Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 17

Sponsored Links

17….

Goga fuskarshi yayi anata yana kuka sosai yace “wake up pls” yay maganan yana turo baki cikin kuka yana kallonta ganin shiru yasa ahankali ya kwantar da ita a kasan wajen, kwanciya yayi shima gefenta yana kallonta shi kanshi baisan meke damubshi ba, fashewa yasakeyi da kuka yarike hanunta dan wani iri heart dinshi kemai, he’s feeling something all over his body, stomach dinshi kaman an watsa ice a ciki sabida wani irin sanyin dayake mai dayake kaiwa kowani nerve najikinshi, ahankali ya daura kanshi a wuyanta yana kuka sosai bana wasaba ahaka shima baccin wahala da ciwo sukai gaba dashi jikinshi yadau wani irin zafi sabida ciwukan dayaji a kafa gakuma zazzabi.

Ahankali Mami ke bude ido, dishi dishi take gani sosai maganar bigmum taji dakuma matse hanunta da akayi. “Maryam kin tashi” dan juyo dakai tayi da kyar ta kalli gefenta Big Mum tagani zaune akan kujera idanunta sunyi ja sosai ta rike hanunta gam, baki Mami tabude zatai magana takasa sabida yanda bakinta yamata wani irin nauyi sai kallon ko ina datake yi dakuma kanta daya mata wani irin nauyi da zafi, shiru tayi tana lumshe ido tana kokarin tunano abinda yafaru. “Maryam” Bigmum tasake kiranta hakan yasa tabude idanunta da kyau tanadan lumlumshe ido sabida yanda kanta ke mata ciwo zatai magana aka bude dakin aka shigo yayyinta Mazane su uku da Abie dakuma Aabid da taga idanunshi sunyi jajir, da sauri Aabid yama rigasu zuwa wajen Mamin, cupping fuskarta yayi kaman zaiyi kuka yace “Mami na ina..ina Aadil?” sunan Aadil daya kira yasa ta lumshe ido da sauri, ahankali komi yafara dawo mata har lokacin daya bude kofar motan yafadi akasan tsakiyan titi, dawani irin sauri tabude ido tai wani irin ihu tana mika hannu kaman zata kamoshi. “Aadilll” arude ta shiga kalle kallen dakin ganin dakin asibiti take babu Aadil a wurin saima ruwa da ake samata fashewa da wani irin kuka tayi numfashin ta na sama sama arude tarike Aabid tace “where’s Aadil Aabid? Tell me what happen to Aadil?” da sauri tasaki Aabid tana kallon sauran yan dakin tana nunasa da yatsa tana magana kaman wacce ta zare. “kufadamin gaskiya ina yarona yake? Ina d’ana? Abie where is Aadil eh” da sauri Abie yakaraso wajen Big Mum ma tariketa ahankali yace “calm down wife, calm down, muma bamusan meya sami Aadil ba, wani bawan Allah dai yakira ta wayarki Big Mum ma aka kira dan anga itace last contact din dakikai waya da ita a phone dinki ance you had an accident u were unconcious” “noooo” ta fizge kanta daga jikin big mum tace “karya kuke yimin kufadamin gaskiya mota ya takeshi ko? Aadil dina yamutu?” kaman wacce tasami tabin brain ta kalli yatsunta kaman yanda Aadil keyi tafara kirgawa cikin sambatu tace “Aadil was counting his fingers playing while I was driving, all of a sudden ya cire sitbelt yabude kofan mota yafice, yabuge yafadi sosai a kasa, matching brake nayi arude na kalleshi daganan bansan meya faruba, tell me!” tai wani irin ihu tana kama rigan Abie dake kanta tace “Abie meya sami d’ana wlh inkamin karya zanyi fushi da dukanku kafadamin” alamu yama Aabid dake zaune yana kallon Mami yamatsa, zama yayi ya bata one side hug yadan jijjigata yace “in sha Allah nothing will happen to Aadil, zamu nemeshi zamu bada cigiyarshi, and we will get d police involve inma d accident was a well careful plan accident dan ayi kidnapping nashi we will know, calm down okay karwani ciwon yakama ki, I swear, I swear to you zan nemo mana danmu” cikin wani irin kuka mara kara tace “promise me Abie u will find my Aadil for me” shima idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi duksun fito yace “I promise you Mum Aadil” tashi yayi da sauri yay hanyar kofa su Suleman zasu bishi yay murmushi irin na tashin hankali yace “karku damu am coming, in baku ganni dawuri ba get d police involve” da sauri Suleman yace “ina zaka Abdullahi?” Juyawa kawai yayi yana kokarin hana kanshi hawayen dazasu zobomai yace “ina zuwa kawai Yaya” ficewa yayi da sauri Mami ta fashe da kuka tai hugging Aabid tace “Son where is your brother? Idan ban ganshi ba mutuwa zanyi wlh, you and Aadil are my entire life, please So..” tafashe da kuka sosai, ahankali yadago kanta daga jikinshi yasa hannu ya share mata hawayen, da muryanshi data dishe sosai yace “stop crying Mami, I will find my Bro okay” gyadamai kai tayi tana kuka, Big Mum ta kwantar da ita tace “kwanta ki huta ruwan ya shiga jikin ki da kyau” tashi Aabid yayi yafita shida Yayin mamanshi.

Related Articles

 

Sosai Abie ke zuba wani irin uban gudu akan hanya, bini bini yake share yan hawayen dake zubomai, sosai yay tafiya kaman zaibar garin kano sanan ya yanki cikin wata yar karamin kauye yadinga kutsawa cikin kauyen nan da jeep dinshi haryakai wani babban farm house, a kofar gidan yay parking yafito rike dawata yar jaka yarufe motar, yaciro wasu key yabude gate din ya shiga, gidan ciyayi sunma soma girma kota ina, ya karasa har gaban wani flat dake compound din ya shiga yar barandan dazai sadashi da daki rike da makullin da wayarshi, ciro key yayi yabude kofan ya shiga ciki, babban falone dayay dan kura da alamu an dade ba’a shiga gidan ba, wani dan corridor yayi hanunshi har rawa yake yabude wani katoton makulli dake makale jikin kofan ya bude sanan ya zare ya ijiye key yabude kofan amugun hankali ya shiga dakin, dakine da komi nacikinshi ja, kaman dajan kyalle aka zagaye bangon dakin, kasanma wani irin jan carpet ne ja sosai a shimfide kota ina, ahankali ya shiga dakin da yay dan kura ya maida kofar ya rufe yasaka sakatan sama data kasa sanan ya shigo ciki ya ijiye jakan daya dauko akasa duk da sauri sauri yake komi ya zage jakan ya bude wasu jajayen kayane suka bayyana da sauri ya kwabe manyan kayan jikinshi ya ijiye kasa sanan yadau jajayen kayan yasaka babban bubun rigane dake jamai har kasa da sauri ya tsugunna ya kwashi kayan daya cire ya maida cikin jakan yaciro ashana daga jakan ya daga jakan ya jinginata da bango yatashi yaje gaban dakin inda wani manyan gumaka suke da aka musu zane a fuska kaman da chalk, kafafunsu daure dawasu irin bangles sai kuma jajayen candles guda shidda suma, kneeling yayi ahankali agaban gumakan sanan ya kyasta ashana ya kunna duka candles din sanan ya hura tsinken ashanar ta mutu ya yar a gefe, shiru yayi yana tunani yana kallon gumakan kafin ahankali ya dukar da kanshi yahade hannayenshi biyu agaban gumakan yace “Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, macukubelebele kaino kaino, macukubelebele kaino kanooo” shiru yadanyi zuciyarshi namai wani irin azababben zafi, ahankali cikin wani irin dishashiyar murya yace “Ozo ka bayyana agareni inada bukatar ka, I summon you Ozooo” bai karasa kiran sunan ba wasu mutane guda uku suka bayyana a dakin a tsaye da ba’a ganin fuskokin su suna sanye da jajayen dogayen riguna daya rufe har kafarsu sai babban su dake sanye cikin black doguwan riga shima kanshi akasa yana rike dawani karfe dakeda Kwai kaman kwan jimina asaman karfen, cikin wani irin magana mai echo sukace. “mesa kake neman Ozo” kaman jira yake ya rarrafa da gudu yaje gaban me bakaken kayan yay kneeling yana hada hannayenshi yace “great one Ozo, Ozo nakiyaye kowace irin dokan ka, wanan zoben” yanuna babban zoben yatsarshi arude yace “kaman yanda kace bantaba cireta daga yatsata ba, Ozo nasan ni mai laifine tun kafin na shigo kungiya aka fadamin sharuddan kungiya wacce shine d’a namiji dazan fara haihuwa a duniya nakune shine sacrifice dazan….” yay shiru hawaye na zuba daga idanunshi sosai da kyar cikin wani irin asalin tashin hankali yace “great Ozo bantaba sanin haka abin yakeda mugun wuya and tough ba saida na haifo yan biyuna mazaje kyawawa” yadanyi shiru yana goge hawaye sanan yace “great one Ozo da gudu nabarosu a asibiti nadawo gida na shiga boyayyen daki namaka kira ka amsani, ka bayyanan min, naroki afuwa da alfarma akan karku daukemini Hassan wanda yake na farkon, karku kashemin shi, great one Ozo nasan kamin adalcin da baka taba yima wani a kungiyan nan ba, kabani zabi biyu masu sharudda sabida yanda ka tausayamin kakuma Soni, zabin shine ko kukashe shi kusha jini, koku shanye min shi, da ranshi amma shida yaro basuda bambamci, da gudu na yarda tsabagen yanda nakeson Yan biyuna, gakuma wani irin special son Hassan din da Allah ya dauramin danshi nafara dauka a hannuna a tsumma kafin na dauki dan uwanshi Hussain, na yarda da Hassan mutu gwara kunsaka ranshi a kwalban kunyi duk yanda kukaga dama dashi daku kashemin shi na yarda dari bisa dari ku maidashi yaron kusa ranshi a kwalban bakomi, sai kuka fara koromin sharuddan zabin danayi na karya mutu, kace duk wani ciki da Maryama zatayi tun cikin na wata biyar zaku shanye cikin, haka na yarda cikin da Maryam ke dauka dai, dai, dai, har sau uku Maryama nayi duk kuna shanye wa tana bari duk sabida karku kashemin abin kaunata Hassan ban damuba har mahaifanta ya sami matsala tsabagen wankin ciki da ake mata tadena samin cikin, bayan haka kuka bani sharadin cewa ko bayan shanyayyen dan nawa yay girma bazai sake yay aureba shima na yarda to tayaya ma mara lafiya yaro mai kwakwalwan yara zaiga mace yace yanaso duk na yarda, kun hanani cin naman rago duk banaci, kun hanani cin dabino shan zuma duka banyiba dukdan karku kashemini Hassan, mesa yanzu zaku chanza komi ki daukemin farin cikina eh bayan na kiyaye kowace doka da sharuddan ku eh Ozo the great one?”.
_🌹IN BANI🌹_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button