Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 10

Sponsored Links

PAGE 10

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

Related Articles

LITTAFIN GARKUWA NA KUƊINE, TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta number 09097853276 domin samun cikekken labarin, ko kiyi min transfer ɗin 1k ɗan samun SP GROUP ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276

FREE PAGE

Cikin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ya Ba’ana me wannan, abu kamar macizai”. Da sauri ya meda ya rufe kana ya miƙe cikin yin ƙasa da murya yace.
“Kinga ni kada ki tayarmin da hankali kinsan bana son ganinki cikin tashin hankali, in sha Allah nine da nasara ko dai bakya so nane”.
Da sauri ta girgiza kanta tare dasa tafin hannunta ta rufe bakinta.
Ganin haka ya kwashi abinshi ya tafi.

Ita kuwa koda ta shiga gida, gefen Inna ta zauna tare da cewa.
“Inna ku cewa Bappa ya cewa Arɗo ya hana gasar nan, kada a cutar da Ya Salmanu”.
Cikin sanyin jikin da duk kwanan haka inna ta zama, a hankali tace.
“Uhumm ba komai Shatu in sha Allah duk abinda zai faru da sanin Allah.
Yanzu ke yaushe nema zaki koma hutunmu?”.
Kanta ta gyaɗa a hankali tace.
“Rana ita yau zan koma kimga saura mako ɗaya kenan”.
Ummey ce dake gefe ta ɗanyi ajiyan zuciya gami da cewa.
“Alhamdulillah ni in kin komama hankalinmu zaifi konci, domin muddin kinanen sai Ba’ana yayi ta kalato fitina”.

Shiru sukayi baki ɗayansu, jin an fara kiran sallane tasa, duk kowa yayi al’wala haraman salla.

A daren ranar kuwa Ya Salmanu da abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za’ayi kuma tunda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.

Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
Haɗuwa a filin da za’ayi shaɗi.
Mutanen sun cika maƙil dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.

Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan Arɗo Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman Arɗo yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa.
“Haƙiƙa naso a janye wannan shaɗi, domin nasan abun bazaiyi daɗin ganiba ace Ba’ana na zane Salmanu ɗan Arɗo ga wannan rugar, amman kaƙi ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda ɗana yayiwa ɗanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taɓa samun wanda zaifi ƙarfin ɗanaba”.
Shiru Arɗo Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi Arɗo Yabani yace.
“Duniya da faɗi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za’a samu wanda zaifi ƙarfin ɗan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin ɗan ka”.
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
“Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taɓa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu”.
Wani dogon numfashi Arɗo Yabani yaja tare da cewa.
“Uhummmmmm”. Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaɓe rigarsa ya juya ya tafi yana faɗin.
“In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira”.
Da ido Arɗo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam Chuɓaɗo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya ɗan matso kusa da Arɗo a hankali yace.
“Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba’ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaɗai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba’ana ya gudu”.
Murmushin da yafi kuka ciwo Arɗo Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
“Kuje Salmanu, Allah ya bada sa’a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, taƙadiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa’a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faɗawa auren wannan azzalumin”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa Arɗo, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba ɓata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaɗi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ƙabulun, Ɓachamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu taƙadiri sama da Ba’ana sabida tunda ake gasar Shaɗi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba’a taɓa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya ɗaga hannun to babu mai ɗagawa.
To sanadinshi aka hana Shaɗi a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba ɗaya Rugar Bani ta cika maƙil da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za’a gobza yanata rere kirari wa Ba’ana.

Isowar su Arɗo yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ƙa’idar gasar Shaɗi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ƙetare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya ɗauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za’a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaɓi wanda takeso, don anada yaƙinin duk wanda ta zaɓa, zai iya kare kanshi tunda ƙarfinsu yazo ɗaya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ƙa’idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba’ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa ɗinnne.

To dole a ƙa’ida Ba’ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.

Nan kuwa take al’kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaɗi na cikin tanɗun masarautar Arɗo Yabani wanda an ƙara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya miƙa wa Salmanu, bulalin,
kana ya ɗaga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba’ana.
Shi kuwa Ba’ana tsayuwa yayi ƙam tare da ɗan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya ɗan ja da baya,
kana ya tattaro ƙarfin shi ga ba daya, ya ɗaga kitsetsten bulalan nan, ya taƙarƙara ya zabgawa Ba’ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba’ana, ƙim ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ƙebtaba.
Sake taƙarƙarewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ƙabilar ɓachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ƙarfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ƙarfinshi yake kware baki yana cewa.
“Ɗaya! Biyu! Uku! Huɗu! Biyar! Shida! Bakwai!!!”.
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba’ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

Ƙa’idar bulalin shaɗi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ƙarfinsa yana zabgar Ba’ana, yana tsaye ƙiƙama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba’in da takwas ko gezau.
Gaba ɗaya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ƙarfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50″.
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ƙabilar ɓachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban Arɗo yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba ɗayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ƙarfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba’ana yayi tare da gyara riƙon da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya ɗan koma da baya, kana ya ɗago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi, gaba ɗaya inda bulalar ya taɓashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buɗe idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faɗo ƙasa, ci gaba da irgens yayi.
“Ashirin da uku! Ashirin da huɗu!!”.
Wani irin tsalle Ba’ana ya buga da iya ƙarfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba ɗaya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son ɗaukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faɗi.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
“Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu”.
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan Arɗo Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiɗe domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.

A can wurin gasar Shaɗi kuwa, ganin tuƙuru Ba’ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin ɗin ƙa’idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ƙabilar ɓachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wuƙa.

Lokaci ɗaya wurin ya hargitse gaba ɗaya.
Aka kaure da faɗa saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ƙabilun Ɓachamawa suka gudu.
Allah ya takaita faɗan baiyi nisa ba, a take ɗaya daga cikin police ɗin wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ƙanin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar ɗan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sauƙi.

Shi kuwa Ba’ana daga nan izayarsa ta ƙaru manufarsa shida ƙabilar ɓachamawa shine. Su tarwatsa al’ummar fulanin Rugar Bani baki ɗayansu.

Zuwa yanzu kuma ko ƙudane in dai na mijine to bazai sauƙa kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.

Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.

Yau kwana huɗu da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma’a ne.

Kasan cewar jummace yasa gaba ɗaya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam’in sallan jumma’a.

Iro ɗaya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haɗu da gungun matasan Ɓachamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
“Kai ɗan fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?”.
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
“Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani”.
Cikin mugunta ɗaya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi”.
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
“Kada ka sake dukana”.
Kusan a tare suka haɗa bakin wajen cewa.
“In mun dakeka sai me?”.
A kufule yace.
“Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba”.
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da ɗan lenge-lengen saurayi matashi ɗan Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, ɗaya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ƙugunshi, da ƙarfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wuƙan a cikinsa wani irin ƙara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma’a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda suka daddatseshi da wuƙa.
Daga nan suka kira Ba’ana a waya, nan take ya kaɗa shanayen yace. “Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza’a zargekuba”.
Haka kuwa sukayi, suka kaɗa kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce ɗakinsa bayan ya bawa uwarsa lbri.

Koda aka taso sallan jumma’a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la’asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ƙara tashi.
Cikin kiɗima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba.

Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji,
Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini.
Nan suka ɗauki gawa suka koma cikin gari dashin.

Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba ɗaya ma sai ba’amaida hankali kam ɓatan shanunba,
Hankali ya tashi, ɗauki ɗai-ɗai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin,
Gashi kisane da babu wanda za’a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case ɗin, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers ɗin shiyasa suka korasu da batun.
Salmanu wanda shine ɗan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ƙarƙashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba’ana ya kasheshi.

Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka Arɗo Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan ɗin, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero.

Koda sukaje masarautar Numan ɗinma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu.

Dole suka dawo suka nade hannun suka kai kukansu ga, Allah, sai dai sun ɗauki mataken kare kai da kai, bisa shawarar daddatawa cewa kada makiyayan ko manoma su yarda su rinƙa rabuwa a daji ya zama suje tare su dawo tare da hakane zasu gane mai ke musu ɗauki ɗai-ɗai ɗin.

Yau la’hadi tunda safe, Aysha keta shirin komawa makaranta. Sabida hutunsu ya ƙare.

Tafiyan safe takeso tayi shiyasa ta gama shirinta da wuri.

gaba ɗaya suna tsakiyar gida Yayunta maza sune zasu rakata bakin hanya.

Haka nan taji bata son tafiya ta barsu, tsoro mai yawa ya rufeta Especially in tayi tunani da yadda ake kashe makiyayan.

Durƙushe take gaban Bappa yana yi mata masiha mai ratsa jiki da zuciya ya kare nasihar tashi da cewa.
“Allah ya miki al’barka Shatu, Allah ya kaiki lfy.”
cikin sanyin murya tace.
“Amin Amin Bappa ngd matuƙa”.
Sai kuma ta kalli Ya Giɗinta da ya zuba mata ido tamkar bai taɓa ganintaba, cikin sanyin murya yace.
“Yanzu shike nan zaki tafi ki barmu, ki tafi can ke ɗaya ki zama baki da kowa naki a kusa”.
Haka nan kalamanshi ya karyar mata zuciya, sai kuma taji hawaye nason zubo mata.
A hankali tace.
“Ya Giɗi bazan daɗe ba zanzo”.
Cikin sanyi Seyo yace.
“Allah yasa ki samemu in kinzo ɗin”.
Da karfi ƙrjinta ya bada wani sauti mai karfi, ta buɗi baki zatayi mgna kenan Ya Lado ya ɗanyi murmushi cikin sanyi yace.
“To Shatu Ni zan tafi inje in kunce dabobbin, bazan samu daman rakakiba, Allah ya kaiki lfy, ya ƙaddara saduwarmu kan al’khairi, ki yafe”.
Kawai sai taji hawaye na zubo mata, cikin dariya ya Gaini yace.
“To kunga kun sata kuka, Shatu ko dai bakya son komawane?”.
Cikin rawan murya tace.
“Inaji bana son rabuwa daku”.
Murmushi inna tayi tare da cewa.
“Ai kuwa dole ki rabu damu, domin lokaci yazo”.
Ummey dai ido ta zuba musu.
Shi kuwa Ya Lado da murmushi a fuskarshi ya fita yana ɗaga mata hannu.
Bappa ne ya ɗanyi murmushi cikin sanyi jiki yace.
“Maza tashi ki tafi, ki gaida Aminiyarki Rafi’a, Seyo Giɗi Gaini ku rakata har bakin titi”.
Da sauri suka miƙa.
Ita kuwa Aysha kamo hannun Junainah tayi wacce tayi kasake tana kallonta cikin sanyi tace.
“Ƙanwaliya, sai na dawo”.
Kai ta gyaɗa mata cikin sanyin da sam ba ɗabi’arta bane a hankali tace.
“Addana, bana son ki tafi”.
Shafa kan Junainah tayi, kana ta faɗa jikin Inna, tana zubda hawaye, sake Inna tayi sannan ta faɗa jikin Ummey, murya can ƙasa Ummey tace.
“Tashi ku tafi, Allah ya sadamu da al’khairi, Shatu”.
Da kuka ta fita, ta barsu jiki a mace.

A hankali suke tafiya tafiya, suna hira, kayan lambu da suka cika mata bakko dashi na hannun Giɗi, jarkan nonon kuma na hannun Seyo, ya Gaini kuma, jakar kayantane a hannunshi, da kwaryan kwan zabbi, kamar dai yadda suka saba, suna tafe suna, hira suna gab da bakin hanya.
Ba’ana ya isosu aka ci gaba da tafiyar,
suna isa motar da zata wuce cikin Yola (Ɓadamaya) na isa,
saida suka samata kayanta, kafin, tazo har zata shiga taji Giɗi na riƙe da hannunta juyowa tayi ta kalleshi cikin murmushi yace.
“Kinsan abinda zamu iya aikatawa a duniya da abinda bazamu iya aikatawaba”.
Kai ta gyaɗa mishi alamar eh, murmushi yayi kana yace.
“To ki ƙara yarda zamu zamu zama GARKUWA’nki muddin muna raye.”
Murmushi tayi cikin ɗan jin daɗi tasan akan mgmar auren Ba’ana yake nufi.
Ido ta zubawa Ya Seyo shi kuma sai murmushin shi nan yake mata,
Ya Gaini kuwa hawayene ya cika masa ido shiyasa ya juya ya bata baya.
Cikin sanyi Seyo ya matsota kana a hankali yace.
“Ki sanarwa duniya halinda muka ciki in kin samu dama Aysha, ki sanarwa duniya Fulani ba ƴan ta’adda bane ba ƴan bindiga daɗi bane ba kuma ƴan Garkuwa da mutane bane, wasu kesa rigar Fulani ke wanzar da ɓarna da wasu ƙalilan na mugayen daji.”
Cikin rauni ta zuba mishi ido tana kallon kekyawar fuskarsa, da gyaɗa mishi kai.
Ba’ana ne ya ɗan kalleta tare da miƙo mata damin kuɗi yace.
“Mata zanyi kewarki, amman ba matsala duk ƙarshen mako zan ke zuwa.”
Drivern ne ya katse su da cewa ta shigo su tafi, haka yasa ta juya da sauri ta shiga, yaja suka tafi tana ɗaga musu hannu, suma basu tafiba saida sukaga motar ta ɓace musu.

Juyawa sukayi suka nufi cikin gari.
Shi kuwa Ba’ana da ido ya rakasu a a baiyane yace.
“Zanga ta yaya zaku zama GARKUWA’nnata, dan na fahimci duk bakwa son aurena da ita, toko zanyi mgninku.”

Su kuwa basuma juyo sun kalleshi ba.

Ita kuwa Aysha tana komawa ta samu, Rafi’a ta dawo ta gyara musu komai na ɗakinsu, to samun Rafi’a da tayine yasa ta ɗan samu nitsuwa, ranar kam wuni sukayi suna hira, darema haka sukayi ta hirar yaushe gamo.

A Rugar Bani ( Rugar kikan) kenan nake nufi. kuwa, su Ya Gaini suna komawa suka tafi kiwo, kamar dai yadda suka saba, sukaje kiwo lfy suka dawo lfy.

Washe gari ranar Litinin!

Saudia.
Sheykh ne konce, bisa wani fitinenne gado yayi lib cikin tattausan blanket,
bacci yakeji yasa gaba ɗaya jikinsa yayi lakwas sabida jiya a harami ya kwana ɗawafi, shiyasa yana dawowa ya konta. Yanayin wayarrshi na bada ɗan sassanyan sautin,
wani irin ɗan gajeren tsaki yaja, ba tare daya buɗe idanunshiba ya miƙa hannun kan bedside drower’n glass dake kusa dashi, lalubo wayar, yayi tare da ɗan liƙa yatsarsa kan gilashin wayar ya amsa kiran, kana ya ɗauwara wayar bisa kunnenshi a hankali cikin muryar bacci yace.
“Assalamu alaikum, Umaymah”.
Murmushi Umaymah tayi cikin son ɗan yar uwartata tace.
“Na’am Jazlaan ya akayi”.
Cikin murya baccin ya kuma gyara konciya tare da cewa.
“Umaymah baki amsa sallamar ba”.
Da sauri tace.
“Afwan Jazlaan, Wa alaikassalam”.
shiru yayi.
ita kuwa murmushi tayi tare da cewa.
“Naji kamar bacci kakeyi ko?”.
Murya can ƙasa yace.
“Uhummmm”.
Da sauri tace.
“To yi baccin sai ka tashi muyi mgna nasan a harami ka kwana”.
Da sauri yace.
“No Umaymah gaya min menene?”.
Dan shi a zatonshi ko akan Ya Jafar ɗinshi ne.
Ita kuwa Umaymah cikin hikima tace.
“Uhum dama batun Jazrah ne”.
Fuska ya kwaɓe kamar yana gabanta cikin nuna ko in kula yace.
“Menene kuma hakan? Umaymah”.
Kai ta jinjina dan tasan a rina, cikin tsare gida tace.
“Ina nufin Jazrah ƴar Ƴayan Sitti Uncle ɗinmu Aliyu”.
Numfashin ya ɗan fidda cikin ƙosawa da zancen yace.
“Ni ban santaba. Umaymah zanyi bacci, kaina ciwo.
Kin yarda in katse kiran Please Umaymah kada kicemin a a dan Allah”.
Murmushi tayi wato duk yadda mutun ke zaton Sheykh ya wuce tunanin mai tunani a hankali tace.
“Kashe, Allah ya muku al’barka”.
Da sauri yace Amin Amin kana ya katse kiran,
hannu yasa ya cusa wayan ƙasan pillow’nshi.
Kana ya gyara konciyarshi afili yace.
“Ni ina zan kai mace? Toma me zanyi da mace a rayuwata.
Zakuna damuna da wata Jazrah mai koɗeɗden fuska”.
Daga nan ya lumshe ido yaci gaba da baccinsa.
Haroo dake bakin kofar shigowane yayi dariya kana yace.
“Uhum zaka san me zakayi da ita ai Ustadz ai ba’a gane maci tuwo sai miya ta ƙare, dama kirarinku ustazu ƙalilan iya shege kasiran, wai me zanyi da mace, hmmm miskilanciba ba”.
Daga nan ya koma da baya dan dama Sitti ce ta aikoshi ya kira mata Sheykh ɗin, akan yazo yaci abinci kafin yayi baccin wai.
Koda ya koma sanarwa Sitti cewa yama rigada yayi baccin sai suka zauna na nan sukaci gaba da hiransu…

A nan gida Nigeria kuwa cikin Rugar Kikan.
Tunda safe duk makiyayan garin suka tafi kiwonsu.

Sosai suka shiga irin tsakiyar tsaunuka, wasu na nan wasu na can suna dai hango juna da, sabida abu na kiwo bazai yiwu su zauna wuri ɗaya ba, dama sai in zasu komane suke haɗuwa baki ɗayansu.

Misalin karfe uku da rabi na yamma, duk kowa ya fara ɗan zagawa cikin kwazozzobon dake gefensu da. Yin ɗaharan yin al’wala.

Ya Gaini ne ya fara gangarawa cikin korin babu sanda bare wuƙa a jikinshi. Ko buta babu a hannunshi Don akwai ruwa a cikin kwarin dashi suke al’wala, a hankali ya tsuguna yayi buƙatarsa kana.
Ya dawo wurinda suke al’wala ya tsugana yayi al’wala.
A hankali ya yunƙura ya tashi.
Ɗago kanshi da zaiyi yayi dai-dai da…..!

 

By
*GARKUWAR FULANI*

 

Wasa farin girki, yanzu ake nutsawa ciki.

Da yawa naga basu fahimci banbancin. Garinsu Parvina da kuma Rugar Bani ba. To ku saurara, Rugar Arɗo Babayo, itace Rugarsu Parvina, kuma a can ƙasar Cameroon yanki Yahunde Rugar take.

Sai kuma ɗaya rugar wacce a nan ƙasarmu Nigeria take yankin Adamawa state, wani dalili yasa na sakaya sunayen garuruwa da ƙasar tamu da masarautun. Amman nasan duk mazauna Nigeria Adamawa zasu gane Rugar Kikan nake nufi nasa Rugar Bani Numan nake nufi nasa Shikan, dama duk sauran jihohinmu na sakaya sunayensu sabida wani dalili Amman nasan duk munsan inda tushen ƙabilar ɓachama suke.
Amman ba mmki in medasu yadda zakufi ganewa.
Ba wata ƙasa bace Kautal Nigeria nake nufi🤝🏻🥰

 

By
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button