Daurin Boye 26
26
*DB*
Duk wadda ta gaya mata baqa kan rashin haihuwarta saita maida masa martani,inna yelwa kawai take dagawa qafa,itama randa ta gaji ranar ta maida mata,daganan cacar baki ta barke a tsakaninsu,har baffale ya dawo ya taddasu haka
“Na gaji da zaman wannan yarinyar mara mutunci a cikin zuri’ata,yarinyar kamar ‘yar fata,kamar ‘yar Allah bani?,to lallai lallai saidai ka saketa ta koma gidansu,yau dai ba zata kwana cikin zuri’ar modibbo ba” kai baffale ya kwantar yana bata haquri amma sam inna yelwa tace batasan wannan zance ba,tace saidai ya zaba ko matarsa ko ita,hakanan baffale yana ji yana gani yayi mata saki daya,tana kuka ta tattara kayanta ta dawo gida
Zaman nata a gida nan ma ba wani dadi ne dashi ba,saboda adawa suka dinga sosai da inna kulu,kusan ta wani janibin idan aka karanci halayyar mahaifiyarki lafiya lau za’a zauna da ita,duk da tana da wuyar sha’ani amma tana da dadin zama,duk da baffale ya saketa sai ya zamana kamar ba’a rabu ba,kullum suna tare kusan idan baida wani uzurin da zai gabatar to suna tare da ita,tuni ya maidata da baki,gidanne kawai bai maida ta ba,sanda labari ya kai kunnen inna yelwa tayi tashin hankalin rabasu amma ina sam haqanta yaqi cimma ruwa,a sannan ma ashe tana da ciki tun kafin ta baro gidan mahaifinki,bai bayyana kansa ba sai a sannan.
Tofa sai sabon rikici ya kunno kai,inna yelwa ta kafe kai da fata kan cewar ciki bana danta bane,yayin da mero ta kafe itama ciki na baffale ne,a sannan baffale baya nan,ya tafi neman kudi garin legos,rigima taqi ci taqi cinyewa,inda alqali ya sake shiga karo na biyu,yace a jira har sanda Allah zai dawo da baffale aji ta bakinsa,hakanan mahaifiyarki ta dinga rainon cikinta a gida,har sanda cikinta ya isa haihuwa baffale bai dawo ba,da yawa suna cewa zaunar da shi inna yelwa tasa akayi don kar ya dawo sabo da ita,haka dai zance keta yamadidi.
Wata tara da kwanaki ta haifeki,kama ta bayyana ta zahiri,kama irin ta ahalin gidan moddibo,ran kwana bakwai aka saka miki sunan aishatu,ba ragon suna ba rigar sakawa,babu kuma wani daga gidansu mahaifinki,a sannan naja’atu bata damu ba,tasan cewa da masoyinta ya dawo komai zai dai daita.
Watanki takwas sannan mahaifinki ya dawo,ranar daya dawo bai zarto ko ina ba sai wajen naja’atu,yayi murna matuqa da samunki sannan ya sake jaddadawa naja’atu cewa zata dawo dakinta ranar juma’ar da zata zagayo,a haka suka rabu,daga bangarenshi ba wanda yasan da wannan magana,ita kuwa tuni ta shaidawa ‘yan uwanta ta kuma soma shiri,labari yakai kunnen inna yelwa,ta kuma ci alwashin daukar mataki,wanda shi ya kaita ga barin garinmu na kwana biyu sannan ta dawo,ba wanda ta gayawa me tayi,babu kuma wanda ta gayawa imda taje,ta dai dawo ta ja bakinta tayi shiru.
Ranar juma’ar kuwa aka yi mata rakiya,saidai inna yelwa ta tsare qofa ta hana a shiga da ita ciki,ta cika ta tunzura da taimakon zugar faccalolin ta,budar bakinta ma cewa tayi ita sam bata yarda da cewa ma diyar baffale bace goye a bayanta,tana shakka,tunda shi tunda ya dawo bai nemesu ba bai kuma yi maganar ‘yar ba,bai kuma ce tashi bace,yayin da naja itama ta dage kan ba zata koma gida ba…gidan mijinta yau zata kwana,tunda shi ya maidata,babu dalilin komawarta gidansu,sannan ‘ya ta baffale ce ko sama da qasa zasu hadu shi ya san da hakan,a nan inna yelwa ta bazama yara nemanshi sai gashi kuwa,tsatstsareshi tayi da ido tana tambayarsa yaushe ya maida naja bai nemi yardarta ba,rudewa yayi ba irin wadda ya saba ba duk sanda yayi mata laifi,ya kuma hau kame kamen cewa naja din ce ta dage kan komawarsu,abinda ya bata mamaki kenan ya daure mata kai,itadai tasan tare sukai maganarsu,ya kuma nemi ta koma din ya kuma amince,to amma duka ba wannan ne babban abinda ya girgizata ba,yadda inna yelwa ke shegantaka masa yarinya tana ba cikinsa bane yayi gum da bakinsa bayan yasan nashi ne,a nan fa halinta na qwatarwa kai ‘yanci ya motsa,tace ba zata yarda ba,ta garzaya wajen alqali wanda ya saba shiga rigimar tasu,nan ya tattarasu ya tambayesu,sai a nan baffale ya amsa kaman yana dari dari da inna yelwa,da alamu dai akwai wata a qasa kenan,ganin ya amsa alqali ya kashe case din,naja’atu ta koma dakinta,saidai abinda baffalen yayi ba qaramin bata mata rai yayi ba.
Bayan komawarta sai zaman nasu ya sauya salo,ba wani jituwa can tsakaninsu,haka ma jama’ar gidan abun nasu ya sake qamari,bata shiga sabgar kowa suma basa shiga tata,duk wanda ya sake ya shiga gonarta kuwa zata nuna masa kurensa,bata barin kota kwana,hakan ya sake saka rashin jituwa mai qarfi tsakaninsu,baffale kam tana zaune da shine kawai saboda darajar soyayyar da sukayi a baya bata manta wannan ba,kasancewarta mace wadda bata da saurin mance abu.
Al’amarin ya fara ne lokacin da naja’atu tayi watanni hudu da dawowa gidanta,a sannan kika cika shekara guda a duniya,mahaifin naja’atu da muke kira baffa salihu ya hada mata gara mai yawa,garar haihuwa ce wadda ba’a yi mata ba saboda bata dakinta a sannan.
Ranar kai garar ina cikinsu,a sannan nima ina goyon suwaiba,naja batasan da zuwanmu ba,saboda haka tana sashinta,da sallamarmu gami da guda muka shiga gidan,duk matan gidan suna qasan bishiyar nan da sukan zauna kulli yaumin,sai aka rasa mai amsa mana sallamarmu sai ido suka bimu da shi,ganin haka rakiyar mai bin naja tace mu wuce bangaren najar kawai,kai tsaye can muka dosa,sanda muka shiga gidan mun isketa a sashenta tana dinkin hula,fes da ita ita da sashen nata kasancewarta gwanar tsafta,da farincikinta ta shinfide mana tabarma a tsakar gidanta tana fadin
“Amma kun yimin ba zata,da kun iske ni kuma bana nan fa?”
“Saimu koma da kayanmu mu cewa baffa salihu kince bakiso” dariya aka saki baki daya sannan tace cikin farinciki
“Kayan baffa ai bana mayarwa bane”.
Kayan muka soma nuna mata,sai ta dakatar da mu tace bari ta kira sauran matan gidan,tayi hakanne saboda haka ake,a qa’ida ma su zasu tarbemu,uwar mijin kuma ita zata saukemu a wajenta,tana shirin fita da goyonki a bayanta saiga inna yelwa afujajan cikin fushi,sauran surukanta matan ‘ya’yanta biye da ita,da kallo naja ta bisu da shi,duk sanda irin hakan ta faru tasan Allah ne kadai yasan sharrin da aka yi mata wajen inna yelwa,Allah ne kadai yasan me akaje aka gaya mata,tasan cewa yau babu zaman lafiya kenan,ta quduri aniyar komai ta fanjama fanjam ba zata lamunci a taka ta ba
“ku tashi ku fito munafukai algungumai irin masifa jinin tsiya,manufukar data gaya muku babu abinci a gidan nan qaryarta tasha qarya…tun kafin ayi daran akai kwandi….tun kafina a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta,bamu gaji yunwa ba bamu santa ba,kuma zuwanta cikinmu bazaisa a fara yunwa ba,ku kwashe tsiyarku ku koma da ita tun rayuka basu baci ba” baba ladi dattijuwar cikinmu,wadda take yaya ce ga baffa salihu tace
“Haba yelwa…haba ke kuwa….idan ana harkar arziqi ai tsiya bata shigo ba,gara ce ta jikarki da aka saba yi wadda bamuyi ba wancan karon saboda najar bata dakinta yanzu muka biya ta…” Tsawa inna yelwa ta daka mata gami da kiranta tsohuwar banza tayi wa mutane shiru,hakan shi ya sake tunzura zuciyar naja itama ta tanka
“Karki sake kiran uwata da tsohuwar munafuka…akan meye ne inna duka wannan masifa da bala’in?,tunda na auri danki ban huta ba…wai duka dai akan baffale ne wannan?”
“Eh…a kansa ne idan kin haifu cikin uwarki sahura da ubanki salihu ki barmin dana kiga idan baqar magana ma zata sake shiga tsakanina dake har abada….kai manu…matsa kuyimin koli koli da kayan wadan nan matsiyatan na daina ganinsu” ta baiwa matasan jikokinta umarni,kafin qiftawa da bismillah yaran sun soma diban kayan suna watsawa farfajiyar gidan,wadda ki cike da kwatami da qazanta,haka suka dinga watsi da duk abinda muka zo da shi yana dilmiya cikin tabi da gulbi muna kallo,tsabar baqinciki naja kuka ta saka ta dora hannu a ka,ana tsaka da wannan abu baffale ya shigo,ranta sai ya danyi sanyi tayi wajenshi tana zayyana masa abinda yake faruwa ga zatonta zai dakatar da su,sai yayi wajen mahaifiyarsa wadda ta dubeshi kai tsaye ta bashi umarni
“Ka saketa baffale idan ni na haifeka,saki biyunta nakeso ka qarasa mata” juyawa yayi ya dubi naja,kai take kadawa cikin kuka
“Karka aikata abinda zai zama dana sani a garemu…karka karya alqawarin daka yimin…”
“Bazan taba dana sani ba don na rabu dake…..naja na sakeki saki biyu….kai manu ku shiga dakinta ku fitar mata da kayanta” ya sake baiwa yaran umarni,kafin kace kwabo kayan ta sun soma watangaririya,tun daga tsakat gida har zuwa katangar bayan gida ta nan suka dinga jefa wasu sai da muka zagaya muka tsince,hatta da suturarta ta sawa basu damu da wankinta da guga ba haka suka dinga watsi da ita.
Mun jata kan ta wuce kawai mu tafi don wasu kayan ma ba zasu debu ba amma ta doje,ta koma ta dubi innayelwa daje tsaye ita da surukanta,wanda kowaccw farinciki take yau naja tabar gidan tsabar hassada da kishin banza mara amfani
“Yelwa….saboda danki kika yimin haka?….burinki ya cika danki ya sakeni….amma ki sani akwai ranar nadama,idan danki ne na barshi kenan har abada,ba danki ba duk abinda ya danganceku ma…” Ta qarashe maganar tana kwantoki daga bayanta,a sannan kina bacci duka bakisan abinda ke faruwa ba,shimfide musu ke tayi,tana shirin juyawa inna yelwa ta saka dariya
“idan kin haifu ke cikakkiyar ‘yar halak ce ki sallama mana ita kiga idan ba zata rayu ba” wani irin kallo ta juya tayiwa inna yelwa,ta yiwa baffale nashi sannan ta qaraso cikinmu cikin matsanancin fushi mukayi gaba,a sannan babu wanda yaga rashin dacewar barinki saboda bacin ran abinda suka yi mana,a sannan babu wanda ya zaci wannan qiyayyar zata shafeki ta raba tsakaninki da mahifiyarki,babu wanda ya zaci lamarin zaiyi dogon zango har ya cimma wadan nan shekarun,yadda naja tace ta bar baffale har abada hakan ce ta faru,hatta da qofar gidan ta daina wucewa,hakanan duk wani lamari daya danganceki ta shafeshi a babin rayuwarta,bata zancanki bata yarda ayi mata zancanki,bata rabarki bata yarda ki rabeta.
Hankalinmu bai dawo jikinmu ba sai sanda labarin wahalar da kike ciki ta riskemu,a sannan duka bakifi shejara hudu a amma yadda ake tafi dake tamkar wadda ta shekara goma,duk da tun sanda mahaifiyarki tabar gidan hankalin baffale kacokam ya koma kanki,kulawarsa duka tana gareki,a hankali sai ya soma bagarar dake kema,wanda mutane da yawa sunyi amannar an kawar da hankalin baffake ne daga kanki da mahaifiyarki,ba’a hayyacinsa yake aiwatar da komai ba,a sannan mukayi yunqurin karbowa naja ‘yarta amma taci alwashin duk wanda ya taka gidanma babu ita babu shi har abada,a sannan baffa Allah ya masa rasuwa.
Hankalinmu bai sake tashi ba sai da kikayi wayo kika soma bibiyarta da kanki,amma wata iriyar tsana kyara da hantara ta dinga giftawa a tsakaninku,ba wanda bai mamakin wannan al’amari ba,har aka dinga zaton anya ba jinnu ne suka shiga jikin naja sukai amfani da abinda ya faru ba suka farraqaku,saidai daga baya muka fuskanci ras take bata da wata matsala,taja kunnen duk wani wamda yake ganin ya isa ya kawo daidaito kan lamarin,akwai wadanda sanadiyya daidaita lamarinku har yau babu jituwa tsakaninsu da mahaifiyarki,da tawa daga cikin ‘yan uwa jin haushin abinda take miki yasa suka fita sabgarku gaba daya ke da ita,suna ganin kunfi kusa ai,duk yadda zasu soki basu kai ya uwar data haifeki ba…..to kinji indo…wannan shine sila kuma mafari”gwaggo asabe ta qarashe fada tana sauke numfashi.
Kuka sosai aysha takeyi,tausayin mahaifiyarta na ratsata sosai na irin wulaqanci da cin zarafin data fuskanta….yayin da wani bari na zuciyarta ke qalubalantar matakin data dauka akanta,ita meye laifinta,ba itace sila ba,ya akayi mahaifinta da mahaifiyarta qarshensu yazo da haka duk sa irin soyayyar da gwaggo asabe ke fadin sun yiwa junansu,anya kuwa batayi kuskuren amincewa da khalipha ba kan cewar zai mata riqo irin wanda yayanta ciki daya zai mata,zai bata family da zatayi farinciki da su,zai bata dama da ‘yanci duk kalar wanda ya dace?,ga masoya yadda suka qare…ina ga ita da zatayi rayuwar alfarma a qarqashinsa,ina ga ita da take da tabbacin ba soyayya ce ta hadasu ba,ba itace jigo ba…tausayi ne da taimako da zaiyi ma rayuwarta.
mero ma dake gefe tayi mutuwar zaune tana juya lamarin,ba shakka tana iya tuna wasu abubuwa da suka dinga biyo baya,irin shige da ficen da faccalolin ummin suka dinga yi suna yada cewa aysha shegiya ce,wanda banda Allah nasom baiwar tasa da tuni ya bita,sai ubangiji ya dakushe hakan daga qwaqwale da bakunan al’umma cikin lokaci qanqani da soma yada qaryar.
Kuka take sosai,tana sake tilawar labarin cikin kwanyarta daya bayan daya,tana fidda kuskuren kowan kowa a ciki,sosai tsoron maza ya kamata,firgici lokaci guda ya shigeta,tana ganin wautarta da kuskurenta na aminta da zama da ahalin khalipha,da wanne ido zasu dauketa wanne kallo zasuyi mata,ashe tabon dake cikin rayuwarta ya wuce iya yanda ita take tunani?.
Sai data ci kukanta sosai ba wanda ya tsaidata a cikinsu,domin dukkaninsu sunsan ba abu bane mai sauqi kashe irin wannan wutar,ba kuma qaramin al’amari bane gyara barnar da tayi shekara da shekaru da afkuwa ko ace tana afkuwa ma,a hankali ta dinga baiwa kanta baki,ta dinga qoqarin tsaida hawayenta,da kumburarrun jajayen idanunta ta dubi gwaggo asabe
“Na gode qwarai gwaggo,na gode da fidda ni da kikayi daga duhu xuwa haske,na gode da kika budemin abinda na jima ina neman sani a kai,na gode da kika kwancemin DAURIN BOYE” tana kaiwa nan ta miqe ta shiga bandaki,alwalar sallar magariba ta daura wadda ta gabato sannan ta fito ta soma shirin salla
“Kici daga da addu’a indo…komai mai wucewa ne da yardar Allah” cewar mero dake duban aysha cike da tausayi,murmushi mai ciwo wanda kai tsaye za’a iya kiranshi dana yaqe ta saki sannan tace
“Na sani mero…kuma ina fata wataran hakan ya zama tarihi”
“Amin ya Allah” ta fada itama tana shiga bandakin don daura alwalar.
Tana saman abun sallarta bayan ta idar,tunaninta ya rarrabu kashi kashi,daga nan inda take tana iya jiyo hayaniyar ‘yan biki wadanda ke shirin tafiya dinner din asma’u,wayarta da tayi qara ita ta yanke tunaninta,ta waiwaya ta jawota sannan ta daga ta kara a kunneta,aliya ce tayi sallama cikin tsokana,wannan karon ranta cunkushe yake shi yasa bata samu damar maida mata ba
“Gobe ne tafiya qauyen ko?” Aliyan ta tambayeta bayan sun gama gaisawa
“Ke da kika ce ba zaki ba?…..” Ayshan ta tambayeta a sanyaye
“Haba sashen,ko mafarki kikayi nace haka zaki yarda?….wasa nake miki…ko ramin kurege kika shiga ai naa shiga,haushi kika bani da kika qi yarda ko dan jan lalle ayi miki,na rasa wacce iriyar amarya ce haka?”
“Ta buzuzu mana…” Ta bata amsa qaramin murmushi na subucewa daga kan lebanta,sanadiyyar tuna aurenta na fari da tayi,wanda ko wankan arziqi bata yi ba randa za’a kaita bare a kai ga wani gyaran jiki da lalle,gwara wannan ta samu gyaran jiki yadda ya kamata,lallen ma itace bata so ba,jin abinda ayshan ta fada yasa aliya bushewa da dariya
“Au dariya ma kike?…..ni son ganinki ma nake fa akwai maganar da zamuyi”
“Har kin sani zumudi….Allah yasa ta samu” karyar da kai ayshan kawai tayi tana tuna yadda al’amrin ya kasance,tana tuna ayanzu waye khalipha na ainihi…hakan ba qaramin fadar mata da gaba yake ba
“Ko na taho yanzu?” Aliya ta katse mata tunaninta ta hanyar tambayarta
“A’ah….ki barshi kawai…ki bari ma tattauna gobe idan zamu wuce takai”
“To Allah ya kaimu”
“Amin….ki gaida mama”
“Zataji wlh…ai ran daurin aure tare zasu taho takai din da abba”
“Kice mata karta wahalar da kanta…ba komai ma za’ayi ba acan din,kawai nima dai inason asan asalina da tushena…kuma nima na jaddawa kaina wace ni…kar duniya ta rudeni”
“Koke ba zakiyi komai ba mu zamuyi malama….sai da safe” ta fadi tana katse wayar,itama aje wayar tayi,batasan wani matsayi zata baiwa aliyar ba,batasan wanne irin qauna take mata ba,tasani kawai Allah shi ya hada qaunarsu,ba wai don tana da wani abu da za’a qaunaceta ko a sota dominshi ba.
Bata bar kan abun sallar ba sai datayi isha’i,zuwa sannan hayaniyar gidan ta ragu saboda ‘yan biki yawancinsu sun tafi sai dai daiku,jifa jifa mero na janta da hira don ta saki jiki tana kuma hada musu kayansu da zasu juya gobe da safe,anty safiyya ce ta shigo da sallama dakin,fuskarta qunshe da fara’a cikin ankon lace wanda sukayi iya su hudu ‘ya’yan mummy yayyen amarya,tayi kyau sosai kasancewarta gwanar ado ce da kwalliya,duban aysha tayi tadan bata fuska
“Haba aysha…ya na ganki zaune kuma?,dinner din fa,kowa fa ya wuce iya mu mukai saura” murmushi ta dan saki,ina ita ina wannan waje?,ko giyar wake aka bata tasha ai ta wartsake
“Bana dan jin dadi ne sosai anty….bazan iya zuwa ba…afwa don Allah”
“Ayyah me ya sameki?”
“Dan ciwon kai ne kadan…amma na sha magani ma nasan zai sauka in sha Allahu”
“Sannu Allah ya sawwaqe yasa kaffara…kin kusa tafiya gidanki ki huta baki daya in sha Allah….amma ki miqe ki daure ki saka kayan da akace zaku saka yau din saboda masu shigowa” dan tunani ta shiga kadan wanda tuni har anty safiyya ta dagota
“Karki cemin cikin kayan da daddy yayi muku ba’a kawo miki komai ba?….” Shuru ita dai tayi ba tare data amsa ba,juyawa tayi fuuu zata fice,da sauri ayshan ta cafko hannunta,tayi narai narai da fuska idanunta sukai qwalqwal kamar zata fidda hawaye,dama har yanzu zuciyar a karye take
“Don Allah anty safiyya ki bar zancan nan karki tada komai….kinga dai yau duka abubuwan da suka dinga faruwa…karki silar tashin wani abu kuma,kiyi haquri” cikin sanyin jiki take duban ayshan,tana da sanyin rai da kyakkyawar zuciya,tana da nagarta da dattako,tana mata kaykkyawan fatan tayi dace da abokin rayuwa mai irin halayenta
“Shikenan aysha..ubangiji yayi miki kyakkyawan sakamako….yasa kin dace har abada”
“Amin amin anty safiya” cewar mero,bata sake cewa komai ba ta juya ta fita ranta sam babu dadi,bata jin dadin wasu daga cikin halayen mummyn dana ‘yan uwanta,batasan meye laifin yarinyar ba,bata da wani mummunan hali qwaya daya tak,kawai don Allah ya yita cikin jinsin talakawa?,kawai don Allah ya sallada zata zauna qasansu taci arziqin da basu suka baiwa kansu ba,Allah ne ya ara musu donsu tallafi bayinsa mabuqata,gashi cikin ikonsa da buwayarsa ya soma yi mata baiwa da kyauta daga cikin ni’imominsa,tana fatan nagartacce ne wanda zata huta ta manta dukkan wata wahala ta rayuwarta.
*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:02 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*ko kuma*
07067124863
*DB*