lafiya kenan?”
“A’ah ai…..”
“Indai ba haka bane muje na kaiki” ya katseta,batasan me kuma zata sake ce masa ba,hakan ya sanya tilas ta bishi wajen motarshi.

Tana gefen sit din driver amma jinta take a matuqar takure ,jinta take kamar wadda ta aikata babban zunubi,kanta na qasa ta jiyoshi yana cewa
“Malama aysha….ya makaranta ya kuma samari?” Banbarakwai ta ji maganar,itakam tsahon rayuwarta ba zata iya tuna wani qwaqwaqwaran saurayi data taba yi ba,tun tana qauye zuwa yanzu,dama makarantar yace dai,kusan yanzu bata da wani abu da ya wuce makarantar a wajenta
“Ya kika yi shuru?” Ya sake tambayarta yana kallonta kafin ya dauke kai
“Makaranta alhmdlh” ta fada tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
“Ma sha Allah,samarin fa?” Ya fada yana murmushi
“Hmmmm” kawai tace
“Hmm…kardai kice min babu?” Ya fada cikin sigar zolaya,gaba daya a takure take,sam batason maganar,jinta take kaman ta girmi kanta,bata ma da muhalli ko gurbi sam a rayuwarta ta yanzu,buri gareta na karatu mai zurfi,wanda zai zameta qaqqarfar garkuwa da zata tare duk wani abu mai cutarwa daka iya ci gaba da kawowa rayuwarta farmaki
“Idan har da gaske ne babun?…me zai hana ni a bani dama na shiga layi kuma mutum na farko ko?”shiru tayi tana jin zuciyarta na bugawa,kaman yaya me yake nufi?
“Uhmmm aysha?,kinyi shiru?,ko na barki kiyi nazari?”
“Eh” ta fadi da sauri,saboda shi daya ne mafitar a yanzu don bata da amsar bashi
“Ayi tunani mai kyau” ya fada yana karya kwanar da zasu shiga bayan ta masa nuni da yatsa.

Qofar gidan ya tsaida motarsa tana yunqurin fita ta masa godiya
“Ki daina saurin godiya haka,saboda zan dawo daukarki” kai ta girgiza
“Na yafe wallahi…bansan ma lokacin da zan koma gida ba karna wahal da kai”
“Na gane dai bakison na dawo….fine…samin phone number dinki” ya fada yana miqa mata wayarshi,da ka ta saka masa number sannan ta miqa masa yayi serving,sai data shige cikin gidan sannan yaja motarsa yabar wajen.

Tana shiga aliya tayi tsalle ta riqeta
“Ke…waye ya kawoki?” Murmushi ta saki mai sanyi cikin siririyar muryarta tace
“Wannan itace tarbar da za’amin dama?”
“Yi haquri sashen…wallahi dadi ne ya sakani fadin haka….yau naga abinda ban taba gani ba”
“Rakani na soma gaida mama tukunna”
“Mama bata nan,amma kafin ki tafi zata dawo” ta fadi tana jan hannunta zuwa kan kujerun falon.

Sai data cikawa aysha gabanta da kayan ciye ciye kala kala harta rasa wanne zata ci?,bata barta ba sai data ci tasha sannan suka shiga hira,yawanci aliya ke baiwa ayshan labarai kala kala,ta kuma kwaso mata hotuna ta kalla har ta gaji,daga bisani ta sake tada mata zancan,bata boye mata komai ba don aliya qawa ce ta gari
“Aysha….ki bashi dama ina ganin..bakisan me Allah zaiyi ba,ki manta da da rayuwarki ta baya…ki manta dake wacece ki ki amshi sabuwar rayuwarki” zame hannunta tayi daga na aliya qwalla na cika idanunta
“Ta yaya Aliya zan manta wace ni?,kin manta har yanzu akwai tabo cikin rayuwata,Aliya….mahaifiyata…ta yaya zanyi aure?,ta yaya zan sanarwa da wanda zan aura bahagon labarin dake wanzuwa tsakanina da mahaifiyata…ta yaya zan fahimtar da shi…da wanne ido zan kalleshi na sanar masa?koda na mance komai komai ya wuce banda wannan aliya” ta qarasa tana girgiza kai qwalla na bin kuncinta,can qasan zuciyarta tana jin suya,hannu aliya ta saka tana share mata hawayen fuskarta
“Kinzo gidanmu maimakon ki samu farinciki saiki qare da kuka?,banason haka sashin” murmushi ta saki wanda qasan sa ciwo ne da radadi
“Kinsan me?…..bari na kira ummi kiji ki sake tabbatarwa da maganata na kan hanya” ta fadi tana zaro wayarta,duk da yadda zuciyarta ke bugun uku uku tana mata gargadin kiranta amma bata fasa yunqurin kiran nata ba.

Dab da zata tsinke aka daga,sallamar ummin ta bayyana cikin muryarta,shuru ayshan tayi ta kasa cewa komai har sai data ce
“Wake magana ne?”
“Nic….ce…aysha ce”
“Wace ayshan?” Ta tambaya a dan gintse saboda hasashen da zuciyarta ta mata
“Aysha indo”
“Bakiji me na gaya miki ba ko?…..ke wacce iriyar yarinya ce mara zuciya?….koda yake ba mamaki jininsu sama’ila yake yawo a jininki,gargadina dake na qarshe karki sake nemana na gaya miki” daga haka ta yanke wayar,a matuqar sanyayar jiki aysha ta sauke wayar daga kunjeta,murmushi mai ciwo na tashi saman fuskarta
“Kin ji kuma kin gani ko aliya?” Ta fada a rarrabe muryarta na rawa,saman kafadarta aliya ta dora ayshan sai kuwa ta fashe da kukan data jima tana so tayi bai fita ba,sai qunci da takurar zuci da take fama da shi,babu wanda zata zauna gabanshi tayi kuka har haka,idan ma akwai aminiyarta ce qwaya daya da tayi mata nisa tana nata muhallin a qauyensu.

Tausayin ayshan ya hana zuciyar aliya sukuni,haka ta dinga share qwalla itama,itakanta mamakin wannan lamari take wanda bama ita ba,ayshan ma baki daya batasan daga inda ya somo ba,sai data gama don kanta sannan ta goge fuskarta aliyan na lallashinta da kalamai masu dadi cike da qauna da tausayawa

A gajiye ya koma gida a ranar,hakan ya sanya hatta da abincinsa a dakinsa yaci,hakanan tsakanin amal da zeenart ba wadda ya baiwa damar ganinsa,wanka kawai yayi yayi dai dai qasan carfet yana cin abinci,qwaqwalwarsa cike take da lissafe lissafen ayyukan dake jiransa gobe da kuma cikin satin,a matuqar gajiye ya jawo briefcase dinsa don ya ciro system dinsa,sunyi da wani abokin kasuwancinsa da zasu fara harkar fita da wasu samfurin duwatsu masu daraja zuwa china zasu qarasa maganarsu a lokacin.

Har ya kammala cin abincin amma yana kan system din,sai dayaji bacci na rinjayarsa sannan ya kashe yana zuba hamma,ya bude brieafcase din ya maidata,inda ya aje kudi ya bude ya soma zarasu,don sunyi magana da haidar zai aikashi gidan kawunsu dake da buqatar kayan abinci,dubu dayan ce ta fado,cikin mamaki ya saka hannu ya dagata yana kallo,don har ga Allah ya mance da ita,a hankali ya tuno inda ya sameta,murmushi ya saki yana tuna abinda ya faru,shi kansa abun ya qayatar da shi,tamkar a majigin film,wai shine aka ci kwala ana tuhuma da cin bashin naira dari biyar
“Ya Allah” ya fada yana maida bayansa jikin kujera ya jingina,yadda komai ya faru yana dawo masa fes kamar yanzu abun ke faruwa
“Ita din wacece?” Ya tambayi kanshi,baisan ko wace ba,amma abinda tayin ya burgeshi,hakan yana nuna tana da zuciya mai kyau,ta gefe daya tsiwar asma’u da dagiyarta yana dan burgeshi,yanayin son ajinta,adonta,yana son mace mai ado bawai kwalliya ba,to ita ya fuskanci duka ta hada,a hankali bacci barawo ya saceshi a yadda yake zaunen.

Kiran sallar farko ya farka kaman yadda ya saba,sosai wuyanshi ya riqe saboda yanayin kwanciyar da yayi,da addu’a a bakinsa ya shiga bandako,wanka ya soma sannan ya daura alwala,jallabiyya ya zira bayan ya wadata jikinsa da tsadajje kuma daddadan turarensa mai sanyin kwantar da hankali,idanunsa ya lumshe yana sheqar qamshin turaren yana tuna masa da wata rayuwa can baya,rayuwar da tazo ta wuce musu tamkar a mafarki,dalili biyu yasa yake amfani da turaren lokaci lokaci,na farko yana son qamshinsa,na biyu kuma dukan daya taba ci dalilin turaren a hannun yaya ibrahim,yaya ibrahim din da a yanzu shine gatansa,rayuwa na bashi tsoro,yanayin yadda rayuwa ke garawa tana qara sashi jin tsoron Allah kadaitashi da kuma imani da shi,da ire iren wannan tunanin ya tada sallar nafila kafin zuwan lokacin asubah
.

A kullum babu wata rana da zata zo ta wuce khalipha baiyi ire iren wannan tunanin ba,wani abu ne daya shafi rayuwarsa,abu ne daya tana rayuwarsa ya kuma shiga cikin tarihinta.

Baccin da yaso komawa bayan sallar asubar bai samu ba ya hau net yana rage ayyukan dake gabanshi,qarfe takwas ya fito daga wanka,yana tsane jikinsa da towel kira ya shigo wayarsa,ya qarasa yana duba mai kiran,ramla ce,dauke kanshi yayi kamar bai ganin kiran,yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi,yasan bai wuce ta gaya masa cewa zata zo ba,abinda shi kuma baiso kenan,matsalar daya anni….baisan mai yasa ba….anni nada zuciyar mantuwa da yafiya,ta fishi sanin yaran su su waye suba wajensu suda iyayensu,amma tanayi kamar ta manta koma bata sani ba kwata kwata baki daya,suna zuwa su zauna mata suyu mata hidima,bayan yasan kowacce akwai manufarta cikin zuciya,shikam baijin zai manta ba kuma don bai yafe ba,a’ah..sam,amma iyaye daban suke,duk wani abu daya taba illata ko jirkita duniyar jin dadinsu baijin dan halak zai manta da hakan,dalili kenan daya sanya daga shi har haidar da salim ba wata qwaqwqwarar jituwa ko shaquwa a tsakaninsu da dukka yaran,baiga kuwa dalilin da zai saka ya zabesu a matsayin matan aure ba.

Kiran nata na katsewa kiran P.A dinshi ya shigo,a ladabce ya gaidashi shi kuma ya amsa a mutunce,nan yake sanar masa yau nefa tafiyar
“Wacce kenan haris?
” yallabai south africa din,na tura maka komai jiya ta email dinka da watsapp amma naga kaman baka gansu ba”kanshi ya dafe yana ambatar sunan Allah,shaf ya manta baki daya,don har yau yana da agender tare asma’u a capterian makarantarsu,amma dole ya aje komao saboda tafiyar nada muhimmanci
“Qarfe nawa ne tafiyar?”
“Jirgin qarfe daya ne sir”
“Is ok….ba damuwa” ya fadi yana katse wayar.

A nutse ya shirya cikin qananun kaya da sukai matuqar fidda sigarsa,sun masa kyau sosai,slippers ya saka ya fito izuwa sashin anninsa.

Ko ina agyare yake tsaf yana fidda qamshin turaren wuta na icce tamkar ba safiya ba,manyan abubuwa da yake jinjinawa anninsa da shi kenan,yake ganin da wuya ya samu mace wadda keda kaso daya cikin ukun halayenta,tsanani ko wuya,samu da talauci basu taba sanya annin nashi qazanta ba dai dai da qwayar zarra.

Tamkar ba safiya ba haka falon yake,kai baka ce ana zama cikinsa ba,dakinta ya wuce kai tsaye,a falonta dake manne da dakin gadonta ya sameta,wanda ita da iyalinta kawai ke zama a can,tsaf ya sameta kamar kullum,sanye da atamfar super riga da zani plain,dinkin jikinta yayi dai dai da shekarunta ya kuma yi mata kyau sosai,hannunta riqe da cup na tea na tangaran tana shan dafaffen shayin na’a na’a,yayin da daya hannun nata ke riqe da casbaha tana ja,qamshin falon nata daban da wanda ya baro,cikin fara’a ta aje kofin hannunta a gefe tana masa maraba da zuwa,cike da qauna ya isa gefanta ya zauna gabanta yana lanqwashe qafafunsa
“Barka da safiya anni….”
“Barka kadai muhammadu…..mun tashi lpy?”
“Lafiya lau,ya qarfin jiki?”
“Mun godewa Allah”
“To Allah ya qara lafiya da tsahon kwana mai amfani”
“Amin don isar annabi da alqur’ani….hala yau ba zaka fita bane”
“Zan fita anni….amma sai wajen azahar haka…inasu haidar ne?”
“Salim dai bai jima da ficewa motsa jiki ba,haidar kuwa kasan yana can yana bacci” sumarshi ya shafa sannan yace
“Mtswee….ya kamata na maidasu kamfani hakanan anni…zaman hutun ya isa haka”
“Ya kamata kam…nima ina shirin tuna maka….”.

Amal ce tayi sallama ta shigo falon cikin dinkin doguwar rigar atamfa,tayi kwalliya a fuskarta tamkar ba safiya ba,ta laqanci khalipha sosai,me yakeso meye baya so,kanta a qasa cikin nuna yanayin jin kunya ta qaraso,khalipha ta soma gaidawa wanda hakan sam bai masa ba sannan ta gaida anni,jima kadan tace
” me xaka ci ya khalipha”son samu yace babu komai,amma annin ta hanashi hakan,ko baya sha’awa tace ya karba,don kada ya sosa ran dan uwanshi musulmi yaga kaman ya gwasaleshi
“Bani tea mara madara”
“Kawai?” Ta tambaya cikin salo,kai ya kada mata,sai ta miqe ta fice

“Muhammadu ya maganar da mukayi abincin da za’a kai gidan kawunka?”kai ya kada idanunsa na kallon qasa yace
“Anni….anni keta daban ce….kin manta komai kenan?” Murmushi tayi mai dauke da ma’anoni da dama sannan tace
“Muhammadu…duk wanda Allah ya doraka a kanshi ka riga ka fishi kenan har abada baida yadda zaiyi….sannan rama alkhairi gamai cuta ba illa ne ba…..baida amfani a lokacin daka tserewa wani abu ka dinga qoqari da fadi tashin tunawa da shi,da kuma maida hannun agogo baya…rayuwa idan ta wuce ta wuce kenan har abada,ka kalli gaba…ka kumayi qoqarin gina gaban…ka manta baya…zuciya mai yafiya ita Allah yakeso yake maraba da ita,zuciya mai manta sharri,zuciyar dake manta alkhairi itace abar neman tsari,koda yaushe ka zama mai manta sharri,mai saka cuta da alkhairi ina fata ka fahimta”
“Na fahimta anni….madalla da samun uwa irinki…koda yaushe ina godewa Allah daya bamu ke a matsayin uwa….dai dai da rana daya baki taba umartarmu da yin wani abu ba dai dai ba komai tsanani komai wuya”ya fadi yana gyada kai
“Burin uwa ta gari muhammadu ko yaushe ta dora diyanta kan tafarkin tsira duniya da lahira”
“Haka ne….yau za’a kai in sha Allahu,zan baiwa haidar ya kai masa”
“Allah ya albarkaceka kai da ‘yan uwanka duniya da lahira….ya jiqan mahaifinku”
“Amin summa amin anni”,ya jima suna hira shida ita har haidar da salim suka shigo suka samesu a haka,baibar wajenta ba sai da sha daya na safiya tayi,yana matuqar jin dadin zama da mahaifiyar tasa,macace mai hikima dattako da sanin ya kamata,idan ka zauna da ita ko yaya saika amfana ko ka qaru da wani abu mai muhimmanci da baka sanshi ba.

A dan gurguje ya shirya cikin shigar suits,wanda kallo daya ya isar sanar maka da awanne aji take,yana cikin gyara tie din wuyanshi gaban madubi idanunsa suka sauka kan vivo dinshi dake aje gefan madubi,murmushi ya subuce masa sanda ya tuna agender dinsu da haduwarsu ta qarshe da asma’u,dariyar data dinga masa shida wayar tana masa kallon wani shashasha gaula,tuni ya gama gane inda ta dosa,saidai game din da suke bugawa shida ita hakanan ke burgeshi tare da bashi qawa,yakan raya a ransa tunda har take tsaiwa suyi magana koda ba mai dadi bace watan wata rana zata saurareshi,zata fuskance shi,za kuma ta zama tashi,hakanan yayi sha’awar kiranta,sai ya kunna wayar yana ci gaba da shiryawa tare da jiran ta kawo.

Yana takawa harabar gidan wayar na ringing alamun tana shiga bayan yayi sallama da anni,yaranshi suka bude qofar motocin suna jiran qarasowarshi,ganin haka ya dakata daga dan nesa kadan,ta daga wayar saidai bata amsa ba,hakan ke alamta ta gane cewa shine
“Assalamu alaikum ranki ya dade”
“Ya akayi yaron oga?” Ta fada cikin isgili tana dariya dariya,baki daya ta daukeshi kaman wani abun wasa a gareta,don tasan cewa babu hadin kifi da kaska,babu abinda ya hada kashi da fura,sam tafiyarsu ba daya bace,hanyar jirgi, mota bata isa tabi ba,murmushi ya saki,kafin yace komai tace
“Naga alama kai kam da gaske kake…..tunda har haka ne….kazo ka sameni ina son ganinka” sosai maganar ta bashi mamaki,saidai baiji komai ba,cikin salo yace da ita
“To babu damuwa,saidai yanzu haka oga ya aikeni ne,ya turani wani waje,aqalla zanyi sati biyu haka,idan na dawo zan iya zuwa?”
“Baka da case” tace da shi tana katse wayar,kashe wayar yayi baki daya yana dan nazari,murmushi yake kadan kadan,daya daga cikin yaranshi nazir ya qaraso ya amsa ya mata waje.

Murmushi take bayan ta kashe wayar,babbar aminiyarta husna ta dubeta tana mata wani irin kallo
“Asma me kike nufi ne wai?,mutuncinki kikeson zubarwa kome?,mace irinki maisu hamid su hisham me zaki da wanda ke qarqashin gashin wani….haba asma” dariya ta saki tana duban husna
“Husna…husna…shi yasa nake sonki…tunaninmu daya,ra’ayunmu daya,saidai a wannan karon abinda na hasaso daban da naki,kinsan meke faruwa ne?” Ta fada tana gyara zamanta tare da fuskantar husna sosai
“Saikin fada” ta ambata tana duban asma’un sheqeqe
“Wannam guy din ya hadu tako ina….Allah ya masa baiwar kyau da qira….abu guda ya nakasheshi….bai mallaki hatimin da zai sanyashi mallakar zuciyata ba….amma kowanne mutum da ranarsa…..muhammad namiji ne da zaki shiga da shi kowanne waje da maza masu aji da jin su wasu ne ki kuma kankarowa kanki qima da mutunci….abu daya ne kawai,ki sama masa suttura ki bashi abun hawa duk sanda zai rakaki wani waje….” Kai husna take kadawa
“Maganarki haka take….amma asma’u,gani daya nayi masa naga kaman bazai biyu miki yadda kikeso,a ido kawai tsayayyen namiji ne,yana da wani irin kwarjini da cika ido,anya asma?” Dariya ta saki tana kada key din motarta dake hannunta
“Husnaaaa….kudi sune qarshen zance kin manta?” Murmushi ta saka tana gyada kai tare da gamsuwa da bayanan asma’u,ita kanta ya burgeta qwarai,saidai ba ajinsu bane shi saboda bai mallaki abinda za’a nuna shi ba.

????????????????

Cikin sati biyun ya nemi duk wata hanya da zai dinga tuna mata da shi,batasan ya akai ba,batasan yadda ya samu number dinta ba,sai kiranshi da take samu babu qaqqautawa,bata iya wulaqanta mutum ba kaf rayuwarta,don itama bata saka kanta a lissafin mutane masu daraja ba,bugu da qari alfarma ya nema a wajenta,hakan ya sanya bata qin daga wayarshi koda na zata ce komai ba,ba zata iya cewa komai game da shi ba,don a yanzun zuciyarta tana jin kamar bata mutum ba,batajin zata karbi wani abu da ake kira soyayya,soyayyar da taje jin bata a duniyarmu,bata jin gaske ce,don bata taba dandanata ba bare ta adar da komai a cikinta.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: ???? *DAURIN BOYE*????

*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

HASKE WRITERS ASSO

(Home of expert and perfect writers)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button