Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 15

Sponsored Links

 

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number 07012181461_

Related Articles

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_

Wuce ta Kaka tayi tai dakinta tace “aikuma sai mugani danko ubanki bai isa yahanani kaiki makarantan nan yauba” tai kwafa ta shige dakinta, tashi tayi ahankali tanaji kaman tai kuka ko kadan bataso taje makarantar nan ta tsani zuwa makarantan, mutanen ajinsu sukai dari da hamsin, batason zuwa, dakinta tawuce ta shiga ta shiga bayi dan Kaka tace takaimata ruwan zafi, sirka ruwan tayi sanan tayo wankan bayan tabata kusan 10min a bayin dukdan kartaje school, saida Kaka tazo ta buga kofan tace “jama’a wai bazata fito daga bayin bane, ke kinsan karfe nawa kuwan? Zainaba fa harta tafi abinta, Ihsan ma ta tafi tata makarantan, ke kina nan bayi kina kwainane, wlh koki fito kona fado cikin bayin nan yanzu kuw…” bude kofan tayi tafito Kaka ta matsa gefe tana kallonta, turo baki tayi tawani kumbura taje gaban sip tabude sip din kaman zata balle kofan tsabagen masifa Kaka dake tsaye a inda take tana kallonta tace “wlh kika ballamin sip sai ubanki yabiyani atoh” dogon bakin hijabinta taciro da wani doguwan rigan atampa ja ta ijiye tadau mai ta shafa sanan ta dago ta kalli Kakan dake binta da kallo, akule tace “ni kifita zansa kaya” tsaki Kaka taja tafice tana cewa “kidaiyi sauri ga kokon ki nan afalo, shima kokon dan Allah zanbaki” shiryawa tayi cikin doguwan rigan dayay looking so simple yet elegant a jikinta ta zauna kan gadon tana bude eyeliner dinta tadau madubi taja asaman idonta as usual, bakaramin kyau tayiba ta maida ta rufe ta ijiye, lipgloss tasa abaki tafesa dan simple bodyspray dinta da Abba ke siyoma dukansu duk karshen wata body fantasy na vanilla sanan ta maida kayan kwalliyan tadau channel sandals dinta baki ta saka ta daure igiyan takalmin, bakaramin kyau yama yar farar kafarta ba kaman wata kafar jaririya sanan tadawo tadau jakarta da littatafan ta ke ciki ta rataya jakan akafada kanta ba dan kwali gashin ta daya tsufa sosai sai lilo suke tadau hijabinta tarike a hannu tafita daga dakin, falon ta shigo inda Kaka ke zauna a kasa tanacin dumaman tuwonta acikin tukunyan kasa tai hanyar fita daga dakin Kaka tace “dawo nan kici abincin ki mutafi” makemata kafada tayi da sauri Kaka tacire hanunta daga tuwon ta tashi hakan yasa tawani irin kwasa da gudu tafita daga dakin, cin karo tayi da Ya Faruk yana sanye da white jallabiya tai baya luuu zata fadi da sauri ya tarota tafada jikinshi arude daidai lokacin Kaka tafito da sauri ta kalli Kakan ta tashi daga jikinshi takoma bayanshi ta labe jikinta narawa ahankali tace “Ya Faruk please karka bari Kaka takaini school wai lecturer dinmu zata fadamawa ya dakeni” daga bakin kofa Kaka ke kallonsu tace “ina jinki muna fika, haka nace eh sainasa malamin ku ya dakanmin ke bar ganin Farukun soja ubanme zai iyamin” juyawa yayi ya kalleta fuskarshi adan daure yace “put on your hijab” da sauri tasaka hijabin dayay mata kyau sosai yafito da hasken fatarta, hulan hijabin har goshinta yace “let’s go” ficewa sukayi Kaka tai kwafa tace “wlh zaku gamu danine dukanku munafukan banza” takoma daki, waje sukayi bahalin tacemai zataje ta gaida Mama da Baba yabi yadaure fuska motarshi yabude ya shiga itama ta shiga dayan side din lokacin kusan karfe tara yaja motar har BUK, sosai gabanta keta faduwa tana kallon ko’ina har gaban department dinta ya kaita na Islamic studies sanan yay parking dan dagokai tayi ta kalleshi suka hada ido, ahankali tace “thank you” 3k yaciro daga wallet dinshi yabata yana kallonta yace “make sure you eat” gyadamai kai tayi ta karbi kudin murmushi tayi tace “thank you” ta bude marfin motan tafita, binta yayi da kallo yanda take tafiya a mugun natse kaman tana tausayin kasa kanta akasa as usual tana kakkare fuskarta da hijabi, hijabin nan har kasa dan ko kayan datasa aciki ba’a hangowa, saida ta kule mai sanan yadan fuzar da iska wayarshi dake ringing ya kalla ganin Ammi ne yasa yadau wayan yakai kunenshi. Daga tachan bangaren cike da masifa matar tace “where are you Son, kacemin you’re having headache bazakaje aiki yauba ina kaje this early morning eh Umar Faruk?” shiru yadanyi batare dayace komiba dan ya tsani karya, kuma baya karya, dan ya tsani anamai ihu aka, ahankali yace “sorry Ammi na” cikin fada tace “Faruk kullum kullum saika nunamin ban isa dakai bako son? Am sure kaje gidan wan Baban kane, am sure kaje kai wanan mai aljanun makaranta ne sabida kai hired driver dinta ne ko, Faruk wats wrong with you? Narabaka dasu kakiji, tun baban ka nada rai wanan mayyar wicked Kakan taka tasa aka sakeni dan haka nafa and am going to say it again, jinina bazai kara hada wani abu da wanan family ba, tun wuri kacire yarinyar nan aranka inba hakaba wlh fushin dazanyi dakai wanan karan saiyafi na wanda nai dakai ranan dakaje Lagos ka daukota stubborn boy, and come back home rightaway Dr na jiranka” tai tsaki ta katse wayan, ahankali ya zare wayan daga kunenshi kirjinshi namai wani irin zafi, he don’t know where all this hate is coming from but one thing is for sure yasan idan har abinda Ammi ke fada gaskiya ne, Kaka tasa aka saketa dan Kaka batai laifi ba dan ko kadan Ammi batada kirki yana ganin yanda takema yan aiki wani zubin ma shiyake hanata, yasan mahaifiyarshi sosaisosai. Yakai kusan 5min a wurin yana tunane tunane sanan yaja mota yabar wajen yadau hanyar gidansu.

Faruk yaron kanin mahaifin su Hamida ne, shika dai suka Haifa shikadai ne kuma jikan Kaka namiji, inda Baban su Hamida yahaifi yara bakwai dukansu mata, baban Faruk ya rasu a plane crash ne, his Mum is from a rich wealthy family, bayan rasuwan baban Faruk Faruk yadawo hanun Abba da Kaka, rashin mutunci Ammi tazo tai dasu Kaka akan abata danta, in other to maintain peace yasa Abba yacema Faruk yakoma wurinta but dudda haka kullum yana gidansu, weekend yana yawan zuwa gidan kajin Abba yana tayashi aiki dan sana’ar baban su Hamida kenan saida kaji da Kwai and he’s making it Alhamdulillah Allah ya sanya mai albarka a sana’ar.

**
Dan lekowa tayi daga inda ta labe ganin yatafi babu yasa tafito ahankali tana tafiya da sauri da sauri wani kantin taje dayake safiya ne ba mutane sosai, take away abinci merai da lafiya tayi guda biyu tabiya kudi ta karba tafito tafita daga school din gabanta na faduwa sosai, kasa samin Keke tayi hakan yasa tafara tafiya akasa tana kakkare fuskarta, saida tai nisa sosai tamugun gaji da tafiya takai junction din wani layi keke napep ta tare ta shiga tace “old railway” “hajiya dari uku” ahankali kanta akasa tace “muje” tada keke napep yayi suka shiga hanya, sukayi tafiyan kusan 15 minute yakaisu wurin, ahankali ta sauko taciro dari uku tabashi batare data kalli fuskarshi shi tajuya ta shiga wajen tana kallon kan kujeran da Baba yake zama yanajin yar radio shi ganin bashi yasa ta karasa wajen, takeaways din ta ijiyemai ta ta wuce ciki hango wasu samari tayi kusan biyar ko shida zaune a inda ta saba zama suna kokarin kunna wiwi da sauri ta juya kafinma su lura da ita, cin karo tai dawani abayanta idanunshi jajir da alamun yasha yai tatil yace “ke waya kiraki nan?” kwalama sauran dabama su lura da ita kira yayi yace “babaa jimana, tawaye ne tazo? Ba munce babu wacce zai kira tashi nanba yau” da sauri amugun rude tai gefenshi zata wuce yatareta yace “ki tsaya mana baby nakira miki su, hala wajen Sani kikazo dan nasan mayen da shegen iya zabo zafafan mata” arude tana dan waigen bayanta jin sahun mutane suna zuwa ta kwalama tsohon dake gadin wajen kira. “Baba, Baba” daidai lokacin sauran sun iso wajen fashewa sukai da dariya dayan yace “Baba wai me gadi kike kira? Ke yarshi ce?” daya daga cikin su yace “kaima jibeka dawata magana ina Baba mai gadi yakeda kyan haifan irin wanan lu’u lu’un?” daya daga cikinsu yace “kodai me zuwa bashi kayane?” kulle bakinsu sukayi suna zaro ido irin na isgilanci atare sukace “tsoho yaji chakwai” fashewa tai da kuka ta duka a tsakiyan su tana kwalama Baba kira. “Babaa” daya daga cikinsu yace “ankai Baba kauyen su Baba ba lafiya muma fanshi Baba yau, kingan mu mushida kici har ki koshi ko yan mata” yay maganan zai kama mata hannu boye hanunta tayi ajikinta tafashe da kuka, hijabinta ya fizgo ya mikar da ita tsaye fasa wani irin ihu tayi a mugun tsorace ta bugamai kafarta hakan yasa yay baya yasaketa yana tsaki dan yaji zafi da sauri sauran sukayo kanta tawani irin kwasa da gudu tana kuka wanda ta hambaran yawani irin tadiyota tafadi akasa hancinta ya shiga cikin dan kasan yashin dake wurin.
_🌹IN BANI 🌹_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button