Hariji Book 2 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 2 Page 69-70

Sponsored Links

69 & 70
*Alheri writers asso.*

Beelah yau suka gama makarantan su gabadaya,don haka akazo da mota daga gidan su aka kwashe rankatakaf din kayanta,suka dauki hanyar gida.

Khady da ta kasance maqociyar su beelah kuma Bossom friend dinta , ba’azo an dauketa ba don haka ,akwatun ta ta dauka da basic abubuwanta tabi motarsu beelah suka dauki hanya…🚗

Related Articles

Tunda ta shiga motar,ta Lura beelah Na kumburin iska ,in tayi mata magana sai ta gama basarwa sannan Zata bata amsa da “eh ko a’ah” don haka tun kafin tafiyar tayi Nisa ta kama kanta tamatsa qarshen edge din back seat ta zauna,itama taje dayan edge din suka jingina da murfin motar kowa ya kama chart dinsa

Ana haka sai ga baquwar number an Kira khady ,mamaki tayi tayi tana jujjuya wayar ,ganin +966 yasa ta cikin kogin tunani,wa take dashi a saudiyya? Saida wayar ta katse sannan ,Adnan ya fado mata a rai “Tabbas Adnan ne,ya Allah Na roqeka,kasa zai amshi tayin soyayyata ne” shiru shiru taga ya Kira ta Amma ko alama

Cike da zaquwa ta fara dialling number saidai yaqi d’agawa,wannan ya nunar mata da yayi zuciya ne.
Don haka kunna data tayi ta fara lalubensa a WhatsApp ,though da numbersa Na Nigeria har yanzu yike chart ,aikuwa cikin sa’a ta ganshi online ,batai qasa a gwuiwa ba ta kwada masa cikakkiyar sallama,don bata mantawa da gwasalar da Tasha ranar da tace masa “Hy”
Sosai taga ya Gani Amma bai responding ba,amma dukda hakan batayi zuciya ba ta kama bashi haquri tareda kawo masa uxurinta da ya hanata picking wayarsa
Sai sannan taga ya sauka a online din,jimawa kadan saiga kiransa,ai ringing din farko ta dauka “hello…au..Assalamu alayk warahmatullah”
A ciki ciki ya amsa “khadija kike ko wa?” “Yes haka Nike”
“Na kar6i request dinki Amma da sharadi banson surutu,kuma nan da few weeks zanzo Nigeria asaka mana rana ,but mind you,dont think zan gwada Maki soyayya ne,no at all,mace daya nikeso itace beelah ,a rashin ta zan manage dake wataqila…” Kafin ya qarasa maganar sa ta katse sa

“Ai a hakan ma nine da godiya…” “Ke dakata ba’a katse ni in ina magana ,kudin ki Nike amfani da?”
“Am sorry” ta fada tana rankwafa kanta alamar girmamawa tamkar yina kallonta,idonta yayi qwalqwal da qwalla
“Kina inane nikejin qarar iska?”
“Mun gama school so,yau zamu koma garinmu nida beelah ,gamu a mota”
“Yanzu haka kuna tare da beelan?”
“Eh”
“Sani a loudspeaker”
Shiru tayi ,tana kallon Nabeela da itama gabadaya concentration dinta yike kanta da alamar kamar bata nutsu ba

Wani almurin tsawa ya doka mata “kinko sani ko kin tsaya kallonta?”
“Ya ilahy ,kodai Adnan yina da iskokaine? Inba haka ba ya akayi yasan ina kallonta
“Am…eh ,gashinan Na Saka yanzu ”
“Tana jina?” Ya fada Wanda muryarsa ya Doki dodon kunnen beelah ,a tsorace ta tsare wayar da Ido ,cike da mamaki,ai ko cikin mafarki bani manta muryar Adnan

“Beelah ki tayani rarrashin qawarki ta yarda in turo gidan su a tsayar mana da rana,wai har yanzu bata qare chilling ba…”

“Adnannnn” takira sunansa cikin kwaratsi

“Na’am beelah qawar mata ta to be”
“Zan maganin ku duka,ni zaku zan bata?” Sai sannan khady ta tsoma baki

“Mene Na zambata beelah,cewa kikayi bakiyinsa nikuma naga ina kata’in sonsa

Wani kafurar ashar ta lailayo ta qunduma mata
“Amma dai ai kinsan we broke up da Bf dina ko?”

Dariya ya bushe dashi “oh sorry karki damu,am energetic,zan Iya auren ku dukkanku biyun,don Na tausaya Maki”

“Driver tsaida mota!!!….dije fitar mun a mota salin alin kafin in budeki in wurga a kwalta inbi takanki

“Haba Nabeela,kamar a film ,ya za’ayi in fita a wannan surquqin jajin?” Ta fada a daidai nan drivern ya faka gefe

“Hajiya muyi gaggawar barin wajen nan,akwai hadari a cikin dajin nan”

“Nabeela idan mata ta wani Abu ya faru da ita sai nayi shari’a badake ba da kaf ahalinki,evrything is recorded”

Warce wayar tayi a hannun khady ta cillashi jejin

Qyalqyalewa da dariya tayi “hmmm beelah sanin hakan yasani gaggawar haddace number abun qaunata,da zaki burgeni da kinsamu eresor kin goge qwalwata”

***
Alhamdulillah ,ummuna gamu a cibiyata” ya fadi yina shafa kanta dake kan cinyarsa ,tana dan barci barci Amma bai sure ta ba

“Husby kai dama balarabene ban sani ba? ”
“Kowa ma cikin matana Basu sani ba,u r special to mah heart ,soon zakiji koni wanene

“Ina Alfahari dakai mijina”

Kiss ya manna mata a saman bayan hannun ta ya fara untucking din belt din da ya daure kansa dashi

Miqewa tayi gamida gyara rolling din kanta Na veil din abayar jikinta,ba kunya ya rungumeta suka fara qoqarin sakkowa daga jirgin

Cak ya tsaya ganin wani green din carpet siriri mai furanni jajaye da aka malala a duk inda zai sauke sawayen sa
Wannan is serious ya haka ta faru ? A wani qarni? Tun a wani zamanin rabon da inga wannan carpet din a qarqashin qafana

Cikin fushi ya janye hannun ummi suka ratse carpet din suna taka danda6aryan qasan kamar kowa

A nutse qatuwar jif din motar ta fara sliding din qofarta ,Saida takai qarshe sannan Adnan ya Sako qafarsa,cikin takalmi sau ciki irin Na masarautun larabawa,jikinsa sanye da riga da Wanda mai kama da na Pakistan da wani irin rawani mai jikin zaiba zaiba

A nutse yike takowa fuskarsa fal fara’a ,bayansa matasan matan larabawa ne dauke da wani irin akushi mai dauke da jajayen furanni,suna warwatsawa a gefe da gefensa ,sun hade jikin su da wani irin yadi mai kama da lafaya ,duk kalar dark blue

Tunda yike tunkarosu ,idon ummi ya diddilo waje👀”ina nasan fuskar nan?”
“Mafarkin da Kika saba” murtsuke idon ta tayi ta watsa akan fuskarsa still dai shine gayinan har fara’arsa da siririn wushiryarsa ,”to waye shi?” Kafin ta lalubo amsar taji quliya yace “Adnan my son” ya saki hannun ta ya bude hannu ya fada jikinsa ,sosai taji sunan a ranta tamkar arashi.

A tsorace tace “Adnan kuma?”

A kammale yajuyo da fuskarsa sashinta yina so yasan Wanda take masa tambayar tuhuma kardai amaryar Dady ne da ta kasa barinsa ya taho taremu,akan lokaci

Caraf idonsu ya sarqe cikin na juna ,a take jikinsa ya dau kakkarwa

“Kece?”
Ya tambayeta a matuqar razana
Kafesa da mayatatun idon ta tayi masu sakarwa da namiji da kasala

“Itace wa? Ka Santa ne?”
Girgiza kai yayi gamida ca6e baki ,cikin son maintaining dignity dinsa

“A’ah Na aza amaryar kace Dady”
“Yes itace my wify ,kuma your step ,and aunty”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button