Hariji Book 3 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 3 Page 79-80

Sponsored Links

79&80
*Alheri writers asso.*

Da sauri quliya ya fito a motar ,kafin ya qwalla masa Kira “Adnan meyasa ka dawo ba tareda ka sanar dani ba? Kuma Ina zaka yanzu?”

Qarasowa yayi ya rungume shi “oyoyo dadyna ”

Related Articles

Ummi dakeda sauran 2k a jakane, ta Ciro ta baiwa taxi driver din, ta maida sauran su riyal din saudiyyar a jaka,A nutse take takawa har takai tsakiyar gidan,yace “ummi Baku gaisa da son ba” cak ta tsaya kafin tace
“Husby ciwo kaima ka sani” ta fada a wani shagwa6e
“Eh haka ne ,hakane ,shiga gani nan”
“Yanzu plz”
“Eh ynzun nan”

**
Quliya a gurguje ya shiga gidan ,ko Zama bai yiba,ya fara kiraye kirayen waya ,kafin ayi haka ya Kira Adama da Nnenna ya yi masu jawabi cewa ,in da gaske ne ,An yimun cinnen efcc ,to zansa a tonewa kowa ramin da na birne kudade Na dakunanku sai kowacce ta San yanda zatayi ta kwashesu cikin sirri ta bar dasu gidan nan a yau ba tare da sanin kowa ba
Ai kuwa sun gigice da murna ,kowa ta bazama neman mafita
Waigawa yayi ya kalli Adnan da ummi
“Ku kuma inada gida a suleja ,ba Wanda yasan da gidan,don haka Na baku kaida ita gidan kyauta,zansa a kwashe kudina da suka samu a katafila akai gidan ,daganan sai kusan yanda zakuyi dashi .

Sosai aka ringa haqe kudaden gidan saida suka Kai daya Na dare ba Wanda ya huta,itadai ummy ko daki bata fitoba don taji haushin abunda quliya yayi mata da ya hada shirginta da adnan ,ko meye manufarsa?

Tunda suka kwashi iya rabonsu sauran kawai sai ya tarashi ta back yard din gidan ya sheqa masu fetur suka kama da wuta ,ya ajiye jaka hudu Na en dubu dubu

Tururi da hayaqin wuta da adnan ya gani shi ya sashi ,zagayawa back yard din da sauri,itama ummy ta bi bayansa a hanzarce

“Dady me yasa zaka qona kudi? Ba mabuqata ne? Wannan almuvazzaranci ne ,kuma ayane a cikin qur’ani sural el-israh Bismillahir rahmanir raheem,Innal mubazzirina kanu min ikhwanish sharad’in,wa kana shaydana li rabbihi kafura ,sadaqallalahul azim… Haba dady haba…”

“Dakata son,to ya zanyi?” Kurum sai ya fara zubar da hawaye,bayan ya rungume sa

“Son matan nan ba matana bane ,duk Na sakesu ,saura ummy kadai ,shiyasa Na hada arzikinta Dana yaron cikinta da naka”

A tsorace adnan ya kalli quliya “ko me yasa ka sake su dady ?” Ya fada cikin 6acin rai

Samun waje yayi ya zauna ,suma jiki a sanyaye suka zo suka zauna

“Zakuji kamar nayi wauta ,amma hakane mafita,din in ban raba masu ba dukiyar zai Zama ajalina da iyalina ,kuma inason in raina yarana ba matsi,kudi da na qona kuma in Na rabawa talakawar unguwa ,asirina ne zai tonu sai in kasa samun damar da zan Kula da iyalina”

“Husby har yanzu baka fada mun dalilin sakin matan ka ba”

“This is a long…” A hankali ya fara basu tarikhin sa tunda ga farko har qarshe

Shiru suka yi Kansu duk a kofe ,adnan zufa yikeyi,ummi kuma mai rauni harda kuka

Gyaran murya yayi “karku koresu,nima bazan koresu ba,amma yanzu tunda abunda suke kwadayin ya qare to zasu gudu da Kansu ,kuma nayi rubutu a diary Na ,cewar duk yaransu ba yarana bane ,Na tura duk wasu hajjajina…so ,adnan koda efcc Na shiga komansu ka Kula mun da ummyna da yarona,kaji my son” ya fada muryarsa Na makyarkyata

Duk wasu makaman yaqin adnan watsar dasu yayi “dole in barwa dady hasken qalbinsa zanje in auri khady”

***
Bayan sati guda

Gida tun Ana Dari Darin zuwar efcc har suka gane tabbas jita jita ne,kowa ya saki jikinsa saidai ,quliya yanzu ya bude bankuna ya tuttura kudinsa ta can ,suma haka ya umurci su ummy suyi tayi har su fidda kudinsu cikin sirri.

Yau quliya ya tashi yina so yaje saudiyya yinason yayi migrating kudinsa daga naira zuwa riyal.

Tun dare yike rarrashin ummy amma sai kuka take yi ita lallai sai yaje da ita,amma adnan yace Kar yaje da ita ya barta ta samu cikinta yayi qwari,shima sosai ya qwallafa ransa akan cikin ummi,sam yanzu ya daina mata kallon soyyaya sai kallon anty,amma ita fa har yanzu Dari Dari take dashi .

Qarshe dole ta haqura ya tafi ,ai kuwa adnan Na tafiya kaisa airport duk matan gidan suka fito harda uwar adama

Har daki sukaje suka janyota suka zaga,suka daka ,suka warwatso mata kayanta
“Shegiya a gayas ,kina dawowa sai min kasheki ,wato ke Ina da Miji,ke vakida tausayi ne,ace duk inda kike ga kataranki ga Na miji? Mu hotuna ne?”

“Anty look,ji jikinta,da ankawota er qauye amma ji yanzu ta goge ,Wai ita bata shan tea saidai ta fasa gwongwanin madara ta kwankwade,qaniyarki zakici” Nnenna ta qare maganar tana tsola ta da qafa ,duk hannunta saida ya daddauje jini yina fita

Da qyar taja jikinta ta ra6e a wajen gate tana hawaye me ta6a zuciya .

Sukuwa a gida sowa suka dauka suka tafa harda su Irfan da rufaida

Maman su adama da duk ita ta kitsa masu wannan dubaran ne,cike da kuri ta soma magana
“Me akayi akayi wannan yarinyar da zatayi ta saku kuna wahalar nema mata magani a wajen en bori da bokaye ,mtseww ni kun bani kunya,yarinyar da ,da kissa zaku kadata waje? Bari Kuga bazata iya dawowa ba….” Bata rufe baki ba ,saiga shi Ana yage gate adnan da kansa ya fito ya budo mata qofan ya taimaka mata ya fito da ita ,ya jawo hannunta suka shigo gidan,ko kallon su baiyi ba,s sukazo suka wuce tana dingishi .

Adama zatayi magana ,maman ta toshe mata baki ,ta jata suka wuce ,Nnenna ma qwafa tayi “ku gama kalan naku ,uwar taki ta koma,ni kuma zan Kira tawa maman ,ni da tsafi zata kora min ke”

A daki uwar ta kalli Adama “Ki barsu ,in sunsan wata ai basu San wata ba”

“Mama ,na fada maki ta samu daurin gindine daga sama ,duk sonta sukeyi ”
“Barta yau zata bar gidan nace maki kije kiyi barcin ki harda yawn”

Adnan likitansa ya Kira yazo yayiwa ummy dressing ya bata magunguna,shi da kansa ya shiga kitchen dinta ya soyo mata plantain da kwai ya fasa gwongwanin madara ya juye mata a cup ya kawo mata da ruwa

Tausayinshi ne ya kamata ,oh ashe bayida matsala,miskilancinsa shiyasa Nike masa kallon jin Kai,amma jiba ya watsar da sarautar gidansu a madina,yazo yinama er ba kowan kowa ba girki .

Fuskan ta dauke da murmushi tace “Adnan ba ni da maids wayayi maka girki?”
“Kaji mun er rainin anty,ni fa qwararrene a kitchen mijinki ya hora ni,so ayi ta jan girki,kusha soyayya ni kuma sai in zamar muku cook”

“Daukan cup tayi ta turashi gefe “Ahaf banshan tea”

“Ai Na sani shiyasa Na fasa maki madara”

Zaro ido tayi cikin mamaki ,sai kuma tayi shiru

**
Qarfe daya Na dare

Maman adama da kanta ta fito da ruwan magani jajir,ta tunkari part din ummi,ta hau warwatsawa a duk gaban dakin, sannan ta koma dakin adama “To matsoraciya ,gayinan nayi ba wanda ya ganni,ai shi duk wanda yike da tsoro bazai ta6a,nasara ba. Don haka ni Na gama maki aikina ,yau zan kimtsa gobe zan wuce minnah ,sai ki jira sakamako kawai”

Cikin farinciki ta rungumeta “shi yasa Nike sonki uwata,saura wancan inyamuran”

***
Ummy sosai yau tayi barci Sam bataji kiran sallah ba,sai wajen 6:15am ta farka ,a hanzarce ta tashi zatayi alwala. Saidai duk water supply din part dinta ya lalace dole saidai ta fito tank din waje

A nutse ta dauki madaidaicin buta ,ta chanja kayan jikinta zuwa doguwar atamfa me aljihu ta yafa qatuwar dankwalin atamfar ,cikin nutsuwa take takawa saboda yanda jikinta ya tsamame .

Tana taka qofar dakin ,taji kanta ya Sara ,kawai kamar gunki ta keta ta nufi gate din gidan ,cikin sa’a ba masu gadi ,ta kuwa zare saqata ta fice…

Ta ci tafiya kamar jaka ,kafin ta fito sarari ta samu taxi,ya kaita Tasha amma hannunta ba ko sisi
Yina kaita Tasha ya waigo ya kalleta”hajiya kudin ki ,ga mu a Tasha ”
Wurwurga Ido ta shigayi ba tare da ta tamka sa ba,tamkar motsatsiya ziryan

“Hajiya munzo” kawai sai ta fito zata tafi
Da sauri ya fito “ke ban kudin ki dayallah er rainin aqalu”

Tana kallon sa ,kurum ta fashe da kuka ta saka gwuiwoyinta a qasa “ka bani sadaka don Allah”

Tausayi ta bashi yasan wannan ba qalau take ba,don haka kurum ya juya ya tafi ya barta

Zuwa tayi tana roqon condostan motocin da taji suna “Kano…Kano” ji tayi ranta ya darsa mata ta tafi can ,don kamar tasan wani gari mai kamada kano

“Ku taimakeni kano ,a inji ko boot don Allah” dariya suka fashe dashi ,wannan mata haukane sabon kamu,jita da gani ba wahala a tare da ita

Zolayarta suka somayi ,tana Sako masu soki burutsu ,sukuma suna dariya,suna janta a jiki su dirka mata fyade dama haka sukeyi in sunga kyakyawar mahaukaciya

Drivern da ya kasance dan Kano ne ,ya zo ya janyo ta ya sata a gaba “Ina zaki a Kano?” Dan Jim,tayi kafin tayi firgigit kamar wanda ta tuno wani abu tayi zillo ta nuna shi da yatsa “Dorayi qarshen waya”

Girgiza Kai yayi “Idi hakkin ka ne ,ka nemarwa wannan mahaukaciyar danginta Allah zai baka Lada..”

***
Har gidan me unguwa ya kaita ,aikuwa me unguwa ya rafka salati

“Ummy Ina quliya,kece haka?” Yina ambatar sunan quliya taji ranta yayi baqiqirin, kurum tana miqewa ta tsinke me unguwa da mari ,ta kama gemunshi ta ja da qarfi,tana masa kasheji

“Kai tsohon banza,sau nawa zan fada maka me wannan sunan ban sanshi ba”

Tausayinta ne ya kama shi ,ko jin radadin izayar jan masa gemu da tayi beyi ba

“Allah sarki ,Idi kake kowa? Wannan ermune ,alkalin alkalai Na qasa take aure,allah ya biya ka ,kaji ,Kai dan inane?

***
Adnan hankalinsa ya tashi da ya laluba 6at ba ummi ,Ina zata da ciwo,ga cikin dady? Me zan fadawa dady in ya dawo ya tmbayeni amanarsa?

A take ya fita neman ta,da cikiya a duk kafafen watsa labarai da ofisoshin en sanda

***
Quliya yina gama abunda yakeyi,cikin tashin hankali ,ya dawo Nigeria,tunda ya Kira layin ummy yina ringing a bedroom dinta saidai ba a dauka,ga adnan Kiran duniya a kashe .

***
Quliya kuwa,***
Yina sauka yaji gidan sun shirya qwarya qwaryan get together ,a tsakar gidan suke rawa da ta6are a hannunsu ,manyan mata suna rawa suna bin waqar *”Wayyo Allah a kora kishiya”* suna kararaf da ta6are wa junansu ,suna yankan naman ragon da aka gasheshi a tsakar gidan yina ci da wuta ririyy yina diga da mai ,kowa in ta gaji da rawa ,Taje ta yanki nama tana korawa da lemu .

“Akori kishiya ? Wani haukan kuma?” Quliya ke saqawa a ransa.

Ai quliya Na shiga suka fara tarwatsewa suna shiga motocinsu suna barin gidan

Tundaga varendar yike kiran “Adnan!! Ummy!!!”

Tsaki Adama tayi “shegen bisa to Na kad’aata”

Fitowa yayi a fujajan ya samu mai gadi “Ina su ummy Na”
“Alhaji kayi haquri ,wallahi ba laifi Na bane..” ai kafin ya qarasa ya daukesa da mari ,ya shaqo wuyarsa

“Ina matata da yarona?”

“Alhaji ka tuhumi su hajiya,wllahi suna da masaniyar 6atarta”

Wancakalar dashi yayi ya koma yina kiransu a bala’ance
“Nnenna…Adama,ina ummy?”

Maganganun rainin wayo suka kama yi masa aikuwa zuciya Na dibarsa ya rufeshi da duka kamar zai hallaka su

Nnenna da taga zata mutu ne ,cikin kakari ,ta nuna Adama

“Wannan da uwarta suka yi mata asirin hauka”

Jikinsa a take ya dauki rawa .

“duk halarcin da nayi maku ,Na kintsa shegun yaranki , tukuicin da zakiyimun shine ,ku koramun matata da ciki? Wato bazaku bar ‘ya’ya N… Muryarsa cijewa yayi kurum sai dafe Kai yayi

Bari in fada maku sakin da ban furta maku ba “Duk kan ku Na sakeku sakin da babu kome har Abadan”

Fasa ihu suka yi ,shikuma ya fice don Zama bai gansa ba

“Masu gadi ku riqemun , adama karku bari ta fita”

***
Mai anguwa dake gidansu ummy yina kwatanta kiran layin quliya ,Hauka tuburan ummy keyi har an daddaureta da kacaa .

Cikin sa’a ya shiga , lokacin yina gaban A.c din police ,ya aje wayoyinsa akan tebur,sai gani yayi sunan baba mai unguwa yina yawo akan screen dinsa,sosai gabansa ya fadi,saidai dolene ya dauka don bazai iya qyale kiran dangin ummi da maji6antarta ba

A hankali ya dauka suka gaisa sama sama
“Ga ummi an kawo ta gida ba lafiya” an sameta,to ganinan zuwa”

A fujajan ya fice ya sa driver dinsa suka dauki hanyar kano a mota.
***
Quliya yasha kukan ganin ummy a wannan yanayin “ummi ki yafemin ni Na ja maki”

A lokacinma barci take yi ,amma duk ta yayyakushe kanta

“Alhaji ai cuta da ga Allah ne wallahi ba komai ” hajjo ta fada ,tana jan carbi ta wani zira hijabi wuyar Na kallon kumatunta tsabar ba a saba sakawa ba .

Ummi da bude idonta kenan ta watsa shi akan quliya

“Wayyyo Allah shine mugun, kashe mutane yikeyi ,baku ganin jikina ,haka yayi gunduwa gunduwa dani da wuqa,ko ba haka bane munafukin Allah ,kake zare muna Ido kamar zagezagi”

Tsam ya miqe ya soma aniyar kwanceta
Uwale tsaf ta miqe tayi bakin qofa da gudu

“Alhaji karka soma kwanceta wallahi qaqqarface ,zatayi maka illah ,da qyar mazan anguwa suka taru aka qulleta da kacan nan

“Ina bazan iya barinki ummi a cikin kaca ba,ina sonki da lafiyar ki ,kuma Ina sonki ,a halin lafiyar ki ,zan cigaba da sonki har sanda zan yi numfashi Na Na qarshe ” kurum sai ya fashe da kuka

Tausayi ya basu sosai ,itadai ummah haka take roqon sa harda saka gwuiwarta a qasa Kar ya kwanceta

Ganin surukuwarsa a qasa ya sashi tashi ya fita ,ya cigaba da neman layin adnan ,wannan karon yina ringing amma yaqi dauka don ya dawo gidan kuma yasan quliya yasan komai ,saidai baisan anga ummi ba,a qarshe text ya tura masa

“Ummi gata a gidansu na kano,naso inyi maka magana masu mahimmanci amma kaqi dauakar kirana ,a tunaninka bazan dauki qaddara ba ko? To yanzu zan kwano Abuja ,kasa likitarmu ya hada mana connection da psychiatrist a qasar da ta dace ,kafin in taho”

Yina ganin text dinsa yaji sanyi a ransa amma yayi ta kakarin Kira kuma ba network ,gudu Na hauka sukayi Allah ne ya kaisu Abuja lafiya .

Saidai suna dab da shiga garin Abuja ,motarsu ta ci karo da wata babbar mota da ta biyo one way ,aikuwa ya fada jaji ,ya Doki wani bishiya motar ta jujjuya ta kife ta tawarwatse

Cikin jini quliya yaji ringing din wayarsa “Son ,Ummina,yarona ,karka bari su tozarta Na baka amanarsu,ka Kula da kanka yarona,sai anjima…”

Tundaga nan hankalin quliya ya gushe ya fara salati

“Dady Mene ne ya faru? Dad…dadyyyyy” kurum sai ya saki wayar ya yanka ihu.

***
Ummi dake daddaure ,kamar wanda akayiwa wani irin allura akaf jijiyoyin jikinta a gigice ta qwalla qara “Mijina!”

Da gudu suka taso ,Tampa haukan ya Dada motsawa !” Cewar umma yau daya duk ta zuge ta jeme,tayi zuru zuru ,tsabagen damuwa

“Ummana !,waya daureni ? Kuma ya akayi nazo nan? Namayi sallar safe kuwa?”

“Ummina da gaske kin warke ne ,bazaki dakeni ba in Na kwanceki ba?”

“Subhannallah , Allah ya kiyasheni ta6ewa ,meyasa zan dakeki ummah Na!?”

***

Motar su quliya a take ta kama da wuta ,da qyar sojojin kan hanya suka zazzaro su.

Allah sarki ne!

Kullu Nafsin za’iqatul maut!

Abunda musilman ciki suke maimaitawa kenan,don sun Dade basuga fatal accident irin wannan ba

“Kamar wannan yina da sauran rai tabbas yina numfashi ,amma wannan dai ya mutu”

Cewar first aids din , daganan aka kwashesu zuwa cikin garin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button