Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 64

Sponsored Links

Gumu tayi gumu hankalin wannan family ya tashi wannan karon lamarin yafi qarfin fushi saidai addu’a saboda Hameed yana asibiti Umaimah ma tana asibiti har satin suna ya zagayo duk inda taso cirewa kanta damuwa da soyayya gami da tausayin halin da Abdulhameed yake ciki ta kasa saboda a jininta yake ji takeyi kamar ta cire ciwon ta mayar jikinta duk da a cikin qahon zuciyarta tanajin ciwon cin mutuncin da yayi Mata a daren da tafi buqatar taimakonsa da kusancinsa a daren ya yanke shawarar datse igiyoyin aurensu saida tayi sati biyu tana jinyar rabuwa da masoyinta a asibiti kadan ya rage itama zuciyar tata ta harbu amma jininta in yana kaiwa dubu ma to ya kai ga kuka babu dare babu rana tazama kamar zautacciya duk wata kalmar bakinta bloody ko ya jiki kace mata to amsarta bloody.

 

Hakan ba qaramin daga mawa su Hajiya hankali yayi ba kakace taga abin na Umaimah ya zama kamar tabuwar qwalwa hakan yasa tasa aka sauke mata qur’ani sannan akayo mata rubutun dangana aka rinqa bata tanasha satinta uku da haihuwa suka koma makaranta sabuwar motar da Hameed ya siya mata wacce yace itace gift dinta ta haihuwar Shuraif ita Daddy ya bata take zuwa makaranta da ita kamar yanda ya kafa mata doka har yanzu haka take bata fasa ba niqaf ne kawai bata sawa saboda dama a dole take sanya shi saboda farin cikinsa.

Related Articles

 

Saida yayi sati biyar a asibitin yana jinya sannan ya fara samun kansa shima da sunanta ya tashi a bakinsa Hajiya tana tausayawa dan nata tasan kafiyarsa shima da rubutun zatasa ayi masa saboda tasan akwai badaqala a gaba.
Haka suka koma gda dashi duk yawan gdajensa amma yaqi komawa ko daya daga ciki shima dakinsa tunna samartaka yasa Daddy dole saida ya gyara masa ya koma cikinsa sai lkcn ne Hajiya ta samu damar zuwa ta debowa Umaimah kayanta tsaf shikuma yasa gdan a kasuwa saboda ko gdan bazai qara zuwa ba balle ya tuna da baqar rayuwa da baqar ranar data riskesa a gdan ranar dabai taba tunanin zuwanta ba a rayuwar aurensa da Bloody dinsa.

 

Bincike yakeyi sosai akan sakin da ake iqirarin yayiwa Umaimah malamai sun bashi fatawa sosai inda kaso mafi rinjaye suka tafi akan ta saku saboda mgnrsu ta cewa lkcn da aka saukar da suratul dalaq manzon Allah ya sauqaqa sosai a cikin lamarina na saki harma yace idan mutum ya saki iyalinsa saki uku a kalma daya to zaa iya barinsa a saki daya idan yayi mata saki daya a baya kuma yazo yayi mata biyu to zaa iya barin biyun nan a daya a hada da wancan na farko ya zama biyu sannan idan mutum ya saki matarsa a cikin maye ko gushewar tunani to wannan sakin babushi.

 

So inda aka samu matsalar bayan wafatin ma’aiki (s a.w) sai abubuwa sukayi tsamari mutane suka rinqa wasa da aure sai mutum ya saki matarsa saki uku kuma yaje ya dawo da ita ko mutum yaje yasha giya ko wani abu me gusar da hankali yazo ya nadawa matarsa duka ya saketa idan ya dawo hayyacinsa ya koma ya dawo da ita wannan abu ya batawa Sayyadina Umar (R.A) rai zamanin khalifancinsa ya kira majalissar sahabbai aka sakewa dokar qwasqwarima saboda sauyawar zamani aka buga mata guduma akan cewa idan har mutum ya saki matarsa saki uku a kalma daya to ta saku sannan ko cikin gushewar tunani mutum yayi saki to matarsa ta saku sannan idan kayiwa mace saki daya sannan kazo zaka sake sakinta bayan kasan da daya a baya kuma ka furta mata biyu to ya zama uku saboda haka ta haramta gareka harsai tayi aure da tsarkakkakiyar niyyah ba niyar kisan wutaba kuma harsai mijin yayi mu’amalar aure da ita sannan tasu ta hadosu suka rabo to a lkcn ne ta halatta gareka sai ku sake daura aure fresh me igiya uku.

 

Wannan kalma ta sai Umaimah ta auri wani har ya kwanta da ita sannan zata halatta gareshi tana mugun dukan zuciyarsa yakanji dama ya mutu ya huta da ganin wannan baqar rana dalilin yasashi dawowa gdan dalilin ya qudurce a ransa bazaiyi aure ba itama bazatayi ba saidai su qare rayuwarsu a haka.
Abu daya da yake cin zuciyarsa yanda Umaiman tayi watsi da duk wani abu daya shafeshi so tari idan bashine yayi mata mgn a gdan ba itadai bai isa ta daga kai ta kalleshi ba yana yawan kiran wayarta amma bata dagawa har layi ya canza musamman saboda ita amma daya kirata tana dagawa taji muryarsa tace “hello bloody ya akayi Allah yasa dai lfy?”

 

Ajiyar zuciya yaja yace “ki taimaka ki fito come pound din gdannan inason ganinki don Allah” murmushi kawai tayi ta kashe wayarta bata fito ba kuma bata sake daga wayar tasa ba ransa yayi matuqar baci amma bashi da yanda zaiyi saboda baya iya fushi da lamarinta wani azabbaben so yakeyi mata wanda yake neman turashi lahira bai shirya ba haka lkc yayita tafiya tafi² har watanni takwas suka shude kullum cikin dagewa a karatunta take inda shi kuma Hameed ya mayar da azumin nafila abokinsa saboda lalurarsa tafi qarfin yace zai rinqayin na litinin da alhamis Hajiya tanajin dadin yanda Umaiman take tsarewa Hameed gida saboda tasan yanda yake rawar qafa akan duk abinda ya shafeta idan ta bashi fuska taasa zasu tafka ta lura basu zama inuwa daya daya shigo parlourn ita kuma zata tashi tabarshi da yayansa hudu Nihal Maliha Shurafah da Shuraif Maliha itace me wayo tunda a qallah yanzu ta doshi shekara takwas itace take cewa uban nasu “Uncle naga Aunty tana fushi dakai kuma kun dawo gdannan dukkanku kuma jiya naga wani yazo gurin Aunty ta fita suna hira har suna dariya” tashin hankali wata uwar zabura da yayi ya fara qwalawa Hajiya kira Hajiya ta fito daga kitchen tana cewa “waikai wanne irin mutum ne kaine diba nan duk yayanka ne amma kaqi hankali ubanme zaka bani kake dokamin kira haka?”

 

Duban Hajiya yayi da idonsa da suka canza kala saboda bala’in yace “wato Hajiya yarinyar nan har kin barta ta fara kawo mana qartin banza gdannan ko to wlh bazai yuwu ba karyata zanyi na balla banza kuma naci uban duk wanda ya qara zuwa gdannan da sunan yazo gurinta haba Hajiya wannan ai cin fuska ne da wulaqanci ansan dai ina gdannan koma meke faruwa zanji baba megadi yasha fadamin yaga wani ya tuqota ya kawota gda ko yacemin yaga wani yazo gurinta to nida kashedi ne nayi muku wlh Allah hauka zanyi a gdannan ga duk wanda ya qara zuwa yayimin sallama da mata shima megadin bari naje wlh ya qara barin wani dan iskan ya shigo gdannan a bakin aikin sa”

 

Yana gama fadamin haka ya fice fuuuu kamar zai kifa riqe haba Hajiya tayi tace “wata sabuwa inji dan caca to uwarka zatayi maka a gdan da zakace baza azo gurinta ba zakuwa kaci kan uwarka wlh Hameed dani kake zance kama godewa Allah Umaimah najin kunyarka ni bantaba ganin yarinya me yakanar Umaimah ba ko baqo tayi da zarar taga yamma tayi zata sallameshi idan nace meyasa tace babu komai bayan nasan saboda Kaine”
Yana fita kuwa yayi katari Dr Sulaiman ya kawota daga mkrnta malaminsu ne tunda ya qyalla yaganta ya dauki so da kulawar duniya ya dora mata da farko Shuraif yakeja a jikinsa saidaga baya daya bincika yaji sun rabu da mijinta sannan ya fara fito mata da ainihin buqatarsa gareta da farko taqi sai daga baya Saudat ta rinqa tausarta tana fada mata shima kyakkyawa ne gashi fari gashi da gani babu tambaya naira ta zauna masa to daqyar dai ya samu ta saki jiki dashi suka fara gudanar da soyayyarsu amma qasan zuciyarta danqare dason dan’uwanta wanda bazata iya gogeshi a mind dinta ba don tasha kiran Dr Sulaiman da Hameed saidai yayi murmushi kawai yace “ sweet Allah yasa kisoni koda rabin son da kike yiwa Hameed ne sweet wlh inasonki fiye da tunaninki na fada miki bantaba soyayya ba saboda tsoron mata nakeji sai a kanki”

 

To yauma zancen da yake mata kenan tayi dariya ta lakace masa hanci tace “sai kuma ka fara da bazawara me yara biyu….” dora hanunsa yayi a saman lips dinta ya kashe mata ido yace “banason ji idan yayanki goma inasonki kuma zan rayu dake zan baki soyayya madara kuma nasani nima zaki soni irin son da kikeyiwa abu Shurafah koma fiy….” Aslm alaikum sukaji anyi musu sallama gabanta yayi mugun faduwa da sauri Sulaiman ya dubeshi yayi murmushi tare da shafa sumarsa ta fullanin asali yace “amin wslm” ya miqa masa hanu amma sai ya noqe ya kalleta da jajayen idanunsa ka cafketa da qarfi yace “dama abinda kikeyi a makarantar kenan idan kinje irin wadannan yan iskan kike kulawa to karatun ma kin daina” yana fadin haka ya figeta ya cillata parlour ya juyo shidai Sulaiman yana tsaye cike da mamaki “dama wannan shine yayannata da take cewa dashi tanajin tsoron yazo gda kada yagansa?” Ya tambayi kansa kafin ya samo amsa yaji muryarsa yana cewa “kada ka qara biyomin qanwa gda wlh zan daureka harsai igiya tayi rara” wuccewa yayi Sulaiman yayi saurin binsa yace “kayi hqr Yaya wlh bada wasa nake ba auran Umaimah zanyi….”

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…*✍🏻
[1/31, 5:48 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GU*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button