Daurin Boye 29
29
Ita kadai da qawayenta ne suka shiga motar,saboda a cewarta idan aka hadata da tsofaffi zasu hanasu sakewa,suna shiga ta yaye lullubin kanta tana kallon cikin motar,ita mayyar mota take ta burgeta,tayi mata kyau sosai komai yaji,tana ji a ranta ita ko irinta zata sa mahmoud ya siya mata,nan suka rare cikin motar abinsu kamar ba amarya ba,ta yiwa driver magana ya saka musu waqa,saida suka zaba daya daga cikin waqoqin mutanen kudu
“Asmaa….haka friends din hamid suka hadu?….ke kinga wani guy dana gani a cikinsu kowa….ke inaga rabo ke kira na nazo bikinki” cewar husna duk girman kanta da fadin ranta,dariya suka sheqe da ita gaba dayansu,nusaiba tace
“Ke husnee….bake daya ba ni kaina wlh da sakin asma zanyi na shiga motar wani guy dana gani wallahi ya tafi da ni,muna zuwa zan sauka na ware nemanshi babu sanya wallahi” kan asma’u kamar zai fashe,tana fari da idanu tace cikin magana qasa qasa yadda driver bazaiji ba wai kar tayi baran barama
“An gaya muku a banza na dagewa hamid dina….ke shifa bai mu’amala da qananun mutane wlh,kaf mutanen da yake harka da su sun isa yadda ya kamata” shewa suka sake sawa suna ci gaba da hirarrakinsu.
Duk inda motocin suka gifta sai sun dauki hankalin mutane,tambarin dake jikin motar ya sanya duk traffic jam din da suka he wucewa ake basu hanya su wuce ba tare da an tsaidasu ba,da yawa da basu san motcin waye ba zato suke wani muhimmin mutum ne ya kawo ziyara qasar,su asma’u sun lura da haka,farinciki kamar ta taka kan shege,tana sake gayawa kanta lallai batayi faduwar baqar tasa ba yadda take zato,ko a yanzu ta gayawa jama’ar unguwarsu dana garinsu ita asma’u tayi aure,hakanan ko waye khaliphan da ake zuzutawa tasan bazai iya tasar ayarin motocin nan ba azo daukar aysha…ayshan data cusa masa ita tunda tasan ba ita yakeso ba ita asma’u yakeso
Ko sau daya aysha bata bari addu’a ta subuce daga bakinta ba,hannunta yana matse gam cikin na gwaggo asabe,haka mayafinta na saman kanta,saidai hawaye kam ba’a magana kamat barinsu ake,tun gwaggo na mata magana da bata baki harta haqura tayi shuru ta qyaleta.
Da yawa daga cikinsu basu gane gidan da aka xo b,saboda da yawa basu samu zuwa yi mata jere ba,hamid ya riga ya fadi adadin mutanen da yakeso suje jeran a sannan don karsu bata masa tsarin gida a cewarsa,asma’un ta biye masa saboda tsanin qauna,hakanan ta tsara mummy,ita kuma ta biyewa tsarin nasu saboda farincikin autarta qalilan daga cikinsu ne wanda basufi mutum hudu ba suka so su gane saboda banbanci qarara dake bayyane tun daga gate din gidan,suma basu kai ga yin magana ba saboda sun zaci haka aka tsara har aka shiga cikin gidan.
Duk yawan motocin tsaf harabar gidan ta lanqwame su,a jere daya bayan bayan daya suka jeru sannan jama’ar ciki suka fara fitowa,kowa ka kalla ido a waje yake duban gidan,kowa tanka kyau da tsarin gidan yake,tun daga harabar gidan zuwa cikin gidan,a sannan asma’u na cikin mayafi farinciki kaman ta taka rawa,tana tsammamin ana magana ne kan gidanta,sai a sannan ta soma zagin su nusaiba cikin ranta,wato qarya suke mata da suka wassafa yadda gidan aysha yafi nata kyau kenan?,so suke su haukatata kenan saboda sunsan yadda ta tsani tayi qasa a rayuwa.
Aysha na mota tana addu’a kafin fitowarta,a sannan tuni asma’u ta isa ga katafaren falon gidan ta yiwa kanta mazauni kan daya daga cikin kujerun falon masu tsakanin laushi da taushi,ranta na haske da maganganun kodawa da yabawa gidan da take iya ji daga bakin ‘yan rakiyar dake ta kunno kai cikin gidan.
Cikin nutsuwa da fargaba take takowa cikin gidan da taimakon aliya da mero
“A’ah amarya asma’u …ya haka?,ko rakiyar qanwar taki aysha kika zo?” Aliya ta fada tana murmushi,wani anu ne ya daki zuciyar asma’u,ta yamutae fuska ta cikin mayafinta tana sauraren bugun zuciyarta dason gane me kalaman aliyar ke nufi,bata kai ga wannan gacin ba muryar anty halima ta karade ilahirin falon
“Ke asma’u garin yaya kuka hau motocin rakiyar aysha?,ko haka dama aka tsara?,kin batmu muna can bilayin nemanki badon Allah yasa fatima taga fitarku ba” anty haliman ta furta da alamun bacin rai qarara ga fuskarta ta ratso falon wadda ta shigo afujajan
“What?!” Asma’u ta fada a zabure tana yaye mayafin kanta tana ware idanunta,da daya da daya idanunta ya dinga sauka kan kowanne lungu da saqo na falon tana qarewa dukiyar da aka xuba kallo a fakaice,a lokacin anty halima na fadan kuskuren da aka samu wanda da biyu take masifar,basu saurareta ba tuni suka sada aysha da daya daga cikin dakunan baccinta.
Bata iya tsayawa ta gama kallon dakin ba ta miqe a fusace ta baro falon,zuciyarta kamar zata fito,ranta na tafarfasa,sai data gwammace bata yaye lullubinta ba bare tayi tozali da irin falon da take mafarki yau gashi ya zama mallakin aysha,ko a harabar gidan duk yadda taso ta hana idanunta ganin komai hakan ya gagara,iya fitilun da suka haske harabar gidan tarwai kamar rana kawai abun kallo ne,cikin fushi ta ciro wayarta ta soma neman lambar hamid,dama yasan ba ita ya kawowa motocin ba,yasan da haka amma yayi shuru baice komai ba,ya janyo mata abun kunya,me xai kata taka gidan aysha?,yqnzu yarinyar zata dinga tutiya da jin ita asma’u da kanta ta rakota gidanta kenan,sai data kusa tsinkewa sannan ya daga
Qoqarin controlling fushinta tayi don kada qilu ta jawo bau,duk zafin kantabtasan inda take tasan halin hamid din sarai
“Haba hamid….ya zaka yimin haka don Allah fisabilillahi….?”
“Lafiya?….keda wa?”
Ya tambaya cikin halin ko in kula,tasan halin kayanta sarai,shariya da halin idont care
“Munbi motocin daukan aysha munyi zaton ni ka aikowa da su?”
“Ni na gaya miki naki ne?….” Shuru ta danyi sannan tace
“Yanayin abunne nayi zaton nawa ne”
“Amma ai already na gaya miki cewa motoci biyu xan kawo,kuma da sunzo din xan kira ki na sanar miki ko?”
“Habba dear ka rufamin asiri don Allah…motoci biyu kaman za’a rakiyar kaza….ai ba girma na bane…kaga motocin rakiyar aysha ne?”
“Ke bana son rainin wayo malama….haka nakeso haka na tsara…bana son hayaniya da hauka aje a batawa mutum waje ba’asan nawa ka kashe ba…ni xaki hada da muhammad mai goro?” Ya qarashe maganar ta sigar tambaya wanda bata fahimci me yake nufi ba
“Am sorry” ta fada a sanyaye
“If kina son zaman lafiya da kwanciyar hankali kibi dokata,ban kuma lamince a qara wata motar kan wadda nace ba” daga haka ya kashe kiran,shuru kawai tayi tana duban su nusaiba dake tsaye gabanta,duk yadda taso ta daure saida kuka ya qwace mata,hamid yana son ruguza ta da gadar mata da abun kunya kuma abun fada,ta yaya za’ayi rakiyarta da mota biyu kacal,anty halima ce ta qaraso wajen tana tambayar meke faruwa,bata iya bata amsa ba sai hannunta data kama suka shige motar anty haliman suka tada ta,tilas saura suka sake hawa motocin da aka kawosu akayi jigilar maidasu.
Tun cikin mota ta dinga jin ta muzanta,duk da cewa ba wadda ta sake ce mata komai amma saitaji a karan kanta ta tsargu da kanta,ba abinda ke mata yawo cikin idanu da kwanya irin gidan aysha,ita kanta ta tabbatar da cewa khalipha ya yayiwa hamid fintikau ya tsere masa,tako ina WUTSIYAR RAQUMI tayi nesa da qasa(daya daga cikin littafan zafafa biyar na billyn abdul),yau BURI DAYA (zafafa biyar mamuhghee)da take da shi ya cika,saidai ta raina cikar burin nata,ashe abinda take hangowa akwai sama da haka?ta yaya akai haka ta faru?,inama ace zata samu SAUYIN QADDARA(zafafa biyar na hafsat rano).
Sai takwas na dare sannan ya kirata ya sanar mata zuwan motocin,anty safiyya ce ta fita sai gata ta dawo ta dubi mummy
“Sai a zabi wadanda zasu je kaita”
“Kamar yaya….kowa zaije kamar yadda aka je na indo”
“Da motoci biyun?” Anty safiyya ta fada tsantsar bacin ran dake fuskarta na nunawa,duk da qoqarin danneshi da take
“Motoco biyu?…motoci biyu kuma?” Mummy ta tambaya tana yatsine fuska
“Ki aika a gano miki” anty safiyya ta fada tana cire mayafinta ta wuce bandaki,don ita bata jin zata ma iya zuwa.
Kai tsaye dakin asma’u mummy ta wuce tana tambayarta zancan motoci biyu da aka ce,ta tabbatar mata haka ne,nan mummy ta hau masifa tana fadin idan ma qyashin bada motocin suke su zasu bada wadanda zasu isa
“Mummy…..kiyi haquri kawai don yace baya buqatar mota sama da biyu”,wannan batun shi ya tunzura mumnyn,tana ganin kawai hamid ya shirya wulaqanta su ne,ta taya har aisha zata fisu yawan ‘yan rakiya da ababen hawa?,ganin yadda mummyn ta hau sosai taqi sauka daga qudurinta na qara motoci,sannan ita ta sani idan haka ta kasance komai zai iya faruwa,saboda haka tayi hanzarin kiran daddy ta gaya masa komai,kashe wayar yayi ba tare daya ce komai ba ya nemi mummyn da kanshi ya bata umarnin ta bada yarinya a tafi kaita,a hadata da manya mutum uku qawayenta mutum uku,baya son qorafi baya son kuma ya qarajin wani abu ya biyo baya,tasan daddyn har yau na ciki da ita kan maganar aysha,tilas ta haqura,aka dauki yayarta daya yayar daddy daya,qawayenta biyu,qawayen asma’un biyu,abun mamakin shine sanda suka fita da amaryar akwai motoci kusan guda takwas,saidai biyu ne kawai nasu saura dangin hamid ne mata,wanda a qa’ida su zasu shiga su fito da amarya amma suka qame cikin mota ba wadda ta tako waje har aka saka asma’un cikin motar aka soma tafiya.
Qarfe tara na dare ayarin motocinsu khalipha da abokanshi suka shigo gidan,daga inda take zaune tana iya jiyo qararsu da maganganu sama sama,duka duka ba’a fi mintuna goma sha biyar ba taji motocin sun sama ficewa daga gidan,cikar mintuna ashirin taji dif alamun babu kowa a harabar gidan.
Ya kusa a qalla minti biyar tsaye riqe da leda,daya hannun nasa riqe da babbar rigarsa yana kallon qofar falon da zata sadashi da ainihin cikin gidan,komai ya qare an gama komai,ya dauko amana da nauyin kula da yarinyar mutane wanda baisan ya zata kaya masa ba,ya cikawa anni burinta me gaba zata haifar?,wani iri zama ne zai kasance tsakaninsu?,tarin tambayoyin daya ringa yiwa kanshi kenan kafin daga bisani ya ambaci sunan Allah ya kama handle din qofar falon ya tura gami da yin bismillah ya shiga falon.
Babu kowa a falon kamar yadda ya zata ,sai ya tsaya yana bin kowacce kusurwa ta falon da kallo,tunda akayi total ya biya kamfanin da zai masa dukkan aikin bai sake bi ta kan gidan ba,sai yaji tsari da yanayin gidan ya burgeshi sosai,komai yayi masa kamar shi ya zaba da kansa,yasan hakan baya rasa nasaba da shigar mahmoud cikin aikin,yasan zabinsa yasan ra’ayinsa shi yasa komai yayi masa a yadda yakeso,baisan a ina take ba ko inda zaije ya sameta,tilas ya zube ledojin saman doguwar kujerar shima yabi lafiyarta ya zauna saman kujerar,sai daya nutsu sosai sannan ya lalubo wayarsa ya soma neman lambarta,kiran farko aka gaya masa wayar a kashe take,hakan ya tilastashi miqewa yana laluben inda zai sameta.
Hannunshi saman handle din qofar daki na qarshe da yake zaton tana ciki,ya dan tura kadan zai shiga sai kuma yaja da baya yana nazari,a lokacin tana zaune gefan gadonta kanta a rufe kamar yadda suka zaunar da ita bata motsa ba har yanzu bata sauya wajen zama ba hakanan bata cire lullubin dake kanta ba,taji motsin bude qofar sai tsoro ya kamata kasancewar taji fitar wadanda suka shigo a dazun balle tace sune,ta takure waje daya zuciyarta na bugawa da sauri,sake buda qofar yayi ya sanya qafarsa bakinsa dauke da sallama,qamshi da sanyin dake cikin dakin ya bugi fuskarsa,qamshin sabbin abubuwa da kuma turaren da baisan na waye ba,komai na dakin kalar purple ne wanda ya ciza,ba qaraminnkyau da tsari shima yayi masa ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki sanda ta fuskanci wanda yayi sallamar ta maida masa amsa cikin dasashshiyar muryarta da tsananin kuka ya disasheta,gabanta ya tsaya hannayensa harde a qirjinsa.
A hankali ta zamo daga saman gadon zuciyarta na qara rauni,sabbin hawaye suna sake kunno kai,saman gwiwoyinta ta tsaya kamar wadda ke shirin yin kneeldown,kanta a qasa duk da mayafin dake lullube a kanta,ta hade hannayenta cikin na juna,cikin rauni da sanyin murya ta soma cewa
“Kayi haquri idan na sako kaina a muhalli ko gurbin da bai dace da irina ba…ina mai roqonka alfarmar kada ka cutar da rayuwata ko ka cusa mata baqinciki kaman yadda sauran mutane kemin a kowanne bigire na rayuwa idan na hadu da su,bansan ainihin kai waye ba sai daga baya,nayi zato ko tsammanin cewa kaidin kamar ni kake,saboda mai matsayi irin nawa shine zaifi kowa fahimtar wace ni?,me nake ji cikin zuciya da gangar jikina,tun ba’ayi nisa ba nake jin na tafka kuskure mai girma….kayi alqawarin saka ni ne cikin familynka saidai gani cikin wani muhalli da yake nunan zan rayu ne ni daya,idan….. “Sai ta kasa qarasawa,tsayawa kawai yayi yana dubanta,mamaki na kamashi,tana nufin batayi farinciki ba da bazatar data faru?,batayi farinciki ba da sauyawarsa daga talaka tilis dare daya zuwa mai arziqin daya gwada ‘yammata da yawa a kansa suka kuma fadi warwas?,bata farincikin ta shigo daula ita din wace irin maca ce?,ita ba kamar sauran mata bace ko kuwa?,sai ya rasa amsar da zai bata,ya sani cewa yana komai ne bisa son rai da jagorancin anni,shi da ita duka babu mai niyya cutata mata
“Bazan taba neman wani abu daga gareki ba har abada irin wanda kike tsammani,idan kuma kina jin dar ne na kasancewa da ni ni daya tak zan iya maidaki cikin gidanmu,kusa da mahaifiyata abu mafi soyuwa a gareni” kasa bashi amsa tayi,sai kanta kawai da take gyadawa,shuru yayi yana kallonta kawai,ta wani barin sai taso bashi dariya duk da wani nauyi da yake ji ya hau saman zuciyarshi,ta cika tsoro da yawa,bata da saurin yarda irin na ‘yammatan zamani,sai yaji yana sha’awar ya zolayeta,abinda bai taba faruwa ba tsakaninsu tsahon tarayyarsu tare,ya gyara tsaiwarsa yana cewa
“Amma fa nidin kamar yayanki nake kin manta?,na gina wannan waje ne da sunanki don nayi alqawarin baki kalar rayuwa da akayi yunqurin hanaki samu,saidai da alamu naga ko sau daya baki kalli koda gadon da kike zaune a kai ba bare ki zagaya gidan kiga yaya yake” shuru tayi tana nazari,tana son tantance da gaske bata kyauta ba ko kuwa ba wani laifi tayi ba,don ita ko dai dai da sau daya batayi sha’awar kallon dakin da take bama,duk da yadda a sanda aka shigo da ita ta dinga jin surutan mutane na yadda gidan ya tsaru har suka bar gidan
“Shikenan tunda baki muradi….me kike da buqatar dauka kafin mu wuce” kai ta gigiza da sauri don gaba daya a tsorace take,bata taba kadaicewa da wani cikin gida haka ba daga ita saishi,don ko dan ladi ma bata taba yarda ta kwana cikin daki daya da shi ba saboda tsoron shegen dukan da take ci,da kuma tsoron abinda zai nema daga gareta wanda a sannan tsanin quruciya yasa ta laqaba masa suna da iskanci kuma dan iska ne kawai keyin hakan
“Dole kina buqatar wasu abubuwa….amma tashi mu wuce ba damuwa” miqewa tayi a nutse tana dan jan mayafinta baya kadan ta yadda zata iya ganin gabanta,shi ya wuce gaba yana latsa wayarsa yayin data bishi a baya,ko a sannan kanta a qasa yake ba inda ta kalla,tana amfani ne da takun sa tana bin bayansa.
A harabar gidan suka tadda mota daya da driver daya,wanda ya taso da sauri ya budewa khalipha murfin motar
“Bismillah” khalipha yacewa da aysha yana matsawa baya,a hankali tayi bismillah cikin zuciyarta ta shiga,driven zai bude masa daya side din ya dakatar da shi,ya bude gidan gaba da kansa ya shiga kusa da mazaunin driver,tsayawa drivan yayi sararo cikin mamaki da rashin sabon ganin hakan,ba tare da khalipha ya dubeshi ba yace
“Halan baka shirya tafiya bane ka bani muqullin”
“Sorry sir” ya fada cikin hanzari yana zaburowa,ya bude sit din driver ya shiga ya tada motar suka bar cikin gidan masu tsaron gidan suka maida qofar suka rufe,suna hawa saman kwalta drivan yayi nufin saka masa cd plate dinsa kamar yadda suka saba yawancin lokaci khaliphan ya dakatar da shi saboda yau bashi da buqatar haka,haka motar ta kasance shuru,sai muryar khalipha dake cike da nutsuwa ba hayaniya da yake reply voice note ta watsapp da yake saurara.
Kanta a qasa yake har a sannan,muryar khalipha da yake amsa saqonni ita ta katseta ta hanata fadawa duniyar tunani kamar yadda ta saba,sai yatsunta kawai da take murzawa tana tunanin yadda zata sami anni,tana tunanin wacce tarba zata samu?,wacce kalar rayuwa zatayi da su?,duka wunin yau da tunanin umminta tayi shi,ta duba wayarta har batasan adadin sau nawa tayi ba,ta wuni da fatan ganin saqonta koda saqon blank ne baya dauke da kowacce kalma,amma a qalla zata san cewa tana tunata a cikin rayuwarta,tana tuna cewa ta taba haifar wata diya cikin qauyen takai,gefe daya kuma mahaifinta na cikin ranta,’yar kulawar data taba samu daga gareshi tana manne cikin ranta,tana roqa masa rahama da gafarar ubangiji,bata fata Allah ya kamashi da haqqinta komai qanqantarsa,ta sani cewa kowanne bawa baya tsallakewa qaddararsa,ta iya yiwuwa tashi qaddarar kenan a rayuwa.
Tafiyar a qalla mintuna arba’in suka iso gidan,tana zaune cikin motar har sanda khalipha ya fita ya mata umarnin ta fito itama,fitowar tayi tana sake gyara lullubinta da kyau,da baya yadan matso inda take tsaye sannan yace
“Zaifi kyau ki bide fuskarki don karki fadi,tunda ba sanin hanya kikai ba” bata qi ta tashi ba ta dan sake jan mayafin baya saidai duk qwaqwarka ba zaka iya ganin fuskarta ba,da haka ta soma binsa a baya suka bi wata siriryar hanya da aka yiwa adon furanni da shukoki masu kyau wadda itace zata sadaka da ainihin falon gidan
[3/6, 9:02 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_
*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_
*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_
*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_
*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_
*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300
*KO KUMA*
07067124863
*DB*