Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 19

Sponsored Links

19

 

 

Cikin sati hudu mummy ta soma shirye shiryen bikin ‘yarta don bana ce shirin bikinsu ba,ta bangaren aysha sam babu abinda ya dameta,kallon komai ma take a matsayin almara,har sannan gani take koda yaushe ma muhammad kamar yadda tafi kiransa,duk da cewa cikin ranta ne bata taba kiransa a sarari ba zai janye shima,bata taba duba da wai cewa baida komai ba,ko bai taba bata wani abu ba,hatta da katin waya bai taba tura mata ba ko na naira biyar,hakanan duk sanda zaizo kayan gwanjo yake sakawa a wanke a goge a kawo masa ya saka,ko ya sayi shadda ready made mai sauqin kudi,wataran yasa a taho masa da babur ya amsa daga can qasan layinsu ya qaraso da shi,wataran kuma ya sauka daga bayan layin ya tako da qafafunshi ya qaraso,vivo qarama itace wayarshi,kama daga hula da takalmi dukka kudinsu bai taka kara ya karya ba,ko sau daya hakan bai taba damunta ba ko a fuska,bata ma daga kai ta kalla bare har ta tantance,wataran yakan jima yana satar kallon fuskarta ko zai fuskanci wani sauyi tattare da ita,saidai sam ko alama bai taba ganin wani abu ba daya danganci hakan.

Daddy da kanshi ya zauna da mummy,tayi masa lissafin duk abinda ake buqata na asma’u,daya tashi gaba daya ya hada ya bata dana aysha dai dai dana asma’un,abun ya qona ranta sosai,wannan karon tamkar zatayi magana,da qyar ta samu ta danne ta karbi komai daga hannunshi ba qorafi ko nuna ba’ayi dai dai ba.

A sannan asma’un na zaune cikin kitchen tana charting,aysha na tsaye bakin gas tana soya mata wainar fulawa,idan ta cire saita saka mata a plate ta miqa mata
“Mummy..kin fito?” Asma’u ta fada tana cire earpiece din dake kunnenta,wanda ba komai take ji ba sai waqe waqen ‘yan kudu
“Na fito” ta amsa mata tana jingina da jikin qofar kitchen din
“Ya kukayi mummy…Allah yasa duk komai yadda na tsara hakan ya bada” ta sake fada tana sauke qafafunta qasa wanda daa suke nade a saman kujerar plastic din da take kai
“Eh haka ya baku” idanu ta zaro tana duban momyn
“Momy?….ya bamu ni da wa?”
“Dawa kikasan yana bakun?”
“Haba momy haba,why…why?…komai sai an hadani da wani,wannan abun fa gaskiya ni ya isheni mommy…kenan har dubai din tare zamu wani kwashi jiki muje?,salona rainani,wannan idan akaji labari ai ajina ya gama zubewa,ince mun tafi tare dawa dina?….wallahi mommy ban yarda ba,tsakani da Allah fa ni ba’a yiwa rayuwata adalci” ta fada cikin fushi tana cika kamar zata fashe,aysha na jinsu,tana kuma sane da cewar da ita ake,saidai ko daya ita ba wannan ne ma a gabanta ba,result dinsu data samu labarin ya fito takeso taje ta duba taga me ta samu
“Ke aysha….zamuje dubai siyayyar kayan aurenku….inaga don ayi serving kudin jirgi dana hotel da kuma abinci da zamu dinga ci kiyi zamanki kawai ki bada list na abinda kike so” mummyn ta fada bayan tana sane da daddyn ya bada kudin duk wani abu da zasu buqata,sai a sannan ta waiwayo ta dubesu
“Ba komai mummy….duk abinda kika siyo yayi” dan jim sukayi baki dayansu,don basu tsammaci sam zata ce hakan ba,duk da sunsan halinta indai aysha ce ba abinda yake damunta,duk yadda aka kai ga cusguna mata tana iya shanyewa saman fuskarta,koda bai mata dadi ba cikin zuciya,wani lokaci sukanyi mamakin hakan,su dauka ko zuciya ce bata da ita ko kuma mene
“Au haushi kika ji?” Inji mummyn ta fada tana son tabbatar da ainihin yanayin aysha,da sauri ta waiwayo fuskarta qunshe da murmushi
“Haba mummy….nima fa tamkar asma’u ce a wajenki,na daukeki kamar mahaifiya ce ke a waje na,ta yaya kuwa uwa zata cutar da diyarta,kawai gani nayi ko banje ba indai ke ko anty asma’u kunje duka daya ne kamar ina wajen ne,sannan gidan ma bai dace mu barshi babu kowa a ciki ba” baki asma’u ta tabe tana jin haushi,yadda duk takai ga son cusguna mata taga bacin ranta hakan yaci tura,bata bari wani abu ya qona mata rai komai girmansa,koda ya qona matan zata iya cewa basu taba gani su a nasu idanun ba
“Shikenan….hakan yayi” cewar mummyn ta juya ta fice,sai asma’un ta miqe tabi bayanta,bata bar wajen ba bata kuma je ko ina ba,ci gaba tayi da soya mata wainar tana ajewa cikin warmer cikin hanzari saboda makaranta da takeson ta shiga.

A bakin matattakala asma’u ta cimma mummy
“Mummy….kawai ni inaga ba sai an wani auno mata kaya daga wani waje ba…..kiyi waya kawai zoo road inda anty halima ta siyawa ‘yar aikinta kayan gado lokacin aurenta,ai suma sun iya su kawo kawai set biyu a zaba,bata kudine kawai da asarar kudi a siya mata kaya masu tsada,tunda ko da can ba saninsu tayi ba bare tasan darajarsu,sannan shi kansa mijin ma bashi da qarfin da zaiyi ginin da zai dauki kayan,kinga anyi asara kenan” ta fada tana duban mummyn
“Haka nake tunani nima….kuma akwai siyayyar da nakeso nayi nima,kudina bazai kai ba,to cikin kudin nata nakeso na cika” murmushi asma’u ta saki
“Yauwa mummy yaushe zamu tafi….inason na yiwa hamid magana zan karbi wasu kudade a hannunsa”tunani tayi kadan sannan tace
“inaga nan da next week ko upper week”
“Allah ya kaimu….bari naje nayi wanka zan shiga school naga result dina”
“Ya kamata….don babanku ya qagu ya gani shima dazu muke maganar” ta fada tana haurawa sama,asma’un kuma ta juya ta nufi dakinta.

Tsaf ta shirya cikin shigar hijabi abinta,tayi kyau sosai cikin hijabin,dama ita tunda can yana mata kyau kai baka ce hijabi bane a jikinta,ta iya ado da shi sosai,a falo suka hadu da asma’un itama ta gama shiryawa,tare suka fito saidai ita parking space ta nufa ta dauki motarta,motar da har yau ta aysha ke rufe cikin tampol bata taba zuwa kusa da ita ba bare ta hau,da daddy yayi magana sai mummy tace ayshan ce tace a aje mata ita ba yanzu zata hau ba,hannunta bai gama fadawa ba,da kansa daddyn ya kirata yace lallai lallai taje ta koya motar a cikin satin,yasa mummyn ta kira wanda ke koya musu mota a gabansa aka yi masa magana,saidai har yau babu shi babu dalilinsa sai tashin zancen,ba kuma kowa ya hanashi zuwa ba sai asma’u,itama hakan yafi mata kwanciyar hankali,don ko sau daya bata taba sha’awar tuqa mota ko mallakar mota ta kanta ba,bata taba wannan burin ba,don ko yaushe tana daukar kanta nan kusa kusa,bata taba barin kanta tayi wani dogon buri ko dogon mafarki ba.

Tana bakin titi a tsaye asma’un tazo ta wuceta motar na tashin kida,duk da taga ayshan tun daga nesa amma bata nuna hakan ba,hasalima baqin gilashin motar ta zuge sama abinta ta wuce,itama ayshan dauke kanta tayi,bata jima ba ta samu napep ta hau.

Kyan da result dinta yayi ya sanyata kuka sosai harda hawaye,tasan cewa tayi karatu tuquru ta kuma yi addu’a,amma bata taba zaton zata samu wannan result din ba,farincikin da take ciki ya shafe komai dake ranta,saidai bata da wanda zasu raba wannan farincikin tare,gefe taja ta dinga trying lambar Aliya amma amsar kamar koda yaushe ne a kashe take,hakanan ta dinga takawa zuwa bakin makarantar fuskarta a washe fes,saidai kana kallon idanunta kasan tayi kuka.

Ta gefan asma’u kuwa tarin carry overn data tarar tana da ita ta dagula lissafinta,ba qaramin tashi hankalinta yayi musamman sanda ta samu labari tun a cikin makaranta kyan da result din aysha yayi,duk da akwai banbancin courses a tsakaninsu,ba haka taso ba,bata son ma hamid yasan ta samu C.O bare ya raina qwaqwalwarta,ta tabbata kam yanzun dole ya sani kenan,hakan ya sanya ta baro makarantar a fusace kamar wani ne yayi mata.

Tun daga nesa kafin ta qaraso take ganin kamarshi,zaune yake dai dai saman babur din,yana sanye da kayan gwanjo kamar kullum shirt da trouser,takalman qafarsa budaddu ne dinkin hannu na kasuwar qofar wambai,hannunsa riqe da wayarsa da yake zuwa da ita yana dannawa,a zahiri ita yake dannawar,amma a badini yana wassafa halayen asma’u wadda tazo ta wuceshi yanzun cikin motarta ta tayar masa da qura,sosai zuciya take ciyoshi amma yana dannewa ta wani gefan,ya tabbatar ba qaramin haquri aysha keyi da su ba,akwai abubuwa masu yawa da bata gaya masa ba gameda da zamantakewarsu shi ya sani,ya tabbatar halayyar asma’un ba qaramin mai haquri bane xaya zauna da ita ba tare da anji kansu ba.

Da sassanyar muryarta tayi sallama daga gefansa,kusan satinta biyu bata ganshi ba,tun zuwan qarshe da yazo ya kawo mata carrot,dama duka duka idan yazo din baya wuce minti talatin ya wuce,saboda dukansu basu san me zasu gayawa juna ba,gwara shi yakanyi qoqarin janta da hira ko yaya irin ta wa da qanwa,saboda yana so ne ta sake da shi,ta dinga sharing matsalarta da shi,kanshi ya daga ya dubeta yana yunqurin maida wayar aljihunsa,duba dayan da yayi mata ya karanci yau tana cikin farincikin da bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba,duk da baisan sila ba sai ya danji dadin hakan,ko ba komai yau yaga sauyin yanayin da ya saba gani kan fuskarta
“Ina yini” ta gaidashi tana dan rusunawa kadan
“Mun yini lafiya…ya gida?”
“Lafiya qalau” ta fada tana murxa yatsunta,shuru ya dan ratsa tsakaninsu,yayin da yake karantarta a fakaice kafin yayi magana
“Me muka samu yau?” Sai ta dago tana dubanshi kafin ta kauda idonta,don ba wani dogon kallo take iya masa ba
“Kamar me…,me ka gani?”
“Labarin zuciya a tambayi fuska inji hausawa?…fuskarki ta labarta min wani abu” murmushi ya subuce mata karo na farko daya taba ganin hakan qarara saman fuskarta,sai yaga ta sauya masa,jerarrun siraran fararen haqoranta suka bayyana,wushiryarta ta fito,haka dimple din dake kwance hagu da dama na fuskarta ya loba,tana son kaifi da saurin ganewarsa,yana da saurin karantar mutum,yana da alamun iya mu’amala
“Result dinmu ne ya fito”
“Ma sha Allah….duk yadda akai an samu abinda ake nema” kai ta kada fuskarta na sake fidda murmushi
“Ma sha Allah….kinga da yayan naki wani ne daya dauki nauyin ci gaban katatun naki” shuru tayi ba tare da tace komai ba,har yanzu kanta na a qasa,shirunta shi ya tabbatar masa da burinta kenan na gaba,saidai yanayin halayyarta ba zata barta ta iya fadi masa ba,murmushi kawai yayi yana kada kai wanda ya ratsa kunnen aysha,sai ya dauke kanshi gefe .

Ya bude baki da niyyar cewa wani abu lantana ta qaraso ta shaida mata asma’u na kiranta zata hada mata abinci zatayi baqo
“Yanzu zan shigo lantana” aysha ta fada,amsa mata tayi sannan ta juya ta koma ciki,khalipha aysha ya kalla wanda ya zuba mata idanu yana son yaga reaction dinta,ya fuskanci ba kadan ba asma’u nada izgili raini da wulaqanci,ta raina ajawalin aysha sosai,hannayensa rungume a qirjinsa,ta soma motsawa sannan tace
“Zan shiga ciki”
“Ni kuma ban gama abinda ya kawoni ba” da mamaki saman fuskarta ta kalleshi,sai kuma ta dauke kai da sauri donbata saba masa irin wannan kallon ba na kai tsaye,duka duka dama zaman da yake idan yazo din baya wuce irin wanda yayin yanzu,girarsa daya ya daga yana so yaga iyakar asma’u ne shi yasa yace haka
“Kina mamaki ne?,ita waccan awa nawa suke da nata sahibin idan yazo?,….ko da yake ni ba sona ake ba ko?” Kunya sosai maganar tashi ta bata,har batasan sanda tace ba
“Me kuma ya kawo zancan soyayya” kafada ya daga yana dan murmushi don yau ta bashi dariya
“Au….haka ne fa” qarar sake bude gate ita ta dauki hankalinsu,asma’u ce ta fito cikin taku dai dai tana jifansu da wani irin kallo na raini da qasqanci,kai tsaye ta nufi kusa da aysha
“Ke….yaushe na zama sa’arki da zan aiko a kiraki har tsahon wasu mintina baki zo ba?”
“Kiyi haquri anty yanzu nake shirin shigowa” aysha ta fada a sanyaye
“Ki wuce kije dalla karki batawa mutane lokaci”
“Bata gama abinda take ba tukunna” khalipha ya fada idanunsa zube fes a kanta,a fusace ta waiwayo da niyyar sauke masa qarshen tsiwarta,amma ga mamakinta sai taji bakinta ya kasa,wani kwarjini na musamman taji yayi mata,sai kawai ta maida idonta kan aysha
“Karki shigo don Allah kici gaba da zama” ta juya cikin bacin rai ta koma ciki,cikin wani irin zafin nama ya diro daga saman machine din nasa
“Macace…ba kuma girmanka bane kai da kanka…saidai kasa ayi maka” wani sashe na zuciyarsa ya tunasar da shi,tilas ya dunqule hannunsa kowanne waje guda ya zirashi cikin aljihunan wandonshi yana hadiye fushinsa tare da qoqarin saita kanshi.

Tuni idanunta ya cicciko da qwalla,duk da bashi take duba ba yakaranci hakan daga sanda ta soma jan hanci
“ka gaida gida” ta furta a hankali
“Kin tabbatar kin gama duk uzurinki?”
“Ka barni naje…koda banje bama sakamakon…” Sai ta kasa qarasawa,da hanzari yace
“Jeki…Allah ya bamu alkhairi” duk da ba haka yaso ba,so yayi yaga iya gudun ruwanta a yau,saidai kuma kome yayi yunqurin yi tare zai barsu da ayshan,koma meye a kanta zai qare ita kadai,yana nan tsaye idanunsa biye da ita har ta bude qofar gidan ta shige.

*oum muhammadiyya*
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button