Hariji Book 2 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 2 Page 25-26

Sponsored Links

25&26
*Hariji*
Oum Aphnan✍🏾

Adnan yina kwance akan gadon har zuwa lokacin bai gama warkewa ba,saidai yina maamakin beelah da har zuwa wannan lokacin bata zo ta dubashi ba ,after all his love and care,anya fulanin Adamawa sunada imani!

Kautar da zargin zuciyarsa yayi Cikin jin zafin kansa da kansa ,ya cigaba da gwada kiran wayarta
Ringing din kusa da qarshe ta d’auki wayar cikeda isuwa
“Hallowww”
Hy babes
Shiru tayi a inda take a dakinta na hostel dinsu dake jami’ar Atiku.. tana hakimce tana girgiza kafa Cikin qawayen ta ,duk suna ,zaune suna cin taliya mai ,zafin gaske da yaji ga lacasera mai sanyi
Kallon qawayen ta tayi gamida yi masu signal tana nuna masu wayar akan tebur tana cigaba da cin abincin ta Bayan tasa wayar a handsfree

Related Articles

“Beelah ta”
A kasaitance ta amsa da “d’an gidan me Shari’a”.
Baijin dadin yanda take kiransa ,kamar akwai rashin da’a ,to amma ya zaiyi so makaho ne
” my bakiji nayi ciwo ba”
“Then?
” sai kizo ki gaisheni”
“Oh really? To inayin primary assignment din da ya kawo ni abuja,wato karatu,don haka in mun gama exams zan zo in dubaka,karkaji ka damu”
“Hmmm aima naji sauki,,ga zuciyata tana azalzalata da son cute fuskar my beelah…” ya fad’a Cikin marairaitan murya
Shekewa da dariya tayi suka tafa da qawayen ta
A take hankalin sa ya tashi ,oh duk ma da mutane sunajin mu
“Beelah keda su waye ?
” vari kaji amsarka”
Ta bashi amsa tana kunna waqa ta dayar wayarta ta kanga masa a jikin wayar ,da sauri ya rintse ido kansa na buga masa ,jin un expected qara a kunnensa.
Da sauri ya kashe yayi cilli da kan wayar
Shegen sama ba zuciya ya kashe wayar.
Zee kallon ta tayi Cikin tausayawa
“Meyasa kikewa mai sonki haka nabeela? Ko baki sonshi ne”
Banson sa na turasa gidan mu? Kawai na tsani uztazancinsa ne Sam baida wayewa,shan ice cream bazai ce dakaiba saidai a baka kudi kayi magana yace kar ya 6atawa ubansa suna a abuja ,sai kace shi kadai ne uban sa ne kadai wani a duniya haba nonsense !”

**
Around 7pm ,gaban campus din yayi tantarwai da hasken sola gamida danjojin motoci lafiyayyu da suke zuwa suna daukan tsala tsalan en matan jami’an ,en mata sai up and down suke yi tsakanin hostel da filin makarantar
Adnan da tun dazu yike bushe a karkashin bishiya da motarsa ,ji yayi kamar ya juya tsabagen takaici ,ace tana kallonsa yazo saida ya sakankance wajensa zatazo amma sai ta shige motar saurayi ta kirasa ta wani ce ya jirata. Ko da yike bari in mata uzuri may be dan uwanta ne ko course mate
Saida ya kwashe fiyeda awa sannan ta yi knocking glass din ,cike da zumudi ya cire securityn motar yina mata barka da zuwa ,harda karkad’e mata inda zata zauna da wani farin handkerchief,Ca6e baki tayi sannan ta gyara zaman wata hadadiya blue gown na zuwa dinner ta zauna .
“Gani shaf shaf zamuje dinner mu na graduation so five minute plz”
Shiru yayi yama rasa me zai ce mata “anyi ni lafiya beelah ta” “lafiya na aza dai dazu munyi waya to wannan wani munafurci ne gaidar uwar mini da tsakar rana ?” Ca6e baki yayi saboda bai wayi hausar ba Don haka sai ya 6ige da washe mata baki “waye kika shiga motarsa am here waiting?
Frankly with all her brags tace “saurayi na” sosai yaji Kalmar ta sokeshi
“Saurayinki?”
Dage masa gira tayi cikeda tabbatarwa ta sauke mirror din saman motarsa tana kallon fuskarta tana cuno baki gamida maida ear piece a kunnenta tana amsa kira
Kashewa tayi ta kallesa kamar batasan a halin da ta barsa ba dangane da maganar ta na baya.
“Hey guy Anfara dinner ni zan wuce so a huta gajiya”
Daganan ta 6alle kofa zata fice “beelah ” ya kira sunanta da dan qarfi
Murya can qasan makoshi ta “ya akayi ubana” beelah kina tunanin wa’innan strange behaviours din da kike mun bazai sa ki fice mun a rai ba?
Da ta juya zata fice ne kalmarsa ya sata juyowa da sauri “kai waye kai a tunaninka dazan ji ko d’ar don mun rabu ? Go d hell out of my life mmmtseww nonsense” daganan ta fice cikeda 6acin rai ,wai kamata saurayi ke gayamun magana son ransa
6amm ta datso masa kofar..
Wani jirine yaji yina fizgarsa da qarfi ya daki sitiyarinsa “dole in barki beelah” da sauri ya finciki motarsa ya karya kwana da nufin futa school din gabad’aya, a makance yike tukin yina wassafa zaginsa da irin muzguna masa da nabila takeyi “Damn it na qyaleki nabeela har sai Kinsan adnan yinada zuciya daganan na dawo gare kin… Wani kaciren jijiyan icce da aka sare ya doka da kan motarsa ,baya motar tayi ta dawo gaba gaarammmm sitiyarin ta doki qirjinsa ,fushhhh ya feso wani irin baqin jini ta hanci da bakinsa a take ya wantsalo da kansa ta wajen glass dinda ya zube feinted….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button