Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 12

Sponsored Links

12

 

Qarfe daya da rabi na rana suka fito daga babban meeting na duka ma’aikatan kamfanin nasa,kai tsaye shida motocinsa suka wuce katafaren gidan abinci na purple palace da yake cin abinci don suci abincin rana,tafiyar minti sha biyar ce tsakanin kamfanin nasu da wajen suka isa sukai parking,tuni nazir ya bude mishi qofa,yana shirin fitowa vivo dinsa dake can gefan set din da yake zaune ta hau qara,shaf ya mance da ita,ya waiwayo yana dubanta,yasan mutum daya ne zaya kira asma’u,ita dince,wayar ya daga ya kara a kunnensa
“Kana ta wajen ina?”ta fada kai tsaye ba tare data damu da yin sallama ba
“Ina wajen aiki”
“Ohk….kazo purple palace restaurant ka sameni” ta fadi kanta tsaye kaman wani yaronta sannan ta kashe wayar,wayar ya sauke daga kunnensa,daya daga cikin yaranshi ya kira da hannu,qarasowa yayi cikin girmamawa ya masa nuni daya matso,cikin kunne ya masa magana ta mintina,kai ya gyada ya wuce zuwa cikin wajen cin abinci,minti biyu ya dawo ya sanar masa da abinda ya aikashi yi,kai ya gyada,sake kiran daya daga cikin yaran nasa yayi ya sukai magana,cikin mintuna sai gashi ya dawo riqe da baqar leda ya bashi,ya amsa,sannan a nutse ya soma cire suits dinshi na saman guda biyu ya bar ta ciki,takalmin qafarshi ya sauya zuwa mai sauqin kudi bayan ya kira daya daga cikin yaran shi ya dauko masa cikin boot din daya daga cikin motocin nasu,eye glasses dinsa ya cire ya kashe wayoyinsa ya ajjiye ya dauki vivo din ya riqe a hannunsa hadi da cire agogon hannunsa shima ya aje sannan ya fito daga motar,da kallo suka bishi,suna yunqurin binsa ya tsaidasu
“Ku janye motocin nesa kadan da nan wajen,karku biyoni ina dawowa”
“Yes sir” dukkansu suka ce,a nutse suka janye motocin suka musu muhalli a wajen da zasu iya ganoshi.

Related Articles

Ita daya ce zaune kan teburin cin abincin tana danne dannen waya, tasha ado cikin gown ruwan bula,ta yane kanta da mayafi ruwan powder mai turuwa,fuskarta sanye da sun glasses daya kusa mamaye fuskarta,da sallama ya qarasa wajen,hannunsa guda zube a aljihunsa,dayan riqe da baqar ledar,kai ta daga tana amsa sallama,ya mata kyau a idanunta sosai,saidai har yanzu bata gaza ganin aibunsa ba
“Kin yini lafiya ranki ya dade”
“Lafiya lau….zauna magana zamuyi” ba musu yaja kujerar da hannu daya sannan ya zauna,ya hade yatsunsa waje daya ya zuba mata idanunsa bayan ya aje ledar a tsakaninsu,kafin wani a cikinsu yace komai daya daga cikin waitress din wajen ta qaraso riqe da purple din leda mai tambarin gidan cin abincin ta miqawa asma’u ta amsa
“Kana kusa kenan dama?”
“Eh….naje wani aike ne na oga nan kusa”
“Yayi yaron oga….”
“Ga wannan,naga ni a hanya ne na miki tsaraba” ya fada yana miqa mata ledar,janta tayi gabanta sannan ta bude,abinda ta gani ciki ya bata takaici fuska a yamutse ta dubeshi
“Meye wannan?”
“D’ata,yalo,guava”takaicin daya qumeta shi ya hanata magana
“dauki muje” ta fadi tana nuna masa ledar da ma’aikaciyar wajen ta kawo tana miqewa bayan ta masa nuni da ledar da aka kawo mata,dariya ce taso subuce masa,sai kawai ya dauki ledar ya bita.

Nasiru shi ya soma tahowa da sauri da niyyar amsar ledar hannusa bayan ya hango fitowarsu,cikin zafin nama ya sanya hannunshi ta baya ya dakatar da shi,hakan ya sanya suka tsaya cak suna kallonsu har suka isa motar asma’un,ta masa izinin ya shiga itama ta shiga sannan ta tada motar.

Shiru ne ya ratsa motar jin hakan ya sanyashi cewa
“Ina zamuje ne?,kar oga ya nemi ni fa”
“Karka sake kawo min irin wancan tarkacen…ko na maka kama da maicin irinsu?” Dasauri ya sauya yanayin fuskarsa ganin ta waiwayo inda yake zaune,ya ragewa fuskar tasa kwarjini da tsare gidan da yayi
“Kayan marmari ne fa”
“Irin naku na talakawa?” Ta fada kai tsaye,cik yaji kalmar ta caki zuciyarsa,an taba gaya masa makamanciyarta cikin wani yanayi can baya daya kasa barin ransa,shiru yayi ya lula wata tsohuwar duniya,hakan ya wanzar da shiru a tsakaninsu har suka iso inda suka niyyaci zuwa.

Qaton botique ne wanda da alamu ke nuna na manyan yara ne,kai tsaye wajen suturun maza ta nufa tana dubawa yana biye da ita,bata masa magana ba,ita da kanta ta dinga zabar t.shirt zuwa trousers masu matsakaitan kudi tana miqa masa hadi da cewa ya duba ya gani,dariya ya dinga yi shi kadai yana biye da ita,duk abinda ta miqo cewa kawai yake yayi,yana yi yana duba price din kowanne riga da wando,a qalla ya manta yaushe rabon daya saka kaya masu wannan farashin,shi yake zabar kayan da yake so da kanshi,saidai ba cikin ire iren wadan nan qananun batique din ba.

Kaya ne kala biyar takalmi qafa biyu,kai tsaye wajen biya suka nufa aka mata total ta cire ta biya,jimillar dubu ashirin,yana biye da ita da kayan har zuwa cikin mota,dubanshi tayi kafin tace
“Ka fara amfani da wadan nan,ranar juma’a ka zabi daya daga ciki ka sanya,zaka rakani wata dinner”
“Ayyah…kinsan oga baya barina inje nan da can,sannan ni kaina bana yawon dare” wani kallo tayi masa
“Ka hadu ta halittar da Allah ya maka,saidai ka kwafsa tako ina,yaushe zan iya zaman aure da kai tabdi” ta fada cikin zuciyarta,amma a fili sai tace
“Kaman kai kace baka son yawon dare…sometimes idan kana wani abun kaman baki karatu ba” ta fadi cikin mamaki,murmushi kawai yayi yana dauke kansa,itama bata sake magana ba ta tada motar tana wani tsare gida suka tafi,saidai tana wassafa yadda zata dinga shiga da shi ne manyan gurare,cikin abokai da sauran ‘yan uwa ko don ta kankarowa kanta mutunci wajen abokan takun saqa

????????????????

Har qarfe shida na safe tana saman abun sallah bata koma baccinta ba,saboda breakfsat da zata shirya na asma’u.

Shida da minti goma ta nufi kitchen din,saidai yau sabanin ko yaushe tun kafin ta qarasa ta jiyo kwarafniya a kitchen din

Lauratu ta taras mai aikin mummy,a mutunce suka gaisa,akwai zaman mutunci da girmama juna tsakaninta da duka yan aikin gidan sabanin asma’u
“Yau kinyi sammako lauratu”
“Wallahi,alhaji ne yace amin magana,mu sama masa tuwon acca da safen shi zaici” murmushi aysha tayi,tasan daddy yana sane baisa an gaya mata ba,tasan yayi hakanne don kawai ta huta
“Idan kin gama hada komai ki barmin zan dafa” aysha tace da lauratu
“Kai…aikin bazai miki yawa ba….bakya gajiya da girki?”
“Girkin daddy ne fa lauratu ko kin manta”
“Af….anyi haka fa,na manta ba’a shiga tsakaninku” dariya sukai baki daya kowa ya kama nashi aikin.

Na asma’u ta fara kaiwa dining saboda taji yau zata fita makaranta da wuri,tun sanda asma’u ta soma cin abincin asma’u taqi abincin duka masu aikin gidan,sautari ayshan itake girkin ta dama na gidan wasu lokutan,bata taba gajiya ko nuna damuwarta ba

Zuwa goma ta gama na daddy shima,ta shirya komai tsaf ta diba zuwa saman dining ta shirya a can,tana niyyar barin wajen taji shigowarsa

A ladabce ta qarasa ta gaidashi ya amsa mata sannan ta gaida mummy sa’adah da suka fito tare
“Ke suka barwa girkin indo?” Cewar daddy yana murmushi,murmushin itama kawai tayi
“Sannu indo bakya gajiya,Allah yayi albarka kinji”
“Amin daddy” ta fada cikin jin dadi,don har ga Allah tana jin dadi idan ya sanya mata albarka,tana jin albarkarsa tamkar ta mahaifinta da ba zata iya tuna yaushe da yaushe ya saka mata ita ba.

Tana tsaka da shiryawa bayan tayi wanka wayarta ta dauki ringing,a nutse ta duba sai taga ahmad ne,ta danji dadi kadan tunda ko babu komai zai debe mata kewa,wata rayuwa ta taso ta kadaici tun da can zuwa yanzu,duk da cewa gidansu na can cike yake da jama’a amma ita kusan ita daya take rayuwarta,ba qawa ba aboki ba masoyi,sai daga baya qawa qwaya tak ta shigo rayuwarta.

tunda tayi sallama hirar tata ta koma eh da A’ah,kusan ahmad ya saba da wannan halayya tata har baya damuwa,yakan ce bai taba ganin mace mara magana ba irinta,itakam saidai tayi murmushi,sun jima suna hira saidai magana ta qarshe daya gaya mata ta sanyata cikin matsananciyar faduwar gaba da fargaba har ta kasa amsa masa
“Aysha ina son a tambaya min daddy izinin zuwa wajenki,inaso na kafa gwamnatina sosai,na gaji da bulayi ta layin waya”.

Sosai take jin tsoro da fargaba suna shigarta,kaman tayi tsaurin ido ko?,haka take ji zuciyarta na gaya mata,saidai wace hujja ta riqa da zata dakatar da ahmad din?,kan wannan batun sukayi sallama da ita,bai damu da jin cikakkiyar amsa daga bakinta ba,tunda ya sani magana wuya take mata.

*_BAYAN SATI DAYA_*

Xaune take dai dai cikin dakin nata gabanta cike da tarin litattafai,karatu take tuquru saboda jarabawa dake doso su.

Kiran mummy sa’adah ne ya shigo wayarta,a mamakance take kallon wayar don iya saninta indai tana cikin gidan masu aikin gidan take aikowa suyi kiranta,don ita ba ma’abociyar zaman falon gidan bace,zaiyi wuya ka sameta a falon indai ba wani abun zata yiwa mummyn daddy ko asma’u ba.

” kizo falon daddy yana nemanki”
“Toh” ta amsa,ta aje wayar cikin sanyin jiki,don tunda take zata iya irga shigarta falon daddyn,hijab ta lalubo cikin kayanta ta zura ta fice.

Yana zaune yana kallon labarai tare da shan coffe,yayin da mummy ke hakimce zaune a gafensa tana amsa wayar halimatu babbar diyarta,shi kadai ya amsa sallamar ta samu guri gefe daya ta zauna har mummy ta gama amsa waya.

“Aysha…na kira ki ne kan maganar ahmad yaron wajen hajiya laraba……sunxo sun sameni kan na bashi daman zuwa wajenki,yaya kike gani?” Ya qarashe maganar yana duban asma’u dake shigowa falon”shiru tayi kanta a qasa,rashin sabo kunya gami da tsoro suka baibayeta,shiru ya ratsa falon,yayin da agefe guda takaici ya kama asma’un,har yaushe ahmad ya soma son aysha?,yarinyar na nufin zata auri wani mai abun hannu kenan kamar ita?,sam ba zata taba bari hakan ta faru ba,sam ayshan bata cancanci shiga familyn alhj uba ba,don ta sani cewa ko su ba zasu nuna musu arziqi ba,ganin har lokacin bata ce komai ba ya sanya daddy yace
“Naga alamun kamar ba zaki sake kiyi magana sosai ba,bayan ke da asma’u duk daya kuke a wajena….shikenan kije ki duba ki gani?,idan har kin aminta da shi saiki sanarmin,ko ki sanarwa mummynku idan ma kina jin kunya saita sanarmin sarkin kunya,tashi kije koda wani abun?” kanta a qasa cikin kunyar tata ta kada kai alamun a’ah sannan ta miqe ta fice tana cewa sai da safe,duban asma’u daddy yayi
“Auta…ya akayi?” Cikin shagwaba kamar wata qaramar yarinya tace
“Daddy motata….daddy wahalar dani kawai takeyi,daddy ina buqatar canji”
“Motarki ko motarku keda aisha” mummy tayi saurin cewa don kada asma’un ta kwaba musu,itakam har ga Allah ma ta manta wai da wata aysha aka basu motar
“Yanzun ya kikeso ayi” ta samu abinda takeso,hakan ya sanya ta sake shagwabewa
“Daddy…canzata mukeso ayi mana”
“Amma baki fadi haka ayshan na nan muji nata ra’ayin ba” ranta ya baci a take,gani take kamar a yanzu aysha tafi matsayi a wajen daddyn fiye da ita,komai zaiyi tsakaninshi da ita sai ya sako ayshan,ko misali zai mata da wuya ya tsallake kan ayshan
“Banda abin daddy….ai kasan kunya gareta,ko tana nan dinma babu abinda zata ce”
“To mummyn yara” ya fada yana murmushi,shiru yayi na dan sakanni sannan yace
“Shikenan….yanzu kinsan abinda za’ayi?” Kai ta kada cikin zumudi
“Akwai wani abu da nake jira nan da qarshen watan nan,idan har komai yamin yadda nakeso,na muku alqawarin motoci ke da ayshan kowa tashi daban…kinga sai ku daina sharing haka nan” sosai albishir din ya faranta ranta,saidai ra gefe guda kuma baqin ciki nason hana murnar tata tasiri jin cewa wai ita da aysha za’a siyawa motar,bayan ita tazo ta roqi alfarmar
“Qwace goruba a hannun kuturu bazaiyi wuya ba” ta raya hakan a ranta,hakan data tuna ya sanyata warewa sosai ta yiwa daddy godiya cikin farinciki,sannan tayi musu sallama ta fice.

Saidai bata wuce dakinta ba,dakin mummyn ta koma ta zauna bakin gado tana jiranta bayan ta kunna t.v plasma tana kallo cikin tashar zee world,tasan lallai mummyn zata dawo ta shirya kafin ta koma dakin daddyn,awa guda cur kuwa saiga mummyn ta shigo,duban asma’un tayi cikin tana ciro kayan bacci
“Ya akai?,me kike har yanzu a nan baki kwanta ba?”
“Mummy….magana nakeso muyi”
“Uhmmm…ina jinki”
“Mummy….ya za’ayi ahmad din mummy laraba ya rasa yarinyar da zaice yana so da aure sai aysha?,haba mummy,wannan ai abun ayi daku ne cikin da’irar qawayenku,kuma wallahi wasu ma sai sun zageki suga kaman kin cutata masa saboda ba yaronki bane zako hadashi da wancan yarinyar da duniya bako daya ta juya mata baya ta rasa mai tallafarta sai mu”
“Na rigaki wannan hasashen,na kuma yi maganin matsalar….lokaci kawai nake jira,don duk wanda keda jibi da ni bazan taba bari ya aureta ba,bazan ce kada tayi aure ba,amma taje can ta samu dai da ita,dai dai ruwa dai dai qurji,amma familyn alhj baba ai ya tsere ma sa’anta”
“Yauwa mummy….ashe kema kin fahimci hakan…ammm sannan mummy….zancan siya mana mota tare” sai ta marairaice murya
“Mummy wallahi daddy yana saidamin mutunci ko cikin qawayenki mummy….ya za’ayi a dinga mana abu iri daya nida ‘yar ruqo fisabilillahi mummy,ina laifin ya hada kudin motocin biyu ya siya min qwaya daya 2019?”
“Kina westing time dinki ne kan wannan maganar,kin riga da kin sani tunda har yayi niyyar saiya babu wata hujja da zata dakatar da shi,wancan issue din zan iya kuma zan maganinsa cikin ruwan sanyi wannan kam saidai kiyi haquri” kamar zata saki kuka tace
“Please mummy mana…ni kadaice fa kuma haka ya kamata naci gaba da kasancewa,mummy bai kamata na dinga abu iri daya da yarinyar riqon gidanmu ba,duk halaccin da muka yi mata kuma saita dinga shiga rayuwata haba mummy ki duba ki gani mana?”
“Alright,zanyi wani abu a kai,amma banso ki nuna masa komai koda ya riga daya siyo motocin”
“Thats my mom,shi yasa ko yaushe nake cewa nafi kowa sa’ar mummy a duniya”
“Uhummm,da yake nayi accepting duk abinda kike so ko?”
“Noooo mummy…duk abinda nazo da shi ai dai dai na fadi,kuma ci gaban ‘yar autarki ne ko?” Ta fada tana rungume mummyn ta bayanta
“Naji ni barni na shirya wuce kije ki kwanta”
“Ok mummy,gud nyt”
“Allah ya bamu alkhairi”.

Tana ratsa falon tana murmushi,duk plan dinta ya tafi yadda ta tsara yadda takeso,a rayuwa tana haushin aysha,ji take ayshan ta kai mata ko ina ta tsare mata wani abu,duk da azahiri babu wani abu da ayshan ta tsare mata,kyau irin na ayshan da sanyin hali nagarta da haquri sune abubuwan da suka tsonewa asma’un ido ba tare data san da hakan ba,a karan kanta tana ganin ayshan bata mallaki komai ba bare tayi hassada da ita,ita din ita keda komai,ita ta mallaki komai.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WITSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA MAI BUQATAR WADAN NAN LITATTAFAI SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
(08030811300)

*DB*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button