Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 7

Sponsored Links

0?7?

 

Bayan ta kammala sallar tana zaune saman abun salla,yaran gidan na shigowa da daya da biyu,wasu tana nan aka haifesu wasu bata nan,wasu ta tafi a sanda suke da qananun shekaru wanda zuwa yanzu sun girma,sa’anninta kuwa suka taso tare wanda taci wuya wajensu yanzu babu kowa cikinsu,kowacce tayi aure tana gidan aurenta da yaranta,duk yaron daya shigo bata rasa dan abinda zata bashi,a haka har uku na rana ta kusa ba wanda yabi ta kanta,sai bayan ukun sannan innan ta tura mata wata langa wadda ke dauke da shinkafar hausa fara qal da man gyada da yaji,ta dan soma curewa waje daya saboda tayi sanyi sanyi,bata damu ba ko dama can ita ba mai damuwa bace taja ta tsakura ba da yawa ba ta rufe kwanon,inda Allah ya taimaketa a halittarta ita din ba ma’abociyar son cin abinci bace,lamarin daya taqaita wahalarta qwarai da gaske a shekarun baya da suka shude.

Related Articles

Mayafinta ta rataya tare da maqala ‘yar jakarta bayan tasha ruwa ta wanke hannunta tana duban innar
“Inna zan qarasa gidansu inna kulu” wani kallonta watsa mata sannan tace
“Zaki dai je ganin uwarki ko?,uwar da bata damu da rayuwarki ba” Kanta ta kada can qasar zuciyarta tana jin babu dadi,komai lalacewar uwa uwace,sam bata jin dadin kalaman dake fitowa daga bakin inna kulu ko yaushe akan mamanta,batasan wanne irin rashin jituwa bane haka a tsakaninsu tsahon shekaru tun tasowarta amma har yau bata sauya zani ba
“Bansan ma sunzo ba inna,zanje na duba jikin kawun ne” baki innar ta tabe tana ci gaba da abinda take ba tare data tanka mata ba,har ta gaji da tsaiwa haka nan taja jikinta a hankali ta fice daga dakin ba tare data sake cewa komai ba itama.

Wannan karon tsakar gidan nasu babu jama’a sosai sai yara jefi jefi,kowacce tayi sashinta masu wankan da ba’a yiba tun safe nayi,da masu shara da wanke wanke,ba zasu sake hallaraba wajen ba kuma sai bayan sallar la’asar,hakan shinya bata damar ficewa hankali kwance daga gidan ba tare data sake jin wani abu da bazaiwa kunnuwanta da zuciyarta dadi ba,tun tasowarta haka taga gidan nasu,wannan zaman dai sai an yishi a kulli yaumin.

Da gudu yaron ya biyo tayarsa da yake garawa wadda bata tsaya ko ina ba sai gaban aisha,dafe tayar tayi ta daga kanta tana duban yaron,kallo daya ta masa ta tabbatar jininsu ne,don yana kama da umminta sosai,kana dubanshi kasan daga duk inda ya fito ba waje bane na wahala,sanye yake da wando da t.shirt wadda ta dace da kayan nashi,duk da sun debi qura da jar qasa kadan sanadiyyar wasan da yake faman yi babu ji babu gani amma kana kallonsu kasan masu tsada ne,kallonta yayi sai ya dauke kai yaci gaba da gara tayarsa alamar bai santa ba,ita dinma bata sanshi ba,amma bata tantama shine yaron data ji labarin ummin nata ta haifa bayan shekararta daya da komawa gidan daddy zuwanta na farko ziyara qauyen
“Laaaa,anty indo” taji an ambata qasa qasa,waiwayowa tayi tana duban mai kiran sunan nata,wanda tasan masu kiran nata da wannan sunan wasu kebantattun mutane ne.

Basma ce wadda a qa’idance zata kira da qanwarta,saidai a zahirance kai ba zaka ce qanwar tata bace musamman a shekarun baya da suka shude,gwara a yanzun da yanayin rayuwarta data basman ta saje,mutane da dama wadanda basu sansu ba kan sheqe da dariya idan ta nunata tace qanwarta ce saboda banbancin yanayi na rayuwa da tazara mai tarin yawa a tsakaninsu,saidai a yanzu da rayuwa ta soma zuwa mata da wasu daga cikin sauye sauye zaka gasgata cewa qanwarta ce karon farko saboda yanayi na daidaikun kamanni data dan debo nata.

Fuskar yarinyar qunshe da murmushi kamar yadda fuskar aysha ki cike da fara’a ta qaraso gabanta ta kama hannayenta
“Anty indo dama kina nan?,yaushe rabon dana ganki anty?,tunda kika koma inda kike sai a dade ba’a ganki ba me yasa?”
“Inda na koma din ba cikin garin nan bane basma,kuma makaranta nake zuwa bako yaushe nake da lokacin zuwa ba….yaushe kuka zo?”tayi dukka maganar tata cikin fara’a
“yau kwananmu uku,gobe ko jibi abbu zaizo ya daukemu” cike da zaquwa tace
“Harda ummi?” Kai basma ta kada
“Harda ita,tana cikin gida ma,shigo muje ki ganta”ta fada tana dan jan hannun ayshan, faduwar da gabanta yayi shi ya tilasta mata lumshe idanunta kafin daga bisani ta budesu,Allah ya sani tana sonta,tana son ganinta,tana son ta rabeta,amma bata san me yasa duk bata da wannan damar ba,batasan me ya haifar da wannan babban gibin da baraka dake tsakanin dangantakarta data mahaifiyarta ba da kuma gidansu mahaifinta,a hankali ta bude idanun ta dafe hannun basma dake cikin nata
“kije zan shigo,kinsan me zai biyo baya idan ta ganmuntare aiko?” Fuskarta a bace ranta a hade ta kada kai
“Shikenan,amma don Allah anty karki koma ki shigo din”
“Yanzun nan kuwa kada ki damu,zan leqa gidan mero ne”.

A haka suka rabu ta shiga layin gidan meron,tayi hakanne kuwa don tana jiyewa basma hukuncin da zai biyo baya idan ummin ta gansu tare,ba qaramin aiki bane a wajentan ta lakada mata dukan da zata ji a jikinta,tunda tun kafin takai hakan take dakuwa wajenta matuqar zata gansu tare,ko zata ga ta bata wani abu,wani lokaci idan ta tsawaita tunani kan wadan nan cakudaddun al’umaran takanji kanta tamkar zaya tsage,bata da amsa bata kuma da mai bata amsar,sai tarin tsana da tsangwama da take fuskanta aduk sanda tayi yunqurin tambayar wani makusancin lamarin kan meya faru a baya?,meye sanadi?,mai ya haifar da haka,wasu sukanyi gaba su barta a nasu tunanin tasan komai,tsabar rainin wayo ko wahala ce ta soma taba qwaqwalwarta,da wannan tunanin na tsohon shafin rayuwarta ta qarasa gidan qawarta ta quruciya wato mero.

Cikin farinciki suka rungume juna ita da mero,da qyar suka samu wajen zama kowa na zumudin ganin dan uwansa,abota ce da ba zasu taba mantawa da ita ba,abota ce data yiwa aysha rana,abota irin wadda ta kasa samunta daga yan uwanta a wancan lokacin
“Indo….ashe komai na rayuwa mai wucewa ne…kin ganki ko indo kin zama matar birni,don ma har yau babu qibar da kika qara” mero ta fada tana kama habarta,qaramar dariya aysha ta saki tana kada kai
“Mero har yau halayyarki ba zata sauya ba kenan….komai na rayuwa mai wucewa ne mero,amma banda abu guda,wanda bana tsammanin zai wuce” ta qarashe maganar fara’ar fuskarta na raguwa,da alamu maganar da take cikin zuciyarta ta taba ranta sosai,hannu meron ta aza bisa kafadar aysha tana cewa
“Ba abinda ke tabbata a duniya sai ikon Allah indo,kici gaba da sakawa ranki salama,kici gaba da sawa ranki cewa watan watarana zai zama labari tamkar ba’a yiba,umminki mutum ce kaman kowa,zuciyarta na hannun ubangiji,kuma yana da ikon sata ta sauya aduk sanda yaga dama koda bata so yin hakan ba” cike da gamsuwa take gyada kanta gami da sanya yatsunta ta dauke qwallar data sauko mata,zuciyarta na samun nutsuwa da kalaman mero
“Haka ne,na gode qwarai Allah ya qara zumunci”
“Ba wannan tsakaninmu indon baffale,yanzu mutuminki zan dafa miki ko kuwa?,yau ban dora sanwa ba a gidan nan duka yaran suna gidan gwaggwan habu shi yasa ban dafa komai ba” dariya indo ta saki saboda tuno wani abu da tayi
“Hoooo,meron habuwalle,bada kanki a sare…waima yana ina” dariya mero ta saki
“Zaku taba diramar taku ne?,yau tun safe ya tafi hungu ina jin kuma bazai shigoba sai gefin magariba,amma ai tunda kina nan zaku hadu ne” ta fada tana yunqurin tashi
“Kinga yi zamanki karki wahal da kanki,ban jima da cin abinci ba na fito” komawa tayi ta zauna tana dubanta
“Wanne abinci ko muna abinci,sun baki wannan busashshiyar shinkafar tasu da ke kika jima da yin bankwana da cin irinta,ni bansan meke damun jama’ar gidanku ba,ga arziqin abinci gar abinci amma su basu raba kansu da cimar da kowa cikin karkarar nan ke fatan bankwana da ita ba” dariya aysha tayi kawai tana jin mitar mero,itadai indai aka taba indo tofa za’aji kansu da shi koda waye ma,zata iya cewa su biyu ita da aliya bata taba samun soyayya kamar tasu ba,tabbas idan wani ya qika wani zai soka haka rayuwa take.

Ledar data zabo mata atamfofi cikin nata ta miqa mata,ta daga tana ta murna da godiya,duk da cewa bata rasa komai gidan mijinta ba,habu mutum ne mai zuciyar kula da iyali wanda irinsa daidaiku ne cikin karkara a halin yanzu.

Sun dan jima suna hira sannan sukayi sallama da alqawarin gobe idan bata samu taje gidan gwaggwo asabe zata dawo susha hirarsu.

Tamkar mara gaskiya haka ta dinga taka dogon soron gidan kakannin nata,ba komai ya haifar da hakan ba illa tunani da zaton mahaifiyarta a halin yanzu na cikin gidan,tsakar gidan fetal yake babu kowa,bata ji motsi ko hayaniyar kowa ba,hakan shi ya sake bata qwarin gwiwar kutsa kai cikin gidan bakinta dauke da sallama,inna kulu dake qasan rumfar da suke girki ce zaune gaban murhu tana ta aza wuta bisa dukkan alamu wani abu mai buqatar wuta da yawa take dafawa,waiwayowa tayi tana amsa sallamar kafin daga bisani ta dan washe fuskarta tana fadin
“Indo….yaushe kika shigo garin?”
“Wallahi inna dazu dazun nan”
“To maraba,qarasa daki nima gani nan tasowa”
“Toh” ta amsa idanunta na satar kallon kebantaccen dakin da tasan cewa mahaifiyarta na sauka ciki duk sanda tazo garin,dakin a bude yake saidai an dan karashi hakan yasa ba zata iya gane da mutum ko babu ba da haka ta sanya kanta cikin dakin inna kulu dake falle daya dauke malale da leda da labulaye gami da lailayayyen gadon qarfe da doguwar kujera qwaya daya wanda dukkan wannan gyaran aikin ummin nata ne.

Tana shirin zama gefan gadon inna yelwan qamshin turaren ya ziyarci hancinta,qamshi ne data san cewa ba irin wanda inna kulu ke amfani da shi bane,hakan ya sanya ta soma baza idonta cikin dakin,tashin farko jikinta ya soma rawa har ta kasa hayewa saman gadon qarfen mai tudu wanda ya sha katifa,ta zame baki daya zuwa qasan ledar dakin ta zube ragwaf cikin rawar jiki,umminta ce zaune kan kujera qwaya daya dakin,sanye take cikin wani legos lace mai kyau da tsada peach wanda aka yiwa dinkin buba qarama da plain zani,hannunta sanye da awarwaro da zobe,haka wuyanta da kunneta sanye da sarqa da dan kunne,tayi fresh tayi kyau fiye da yadda ta santa ma ashekarun baya,tunda aqalla yanzu ta kusa shekara biyar rabon data sanyata a idanunta,daurin dankwalinta dai dai da zamani,idanunta na kan wayarta qirar samsung torching dake hannunta tana shafawa,cikin rawar murya ta hada lafazin
“Ina wuni ummi….” Shiru taji kamar yadda ta zata,tamkar babu wata halitta a dakin bayan ita,ko motsi ummin bata yi ba bare ta saka ran amsawarta,kai ka rantse da Allah bata san akwai halitta cikin dakin ba
“Ummi bar….ka da yamma….an yini lpy?” Ta sake maimaitawa,saidai kaman waccan karon wannan karon ma ko motsi bata yiba bare ta amsa,abu guda ne ya banbanta yanayin shigowar ‘yan matasan yara maza guda biyu a guje daya yana bin daya cikin dakin suka afka jikinta suna rigima kan wani abun wasa,sai sannan ta dagonta rungume wanda ya fado jikintan tana duban babban dake tsaye
“A’ah,a’ah abba yaya?,bana hanaku irin wannan guje gujen bane wai?”
“Ummi…..”
“Kul na sake jin wannan sunan a bakinka”
“Mami nawa ne fa,ya bar nashina gida tun shekaran jiya da zamu taho na sakoshi cikin trolly na,shine yanzu ya dauke yace wai nashi ne”
“Shine zaka biyoshi haka?,bana son sakarcin banza…oya maza wuce daki kaje ka canza wadan nan kayan daka bata” ta fada tana ware masa idanu,haka nan ya juya ya fita yana cuno baki,shi kuma wanda ke jikintan yana ta dariya abinsa alamun ya samu nasara.

Idanunta ta maida kan basma daketa kallon aysha dake takure gefe guda kanta a qasa tana son yi mata magana amma tana shakkar ummin tasu,tsawa ta katsa mata
“Fice a gun,kar na sake ganin qafarki tsaye a wajen nan”
“Amma mami……”
“Ubanki nace….kama hannun yusra ku wuce daki ki gyara sauran kayanku da baki gama hadawa ba” kamar zata fashe da kuka haka basma matashiyar dake da shekara goma sha hudu ta kama hannun qanwarta dake da shekaru goma suka fice,sai data ga ficewarsu sannan ta daga yasir dake jikinta ta kama hannunshi suna niyyar ficewa a dakin,sai a sannan aysha ta daga kanta tana duban mahaifiyar tata da idanunta dake cike fal da qwalla,cikin rawar murya tace
“Ummi….ki yafemin don Allah duk abinda nayi miki…wanda na sani da wanda ban san……”
“Idan kika qara yimin magana Allah ya isa ban yafe ba” ta fada cikin tsawa sannan taja hannun yasir,cike da tsantsar tashin hankali ta bita da kallo qwalla na silalo mata suka ratse inna yelwa dake tsaye da kwano a hannunta
“Kuma ga naman naki binta”cewar innar
“samin a daki na” ta fada tana yin gaba,haka nan ta juya kuwa tabi bayanta.

Sanda ta dawo har aysha ta gama cin kukanta ta gode Allah,sai tuquqi da zuciyarta ke mata kadai,muryarta a shaqe suka gaisa da inna yelwa,ta kuma tambayeta jikin kawu ta sanar mata da sauqi,ko kadan bata tada zance abinda ya wakana tsakaninta da umminta ba,wannan ba shibe karo na farko ba da irin hakan ta taba faruwa ba,shi yasa sam aysha batayi mamaki ba,inna kulu na haka ne saboda ba ita ta haifi umminta ba?,koko tana haka ne saboda alkhairin da take samu daga wajen ummin nata kada ta yiwa kanta sanadi,saboda ta sani tsaf zata yanke duk wani alkhairi da take mata matuqar zaka shiga maganar data hada da ayshan,biyayya kusan duk wanda yaga yadda take mata za’a ce takewa binta,wanda hakan kusan kowa ke ganin bai rasa alaqa da abun duniya da take samu daga wajenta,zuciya da jikinta duka babu dadi hakan ya sanya bata iya tsaiwa taga dawowar kawu ba bare ta dubashi tayi sallama da inna yelwa da zummar ta dawo gobe.

Tana tafe tana share hawaye,sam bata ka biyo ta hanyar da jama’a suke wucewa sosai ba don bata da buqatar tsayawa tayi magana da kowa,kasancewar tunaninta bai tare da ita hakan shi ya bashi nasarar shan gabanta ba tare data lura ba,sai jan baya da tayi da sauri sabida ganin inuwar mutum a gabanta ta hasken farin wata,a nutse ta qare masa kallo haqoranshi a waje kamar yadda ta sansu yana washe mata baki shi a dole fara’a
“Indo matata…..yau a gari?” Kalma mafi muni data tsana taji ta kenan daga bakin dan ladin tun a shekarun baya zuwa yau,bata taba ganin dan akuya mara kunya irinsa ba,tun a baya neman tsari take da shi balle a yanzu da ta soma samun sa’ida da sauqin wahalar rayuwa,ta kuma san inda duniya ta dosa,bata iya amsa masa ba illa ce masa da tayi
“Dan matsa min malam na wuce sauri nake”
“Haba indo,yanzu fusabilillahi ke ba zaki haqura ki karbeni a matsayin miji ba kije ku zauna tare da ‘yar uwarki,naga dai ‘yar uwarki ce,abu shekara da shekaru amma kin kasa haqura,duk abinda na dinga yi miki sharrin shaidan ne da zuciya” bacin ransa da wanda ta qunso ya taso ya tokareta,cikin zafin nama da zafin zuciya ta kewayeshi fuu tayi gaba,binta yaci gaba da yi yana magiya saidai banza ma ta fishi a wajenta,don sam bata masa kallon mai hankali,ta sani cewa tsantsar kidahumanci da jahilci kadai sun isa su maidashi mahaukaci tuburan,bare ga shegiyar mai saurin tarwatsa rayuwar koma waye wato qwaya da yake afawa lokaci lokaci,bata taba zaton inda yana da cikakken hankali zai iya tararta ya dubi qwayar idonta ya mata magana ba,bai qyaleta ba sai da yaga shigarta cikin gida sannan ya haqura ya juya yana jin takaicin rasa indon da yayi,tana qiyasta yadda tayi kyau ta goge da tuni yana can yana mora,yanzu gashi yana can yana fama da ladidi.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 8:49 PM] Binta Mustapha: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER ( 08030811300)_*

*DAURIN BOYE*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button