Daurin Boye 33
33
Bayan sun kammala break din hira ta balle,wanda kusan haidar da mus’ab ne suka hada rudun,sun saka rahama gaba sai cakar da ita suke,itakam tayi kicin kicin don bata son raini,nan ma saida khalipha ya tsawatar,qarshe tashi tayi ya basu waje,amal itama ta miqe tana sauka qasa don zuwa kitchen ta samu ruwan da zata sha.
Mus’ab kewa anni qorafin motarsa tare da roqarta ta bashi daya cikin wanda ya khalipha ya bata,wasa qasa yake maganar saboda yadda khalipha ke harararshi “Shikenan….a baiwa diyata dayar,kai kuma ka dauki daya,amma fa aro…” Ta qarashe fada tana dubanshi,dan tsalle yayi kadan saboda yasan ta fadi ne kawai qarshe dai ta zama tashin halak malak
“Yes my anni!…..thank you” hannunshi khalipha ya saka a aljihu ya ciro muqullan mota yana fadin
“Kin tunamin kuwa anni….ina haidar…idan kun samu lokaci ko zuwa dare ne kuje ku dauko motarta dake wancan gidan…wacce zata yi amfani da ita kenan anni?”
“A debosu duka ta dinga hawa wadda takeso ko ‘yata” kunya ce sosai ta kama aysha da wani irin nauyi,ita dako rage hanya ba’a qaunar ayi mata a rayuwa yau ita ake cewa ta dinga hawa mota bama daya ba har guda biyu?,itakam wacce irin qauna mutanen ne ke mata ne
“Allah ya saka da alkhairi ya jiqan magabata ya qara lafiya..na gode”
“Amin…amma babu godiya saboda tamkar ‘ya kike kema,ku bata muqullanta ta soma hawa duk sanda takeso” dan dubanta khalipha yayi sannan ya maida dubanshi ga anni yana miqewa
“Banjin ta iya driving….”
“Faduwa tazo dai dai da zama….sai na koya mata kawai” mus’ab yayi hanzarin fada,harara khalipha ya maka masa wadda ta sanyashi ya nutsu sannan ya dubi anni
“Zan fita amma bazan jima ba zan dawo”a dawo lafiya suka yi masa gaba dayansu.
Ranar a nan ta wuni gaba daya,ko da su atika zasu shiga girkin dare a lokacin bata jima da gama sallar la’asar ba binsu tayi kitchen din,kusan ranar gaba daya ita tayi girkin daren sai tattaimaka mata da suka dinga yi da wasu abubuwan,da fari qin sakar mata sukayi suna tsoro suna dari dari,daga bisani dole suka sakar mata din ganin yadda take komai cikin qwarewa,a nan suka saba sosai dasu atikan kamar sun jima tare,qarfe shida suka gama ta baro kitchen din ta koma sashensu ta shiga wanka.
A hankali ta tura qofar dakin kaman yana nan duk da tasan baya nan din,gefan akwatunanta ta nufa ta bude,doguwar riga ta ciro ta ajeta saman akwatin sannan ta shiga bandakin ta tura qofar ta sama tara ruwan dumi,ba jimawa ya cika ta soma wankan tana jin dadin dumin ruwan da yadda yake bada qamshi shi da kansa ruwan,ita kadai cikin ranta take jinjina gayu irin na khalipha da son qamshi.
Shida saura ya shigo gidan kamar yadda ya saba sai daya biya yaga anni kafin ya wuce sashensa,annin tana ta qorafin wunin da yayi yauma a waje,dariya kawai yake yana jinjina yadda anni keso ayshan,ya sani duk don saboda ita yayi hakan,tabe baki rahama tayi bayan ya wuce wadda ke zaune gefan annin tana latsa waya ta kalleta
“Nikam wannan auren soyayya akayi?,ango da sai kayi satima kuna gida daya baka ganshi ba amma shi kwana biyu kacal ya soma fita yana wuni?,kodai bata iya kula da miji bane?”
“Banda abinki rahama wannan ai zancanku ne keda yayan naki” anni ta fada tana miqewa don da wuri take daura alwala kafin a kira sallah ta shige toilet abinta,hada ido sukayi da amal,saita saka dariya wadda tayi ne kawai don ta qular da rahaman itama ta miqe ta bar falon ta shige dakinta
Cikin satin aysha ta soma koyan mota sosai ta hannun aliyyu,wanda sam khalipha ya hana mus’ab yace haidar din ya fishi nutsuwa,tun tana dari dari da su har ta soma sakin jiki,haidar nada kirki qwarai,yana da daraja mutum,yadda yake bata girma abun har kunya yake bata,idan taga yadda yake tsarewa rahama da amal gida idan baiga dama ba sai abun yayita bata mamaki,suna kamanceceniyar halayya da khalipha ta wani fannin,zamanta cikin gidan sai ya soma yi mata dadi,ta soma sakewa musamman idan tana tare da anni,duk wata kunya da surukuta anni ta soketa tsakaninsu,sukan zauna su taba hira duk da har yanzu bata iya bude baki sosai tayi magana yadda ya kamata mai tsaho,saidai tana qoqari matuqa wajen ganin ta saba dasu din.
Sati uku da biki ta soma warwarewa sosai,janta a jiki nuna mata ita watace da mu’amala mai kyau shi ya taimaka wajen samuwar wannan sauyin,saidai abu daya da bata jin dadinshi shine yanayin yadda rahama take mu’amalantarta,takan bata girma dai dai gwargwado,hakanan bata shiga sabgar da bata shafeta ba kamar yadda haka halayyarta take tun a gida,saidai duk wani motsi na ayshan a idonta yake kamar wadda aka baiwa gadinta,hakanya sanya itama ta iya takunta take matuqar taka tsantsan da ita.
????????????????
Parlour din asma’un cike yake da qawayenta na makaranta wanda ta gayyacesu suzo gidanta kwanaki sati hudu da tarewarta,manyan qawayenta ne da take ji da su ko ince a kullum take qoqarin yin abinda zata burgesu su fahimci cewa ita din ba qaramar mace bace,a ranar ta baiwa yarinyar da aka kawo mata a matsayin ‘yar aiki qwaya daya ‘yat qabilar igbo umarnin ta dafa musu abinci har kala uki,baya ga snacks da lemuka da aka jibge tsakiyar falon,anaci ana kwasar shafta.
Gaba daya hankalinsu yayi gaba babu wadda taji kota lura da shigowarshi,fuskarshi tamke yake bin kowacce da kallo,sai a sannan suka ankara da shigowar tasa,nusaiba itace ta soma masa magana cikin wasa irin na qawar amarya
“Ango kace kana kusa da dawowa ma kenan…..dama kai muke jira ai” maimakon ya sake mata su gaisa kaman yadda suka saba yi a lokacin hidimar biki saitaji yaja tsaki tare da yin gaba ya haye sama,dukansu baki galala suka bishi da kallp har ya gama hawan
“Ke….haka naki mijin kuma yake?” Cewar daya daga cikin qawayen tana riqe da haba cikin mamaki
“Wannan ko anya asma’u?,kinga kallon raini da wulaqancin da yake mana kuwa?”dayar ta kuma fadi
” ni ban gaji wulaqanci ba wlh,oya ku tashi kawai mu wuce”cewar husna babbar qawar asma’un da take ji da ita,sai a sannan da taga suna shirin miqewa asma’u da wani baqinciki ya qumeta da azabar kunya ta magantu
“Babu wannan maganar don Allah kuyi zamanku ina zuwa….yana da fushi ne zai iya yiwuwa a waje aka bata mishi rai bari naje” ta fada da sauri tare da miqewa tayi hanyar stairs ranta na bala’in baci.
Tura qofar dakin tayi,saita sameshi yana tsaye ya kwabe rigarshi saura singlet yana shirin cire dogon wandonshi ta shigo,cikin nuna bacin rai da fusata ta kalleshi
“Haba hamid….ya zaka kunyatani gaban qawayena don Allah?,me suka taba yi maka zaka yi musu wannan wulqancin?,so kake suje gaba su samu abin bada labari?” Bai tankata ba har sai daya cire wandon saura gajeran wando kawai sannan ya dago ya dubeta cikin qanqan da idanu
“Ke,an gaya miki bansan ciwo kudi ba?,ko an gaya miki tsintosu nake?,ohk kin zaci za’a ci gaba da yadda aka saba ko?,toni ba haka nake ba,nasan ciwon kudi nasan mutunci da darajarsu,haka kawai ki taramin garadan qawayenki ki kwaso abinci da abun shan da a qalla zamuyi sati muna ci ki jibge musu don tsabar burga?,to wallahi kiyi gaggawar zuwa ki sallameshi ki kuma kwashemin kayan abincina ki maida store” tsantsar bacin rai da mamaki ne qarara ya bayyana a fuskar asma’u,tana jin ya xama lallai ta nunawa hamid bacin ranta qarara saboda gaba
“Me kake nufi hamid?,qawayen nawa?,to wallahi babu inda zasu,kayan abinci kuma da kake magana ai daga gidanmu aka hadoni da shi ko?” Dawowa yayi da baya maimakon daa da yayi gaba zai shiga wanka
“Haka kika ce?,don an kawo wadan nan matsoyatan kayan abincin kike gaya min haka?,ohk fine….ki gayamin nawa na kashe miki wanda sunyi ninkin baninkin kudin kayan abincin da aka kawo min?,koni na gayawa iyayenko ina da buqatarsu ma?,a matsiyaci kika aureni?,tunda ba zaki iya sallamarsu ba ni zan iya” ya fadi yana nufar qofa,da mamaki ta soma tsaidashi saboda singlet da gajeran wandon dake jikinsa amma ko juyowa baiyi ba bare ya saurareta.
Kaf dinsu saida kowacce ta miqe tsaye a tsorace ganin mijin qawar taso a haka,dubansu yayi sannan ya soma magana
“Kafin na qirga biyar kowacce a cikinku ta kwashi matattun qafafunta tabar min gida tunda yunwa ce ta kawoku,kada wadda ta sake zuwa min gida tasha min koda ruwa ne bare abinci,ku cika cikinku a gidajen ubanku kafin kuxo” cikin bacin rai husna da take jin tafi qargfin wulaqanci ta soma maida masa martani,kanta yayo wanda hakan ya sanya suka qarasa ficewa a guje ba shiri ba tare da sun tsaya daukan kayayyakinsu ba,bayansu yabi cikin daga murya yake baiwa inyamurin mai gadinsu umarni cikin karyayyen turanci
“Maza ka sakar musu karnukan nan su qarasa rakasu” jin abinda yake fada ya sakasu qara mai,taimakon da Allah yayi musu daya motar da suka zo cikinta tana qofar gidan basu shigo da ita ba saboda motocin hamid guda uku dake harabar wajen data asma’u daya data zo da ita ta cike wajen.
A tsaye a falon ya tadda asma’u tana qwallar takaici tare da tunanin anya kan hamid daya kuwa?,lafiyarsa qalau?,kodai ya soma bin hudubar yayyensa mata randa sukazo da sunan sunzo ganin amarya da sukaji suna gaya masa
“Wannan matar taka sai kayi da gaske,makarantarsu daya da nabihat,bata da kirki batason talaka,dagawa gareta da girman kai,hakanan kudinka takeso tosai kayi tsayin daka idan ba haka ba rainaka zatayi wallahi” abu daya ne bata sani ba,hamid mutum ne mai shegen son abun dunuya,yana da dukiya amma ta cinsa ne iya shi kadai,ko sanda yana gida wani abun sai ya rataya a jikin mahaifinsa yayi masa bazai taba qwandala tashi ba,irin yaran nan ne dako.iyayensu basa iya taimakawa banda Allah yasa mahaifin nasa yana da wadata shima,saidai matsalarsa daya mahaifin nasa,mutum ne da bashi da tattali,yana da son nunawa duniya shi wani ne ko nawa zai kashe akan haka zai iya,ya kuma yi nasara don sunansa ya dan fita,sakamakon yadda yake nuna qaryar arziqi don baikai nan ba.
A parlour ya taras da ita zaune tana gunjin kuka,kota kanta baibi ba ya wuce zuwa sama abunshi ya dauki wankanshi.
Minti talatin ya sake saukowa,ya tsuke cikin qananun kaya,yana dannan waya ba tare daya dubeta ba koya kula da kukanta yace
“Ina abinci na?” Shuru tayi masa da fari har na tsahon minti uku
“Ina abinci na!” Ya sake tambayarta karo na biyu cikin qaraji da fushi wanda ya kada mata ‘ya’yan hanji ta soma qwallawa rebacca kira
“Ohkey…..wai na tambayeki mana?,na kawo mai aiki ne donta kula dani ko don ta tayaki aiki?”
“Duka gaba daya” ta bashi amsa cikin bacin rai,cike da fushi yake nuna kanshi
“Ni kike baiwa amsa haka kai tsaye?”
“Waikai hamid me yake damunka ne?,ya za’ayi mu rabu lafiya da kai sannan kazo kana min wasu abubuwa kaman dan qwaya?” Dariya ya saki
“Au bakisan dam qwayar bane ni?,yau zakisan ni cakken dan qwaya ne tunda baki iya zama da miji ba” ya fada a sanda rebacca ta gama jera abincin ta fice,don kusan duk a kunnenta ake komai,zama yayi ba tare daya sake dubanta ba ya take cikinsa da abinci sannan ya miqe yasa kai zai fice,har yayi gaba ya dawo da baya
“Ina canjin cefanen da lado yayi dazu?” Cikin mamaki take kallonshi,a arziqinsa bata taba tunanin zai tambayi wani canji cefane ba wanda baifi dubu daya ba,ita a wajenta dubu daya ba komai bace
“Dubu dayan kake tambayata?”
“Ita ba kudi bace?…ko satowa nakeyi?,tashi malama ki dauko min” bacin ranta da mamakin sauyawar hamid dare daya suka sake yawa
“Bazan bayar ba,wannan wane irin nuna talaici ne?,dubu daya kawai?” Mari ya kai.mata Allah yasa tayi gaggawar kaucewa
“Ni zaka mara hamid?”
“Na nuna miki kadan daga abinda zan iya yine idan har na dawo baki nemo min dubu dayata ba duk inda kika kaita” daga haka ya juya ya fice abinsa,da kallo ta bishi hadi da hawayen takaici,a rayuwarta tunda taje ta taba daukar koda dubu dari ta riqe hamid zai magana akao bare dubu daya?,tunda take rayuwar gidansu ta taba baiwa dubu qwaya daya wani muhimmanci mai yawa?anya lafiya ko hamid yake?,kanta bazai iya daukar wannan abun ba haka ya sanya kai tsaye ta soma kiran lambar mommynta
Tana dagawa mummyn ta fashe da kuka,a rikice mummyn ke cewa
“Ke…lafiya asma’u,me ya faru?”
“Mummy hamid ne…”
“Hamid?,me ya sameshi?” Nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar mata,take mummyn ta cika tayi fam
“Lallai yaron nan mugun dan iska ne,ce masa akayi baiwa aka kawo masa da zaice zai dakeki?,to wallahi daga yanzu ba yarda ba,duk sanda ya sake yunqurin dukanki ki tattara ki taho gida,idan yaso babanki ya masa jan kunne mai qarfi”
“A’h mummy,basai na taho ba,kinsan ma halin daddy baya yarda da irin wannan”tasan sarai ba wai daddyn take dubawa ba kawai,tsabar son miji ne
“Karki sake ki yarda dai ya dakeki wallahi ban lamunta ba,duk abinda ya sake faruwa ki sanarmin don bazan lamunci wannan iskancin ba” da haka suka rabu da mummyn ta aje wayar tana dakon dawowar hamid din.
????????????????
A hankali ta turo qofar falon tamkar wadda ke sanda,idanunsa ya dago daga saman screen din system din da yake aiki akai,qwayar idanunshi wanda suke cikin farin gilashi da yake aiki da shi lokaci zuwa lokaci idan zai jima yana kallon screen ta fito tarwai,saidai ta danyi ja kadan gami da lumshewa saboda gajiya da kuma bacci da yake ji,a hankali ta janye tata qwayar idanun kamar yadda shima yayin ya maida kan screen din,cikin muryarta mai sanyi tayi sallama tana takowa cikin falon,tun dazun ya shigo don shi baima zauna ba a falon bayan sun gama cin abinci ya yiwa anni sallama yace yana da aiki da yawa yau,a can ya barta tana jin caftar su haidar tana kwasar dariya a ciki,ta sake sosai yau saboda rahama bata nan ta tafi gidan qanin anni zata musu kwana uku
“Zo” taji ya fadi sanda take shirin gifta shi,saita dawo da baya ta samu waje nesa kadan dashi ta zauna bayan ta nade qafafunta a qirjinta ta rungumesu kamar wata ‘yar mage,bai dago ba har sai daya kammala tura wani saqo sannan ya rufe cumputer din ya zare gilashin fuskarsa yasa handkherchief ya goge idanun nasa sannan ya dubeta,kusan a tare suka kalli juna kowa kuma ya janye idanunshi,baisan me yasa sau da dama sukan kalli juna lokaci guda ba su kuma janye lokaci guda
“Meye babban burinki yanzu a rayuwa?” Ya jeho mata tambayar kai tsaye,shuru ne ya ratsa dakin tamkar ba kowa a ciki,ya kafeta da idanu yana karantarta,yayin da ita kuma take kallon tafin hannunta tana matsawa kamar wadda yakewa ciwo,abu biyu,abu guda biyu ne yake mata kai kawo a ranta,burinta na farko a duniya ta samu kusanci yarda da aminci na mahaifiyarta,burinta na biyu na biyu shine ta samu ilimi mai zurfi,ilimin da zai sauyata,ya zamewa rayuwarta garkuwa,karatun da tayi har yanzu bataji ta qoshi ba,har yanzu tana da qishirwarsa,har yanzu bata jin ta cimma gaci.
“Mahaifiyata….ina da burin naganni ni da ita tamkar kowacce ‘ya da uwa” sai tayi shuru tana hadiyar zuciya kadan kadan,tana son danne mikin daya taso mata
“Bayan wannan fa?”
“Karatu” shuru ya sakeyi yana nazari,kafin daga bisani ya jawo wata paper ya danyi rubutu ya ninketa
“Kina da jamb?” Kai ta gyada da sauri
“Eh last year nayi,ta na nan”
“Good,kina da zabin makarantar da kikeso?”kai ta kada
“Duk wadda na samu inaso,matuqar dai makaranta ce” kai ya jinjina na tsahon wasu mintuna kafin yace
“Is ohk,zakije wudil?” Kai ta jinjina itama da sauri murmushi na qwacewa daga fuskarta,ganin mafarkinta na nesa na shirin zuwa kusa,burinta na gab da cika
“Ba damuwa” ya fada ta sigar dake nuna ya sallameta,da hanzari ta miqe tayi daki,cike da farinciki ta dira saman carfet din dake gefe guda wanda ta maidashi makwancinta,don ko da wasa bata taba hawa gadonshi ba,murna take sosai ita kadai a dakin,ba don dare yayi ba da ba shakka saita kira aliya ta shaida mata,don ba’a boyewa abokin kuka mutuwa.
Sai data gama dararta sannan ta soma sauya kayan jikinta zuwa na bacci masu kauri da taushi,ta saka dan qaramin hijabin da take kwana da shi wanda iyakarsa qirji ta shiga toilet ta daura alwalar kwanciya bacci(yana da kyau mu kasance cikin alwala a duk sanda zamu kwanta bacci,domin hakan ba qaramin kariya bace a garemu daga sharrin shaidanun mutane da kuma shaidanun aljanu,bama lokacin bacci ba kawai,a wuninmu gaba daya yana da kyau mu dinga zama da alwala,Allah yayi mana tsari,yasa mu dace duniya da lahira amin summa amin).
Tana zaune tana karanto addu’ar bacci taji ana knocking qofar,sai a sannan ta tuna bata rufe ba,tsuru tsuru tayi da ido ita batayi magana ba hakanan bata miqe ba,jin shuru yayi yawa yasanyashi turo qofar ya dubeta yana kauda kai
“Am sorry zan dauki blanket ne” sai kuma ya dawo da kanshi inda ya ganta,zai magana sai kuna ya fasa,ya isa ma’ajiyarsu ya dauki daya hadi da pillow sannan yace
“Me yasa kika zabi kwana a qasa?”
“Babu komai” ta fada a sanyaye,baice komai ba ya juya ya fice daga dakin,ta qarasa addu’arta ta koma ta kwanta ranta fari qal idan ta tuna batun ci gaba da karatunta.
Qarfe shida na safe ta gama shiryawa tsaf cikin lafaya,ta nade jikinta sosai kamalarta ta fito,fatarta data sake kyau da qyalli sakamakon isashshen hutu ta sake bayyana sosai cikin kalar tufafin dake jikinta,ranta fari qal,yau ita daya tasan farincikin da take ciki,duk zumudi ya cikata sakamakon screening da zata wudil,a haka ta fito parlourn ta tadda shi tsaye yana kurbar ruwan dumi a cup,wanda sabonshi ne hakan duk safiya kafin yaci komai,don yana wanke duk wani system na jikin mutum tare da inganta lafiya,ido ya dan xuba mata ganin yadda take ta faman zumudi,fara’ar fuskarta tafi tako yaushe,wanda hakan ya sake bayyana mishi irin yadda take qaunar karatu a rayuwarta,gaidashi tayi ya amsa taci gaba da tsaiwa tana jiran jin me zaice,sai daya gama shan ruwan sannan ya aje cup din
“Ban sanarwa da anni ba….bansan ya zata dauki zancan ba”duk sai taji daukinta ya tsaya,kuzarin data fito da shi ya ragu,dan soma takawa yayi ya nufi qofa a sanyaye tabi bayanshi.
A parlour suka tadda haidar riqe da muqullin mota kamar yadda khalipha ya tsara shi zai kaita,da alama magana suke da anni,dubansu take har suka qaraso cikin falon,aysha ce ta soma gaidata sannan haidar itama ya gaidata,daga bisani ta koma gefe ta lafe tana ji suna gaisawa da khalipha
“Me zasu yi a wudil da safiyar nan?”
“Screening zasu….zan miki bayani anni”
“Screening?” Ta maimaita tana danyi shuru kamar mai nazari,kada kai tayi daga bisani sannann tace
“Haka zaku tafi kenan baku karya ba?”agogo haidar ya duba sannan yace
“Zamu karya a hanya karmu bata lokaci,amma ban sani ba ko anty zata ci wani abun”
“Na qoshi” ta fada da sauri wanda har hakan ya sanya khalipha waiwayowa ya dubeta,yayin da anni ta saki murmushi saboda ta karanci zumudin da takewa tafiyar,duk da bata gama fahimtar tafiyar ta meye ba
“Allah ya kiyaye hanya,saikun dawo” anni ta fada suka juya suka fice khalipha na jawa haidar kunne kan tuqin ganganci.
Dubanta ta dawo dashi kanta,filon dake saman kujerar ya janye mata alamun ta zauna,babu musu ta zauna din tana hade hannayenta waje daya,shima ya zauna daura da ita kansa na dan kallon qasa
“Kiyi haquri anni,naso muyi maganar dake kafin wannan lokacin amma na sha’afa saboda yawan hidimomin dake shigo min…..na samu wata dama ne daga wani kamfani dake da reshe a mafi yawancin qasashen duniya….to amma wannan dama daci gaba ba zasu tabbata min ba har sai na sake qaro karatuna,wanda hakan zai zamemin kamar jifan tsuntsu biyu da dutse daya ne,zan kai wani mataki mai girma cikin reshensu dake qasar nan,sannan namu kamfanin zai sake samun ci gaba da daukaka da yardar Allah,karatun duka zai daukeni ne tsahon shekara biyu….mun dauko humaira daga ainihin inda suje ruqonta don mu samawa rayuwarta nutsuwa jin dadi da kuma ci gaba,sai na tattauna da ita game da meye burint,ta sanarmin karatu ne,hakan ya sanya nayi tunanin me zai hana na maidata makaranta yadda take da buqata,nq bata zabi ita da kanta ta zabi waccar makarantar,tunda dama can ta cike first choice da second choice dinta,dalili kenan da yasa na tura ta can din….amma nasan hakan bai kamata ba,ya kamata na fara yin magana dake kafin duka na yanke wadan nan abubuwan” kai ta jinjina,ta tabbatar duk abinda khalipha zaiyi yana zurafafa tunaninsa kafin yanke komai,hakanan baya aiwatar da komai saida dalili,sannan tunda suke ita da shi bai taba yanke wani hukunci ba tare daya shawarceta ba,bai kamata don an samu akasi a wannan karon ta manta baya ba ta tuhumeshi
“Tunda har haka takeso babu damuwa,Allah ya bada sa’a ya taimaka,saidai kai din kar ka manta cewa da da yanzu ba daya bane,zaka tafi har tsahon shekara biyu wata uwa duniya?”
“Zan dinga zuwa duk sanda aka samu chance….”shuru ta sakeyi sannan daga bisani tace
“Shikenan..amma dai kayita istikhara ka barwa Allah zabinsa,idan alkhairi ne dukkan abubuwan daka zayyana Allah ya tabbatar da su,idan babu alkhairi kuma ina roqon ubangiji yayi maka musaya da mafi alkhairi,sannan kayi shawara da matarka”
“Amin ya Allah anni na gode…Allah ya jiqan magabata”
“Amin amin”
“Zan shiga ciki inason na sake hutawa kafin goma na wuce office…”
“Allah ya nuna mana” har ya miqe ya soma taku ta kira sunanshi,dawowa yayi da baya ya zauna hannun kujerar daya tashi a kai
“Khalipha…na baka shawara?” Cikin mamaki ya daga kai yana duban annin,lafazin nata ne ya dan bashi mamaki,kai ta kada
“Qwarai kuwa shawara,domin kuwa abinda ya shafi rayuwarka ne kai kadai” sai ya samu kanshi da kada kai
“Ka riqe aysha da kyau,don ina tsammatar ita din matar aure ce ta gari irin wadda kowanne namiji yakeso” iya abinda ta fada kenan taja bakinta ta tsuke,ya tabbata ta fadi hakanne ta bar mishi saura yaje yayi nazari a kai
“In sha Allahu” kawai ya fada yayi mata godiya ya miqe ya fice.
Har ya nufi sashensa sai ya sauya akala zuwa sashensu haidar,ya tura qofar ya shiga ya ratsa falonsu sai ya wuce dakin mus’ab,yana kwance dai dai saman abun sallah yana kwasar bacci abinshi,da alama yau baije masallaci ba a daki yayi sallah,hannu khalipha yasa ya daka masa duka a qeyarsa,miqewa yayi a zabure da har zai soma masifa ga zatonshi haidar ne sai kuma yaga khalipha tsaye a kanshi hannayensa harde a qirjinsa yana dubanshi,kai ya sadda yana gyara zamanshi
“Wato duk fadan da nake maka kan salla bisa jam’i baka ji ba ko?”qeya ya soma sosawa cike dajin nauyi da kunya
“wallahi ya khali….”
“Shutup…..kasan muhimmancin sallar asuba da isha’i a jam’i kuwa?,annabi S A W yace idan kaga sallolin nan guda biyu sune mafiya nauyi akan munafukai,suna yiwa munafuki wuya da nauyi, sallar asuba da isha’i,sannan ya sake cewa da mutane sunsan me yake cikinsu da sunzo musu koda dajan gindi ne…ka shiga taitayinka,karka sake ka shiga sahun wadancan mutanen,annabi S A W a lokacinsa yace badon mata da yara dake cikin gidajen wadanda basa halartar sallah asuba ba,da ya umarci wani yaja mutane sallah,shi kuma ya dauki itace ya zagaya gidajensu ya kunna musu wuta,ibn ummu makhtum mai yiwa annabi kiran sallahn farko makaho ne,ya nemi uzuri wajen annabi S A W kan bashi da d’an jagora,sannan hanya akwai kwazazzabai a hanya shin ya iya zama a gida yayi sallar asubarshi?,har annabi ya bashi daman ya zauna har ya tafi yayi kiranshi ya dawo,ya tambayeshi daga gida yana iya jiyo kiran sallah?,yace masa eh,yace to lallai lallai dole ya taho masallaci ya halacci sallah cikin jam’i,saikai da baka da wuni uzuri?,saika kai sha biyu na dare kan waya daya na dare,ka kasa tashi sallar asuba wace hujja zaka gayawa Allah” sosai jikinsa yayi sanyi,a hankali yace
“In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba ya khalipha nayi alqawari”
“Ka kiyaye karna sake ganin irin haka ya faru,kada na sake zuwa masallaci ban ganka ba”
“In sha Allahu” ya fada cikin nadama
“Ka tabbatar ka fito qarfe goma zamu fita ni da kai,haidar ya wuce wudil,karka sake na rigaka fitowa” ya fadi yana bude qofar fita daga dakin
“In sha Allahu yaya” daga haka ya fice zuwa nashi dakin.
Koda ya shiga ya cire jallabiyyar jikinsa ya kwanta don ya sake ri tsawa sai ya kasa,maganganun anni ke dawo masa,ya kasa gane ina ta dosa,duk wata kulawa da yayi alqawari yana baiwa ayshan,ba wata takura cikin rayuwarta sam,ya kasa gano komai haka bacci yaqi daukarsa,dole ya haqura ya miqe ya sauya kayan jikinsa zuwa wanda yake amfani da su idan zai shiga gym dinshi ya fice zuwa dakin motsa jikin.
_Ya Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan_????
*mrs muhammad ce*??
[3/7, 7:28 PM] Binta Mustapha: *_KIBIYAR AJALI SULKE BA YA TSARE TA SAI TA WUCE._*??