Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 21

Sponsored Links

21

 

Goma na safiya ta kammala duk abinda take,saboda ta sani tsaf zata iya ganin Aliya a lokacin,cikin dakinta ta zauna tana ‘yan gyare gyaren da suke maganin zaman banza da kuma hana kai tunani,don babu wani abu qwaya daya dake buqatar gyara cikin dakinta,tana da bala’in tsari komai nata a jere yake daki daki,tana da tsafta komai nata kal yake kaman ba’a zama cikin dakin,tun da can tana da son tsafta,koda bata da sabulun wanki ko wanka,haka zata dibi toka tayi wanka,ta sake saka tokar ta sabe kayan sawarta duk da cewa ba wai fita suke ba amma tana rage dauda,kuma tana jin dadin sanyasu a jikinta a hakan.

Related Articles

Sha daya na safe wayarta dake aje gefanta ta dauki ringing,da sauri ta duba aliya ce
“Ina bakin gate zo ki shigo da ni…”haka ta fada mata,yawancin lokuta indai tazo din ayshan take kira tazo ta shiga da ita duk don kada wai su hadu da asma’u tayi mata kallon banza da wofi,don ba qyaleta zata yi ba.

Murmushi suka sakarwa juna sannan suka tako zuwa cikin gidan tare,gab da zasu shige sashen dakin ayshan sukayi kacibus da asma’un sanye da kayan bacci zata shiga kitchen,da alama yunwa ce ta tasheta,don tana iya kaiwa azahar a daki tana kwance kurum kamar ruwa,har ta gota sai ta dawo da baya tana duban aliya
“a’ah….anzo shirye shiryen bikin ne?” Ta furta cikin siga ta izgilanci tana dariya dariya
“Ai gwara a bada himma…mai kwarmin ido da wuri yake fara kukansa ko?,duk da yake ma a qauye za’ayi komai,ta kwana gidan sauqi” ta qarashe tana dariya,da sauri aysha ta matsa hannun Aliya tana mata nuni da kada ta kulata kenan,aliyan ta fahimci haka,saboda haka ta watsawa asma’un kallon banza sannan tace
“Kinci sa’a cikin gidanku nake…..ki tareni a waje” ta fada a zafafe tana jan hannun aysha sukayi gaba
“Ba komai….duk nasan meke damunku” ta fada tana dariya tayi kitchen,iska ta furzar daga bakinta bayan sun shiga dakin ayshan,bata iya zama ba ta dubi aysha
“Har yau wannan mara mutuncin tana nan tana iskancin nan nata….abun ma kamar gaba yake sakeyi saboda rashin taka mata burki da bakyayi ko?” Murmushi aysha ta saki tana gyara ma aliyan wajen da zata zauna bawai don akwai datti ko kaya a wajen ba
“Karki damu…..duk abinda take ba shine a gaba na ba…saboda baki taba gani an gutsuri naman jikina saboda haka ba….hasalima qimarta nake gani har kwanan gobe….saboda jinin daddy ce ita….daraja ba qarya bace…ko a lahira wani yana cin darajar wani….karkuma ki manta cewa ni din ba kowa bace….face yarinyar da hatta mahaifiyarta ta gujeta”ta qarashe cikin karayar zuciya
“wannan ba hujja bace” aliya ta fada hannunta riqe da qugunta tana kada kai
“Manta da wannan…..zauna muyi hirar yaushe gamo” ta fada tana murmushi tamkar ba abinda ke damunta a rayuwa,saidai can qasar zuciyarta tana jin tafi kowa matsala a rayuwa
“Ba hirar yaushe gamo zamuyi ba aysha….mu tattauna maganar dake gabanmu” ta fadi tana zama,yayin da ayshan ta yiwa kanta mazauni itama kusa da ita.

Kaf babu abinda ta boye mata ta zayyana mata komai,shuru ne ya ratsa dakin yayin da aliya ke hadiyar yawu idanunta fes kan fuskar ayshan
“Aysha…” Ta kirata still tana kallonta
“Na’am” ta amsa tana dubanta
“Kin gamsu har cikin ranki zaki auri wannan mutumin zaki zauna da shi?” Tayi mata shigen tambayar da khaliphan ya taba yi mata,kai ta jinjina don ta tabbatar idan tace bata so tsaf aliya zata rusa komai,to idan ta rusa dinma me zata zauna taci gaba da yi cikin gidan?,meye amfanin zamanta?,a gaba wa zata hadu da shi?,gwara wannan ya nuna alamu na tausayi a gareta
“Shikenan….addu’a zamu ci gaba da yi Allah yasa kin dace…ina fata kuma asma’u idan ma tayi da niyyar mugunta mugun abinta ya koma mata kanta,auren mai kudi ba shine dacewa ba,aurwn mai kudi ba shine samun kwanciyar hankalin gidan aure ba,auren mai kudi bai cikin manyan jigon dake sawa a auri namiji,ni’ima ce da idan Allah yaga dama zaiwa wanda yaga dama bawai don yafi sonka cikin halittarsa ba,hasalima ba kowa ke dacewa kan hakan ba,amma sashin abu daya bana son kice zaki rage na hidimar biki da akewa kowacce diya mace budurwa,don kema ita ce….saboda haka zamuyi komai kamar yadda akeyi” dariya aysha tayi ta karyar da kai tana duban aliya
“Kiyi haquri sashin karki dora min abinda bazan iya ba,wallahi Allah bana sha’awar yin komai….kin manta cewa muhalli kawai zan sauya ba wani abu ba….ni haka nake ji a jikina bawai aure zanyi ba”
“Sai kuma kiyi…” Aliya ta fada tana tura dankwali gaban goshi,hakan da tayi ya sanya aysha qyale maganar don bata fiya son jayayya ba,saidai har cikin ranta bata jin tana buqatar yin wani abun.

Hira sosai suka sha da aliya,wanda tana yi tana jefo maganar biki da wani abun da za’a gudanar,itadai murmushi aysha take,komai ma ganinsa take kamar almara sani ne aliyan batayi ba take zancan wani biki,wayar aliyan ce ta fadi tunda ta sauka anijer din,bata kuma haddace lambar aysha ba,mamanta kuma itama bata gari bare ta aiko a karba mata lambar ta tura mata.

Sai qarfe uku aliya ta shirya tafiya,tare suka fito tana tako mata har wajen gate,daga can ta hango kamar shi,yana tsaye gaban mai saida agwaluma da goba irin masu turowa a baro din nan yana siya,kanta ta dauke har zasu gota shi taji ance
“Sannunku” tare suka waiwaya,ayshan ta saki dan qaramin murmushi
“Barka da yamma” ta furta a hankali,har yau bata sakewa da shi jinsa take kamar baqonta
“Barkanki…”ya amsa mata yana miqa mata ledar agwalumar daya siya mata a baqar leda
“Na gode,bari na dan raka qawata” ta fada bayan ta saka hannu biyu ta karba a mutunce
“A dawo lafiya…amma ai ba haka ake ba…bari ni nayi karambani….qawa ni suna na muhammad khalipha….nine sabon yayan aishatu” duban ayshan aliya tayi don bata gane me yake nufi ba
“Sabon yayanta da za’a daura musu aure….” Ya sake bata haske,qasan ransa yana dariyar yadda ta kasa gane zancan da farko
“Ohk….kacemin ango ne” ta furta cikin fara’a,sannan suka gaisa,nan suka barshi su kuma sukayi gaba,sosai aliya ta damqe hannun aysha
“Sashin….wannan kyau haka?….haka yake da kyau….ke ni kaman ma na san fuskarshi wallahi,kamar na taba ganinsa amma na manta a’ina….gaskiya kyakkyawa ne” itakam murmushi kawai tayi,don bata iya qare masa kallo bare ta rarrabe da kyansa ko muninsa
“Gaskiya kin dace…da alama sashin yana da kirki….saidai abinda ban gane ba….meye na wani cewa yayanki…..yana nufin a hakan zaku tafi wa da qanwa?” Ajiyar zuciya aysha ta saki
“Koma mene ni indai zai sanyani cikin ahalinsa,su zauna da ni zuciya daya su riqeni kamar daya daga cikinsu,na samu walwala da kwanciyar hankali magana ta qare” kai aliya take kadawa sannan ta dan dakata da tafiyar da take ta dubi aysha
“Ban yarda da wannan alaqar ta tafi a haka ba aysha….kisa a ranki aure zakiyi kamar kowa” murmushi tayi tana rausayar da kai bayan ta kallo gefe guda
“Nima ai ba kamar kowa bace aliya ki duba fa ki gani….ba wanda ya nemeni don zanyi aure…ban taba tattauna maganar dake damuna da kowa ba saike…kina nufin da ni ‘yar gata ce…kina nufin da ana sona dukkan abinda ya faru din nan zai faru?” Ta qarashe tambayar idanunta cikin na aliya,da alamar akwai abunda ke taba ranta qwarai,kama hannunta aliyan tayi qasan zuciyarta cike fal da tausayinta
“Karki damu da kowa….karki damu da komai aysha…koba kowa mu muna tare…ki koma ki jirayi lokacin zuwa gyaran jiki….kin bar angonki kuma a tsaye,idan wata tazo wucewa kuma ta qyasa kanshi ba ruwa na,tsaf zata qwaceshi a hannunki da wannan sanyin naki” ta qarasa fada cikin sigar zolaya,dariya ta baiwa aysha har sai da tayi ta fito,har yau ba zata iya tantance wannan kyan da aliya ke fada ba
“Amma fa karki tsorata….don bai fiki kyau ba qawata” dariya sosai wannan karon ta baiwa ayshan,wanne kyau ne da ita?,yaushe ta samo kyan,mamaki take duk sanda aliya tace mata tana da kyau
“Ki gaida mama” suka qarke sallamar sanda wani mai napep yazo wucewa aysha ta tsaida mata shi suka tsadance yaja suka tafi.

A jingine ta sameshi jikin katangar qofar gidan hannayensa rungume a qirjinsa,ta saci kallonsa tana son gano kyan da aliya ke fada saidai hada idanun da sukai ya hana hakan tasiri,tana jin nauyin ya ganta tana kallonshi ba tsari hakan a wajenta,kauda kanta tayi sannan tayi gaba zata shige
“Da kin tsaya mun gaisa….wucewa zanyi daga aiken oga nake karyaga na jima ban dawo ba” bata ce komai ba ta dawo da baya,nesa dashi ta tsaya kamar yadda suka saba,a fakaice yake karantarta kamar yadda ya saba,yana mamakin halayenta sosai,sam.bata damu da wasu qyale qyale ba na rayuwa,tunda yake zuwa kulli yaumin cikin hijabi yake tadda ita,bata da yawan kazarniya ko rawar kai irin ta ‘yammatan yanzu,bata da surutu bata da kallo,zai iya zuwa ya tafi baifi ta kalleshi sau biyu ba,shi dinma bawai ta kalli cikin qwayar idanunsa ba kai tsaye,dama ba wani hirar arziqi suke ba,yana zuwanne kawai saboda anni dake yawan cewa yaje din bai kamata ba,bataso tazo taqi sakewa da su,ya zamana bata saba da kowa ba
“Biki yanata qaratowa kinjini shuru ko?” Ya fada yana shafa sajen fuskarsa,ba abinda ta fada har ya gama jiran amsa ya dora
“Ina can ina fafutuka ne….duk abinda Allah ya hore zaki jini in sha Allahu…me dame zakiyi ne da bikin?,a ina zakiyi taki walimar?” Dan motsawa tayi kadan hannayenta rungume a qirjinta ta cikin hijabinta
“Karka matsa da yawa….qauye ma zan tafi a satin bikin” cikin mamaki yake dubanta
“Qauye kuma?…..me zakiyi a can?” Sai a sannan ta daga idanunta ta zubesu fes a kansa kafin ta sake janyesu ta maidasu qasa
“Can ne tushe na…kuma daga can nakeso a dauko ni….bani da inda yafi can” tayi shuru tana jiran jin me zaya fadi,gaba daya ta gama burgeshi,a wannan zamani da yawancin mutane ke bala’in gudu da qyamatar qauye….suke jin haushi da takaici idan an kirasu ‘yan qauye,suke bata rai idan ‘yan qauye sun rabesu,a sannan ita ta zabi ta nuna su a matsayin danginta,ta zabi kowa yaje ya ganta a cikinsu,take daga hannu tana gayawa duniya daga inda take
“Babu matsala…..duk da haka za’ayi abinda ya samu da yardar Allah….sakamin number wayarki don Allah koda buqatar kiran zai taso” ya fada yana miqa mata vivo dinsa da ya baiwa nasir dazu ya saka reza ya jijji mata ciwo,saika dauka tsabar dadewa ne ya saka ta qoqe,idanu ya zuba mata sanda ta amsa ko zaiga qyama daga gareta ko wani abu makamancin haka,saidai fuskarta na nan a yadda take ta soma jera masa lambobin,saura lamba biyu ta gama sakawa wayar ta dauke dif,yasan da faruwar hakan amma sai ya nuna kamar bai kula ba,cikin damuwa ta dago ta dubeshi
“Ta dauke wayar ko chargy ne babu?”
“Subhanallah….,dama yau tun safe take haka….miqo in gani,Allah yasa ta tashi,gashi oga zai iya kirana kowanne lokaci” ya karba yana cire batirin,ya sake maidawa ya kunna duk da yasan ba sake tashi zata yi ba,ai kuwa bata tashin ba,fuskarsa cike da damuwa yace

“Idan akwai paper da biro taimaka ki rubutamin nayi maza na wuce nakai masa saqon tunda taqi tashi”
“Mu gani” tace tana miqa hannunta,wayar ya miqa mata kamar yadda ta buqata,sai yaga ta bare batirin ta ciro layin dake kai,dama babu memory a ciki,wayarta ta bude ta cire nata layukan ta dora nashi ta kunnata ta tasheta sannan ta miqa masa
“Kayi amfani da wannan,zai iya kiranka kafin ka qarasa inda yake yaji a kashe,zai kuma ji dadi….me yiwuwa ka sabawa dokar aiki ka biyo ta inda ba wajen aikinka bane a lokacin aiki” mamaki fal saman fuskarsa yake duban wayar data miqo masa,bawai mamakin tsadar wayar ba,don ya jima rabon ma daya riqe waya mai qaramin kudi kamar ta,mamakin yadda ta bashi wayar kanta tsaye yake,baya manta sanda asma’u ta soma ganin wayar hannunsa,sanda ya bata wayar yace ta saka mishi numbers dinta,sai tada ci dariya sosai kafin tace
“Wai wannan waya ce?” Ya amsa mata da eh,ta bude baki kamar zata sake magana sai kuma ta fasa,ta miqa hannu a qyamace zata amshi wayar sai kuma ta fasa
“Karta bata min hannu da Allah,bari na karanto maka digits din” da toh ya amsa mata,ta dinga karanto masa yana sakawa,sai da ya gama lodawa sannan tace
“Pls duk sanda muke tare ka dinga qoqarin boye wayarka,kar daya daga cikin friends dina su gani ka zubar min da mutunci”

“Ke dame zakiyi amfani?” Ya katse tunaninsa ta hanyar tambayarta
“Karka damu dama ba wani abu nakeyi da ita ba,ina da qaramar nokia zan saka layina a ciki” hannu ya sake miqa wa yana cewa
“Kawo waccar to ko Allah zaisa ta gyaru” kai ta kada
“Karka damu…..akwai wanda zaizo anjima ya karba za’a gyara” sai ta soma takawa tana cewa
“Ka wuce karka yi laifi…..sai anjima ka gaida hajiya”.

Ya dan jima a tsaye a wajen yana juya wayar a hannunsa kafin ya soma takawa yana barin layin zuwa layin da motocinsa ke jiransa,duk a tafiyar mamakin abinda tayi ne ya masa rakiya,ya dinga jujjuya halayyarta yana hadata data asma’u,bai manta ranar data ciro dubu daya guda ta bashi da niyyar biya masa bashi duk da batasan waye shi ba
“Irin wannan sharp sharp haka yau….”cewar mahmoud dake danne danne a system din dake saman cinyarsa
“ka manta ina kan hanyar aiken oga”ya fada yana murmushi sanda motocin suka soma dagawa suna barin layin zuwa saman kwalta,dariya mahmoud ya saki sosai sannan yace
“Allah ya shiryeka khalipha….Allah ya nuna min ranar da qaryarka zata qare” bai amsa mishi ba sai wayar data bashi daya zaro ya jefata inda yake ajiye ajiyensa cikin motar,yana shirin maida locker ya rufe sai ya cireta kuma daga ciki ya hadata da wasu dacument nashi da zaije gida da su.

Wayarshi ya dauka bai ko saurari zancan da mahmoud ba ya soma duba miscal din da ya tarar,sai daya gama sannan ya lalubi wata number mai dauke da sunan anty ruqayya akai,tana shiga aka daga ba tare da jinkiri ba
“Manya…..yanzu nake shirin nemanka ai” murmushi ya saki sannan yace
“To ya akayi….ya ake ciki?”
“Komai ya kammala,yaushe zaka shigo ka gani?”
“Ba lokaci anty….amma zan duba idan na samu chance zan shigo”
“To shikenan…ka cema anni inata kiran layinta bai zuwa”
“Annin?” Ya tambaya yana dan fiddo ido kaman yana gabanta
“Bari na dubata” ya sake fadi da sauri yana katse kiran,kai tsaye annin tashi ya kira,ba jimawa kuwa ta daga ,ajiyar zuciya ya saki har sai data jiyoshi
“Ya akayi khalipha?,lafiya dai ko?”
“Anty tace tayi kiranki bata sameki ba….” Murmushi ta saki mai dan sauti,tasan ya kira ne yaji da gaske ne ko kuma wani abu ne ya faru
“Sharrin qarfen nasara ne….amma wayar a kunne take”
“To alhamdulillah….sai na dawo”
“Allah ya tsare”
“Amin” ya amsa yana jin dadi har cikin ransa sannan ya aje wayar.

“Wai me aka shirya mana ne?” Mahmoud ya sake tambayarsa lokacin da yake laluben number jibril jagoran tafiyar tasu zai tura masa texs
“Name fa?”
“Biki mana….kana nufin ba zamu gwangwanje ba?” Wayar ya aje bayan ya gama tura masa inda zasu yana murmushi
“Kasan wani abu ne mahmoud?….yarinyar ba irin sauran ‘yammata bace ba….tayi universty amma saika zaci ‘yar secondry ce…akwai ciwo a rayuwarta da yake hanata sukuni….,saidai ina fata haka halayyarta take bawai plan bane….saboda mahaifiyata mahmoud bana son abinda zai taba mahaifiyata” kai mahmoud yake jinjinawa cikin nazari sannan yace
“Na yadda da kai khalipha….kana da zuciya da mu’amala mai kyau,in sha Allahu ubangiji bazai bari wani ya cutar da kai ba…..yanzu yaushe za’a kaini wajen amarya?”
“Zaka iya saka kayan gwanjo?”
“Kai….kai ina….bazan iya ba magana ta gaskiya,ina laifin cikin kaya na na lalubo mai sauqi sauqi” harara khalipha ya watsa masa
“Sai kasha zamanka…don dama koni bata gama sabawa da ni ba”
“Aurenku na bani mamaki…..karon farko da na taba ganin auren da akayi babu soyayya tsakanin ango da amaryar amma duka sun amince zasu zauna da juna” ya fada yana dariya dariya,murmushi ya saki khalipha idanunshi na kallon titi
“Kawai abinda na sani shine….zan aureta ne a matsayin taimako da kallonta da nake kaman qanwata dana rasa a baya,zan aureta don in canza mata family…zan aureta don in bata farincikin da iyaye ke baiwa ‘ya’yansu koda ba duka ba nasan zata samu wani bangare daga wajen anni….ina mata kallon qanwa ne bawai matar aure ba…koda na aureta zan bata ‘yancin rayuwa irin na budurwa….saidai zan tsare mata mutuncinta”
“Zai yuwu?” Mahmoud ya tambaya yana kallonshi
“In sha Allah” shima ya bashi amsa bayan ya waiwayo sun hada idanu,kafada.mahmoud ya daga bayan ya danyi nazari kadan sannan yace
“Well….Allah ya bada nasara” bai amsa masa ba saboda sun iso wajen da zasuje din,babban wajen siye da siyarwa ne wanda ba nau’in suturar da basa saidawa masu kyau da tsada na qasashe daban daban,a wajen dukka motocin sukai parking,suka dunguma zasu bishi ya dakatar da su sukayi gaba shi da mahmoud da jibril sai nasir.

“Khalipha….khalipha” yaji ana ambaton sunansa da sauri sanda yake gab da shiga wajen sautin kuma na sake matsowa inda yake,cak ya tsaya sannan ya waiwayo a nutse yana duban inda kiran ke fitowa,zulaihat ce ke takowa cikin sauri idanunta a kanshi tana qare masa kallo
“Ashe haka khaliphan yake?” Abinda take ayyanawa kenan a ranta,wani irin kyau da kwarjini na musamman taga yayi mata
“Lallai talauci masifa ne…ko siffarsa ka ara saiya sauya maka kamanni bare ya kamaka da gaske” ta sake fada sanda take qarasowa inda yake tsayen,tana qarewa motocinsa da suka faka a wajen kallo a dabarance,saidai ta makara,gwani ne wajen saurin karantar mutum wannan baiwa ce da Allah yayi masa,duk kuma wanda ya dan jima tare da shi yasan da hakan,da idanu ya yiwa su jibril alamar su shige,yayin da ya zuba mata narkakkun idanunshi hannayensa zube a aljihun wandonsa,idanunta ta dan kautar saboda kaifi da sukayi mata,kyau da kwarjininsa suka cikata,zuciyarta ta karye har cikin ruhinta tana jin haushin wautar data tafka,da tuni yanzu wannan nata ne,da tuni mallakinya ne inda ta iya mallakar kanta ta boye zalamarta
“Yanzu muhammad haka rayuwa take don Allah?” Ta fada bayan tayi namijin qoqarin tattara dukkan qarfin halin da take da shi,bai amsa ba yadai ci gaba da kafeta da ido,ganin baida alamun amsawa ta sake hada wasu kalaman duk da ta soma karaya saidai tana fatar haqanta ta cimma ruwa
“Ba wanda baya kuskure fa….kuma ni banyi da wata manufa ba…kawai dai kuskure aka samu” ta qarashe maganar cikin lanqwashe murya tana duban cikin idanunsa da wani salon kallo da take fatan ta tafi da hankalinsa,saidai ko gezau,mahmoud ya soma tabashi kadan yana son samun qarin haske ko kuma shi khaliphan yace wani abu,sai a sannan ya dauke idanunsa daga kanta,yana murmushi can qasan ranshi mamaki na sake rufeshi….yana kuma sake baiwa kansa yaqinin babu soyayyar gaskiya a doron duniya…idan ma akwai tayi da nisan da ba kowanne dan adam ke iya kamota ba,hannu ya dagawa mansur daya daga cikin yarashi,ya gane me yake nufi,saboda haka ya tako ya iso gabanshi da jakarshi ya budeta sannan ya miqa masa,hannu ya saka ya bude,kudi ne sabbi a miqe suka bayyana,bandir biyu ya ciro ya sannan yace masa ya rufe jakar,rufewar yayi sannan ya juya da ita ya bar wajen
“Sau daya dama take zuwar ma wani mutumin a rayuwa…kuma hakan ce ta faru da ke” hannunsa ya miqa a nutse ya soka mata kudin jikin jakar hannunta dake maqale a gwiwar hannu yana murmushi
“Ina fata wannan ya zama karo na qarshe da zaki nuna kin taba sanin khalipha a duk inda zaki ganshi….ki huta lafiya” ya fada yana juyawa mahmoud ya bishi a baya ba tare da yace komai ba.

Qwallar da suka cika idanunta sai a sannan suka silalo,kunya ta cikata na mutanen dake wucewa jifa jifa ta inda suke tsaye,gefe guda baqinciki da tarin takaici sun cikata…ba wannan take so ba…..muhammad takeso ya dawo yaci gaba da sonta kamar yadda suke a baya,ya kuma aureta burinta ya cika.

“Ban taba sonta ba…..da fari nagartar ta da na gani a fuska ita ta soma jana….ga zatona zamu dai daita daga baya na koyawa kaina yadda zan sota…..ashe ma tafiyar ba mai nisa bace” ya fada a taqaice wanda yasan ya isa amsa wa mahmoud,saqon ya isa kuwa,don ya gane daya daga cikin yammatan daya nuna yana so ne a baya,ba shakka ya tabbatar batasan waye khalipha,idan yabar abu ya barshi kenan har abada bai waiwayarsa,yana da sauqin kai tausayi da son jama’a,saidai baison yaudara da ha’inci,indai kana son tafiyarku da shi tayi tsaho tilas ka kiyaye wadan nan,sau tari idan ka karanceshi bai bai zaka daukeshi a mara kirki..kuma mutum mai tsauri da dokar tsiya,saidai yafi komai dadin zama da sauqin kai idan ka fahimceshi.

Bai wani jima a ciki ba,kaya ya zabarwa anni kamar yadda ya saba duk bayan wani dan lokaci,ya biya da kanshi kamar yadda bai yadda wani ya yiwa annin siyayya saishi ya dauko kayan da kanshi suna hira da mahmoud jifa jifa suja fito suka bar wajen.

 

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button