Garkuwa 29
By
*GARKUWAR FULANI*Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond da yayiwa wurin labule.
Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ƙafar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya.
A hankali ta ɗago ƙafarta tare da take step ɗin forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba ɗaya sam ganinta baya gaba.
Cikin rashin sa’a kafar ta tsallake step ɗin forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ƙafar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba.
Wani ƙara mai ɗan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran taji ta ina ɗin ta zai karye.
Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faɗi gib a kan stpes ɗin kanta ya bugi dandamalin sama.
A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice,
Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray’n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau.
Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne,
ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu’o’in buɗa baki.
Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki.
Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa.
“Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse”.
Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa.
Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa.
saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi.
Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray’n gefe.
Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma.
Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta.
Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam.
A hankali ya miƙe tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai ɗan sanyi kan ƴaƴan itatuwan da yaci.
System ɗinshi ya ajiye kan Dinning table ɗin, tare da wayarshi.
Gefenta ya ɗan ratsa ya fara taka steps ɗin tare da kallonta a fakaice.
Yana gab da sauƙane ya ɗan motsa lips ɗinshi tare da cewa.
“Kaɗan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba,
Faɗuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin kallon ƙurillaba, na lura ku mutanen wancan dajin bakuda abinda kukafi so sama da kallon killataccen wuri na jikin mutun.
Muddin baki dena satan kallon jikina ba, sai waɗannan mayatattun idanun naki sun tsiyaye kin huta ki zama makauniya babu ɗan jagora.
Kiyi dai a hankali ko kya samu ki mutu da idonki,”.
Ya ƙarishe mgnar yana tafi kamar bashi yayi mgnar ba.
Ita kuwa Shatu hannun tasa ta sharce hawayenta tare da rakashi da hararan kai mugune.
A falon ya samu su Ummi sunata dariya.
Cikin sauri ya kalli su Jamil yace.
“Kai wannan dariyar na menene, ku taso mu tafi masallaci”.
Cikin dariya Jamil yace.
“Allah ko Hamma Jabeer ina zaton Hibba bata taɓa azumi ba sai bana.
Ga yadda ta dawo wuni ɗaya, wai a haka kuma har ta fara lissafin wai yauwa yau mun kai ɗaya mun rage”.
Ɗan gajeren murmushi yayi tare da cewa.
“Muhibbata tashi kije kiyi salla sai ki ɗan konta ki huta kafin a kira isha’i ko”.
Cikin sanyi tace.
“To Hamma MJ”.
Jalal kuwa cikin yin ƙasa da murya yace.
“Gobe ma zakiyi ne ko zaki huta”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Zanyi Umaymah tace, bana ko ɗaya in nasha sai na biya”.
Murmushi ya ɗan yi tare da cewa.
“Ashe dai kin girma”.
Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi kuwa yabi bayansu Jamil.
Duk sukayi gaba, Sheykh kuwa na bayansu.
har yaje tsakiyar falon sai kuma ya ɗan tsaya jin Ummi na ce mishi.
“Shetu fa”.
Cikin saurin tafiya masallacin yace.
“Tana can ta faɗi wai ko ta karye ne naji tana cewa ban dai san mataba”.
Yana kaiwa nan ya fita, ita kuwa Ummi da sauri ta miƙe cikin zaro ido tace.
“Karaya kuma? Innalillahi yaushe”.
Tayi maganar tana nufar falonshi,
A bakin ƙofar shigowa sukayi kiciɓis da ita, da sauri ta tareta tare da tallabota, jin yadda jikinta ke rawane ta jawota suka fito falon cikin tausayawa tace.
“Sannu Shatu”.
Cikin tausaya Hibba taketa jera mata sannu.
Ajiyeta bisa kujera Ummi tayi tare da cewa.
“Baki sha ruwan ba ma ko?”.
Kanta ta gyaɗa mata alamar eh.
Hakane yasa Ummi tacewa Hibba ta ɗebo mata, abin shan ruwan a take kuwa ta kawo mata.
Bayan tasha ruwanne duk suka nufi cikin ɗaki dan yin salla.
Daga yin sallan magriba su Jamil suka dawo sukaci abinci kafin aka kira sallan isha’i, kana suka koma akayi sallan isha’i da asham sannan suka nufi harkokin su.
Shi kuwa Sheykh Jabeer daga Masallacin gidan Radio Ɓadamaya ya wuce, wurin yin shirin Fatawa.
Sai tara dai-dai ya dawo, gida.
A kitchen ya jiyosu.
Bisa alamu duk girkin abincin sahur sukeyi.
Shi kuwa bayan ya shiga, wonka yayi-yayi shirin bacci kana ya fito falonshi.
Soyayyan Arish da kwan ya ɗanci tare da tarfa ferfesun ya ɗan ci. masa biyu.
Jin cikinsa yayi tib ne, ya miƙe ya dawo falon.
zama yayi bisa kujera yana kiran Umaymah,
tana ɗagawa tace.
“Jazlaan ina autata, ya azumin yau dai?”.
Gajeren murmushi yayi tare da cewa.
“Umaymah autarki akwai raki, yau ita har ta fara lissafin an kai ɗaya saura 29/28”.
Dariya ta ɗanyi tare da cewa.
“Kaɗan ma daga aikin Hibba”.
Sai kuma tace.
“Ina ɗiyata kuma, ya azumin?.”
Kanshi ya ɗan jingina da kujera kana yace.
“Alhamdulillah”. Jin muryar Haroon na cewa.
“Wai ɗazu ina ka shigane inata kiran wayar ka baka ɗagawa”.
Gyara zamanshi yayi tare da kurban coffee ɗinshi kana yace.
“Na bar wayar a gida, da ɗaya na tafi na Fatawa”.
“To ya Amarya?”.
“Ban sani ba”.
Cikin dariya Haroon yace.
“Allah baka haƙuri”.
Amsar wayar Umaymah tayi sukaci gaba da mgnar kan tafiyarsu Umrah.
Daga bisani sukayi sallama, ya miƙa ya nufi ɗakin baccinsa.
A kitchen kuwa, bayan sun gama komai na sahur ne.
Ummi ta cewa Shatu taje ta ɗauko Foodflaks ɗin dake falonshi.
To tace kana ta juya ta tafi.
Koda ta shiga ɗan kalle-kalle tayi ganin baya nan, yasa ta harari falon ma gaba ɗayatare da cewa.
“Mugu”. Sannan ta ɗauki kwanukan ta fito.
Duk sauran abincin Saratu suka haɗawa ta kai musu ita da sauran hadiman.
Wanke-wanke tayi kana ta tattare komai sannan ta wuce part ɗin su.
Su kuma ganin har goma tayi ne, yasa sukayiwa juna saida safe duk suka shiga.
Yauma kamar daren jiya haka sukayi.
Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin.
A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna ɗan mirginawa da kaɗan-kaɗan.
Yau wunin azumi na biyar kenan.
Da hantsi bayan sunyi walaha sunyi karatun al’ƙur’ani.
Sanin yanzu Ummi na jin tabsir ɗin da yakeyi a masallacin Masarautar Joɗa ne yasa, Shatu tana gaisheta ta fito.
Hibba kuwa Side ɗin Aunty Juwairiyya ta nufa.
Ita kuwa Shatu falonta ta fito.
Bisa kujera ta zauna, tare da kiran
number Junaidu wanda Rafi’a ce, ta batashi data tare da bata haƙurin bazata samu zuwaba, sabida yayanta yazo sun koma jiharsu tare.
Ringing ɗaya ana biyu Junaidun ya amsa kiran ganin sabuwar number ne ya sashi cewa.
“Ban gane wake mgna ba”.
Cikin jin daɗin yadda taji muryarshi ras alamun ya samu lfy tace.
“Junaidu Adda Shatu ce fa”.
Da sauri ya tashi zaune bisa kekyawan gadon asibitin da yake kai tare da cewa.
“Laah Adda Shatu kece? Wlh ban gane muryarki ba, Adda Shatu ya gida ya kwana biyu, ya kewan gida, ya lbrinsu Junainah”.
Cikin sauri tace.
“Kai Junaidu duka wannan tambayoyin, ka bari mana in tambayeka ya jikinka, yasu Iri da Laure da Innaji da jikin”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah Adda Shatu duk jikinmu da sauƙin wasuma duk an sallamesu, yanzu nida Hamidu da Adamune kaɗai muka rage, kuma jikin da sauƙi sosai.
Sai dan Baba Madune yana shan wuya,
Satin daya wucema an sake yi mishi aiki”.
Cikin sanyi tace.
“To yanzu su waye ke kula daku”.
Kanshi ya rausayar tare da cewa.
“Uhumm mufa yanzu bamu da matsalar komai Adda Shatu kwantar da hankalinki, mun samu gata da kulawar wani babban likita mai mutunci.
An canza mana asibiti ma an kawomu wani asibiti kamar na ƙasar woje”.
Cike da jin daɗi tace.
“Alhamdulillah, dama dukkan tsanani yana tare da sauƙi”.
Dogon numfashi Junaidu yaja tare da cewa.
“Adda Shatu, ashe mun samu nasara, an kora mana mugun babarbarenen nan,”.
Uhum tace a taƙaice.
Shi kuwa Junaidu cigaba da mgna yayi.
“Adda Shatu Ya Salmanu ba lfy, yazo dubamu da jiki shima an kamashi gado.
Shi yake cemin wai su Bappa sun tafi Lardi. Ayyah Adda Shatu yanzu sai yaushe zasu dawo? Kina mgna dasu ne?”.
Cikin dariya tace.
“Faɗi gsky dai Junainah kake son tambaya dai. Junaidu.
Suna lfy ina mgna dasu. Sai bayan salla zasu dawo.”
Da sauri yace.
“Dan Allah Adda Shatu turo min number su”.
To tace tare da gyara konciyarta.
Nan dai suka ɗan yi hira, kana sukayi sallama.
Sannan ta tura mushi number su ɗin.
Suna gamawa ta kira Number Bappa.
Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga.
Cikin jin daɗin jin muryarshi tace.
“Ina kwana Bappa na”.
“Lfy lau Alhamdulillah Shatu ya Azumi, da baƙon wuri”.
Cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah, Bappa yaushe zaku dawo”.
Dariya yayi mai ɗan sauti kana yace.
“Bayan salla”.
Cikin lumshe ido hawaye na zuba tace.
“Bappa ina jin kewarku, bani da kowa nawa kusa dani.
In na tuno su ya Giɗi hankalina na tashi Bappa inyi ta kuka babu mai sanin irin ciwon da nakeji a raina”.
Cikin sanyi yace.
“Kwantar da hankalinki Shatu, su Ya Giɗi suna raye, sai dai suna cikin mawuyacin hali, suna buƙatar addu’o’in ki musamman a cikin wannan mata mai alfarma, na sanki bakya wasa da riƙo da ibada, amman ki ƙara kan yadda kike, in sha Allah wata rana zasu dawo garemu, cikin sauƙaƙƙiyar hanya, addu’a itace abinda suke so, shiyasa na gaya miki abinda Allah ya nuna min a mafarki a kansu”.
Cikin sassanyan kuka murya can ƙasa tace.
“Zanyi Bappa zan ƙara zan dage, kuma zan roƙi a tayamu addu’o’in a masallatai da wurin tabsir.”
Cikin jin daɗi yace.
“Yauwa Shatu na, ki kwantar da hankalinki, ki zauna lfy da mutanen da kike tare dasu, kiyiwa mijinki biyayya, kiyiwa mayanshi biyayya bana son musu in babba ya gaya miki abu matukar bai saɓawa shariyar musulunci ba.”
Cikin sanyi tace.
“To”. Da sauri yace mata ga Junainah”.
Cikin jin daɗi tace.
“To a bata waya”.
Tsalle Junainah tayi tare da cewa.
“Adda Shatu, kizo Lardi garin da daɗi kullum sai an gasa mana zabbi ko Tattabaru, insha nono da zuma inci naman insha zuma, inci su inabi sai na ƙoshi”.
Cikin so da ƙauna da shaƙuwar ta da yarinyar tace.
“Allah sarki Junnu ke ko kewata bakiyi bako?”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Nayi kewarku mana harda Ya Junaidu ma nayi kewarshki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Na bashi number ku, zai kira ku gaisa”.
Tsalle tayi tare da nufar ɗakin Ummey.
Ita kuwa Shatu cikin dariya tace.
“Azuminki nawa”.
Da sauri tace.
“Azumi na ɗaya ranan nayi rabi daga safe zuwa azahar jiya kuma na ƙarisa rabin daga azahar zuwa mangriba”.
Wani irin dariya ne ya rufe Shatu dariya takeyi sosai.
Kewa da bege da son ƙanwar tata ya rufeta.
Da Sauri ta tsagaita da dariyar jin Junainah na cewa.
“Adda Shatu Bappa yayi aure an samo mana wata Inna mai kirki”.
Cikin mamaki tace.
“Ke Junnu ƙarya ba kyau fa”.
Da sauri tace.
“To ga Ummey ki tambayeta kiji”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe jin muryar Ummey cikin sanyi da jin daɗi tace.
“Ina kwana Ummey na ya gida, ya Junnuna nayi kewarku, Ummey wai da gaske Bappa yayi aure”.
Murmushi mai faɗi Ummey tayi tare da cewa.
“To duk Alhamdulillah muna lfy eh Bappa yayi aure an bashi ƙanwar innarku, Indo kin santa ai ita take bin innarku, Bata taɓa haihuwa ba, to ashe mijinta ya rasu.
Shine yanzu aka aura mishi ita. Kuma tanada hankali kamar innarku”.
Cikin sanyin jiki tace.
“Eh na san Umma Indo tanada kirki, to Allah ya baku zaman lfy yasa kuyi irin zaman da kukayi da Inna”.
Amin Amin tace kana tai mata nasiha Sannan sukayi sallama.
Daga nan ta miƙa ta nufi ɗaki dan yin salla.
Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Ummi da Saratu da tun ɗazu tana nan.
Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai.
Kafin shida ta cikama sun gama komai.
Yanzu in sun zo buɗa baki ita da Ummi da Hibba tsakiyar falon suke dawowa.
Jalal, Jamil, Imran, Sulaiman, kuma su zauna a dinning table.
Ya Jafar kuwa wani lokacin har can falon Sheykh zai wuce suyi buɗa baki a tare.
Kana su tafi masallacin.
Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari.
A wurin al’ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta.
Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur.
Cikin kula Ummi ta kalleta tare da cewa.
“Ɗauko kwanu kan nashi”.
Kanta ta ɗan juyo ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ai bai dawo yaci ba ko?”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Baya cin ƙosai, kuma kinga doyan ma jiya baiciba, ya gaji dasu ne, ki ɗauko a juyewa su Saratu shi ki ɗan haɗa mishi wani abu kafin ya dawo”.
Cikin ɗan kauda kai tace.
“Ummi ai ƙoshi yake shiyasa bazai ciba, a barshi kawai in yaji yunwar yacima wani bai saniba, ai yunwa ba Umaymah bace ko ke bare zaku lallaɓashi”.
Dariya Ummi tayi kana kuma ta haɗe fuska tare da cewa.
“Je kiyi abinda nace ko”.
To tace ganin kamar ran Ummi ya ɓaci.
Bayan ta dawo da kwanukan ne,
Suka bawa Saratu ta juye, kana ta harhaɗa wonke-wonken ta fara.
Ita kuwa Shatu cikin yin miƙa tace.
“Ummi me zan dafa mishin?”.
Juyawa tayi tana haura wurin da Fridge yake tare da ce mata.
“Duk abinda kika iya kika san ba mai nauyi bane”.
Kanta ta gyaɗa tare da cewa.
“To”.
Cikin ranta tace.
“Bari inyi Special Arish, in yaga dama yaci in yaso ya bari, mutun sai zaɓe-zaɓe kamar mai ciki.
Dankali ta ɗan ɗebo da Nama, kwai, tumatur, kabeji, Bama, maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita.
Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi.
Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al’basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan.
Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi.
Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan.
Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al’basa. bisa wata a ɗan tukunta.
Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe.
kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin.
saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al’basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu.
Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma.
Kana tasa Maggi da al’basa da Bama ta gauraya kana
Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka.
Kanta ta jujjuya tare da cewa.
“Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo”.
Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa
“Yaushe ya dawo?”
Plate ta ɗauko tare da cewa.
“Tun ɗazu”.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma.
Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace,
Ya akayi kika san ya dawo”.
Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba.
Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe.
Ta shiryashi yayi kyau sosai.
Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi.
Kana tasa spoon da Fork a cikin tray’n data ajiye plate ɗin.
Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki.
Sannan turashi gefe.
Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi.
Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi.
Amsa Ummi tayi tare da cewa.
“Ɗauki ki kai mishi to”.
To tace tare da ɗaukan tray’n ta fita.
A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito,
Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi.
Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv.
Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi.
Kana ta juya a hankali ta fita.
Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci.
Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa.
Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki.
Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo.
Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC’n zatayi.
Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al’wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi.
Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima.
Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu.
Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray’n abincin sahur ɗin shi.
Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi.
Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi.
Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area.
Washe gari da safe yau Jumma’a kuma, yaune azumi na shida.
Bayan sun fitone, Ummi ta kalleta cikin dariya dan tuno yadda ta fito falon Sheykh Jabeer a guje da asuba, tana jan Allah ya isanmata ana tsinka mata zuciya,
Cikin murmushin tace.
“Ummi dariyar me kikeyi ne?”.
Cikin gimtse dariyar tace.
“A babu, yauwa tashi muje ɗazu Gimbiya Aminatu ta aiko, wai tayi kewarki kwana biyu azumi ya ɓoyeki bakije ba”.
Cikin murmushin tace to muje Ummi”.
Ta ƙarishe mgnar tanayin gaba Hibba na biye da ita a baya.
Cikin sauri Ummi tace.
“A haka zaki fita ba al’kyabba”.
Kai ta ɗan dafe tare da cewa.
“Wayyo Allah na, Allah kuwa ni nauyi sukemin wannan tsarabe-tsaraben wuya gareshi”.
Murmushi Ummi tai tare da miƙewa ta ɗauko al’kyabbar.
Tazo tasa kana suka fita.
Da Side ɗin Hajia Mama suka fara,
A falo suka samesu.
Cikin fuskar ba yabo ba fallasa Hajia Mama ta amsa gaisuwar Shatu.
Batool kuwa sai auna mata harara takeyi.
Hira suka ɗan taɓa kana suka fito.
Har sun fito Shatu ta ɗan kalli Ummi cikin sanyi tace.
“Ummi jirani anan bari inje in isar da saƙon gaisuwar Ummey na wurin Hajia Mama”.
Da Mamaki Ummi tace to kana ta juya ta nufi ciki, ganin Hibba za biyota ne tace.
“A a jirani ina zuwa”.
Haka suka tsaya suna jiranta.
A hankali ta turo ƙafar falon.
Da sauri Hajia Mama ta zuba mata ido fuska cike da tsana.
Batool kuwa binta da ido takeyi ganin wani irin takun isa da ƙasaitar da takeyi.
Kujerar dake fuskantar wacce Hajia Mama ke zaune a kai ta zauna.
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya.
Kana ta jingina da kujerar, cikin tsare Hajia Mama da ido tace.
“Uhummmm kin sanni sarai, kar tasan karne, duk motsinki a tsakiyar tafin hannuna kike, dan haka gwara kiyiwa kanki gada ki fita harka da rayuwar mijina! Da ƙannenshi da wanshi. In kuwa kikaƙi zakisha mamakin Shatu.”
Tana faɗin haka ta miƙe, tana kallon Batool da tun randa akace Shatu tazo ta bawa Hajia Mama haƙuri da ta shigo tayi wasu kalaman ya ɗaurewa Batool kai ta kasa tantance tsakanin aya da tsakuwa, shiyasa batayi gigin yin mgn ba, sabida tuno abinda Shatu tace mata a ranar cewa.
“Mijina kike so ko, to kizo in ya amince ya kalli inda kike na daƙiƙi biyu rak zan sashi ya aureki”.
Da sauri Batool ta dawo daga duniyar tunanin da take jin ƙaran rufe ƙofar da Shatu tayi.
Ido ta maida kan Hajia Mama dake gurnani kamar macijiya.
Jim kaɗan ta fito.
Cike da son gano wani abu Ummi ke binta da ido, amman ta kasa gano komai domin Shatu ta iye takunta, ta fito kamar ba itaba gaba tayi.
Kana suka nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu.
Suna shiga ta miƙowa Shatu da Hibba hannu kusa da ita ta ajiyesu.
Bayan sun gaisane ta kallesu tare da cewa.
“Azumi ya boyeku da yake ku ragwagene”.
Murmushi sukayi tare da cewa.
“Kai Gimbiya jiya nefa kawai bamu zoba”.
Cikin kula Lamiɗo dake shigowa yanzu zai sabunta al’wala zai wuce masallaci yace.
“Shatu matar malam bauɗeɗɗe”.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai.
Hibba ce tace.
“Sai na gaya mishi”.
Dariya sukayi kana suka sallamesu suka tafi ganin lokacin sallan yayi.
Har sunje bakin ƙofa Gimbiya Aminatu tace.
“Yauwa Jakadiya kayan miyanku da saura ko ya ƙare?”.
Cikin rusunawa tace.
“A’a da saura sosaima”.
Kai ta gyaɗa kana suka tafi.
A hanyarsu ba komawane Shatu tace.
“Ummi wanne kayan miyan ne?”.
Cikin sanyi tace.
“To ba kince bakya son na Hajia Mama ba, shine ita kuma Gimbiya Aminatu ta haɗo miki komai yanzu dasu muke amfani ai”.
Cikin gamsuwa tace.
“To wancan ɗinfa ya akayi dashi?”.
“Umaymah ta tafi dashi duka”.
Hibba ta faɗa mata.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ba matsala”.
Nan suka tafi suna salla suka shiga kitchen yau harda Hibba.
Sannu-sannu dai bata hana zuwa sai dai a daɗe ba’a jeba.
Yau an cika azumi goma. Gobe za’a shiga goma na wuya, an gama na marmari.
Yau kuma makara Shatu tayi.
Ganin har su Jalal sun zone yasa Ummi ta nufi ɗakinsu.
Ai kuwa kan gado ta hangosu.
Tadasu tayi kana ta fito.
Tana cewa.
“Shatu kiyi sauri kizo ki kaiwa Sheykh nashi”.
Kusan a tare suka diro ƙasa.
Brush kawai sukayi suka fito.
Da ƙaton hijabin ta fito.
Tana zuwa Dinning area Ummi ta miƙa mata tray’n abincin nasa.
Amsa tayi ya juya ta nufi falonshi.
Tsaye ta sameshi gaban show glass ɗin dake gefen Fridge ɗinsa dake Dinning area,
Cup ne a hannunshi cike da madarar gongoni da molt a haɗe.
A hankali ta wuceshi kaɗan ta ajiye tray’n.
Kana ta juyo da nufin sauƙowa, taku ɗaya tayi a na biyu ta iso gabanshi kenan.
Aka saki bindigar shaidar huɗu da rabi tayi.
Wani irin zabura tayi tare da af….!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, domin shiga Normal group wanda a wata ɗaya za’a, gama Part one. Ko kima kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank, domin samun shiga Special Group wanda a sati biyu cakal za’a gama Part two da izinin ubangiji, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853297.
Ke mai haushi kin turo ɗarinki uku, kinzo kinata haushi, nace ki turo ac no ɗinki in maida miki kuɗinki kin tsaya yimin tumasanci shiyasa nayi Black ɗinki, a rashin Sa’a na haɗa da number ki na goge. Kuma baki Turo ac na na meda miki shi ba. To Alhamdulillah a take a lokacin nayi miki sadaka da ɗarinki uku, ubangijina shine shaidata, banci kuɗinki ba, nasan zakiga PAGE ɗin sabida akwai waɗanda basu san darajar Allah da Manzonsa da iyayensuba, zasu fitar, to kiji ni Shatu na sauƙe nauyin ɗarinki uku.