Hariji Book 1Hausa Novels

Hariji Book 1 Page 7-8

Sponsored Links

Free page 7&8

*Alheri writers Asso.*

By…Oum Aphnan

Related Articles

Shiru Adnan yayi ,wanda ƙuliya yike yi masa laƙabi da *son* yina faman jujjuya shimfiɗeɗiyar wayarsa a hannu

Hmm shi ba ka dawo ƙasar nan bane,dad is out of explanation ,bashida yarda at all ,ya ɗauki ɗabi’ar yahudu (jews) gani yikeyi kowa macucine ,shida zuciyarsa ne kurum ,suke yin daidai,amma ace kamana sai na shiga kitchen nayiwa dad abinci sannan zaici? Kurum ya maisheni cook,ko ɗan daudu,kodai menene ban sani ba…

Kiransa da ya sakeyine ya sakashi yiwa bakinsa birki tareda ɗaukan wayar,cikin kumburarren murya ,irin na sangartattun yaran da aka ɓatawa rai yace “Dadd!”
“Son,inajin bazan samu dawowa yauba ,saboda yanzun nan gomnan kuɗi na central bank,ya kirani a waya ,wai *efcc* suna bincikarsa kuma an gano ya kwashi sunanan kuɗi,in short zan tsaya masa a kotu,ina buƙatar addu’arka yanzu zamu wuce *uk* a bankin acan yayi depositing kuɗin ,so inajin sai mun withdrawing kafin zaman kotun ya fara commensing ,inba haka ba is easy ayi trace up

“Oh dad,to yanzu zaka goyi bayan ƙaryane? Sune fa suke kwashe mana arziƙin nigerian ”

“Son muna magana ne ,ta wire device,duk maganan mu zai iya zama not secured ,in na dawo zan maka bayani”

**

Yau talata ,Aka fara zaman kotu, na ƙarar ummy ,mai satan tagwayen jarirai,saidai shari’ar ya kasance a murɗe,kasantuwar hujjar da lawyan me ƙaran ya kawo akan cewa ummi ita ta sace jariran ba masu ƙarfi baneba,kawai shedar takardan hoton ciki ne ,da ya tabbatar matar tana ɗaukeda cikin jarirai biyu duk maza.
Shikuma lawyan wanda ake ƙara yayi opposing ,maganar ta hanyar bayyana cewa ai indai maganar en takardane,cikin sauƙi ake iya manipulating,wama ya sani ko ita matar ne, me haihuwar ta shirya wannan zambar aka ƙagawa innocent ummy…?

A yanxu haka kotu ta ɗaga ƙara zuwa nan da sati biyu,inda aka umurci lawyan me ƙara da ya gabatar da likitan da yayi hoton cikin for more varifications

**
Wannan shari’ar da aka gudanar dik da a ƙaramar kotune ,ya jawo hankalin mutane da dama ,al’ummah sai cece kuce sukeyi,wasu na ganin sharri akayiwa ummi,wasu kuma suna ganin gaakiyar mutumin akan cewa da gaskene ,unguwar xoma suna satan jarirai kuma sune nan ,suka sace mashi jariransa ,for there mere interest!

_Paid book regular payment #200 vip #400 ,via 7782217014 ,mohammed hassana,fcmb or Mtn card via this number 09065990265_

*Ƙuliya* dake zaune a falon gomnan kuɗi ,yina duba wasu office files da ya fiddo masa ,duk a ƙarƙashin bincikensu,desires ɗin son ganin programs ɗin cikin gida nigeria ne ya shigesa ,don haka a hankali ya chanja channel daga *Aljazera* zuwa *Nta* daidai ana nuna sharia’ar su ummi *life* wanda akeyi a daidai wannan lokacin…

Medicated glass ɗin idonsa me garai garai me tsananin kyau da aka yanka masa a saudi arabia,ya gyara zaman sa sosai ,yanda zai tsaida ƙwarar idonsa akan hoton yarinyar da ake ƙarar .

A take jijiyoyin ƙwalwarsa ya juya ,ya fara hasko masa hoton yarinyar cikin halin tashin hankali ,yina haɗa hoton zuciyarsa da na cikin talabijin ɗin da ake haskowa a yanzu.

*Tabbas itace wannan! her innocent and adorable face without decoration,Bazai iya mantawa ba,her activities concerns is his final considerations …*

***
Bello yina fita daga gidan ,kasa wucewa gidan hayan da hausi take yayi kurum sai ya zarce wani masallaci da ake bari a buɗe ya kwanta yina tunanin balaƙin da ya jefa rayuwarsa a ciki…
Sambatu ya farayi yina magana a zahiri

“Oh ni bello,ina zaman zamana da matata,ni mwaɗayin zama da mata biyu naje na ƙaro wa kai na *harija* ganinan kullum cikin ciwon kwankwaso itakuwa ba abunda ya shafeta ,bata gundura ,wannan tashin hankali da me yayi kama?

Wani ɓangaren zuciyarsa ne ya fara bashi shawaran baragulbin tunani

“To ka saketa mana,tun da ba ɗa ba jika ,ku rabu salin alin ba sagi…nima na huta da kuɗin haya,ƴar jarababbiyar matata ta fiye mun harija!”

Murmushin jin daɗi yayi ,sannan ya sunkuci takalmansa ,ya kama hanyar gidan hayan shi da uwale.
_Typing ✍🏾_

 

*HARIJI*
(Original Romantic love story)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button